Showing 99001 words to 102000 words out of 139192 words

Chapter 34 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

866

komai"

Wani waya yaciro soft toch me kyau yamika mata tareda cewa "ga wannan zamuyi magana dake"

Tace "aa tayimin girma"

Dariya yayi yace "dolene ki karɓa dan ta cikinshi zaki samu abinda kikeso, kuma ina neman wata alfarma a wurinki"

Amrah tace "tom menene?"

Yace "badan na rainaki ba inaso kije gidanmu a matsayin ƴar aiki dan maganar mutane zasuce matata bata daɗe da mutuwa ba na ɗauko wata"

Amrah tace "ba koma zanyi aikin"

Yace "nagode"

Wayar ta karɓa tace "nima na gode"

Sallama tayi acikin gida ta buga tsalle ta diro kasa, Kulu cikin murna tace "bi a hankali dai meya yafaru?"

Amrah cikin murna rungumeta, Kulu tace "sakeni dan Allah"

Saketa tayi tana dariya da fararen hakoranta, idan tana dariya kamar ka saceta ka gudu kyau takeyi sosai, tace "Baba Kulu Allah yabani mafita" nan ta zayyana mata duk abinda yafaru, takara dacewa "bazan taɓa aurenshi ba, koda na haihu saide naci gaba dayi musu aiki suna biyana, dahakane zan tara kuɗi harna nemo ƴan uwana"

Kulu tace "meyasa bazaki aureshi ba?"

Amrah tace "haka kawai be kwantamin a rai ba banji sonshi ba gaskiya"

Kulu tace "amma dani za'a tafi ko? Dan nima inada ƴan uwa masu kuɗi wannan gidanma yayanane ya bani kyauta saide basa sona wai nafiye aure aure"

Amrah dariya tayi tace "ba komai dake zamu tafi kuma nasan dama Mama bason ganina takeba zata barmu mutafi ko?"

Kulu tace "eh"

Washe gari Amrah ce tafito da brush a hannunta, Mama ma tafito kenan zatayi brush sukayi karo, da sauri Amrah tace "ina Kwana Mama"

Mama saida ta kalleta tace "lafiya lau Hindu"

Ɗago kai Amrah tayi da sauri ta kalli Mama jin sunan data kirata dashi, Mama ɗan dariyan takaici tayi tace "brush zakiyine Hindu? Ayya kiyi hakuri kishiyata na dameki da tambaya ko?"

Amrah bakinta yana rawa tace "Mama...me..me kike faɗane?"

Mama tace "haba Hindu nifa na haifike Amrah bazan haifi ƴa ta fini wayo ba, tunda Hindu bata fitomin ba sai yanzu? Sannan wuka bai taɓa zama a waje ba, kuma saida na duba wurin wanke wanke kafin na tambiyi Kulu, bayan tafito daga ɗakinku sai kikayi gudu kika ajiye danki juyamin hankali, kije Amrah bazanyi miki komai ba, badai kinji gaskiyan ba?"

Amrah tace "Mama kiyi hakuri yazama dolene nayi miki haka, kuma yanzu nasan gaskiya amma ki gafarceni har yanzu ina zarginki"

Tana faɗan haka tabar wurin, Mama ma komawa ɗaki tayi.

         "Abdul ne yake driving a hankali yana sauraron wakar rema na "I too like Human" bin wakar yake a hanakali yana enjoying, Wayarshi ce tafara vibrating da sauri yacire a aljihunshi yayi connecting da radio ɗin cikin motar "Dude"

"Nayi fishi dakai tunda katafi baka kirani ba sai yau"

Kabir yace "haba aboki kasan dai bazan manta da kaiba kawai sungulla ne sukayimin yawa, ya kake?"

Abdul yace "lau ya garin naku?"

Kabir yace "garinmu lafiya, ya matarka?"

Abdul yace "lafiyanta lau"

"Ba cewa lafiyanta lau ɗinba shin kana kula da ita kamar yacce kayimin alkawari?"

Abdul yace "daidai gwargwado amma kasan bazan sota bako?"

Wani zafine yake shiga zuciyar Kabir idan Abdul yace bazai sota ba, murya akasa yace "please ka duba yarinyannan she is innocent dan Allah kada kabata wahala ka manta da da kayi sabuwar rayuwa kaddarace haka"

Abdul yace "munafa zama da ita har muyi fira"

Kabir yace "yawwa da haka zaku saba har watarana ka kirani kace Dude nakusa zama Daddy saide kasan me?"

