Showing 84001 words to 87000 words out of 139192 words
domin da yana sonta da ya daɗe da aurenta amma fir yaki yadda shakuwa ce kawai a tsakaninsu dakuma neman ya cusa miki bakin ciki"
"Baby nasan kina faɗan hakane sabida yayanki"
Baby tace "idan kina ganin hakane to hakanne"
Ranta a ɓace ta tashi taɗau jakanta da makullin motarta dakuma wayarta, hanyar fita tayi Fadila tace "ki kara kwana mana Baby"
Baby ko magana batayi mata ba tanufi waje, Fadila tashi tayi tana binta tanayi mata magiyan takara kwana amma ko saurarenta batayi ba, motarta tashige tadanna horn Baba me gadi ne yatashi ya buɗe mata, kuɗi taciro acikin jakarta tamika mishi kafin tawuce, Fadila tsayawa tayi jikinta duk a mace, tasan zata fara wata rayuwa dabata saba ba yanzu babu kowa a kusa da ita babu kowa daga ita sai wannan mugun"
Abdul ganin Kabir yana hawaye ba karamin tashin hankali yashiga ba, sai juye juye yake a ɗakin yarasa meyake mishi daɗi "dan Allah Dude kafaɗamin abinda yasameka me akayi maka kake kuka? Nine ko wani ne yayi maka laifi please kafaɗamin kaji?"
Kabir share hawayenshi yayi wanda yakasa ɓoyesu yace "kaina ke ciwo babu komai, kuma Me martaba yace gobe nakoma gida babu wani excuse"
Abdul yace "nasan halinka idan kace ba komai to bazaka faɗi abinda yafaru ba, to amma kafin katafi inaso ku gaisa da matata tasanka kaima kasanta a matsayinmu na aminan juna"
Da sauri Kabir yace "no naganta a wurin Walima itama taganni sai kayi mata bayani daga baya"
Yana faɗan haka yaɗau makullin motarshi yajuya yakalli Abdul yace "Abdul ka kula da matarka she is innocent kasamu mata, kada kayi sake ka rasata sannan kada ka wulaƙanta ta kada kaci hakkinta sabida musibace cin hakkin mutumin dabaya magana"
Fita yayi yana share hawayen dasuka zubo mishi bayaso Abdul yagani amma abinda be saniba Abdul yarigashi ganin hawayen, jikin Abdul ne yayi sanyi sosai tunda yake da Yarima be taɓa ganinshi acikin wannan yanayin ba sai ranar daya kira number ɗin princess nashi yaji a kashe, fita yayi lokacin har Kabir yakunna motarshi yatafi, da mamaki ya juya yakoma cikin gida, ɗakinshi yanufa ya zauna a gefen gadonshi me kyau da tsada yana tunanin meya samu Kabir haka? Gaba ɗaya hankalinshi ya kasa kwanciya jiyayi hawaye yana zuba mishi daya tuna Kabir yatafi cikin kuka.
Fadila ma acikin ɗaki haɗa kanta tayi da filo tana kuka dan tunanin halinda taga Kabir aciki take, takasa daurewa sai kukane yake zubo mata from no where, cikin kukan tace "Kabir na cuceka nasani amma ka yafemin umarnin iyaye nabi"
Kabir yana tuƙi yana share hawaye daya gajima barin hawayen yayi yana jiƙa mishi gaban riga, dahaka harya iso gida, jiki a sanyaye yanufi ɗakin Abdul "Kabiru lafiyanka kuwa?"
Cewar Dady dayake duba Generator, Be juyo ba yace "eh Dady lafiya" hanyan ɗakin yanufa be kuma juyo ba, Dady ɗan dakatawa yayi yace "to lafiya kuwa? Allah de yasa lafiyan"
Kabir yana zuwa ɗakin yafara jan bedsheet ɗin saida ya janye kafin yadawo kan filo yafara watsarwa yana gamawa yayi kan dressing mirror ya watsar da mayuka da turarukan wurin wasu kwalban turaren suka faɗi akan tyles suka tarwatse, zama yayi kamar sabon mahaukaci komai na ɗakin watsarwa yake yana kuka, daya gama yashiga buga jikin bango da hannunshi kukan fitan hankali yake jiyake kamar yamutu a halin yanzu kozai huta da masifar duniyarnan, saida yagaji yafaɗa kan gado ya haɗa kanshi da katifar yashiga raira kuka.
Baby datayi parkin a gefen titi tahaɗa kanta da sitiyarin motar batasan daga ina hawaye yake zubo mata ba, gogewa take amma sai daɗa zobowa suke, "Adda Fadila na cuceki dana cewa Dady kuna soyayya da Yaya Abdul gashi masoyinki na kwarai shine wanda nakeso, ki yafemin kisa Yarima yasoni koda rabin son dayake miki ne dan Allah"
Wani kukan ne yakara zuwa mata me karfi tunawa da yanda taga yarima yana kuka, horn taji anyi mata a razane tadawo hankalinta, ta kunna motar tayi hanyar gida, Tana shiga tayi parking na motar ko jakar kayan bata ɗaukaba tayi hanyar ɗakinta, Dady yace "Mamana sai yanzu? Lafiya dai kam?"
A sanyaye tace "Eh lafiya"
Tayi hanyar ɗaki, Dady rike baki yayi sannan ya taɓe bakin yaci gaba da gyaran Generator ɗinshi,
Nabila datake zaune a gefen Pinky tace "wallahi yau sai Momy tabani labarin wannan ɗan iskan kuma yanzu ma"
Pinky driven kawai take batama saurareta ba, dan ranta a matukar ɓace da daren nan Nabila tasa momynsu fitar dasu wai zasu karɓi saƙo, wayartace tayi ringing a hankali ta ɗaga tana cewa "hello"
"Ku juyo yanzu kudawo gida Dadynku yana gari"
A rikice Pinky tajuya kan motar tace "Dady yana gari"
Nabila tace "dan Allah kibari muje gidansu Abdul saimu koma"
Baby tace "Amma kina hayyacinki Unty? Dady fa akace miki yana gari"
Nabila cikin lallama tace "ƘANWATA, nasan zaki taimakamin nasamu abinda nakeso, wulaƙantani fa akayi kiyi hakuri kinji"
Pinky juya kan motar tayi tanufi hanyar gidansu ko sauraran Nabila batayiba, Nabila tana ganin haka tace "kada Allah yasa muje ɗin sai me? Wawiyar banza"
Ko magana batayi mata ba dan dukan datasha ɗazuma ya isheta.
Abdul da hankalinshi yakasa kwanciya sai faɗiwa gabanshi yake, yaɗau makullin mota kamar zararre horn yayi tun a ɗaki Baba me gadi ya buɗe mishi get, da mugun speed yaja motar yayi hanyar unguwarsu, gida yaje yayi horn aka buɗe mishi, be wani gyara parking ba yafito yana sauri so yake kawai yahaɗu da Yarima, Dady ne cikin Mamaki yace "Lafiya kuwa Abdul?"
Abdul da beso Dady yasan da zuwanshi ba yahaɗe fuska yace "Eh lafiya"
Hanyar ɗakinshi yayi, yabar Dady tsaye rikeda Kwankwaso yana tunani da mamakin meyake faruwa haka"
Knocking na kofarshi yayi tayi amma bai buɗeba harya gaji yaciro wayarshi yakira bai ɗagaba, saida yayi kusan awa awurin kafin yajuya jiki a sanyaye yanufi motarshi ko magana beyiwa Dady ba.
Dady waya yaciro yakira number ɗin Fadila ringing biyu ta ɗaga batayi magana ba dan lokacin tana tsaka da kuka, Dady yace "Lafiya kuwa Fadila?"
Fadila a takaice tace "Eh lafiya"
Tareda katse wayar dan bataso yasan tana kuka, bin wayar Dady yayi da kallo sannan yakalli sama yace "Allah kaine Allah ka kawo sauki cikin lamarin yarannan"
Gama gyaran yayi yaje yayi wanka, ganin momy batazo ba yasashi zuwa ɗakinta, hawa gadon yayi inda take kwance tahaɗe fuska wai Dady ya zagi ƴan uwanta, Dady yama manta yace "lafiya kuwa Hajiya?"
Momy cikin fushi tace "Eh Lafiya"
Tashi yayi yace "wai miye wannan kalmar take nufi ne na Eh lafiya ɗin? Kabiru yacemin Eh lafiya, Baby tacemin Eh Lafiya, Abdul yacemin Eh lafiya, Fadila tacemin Eh lafiya, Kema yanzu kicemin Eh lafiya? Meyake faruwane a gidannan?"
Momy tace "ai ƴan uwana ƴan uwanane koda buhun shinkafa mua cinye rana ɗaya ai Allah ya hore maka"
Anan Dady yagano Dalilin fushinta, cikin murmushi yace "haba sweethert, shine kike fishi? aini dawasa nake"
"To wasa shine haka?"
Dady yarike kunnenshi yace "sorry natuba"
Ɗan dariya tayi, Dady yace "gaskiya ina ganin kamar yarannan babu lafiya fa kowa jikinshi amace"
Momy tace "kasan sabo yanasa haka nanda kwana biyu zasu warware"
Dady yace "kumafa hakane"
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 57*
~washe gari Abba ne yatashi yana zagawa ko ze sami gidan daze kama musu suyi haya, wata mata ya hango tana soya kosai abakin titi, karasawa yayi wurinta yace "barka dai"
Matar tace "barka"
Abba yace "Dan Allah tambaya nakeda"
Matar tace "Allah yasa nasani"
Yace "Dan Allah miye sunan unguwar nan?"
Matar tace "Jeka dafari"
"Kina nan ne?"
Matar tace "Sunana Kuluwa dillaliya aurena bakwai a unguwarnan ina bada haya idan kanaso"
Abba yace "ba komai amna gidan kanki ne?"