Abdul yace "Aa saika faɗa"

Kabir yace "haihuwan fari idan namiji ne to sunanshi yafara da kalmar K"

Abdul dariya yayi yace "ban ganeba waye kenan?"

Kabir yace "Ah K ai shine Kabir wato takwarana, idan macece kuma nasan zai fara da A"

Abdul yakara cewa "waye kenan?"

Kabir yace "Amrah kanwarka"

Dariya yayi yace "kanwarmu dai dan naga kun wani saba a lokaci ɗaya"

Kabir yace "tabbas mun saba yarinyar akwai shiga rai barima nakirata"

Abdul yace "can ta matse muku"

Katse wayar yayi yaci gaba da sauraren wakarshi, yana isa gida yayi parking motarshi yagaida Baba me gadi sannan yashige ciki, tun daga babban falo yafara jiyo kamshi, ɗan lumshe ido yayi dan yanayin yayi mishi daɗi, ga wutan ɗakin akashe saina show glass ne a kunne blue "so romantic" yafaɗa a ranshi, ɗakinshi yaje yayi wanka yasa kananan kaya, gashin kanshi yashafawa mai wanda yasashi sheki, tajewa yayi yana kallon kanshi, ɗan dariya yayi daya tuna ranar da dady yace idan be aske kanshi ba saiya kwace motarshi, aikuwa sunyi sati suna wasan ɓuya da Dady saida Dady ya gaji dan kanshi kafin yakara janshi jiki "i miss you Dady" yafaɗa kafin yaci gaba da taje kanshi, saida yagama kafin yafita zuwa ɗakin Fadila dan yanaso yaci abinci kuma be gani a dining ba, Sallama yayi, Fadila data haɗa uban tagumi hawaye sai sauka suke wasu na koran wasu, manyan idonta yayi jaa sosai, sannan fuskarta ma yayi jaa, tunanin gida kawai take acikin kwanakinnan tana kewan iyayenta wani lokacin harda Amrah tana jin kewarta, ɗan uwa ba abun wasa ba, tin ɗazu take kuka a ɗaki tarasa yanda zatayi da rayuwarta, dafata yayi da sauri ta ɗago kai ta kalleshi, share hawayen tayi sannan taɗanyi mishi murmushin karfin hali, zama yayi a gefenta ya riko hannayenta duka biyu yariko yana murzawa, sunnar dakai tayi kasa batace komai ba, ido yazuba mata shima bece komai ba, sunkai mintu goma ahaka sannan cikin murya me sanyi da alamar rarrashi yace "Kawata?"

Ɗago kanta tayi idanunta suka cika da hawaye, faɗawa tayi jikinshi tafara rabza kukan datake kokarin ɓoyewa, bayanta yake ɗan bugawa, ɗayan hannunshi ya cusa a gashin kanta me tsantsi yana shafawa tareda cusa yatsunshi tsakiyan kanta, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sai hawaye dasuke sauka a hankali daga idonta zuwa bayanshi, a hankali yakuma cewa "kawata"

Bazata iya magana ba tace "ummm"

"Kidaina kuka kinji?"

Giɗa mishi kanta tayi, be kuma cewa komai ba, saida yaji tafara sauke numfashi a hankali alamar tayi bacci kafin ya cireta daga jikinshi ya kwantar da ita akan gado, blanket yarufeta dashi, kallon fuskarta daya jike da hawaye yayi sannan ya ɗauko tissue ya goge mata fuskar, yajuya ze fita, hannunshi yaji tariko gam acikin bacci, zama yayi a hankali yana kallonta, saida tayi nisa kafin ya zame hannunshi a hankali yajuya yafice, kitchen yaje yafara dafa abinci hannunshi sai konewa yake har yayi jaa amma be damuba yaci gaba da aikin saida yagama haɗa abinci kafin yakai kan dining ya zauna yaci nashi yabarwa Fadila nata, tagumi yabuga shima yana tunanin to meyasa kuka da damuwa haka? Anya ba nine matsalar nata ba? Watakila tanada wanda takeso kamar yacce nima nakeda wacce nakeso shiyasa idan ta tuna take kuka haka, su Dady sam basuyi bincikeba suka haɗa wannan auren, ba komai nanda wasu lokuta zan sawwaka miki kema ki auri wanda kikeso dan bazan saki cikin damuwa ba, na yadda maganar Dude dayake cewa ke innocent ce, bazan shiga hakkinki ba zaki samu mafita"

Magana yake shida zuciyarshi.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 65*

         ~Fadila saida tayi bacci sosai kafin ta farka tana murza ido, dube dube tayi taga ba kowa tasan dai Abdul yananan kafin tayi bacci amma yanzu babu shi, kodai mafarki ne?tashi tayi jin cikinta yana kukan yunwa, a dining ta hango Abdul ya buga tagumi kome yake tunawa oho, da murmushi akan fuskarta takarasa wurinshi "hi frnd"

Ɗago kanshi yayi ya sakar mata murmushi "kin tashi?"

Fadila tace "Umm uhumm shine katafi kabarni"

Kallonta yayi shagwaɓar tayi mata kyau sosai, ɗan iska ta hura mishi tace "Hi magana fa nake"

Dariya yayi yace "zauna kici abinci"

Kallonshi tayi taɗan turo baki tareda cewa "wa yayi girkin?"

Yace "laifine dan Aboki yayiwa Kawarshi hidima?"

Tace "Aa ba laifi bane, amma bari nayi brush tukun"

Brush taje tayi kafin tadawo taja kujeran dayake kallon nashi, signal tayi mishi yanata kallonta tace "Yadai frnd? Naga ka zuban ido ko nakusa mutuwa ne?"

Da sauri ya taso yasa hannu a bakinta yace "shii kidaina ambato mutuwa kinji?".

Dariya tayi tace "to frnd nadaina" komawa yayi ya zauna, yana kallonta tafara cin abincin harta gama "wow gaskiya yayi daɗi ashe ka iya girki?"

"Dama me kika ɗaukeni? Nayi zaman Hostel fa"

Fadila tace "awani gari kayi school?"

Kallonta yayi yace "A Yola"

"Laa garinmu acan kayi school?"

"Eh acan mukayi karatu nidasu abokaina Kabir da Ak da sauransu"

Fadila tace "ah yayi kyau gaskiya"

Ɗan fira sukayi kafin kowa ya watse zuwa ɗakinshi.

           "Kamal daya kwanta rub da ciki tunanin duniya duk sun taru sunyi mishi yawa, tsaki yaja ganin kwanciyar bayayi mishi daɗi yasa ya mike yaɗau filo ya ajiye akan cinyarshi hakan ma baiyi mishi daɗi ba, jingina kanshi yayi da jikin gado ya buga tagumi, Sallama Umma tayi saida ya amsa a hankali kafin tashigo, ganin yanda ya zabga tagumi yasa taɗanyi tsakin takaici "sau nawa zan faɗa maka ka daina sa mutanennan a ranka ka ciresu mana Kamal kafita a rayuwarsu kamar yacce suka fita a naka rayuwar"

Ɗago jajayen idonshi yayi yana kallon Umma, zama Umma tayi a gefen gadon, da rarrafe ya iso wurinta ya ɗaura kanshi akan cinyarshi cikin hawaye yace "Umma nakasa wallahi nakasa, Umma ki taimaka min, inason Fadila amma ta haramta a gareni Umma yanzu bansan ya akayi nafara son cikin jikin Amrah ba inason na rungumeta da abinda yake cikinta, Umma narasa meyake damuna ki taimakawa ɗanki Umma"

"Haba Kamal akansu kake kara ɓata hawayenka? tom shikenan kada kadamu zanyi maganin abin kaji?"

Kamal yace "Umma kinyi alkawari?"

Umma tace "Eh Kamal ka daina kuka kaji ɗana?"

Kamal yace "tom Umma, nasan da Dadyna yana raye da dashi zaki taimakamin"

Umma tace "hakane Kamal da yana raye da zai fini shiga damuwa idan ya ganka a damuwa, share hawaye tayi tace "Dadynka ya soka sosai Kamal hakan yasa yake kiranka da my K, my K shine sunan da Dadynka yake kiranka dashi"

Kamal shima idonshi yacika da hawaye yace "Umma meyasa yake kirana da my K?"

Umma tace "ra'ayinshine hakan, kuma ai sunanka yafara da kalmar K"

Kamal yace "hakane Umma" ɗan turo baki yayi kaɗan cikin shagwaɓa yace "to yanzu bacci nakeji kuma baccin yaki zuwa kisani nayi bacci"

Kara shigewa jikinta yayi sosai,

Umma tace "Kamal baka girma sam nikam da Amrah ɗinma ka zauna da ita kayita mata shagwaɓa watakila zata karɓa maka dan kaga saura jumma'a uku zan ɗaura aure"

Kara shigewa jikinta yayi yace "Umma ki auro me hankali kinji?" ɗan marin kanshi tayi tace "oya yi bacci"

Rufe idonshi yayi yana murmushi haka kawai yaji nutsuwa yana saukko mishi gaskiya uwa rahama ne, dahaka har yayi bacci.

          "Amrah tafara anfani da wayarta da dare tana kwance a gefen kulu ta duba ko akwai data ganin akwai kusan 3.5gb yasa tayi tsalle ta diro, Kulu tace "kina lafiya kuwa kinsan kinada ciki kike tsalle haka?"

Amrah tace "rabona da waya tun ina gidan Kamal yau gashi har zanyi chatting"

App store tashiga tayi danloading ɗin watsapp da Wattpad saita watsapp tayi sannan tafita taje Wattpad login tayi kasancewar tanada account a rayuwa tanason karanta littafi hakanne yasa takeson Wattpad, shafin Jiddah S Mapi tashiga tafara karanta littafin datayi kewarshi me suna ƘANWATA murmushi tayi tace "Baba Kulu nayi kewan karanta littafinnan"

Kulu tace "wani littafi?"

Amrah tace "littafin ƘANWATA"

Kulu tace "can ta matse miki"

Saida tagama karatu sannan tashiga watsapp tana duba mutanen da sukayi chatt, Zee tagani taɗanyi dariya, kasa tafarayi har taci karo da Fadila, ido ta Kurawa hoton Dp ɗin Fadila, tanaso ta buɗe amma jikinta har rawa yake, da kyar dai ta daure ta buɗe, hotonta ne da Fadila da Kamal wanda suka ɗauka ranar da sukaje shan ice cream Fadilace tayi musu selfie dukkansu da Ice cream a fuskarsu suna dariya, da sauri ta ajiye wayar ta dafe kirjinta dayake mugun bugawa, Kulu tace "lafiya?"

Amrah kifa kanta tayi da filo tana sauke numfashi da kyar, Kulu ce tasa hannu ta ɗauko wayar, kallon hoton dayake gaban tayi ta hango wata kyakkyawar yarinya da kuma wani kyakkyawan saurayi sai Amrah acikin hoton, kulu kallon Amrah tayi tace "da Alama wannan itace Fadila wannan kuma shine tsohon mijinki Kamal, to Amma meyasa kika shiga damuwa sosai sabida kinga hotonku?"

Amrah tashi tayi batace komai ba tayi hanyar toilet saida ta juma a toilet ɗin kafin ta fito idonta ya kumbura alamar tasha kuka sosai, Kulu batace komai ba ta ajiye mata wayarta sannan taci gaba da wayar datake itada sabon bazawarin datayi.

_Jiddah Ce....✍️_

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 66*

         ~Amrah sun saba da wannan mutumin me suna Ahmad yakarayi mata magana akan ɗaukanta da zaiyi tace ba komai yazo yasami Mama yayi mata magana tukun, nan Ahmad yace to akan gobe ze shigo,

Washe gari kuwa haka akayi kiranta yayi awaya yace yakaraso fita tayi suka gaisa yace tayi mishi iso zuwa wurin Mama sai yanzu Amrah taji zuciyarta ta tsinke batasan wani hali Mama zata nunawa Ahmad ba, Ahmad yace "idan akwai matsala kibari kawai"

Amrah tace "aa babu komai" gida tashiga tasamu Kuluwa tayi mata bayanin komai, nan Kulu tayi murna dan Amrah tace da ita za'a tafi "yanzu Kulu kishiga kiyiwa mama bayani ko Allah zaisa ta saurareki"

Kulu tace "tom" nan tashiga ta tsara Mama haɗeda rokanta tabar Amrah taje tayi aiki ko Allah zaisa tacika alkawarin datayiwa Abba, Mama dafari taki amma datayi wani tunani tace "ba komai yashigo"

Murna kamar ze kashe Kulu, nan tace Amrah wai yashigo, Amrah ma tayi murna da farin ciki taje wurinshi tace "bismillah"

Nan yashiga ya gaisa da Mama tareda yi mata bayani yace mata akwai yayarshi a garin nan yayiwa mama kwatancen yayar tashi, daganan Mama tace "tom Allah dai ya taimaka sannan zan baka amanar ta"

Yace "ba komai Mama nagode"

Saida suka fita ya ɗauko wani karamar waya da sabuwar Sim yace "ga wannan ki baiwa Mama zaku rinka waya aciki"

Da godiya ta karɓa sannan sukayi sallama, data koma gida ta baiwa Kulu takaiwa Mama, saida taɗau number ɗin tayi saving tukun, sun yanke shawarar jibi da safe zasu tafi, Kulu ce taje kasuwa tasiyo Mayuka da turaruka tacewa Amrah "zanje Abuja nabasu Kala"

Amrah kallonta kawai take batace komai ba.

           "Guyson Gaskiya kana bani Mamaki ace nine natara irin kuɗin daka tara ai bazanma zauna a kasarnan ba wallahi saide aganni a london ina rayuwata da ƴammatan turawa"

Guyson daya ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya hannunshi rikeda glass Cup wanda yake cikeda tsadadden shampain gas ɗin sai tashi yake asama, wani wando daidai gwiwa ne ajikinshi sai vest irin na maza me kyaun gaske, kanshi sai sheƙi yake jikinshi dagani kaga ɗan hutu daka ganshi kasan ya jiku da naira, wani tsaddaden ɗan kunne ne a kunnenshi sai wuyanshi dayasa sarkan gold wanda yake yalƙi, sajen fuskarshi ya kwanta lub lub wani kyau yakara sosai fiyeda da, Murmushi yayi wanda yasa fararen hakoranshi suka bayyana gefen kumatunshi yaɗan lotsa, kallon Wanda yayi maganan yayi yace "Ab wani kuɗi kake magana akai?"

Ab yace "Guyson kuɗin daka nunamin na account naka mana miliyan Talatin wasane?"

Mikewa Guyson yayi da yaɗan kurɓi shampain ɗin yace "biyoni mana"

Ab ne yatashi yafara binshi, wani lungu yakaishi acikin babban gidanshi me kyaun gaske yaciro wani ɗan karamin makulli yabuɗe wani ɗaki shiga sukayi, Guyson ne ya matso wurin wani babban akwati ya janyo tareda sa makulli ya buɗe, Ido Ab ya zaro yace "kut melesi" irin wannan kuɗin idan aka nunawa wanda be saba ganin kuɗi dayawa ba zai iya jin jiri yana kwasanshi, Guyson yace "Wannan shi ake kira Dala"

Ab yace "Aina kasamu waɗannan kuɗin?"

Guyson saida ya rufe akwatin yace "muje ko"

Fita sukayi saida ya rufe kofar suka koma inda suka fito dafarko yace "Ab kasan ina harkan safaran mata bama safara ba ina satan Mata inkaiwa masu kuɗi awani kasar, kaga wancan kuɗin dana nuna maka? Sune kuɗaɗen danake karɓa idan nayi safaran saura kuma suna Account, nayi Alkawarin bazanci koda naira biyar a wannan kuɗin ba, duk kuɗin dakaga ina harka dashi to na aikina ne wanda gomnati take biyana, wancan kuɗin haka zanyi ta tarasu daganan har ranar dazan mutu"

Ab cikin Mamaki yace "to amma miye dalilin yin hakan? Meyasa kake sace ƴammatan kuma baka amfani da kuɗin da aka biyaka?"

Guyson yace "Tambaya me kyau, yaran masu kuɗi nafi sacewa idan kaga na sace ƴar talaka to akwai dalili me karfi, duk yarinyar dana sace to inada babban dalili wanda na barshi anan" nuni yayi da faffaɗan kirjinshi, Ab yace "to amma meyasa kake hakan?"

Guyson yace "akwai dalili"

An yace "kullum saina tambiyeka kabani labarinka koda kaɗanne amma kaki nifa abokinka ne kuma kasan bazan bayyanawa wani sirrinka ba"

Guyson sakin Numfashi me karfi yayi, sannan ya gyara zama yanayinshi duk ya canza, idonshi ne suka ciko da hawaye yayinda karamin bakinshi yafara rawa kaɗan kaɗan, jijiyoyin kanshi suka mimmike, yace "Ab banaso nabada wannan labarin yana sani shiga yanayinda bazaka taɓa zato ba"

Ab yace "ka daure koda kaɗanne kabani labarinka basai duka ba"

Guyson yace "shikenan"

Shampain na hanunshi ya kurɓa kaɗan ya ajiye cup ɗin sannan ya sakko daga kan kushin dayake zaune ya zauna akasa tareda naɗe kafarshi kafarshi kamar me ɗaukan karatu, daganan yace "Sunana KASIM Muhammad Umar, Alhaji Muhammad Umar shine mahaifina muna kiranshi da Dady, inada kanne mata guda biyu Sadiya da Aisha, Mahaifiyarmu itace Fatima muna kiranta da Momy, Dady yanada kuɗi sosai sannan babban ɗan siyasane yana neman takaran governor, muna rayuwa a garin Abuja, Dady tin ina yaro ya nunamin dukiyoyinshi ya ɗaurani akansu hakan yasa na taso shagwaɓaɓɓe bana ganin darajan talakawa ko kaɗan, Sadiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login