Matar tace "eh gidan kaina ne"
Abba yace "tom ɗaki biyu nakeso"
Matar tace "ba komai yau zakuzo?"
Abba yace "yau mukeso mudawo, inada mata ɗaya dakuma yarinya ɗaya tayi aure amma sun rabu da mijin kuma tanada ciki"
"Subhanallah Allah ya tsare mazan yanzu sai addu'a ba hankaline dasuba saki sun maidashi kamar ruwan sha, basu ɗauki mata da daraja ba sun fake da cewar mata sunyi yawa agari, basusan matan ma kala kala bane, idan kasamu wacce iyayenta basa ɗaukan raini zakasan mata basuyi yawa a gariba, haka nida mazajen dana aura kullum faɗa kullum dambe, duk abinda namiji zeyi miki na wulaƙanci yayi miki amma kada yahana kiki ɗu'ami wato abinci"
Abba ganin surutun yayi yawa yasa yace "Allah dai ya kyauta zamuzo anjima saimu jera kayanmu"
Matar tace "to kuje kuga gidan tukun"
Abba yace "ko yaya gidan yake bazamu ki ba"
Yana faɗan haka yakama keke napep yanufi unguwa Unty Jamila, nan ya sanar musu duk yacce sukayi da kuluwa dillaliya, Mama da Amrah sunyi murna sosai, Unguwar Ganye road sukaje suka kwashe kayansu daya rage nan aka haɗa dana gidan Unty Jamila suka nufi Jeka da Fari cikin mota me bodi, kuluwa tana ganinsu tafarayi musu dariya kamar tasansu dama, hawa me bodin tayi suka ɗau hanyar gidan tanaiwa driver kwatance, abakin kofar wani koɗɗoɗɗiyar gida suka tsaya, gidane me ɗaukeda ɗakuna uku wanda yake waje ze iya hango na ciki, gidan dai gashi ka kamarshi, Abba kallon gidan yayi sosai kafin yace "ba komai akwai Allah"
Kayansu suka fara ɗibawa da Unty Sadiya datake aikin aikawa Amrah harara, duk Amrah takasa sakewa, saida suka shirya kayansu tsaf kafin Unty Sadiya tacewa Mama suje kasuwa su siyi kayan Abinci, zuwa sukayi suka siyi komai da komai kafin tayi musu sallama da cewar gobe zata dawo, Kuluwa ce takalli Mama tace "Mama be kamata ace kinsa damuwa a ranki ba yanayin dana ganki nasan kina cikin damuwa, amma hakuri zakiyi dukda nikam banida hakuri agidan miji dan wallahi idan kamin abu dambe zamu kwasa aurena shida yanzu zanyi na bakwai dawani alhaji acan cikin gari"
Mama shiru tayi tana jinta dan matar akwai surutu, saida tagaji kafin ta kyale mama takoma kan Amrah "ke ko meyasa kika yadda ya sakeki da ciki? Ai idan nice ke Hisba zan kaishi sai anbimin hakkina yabari idan na haihu saiya sakeni, tukunna ma nasan ba'a saki da ciki saida gagarimin hujja ko zaki iya bani labarin abinda yafaru?"
Amrah tace "Aa sirri ne gaskiya"
Matar tace "gaskiyane ba'ayi ciki dan tuwo ba, to amma ke kaɗai iyayenki suka haifa?"
Amrah shiru tayi ganin kallon da mama tayi mata, mikewa tayi tace "bari nayi wanka"
Dahaka tasamu ta kaucewa amsar Kuluwa,
Kuluwa tace "nikam ɗaki ɗaya nake anfani dashi shine wancan"
Mama tace "yayi kyau"
Haka sukaɗanyi hira kafin kowa ya watse yaje ya kwanta.
Asuba tagari.
"Yarima daya kwana da zazzaɓi da ciwon kai asuba tanayi yatashi yafara haɗa kayanshi, saida yagama tass kafin yashiga yayi wanka, Me martaba yakira yace aturo mishi driver yau ze koma, yana ajiye wayar yaji sallaman Dady, a hankali ya amsa yanaɗan duƙar da kanshi da yanda ya ɓata ɗakin yayi kaca kaca, da kallo Dady yabi ɗakin sannan ya girgiza kai, zama yayi a gefen gadon sannan yacewa Kabir ya zauna, a hankali ya zauna a kasa kanshi a kasa ya gaida Dady, cikin sakin fuska Dady ya amasa tareda cewa "nazo ne muyi wata muhimmiyar magana"
Kabir yace "to Dady"
Gyaran murya Dady yayi yace "ka ɗaukeni a matsayin mahaifi?"
Kabir yace "eh"
Dady yace "ni abokin Babanka ne nasan ze yadda da duk wani zaɓi danayi maka, na zaɓa maka Nabila a matsayin matar aure"
Kabir ɗago kanshi yayi yakalli Dady, Dady yace "eh idan har ka ɗaukeni a matsayin mahaifi to ka yadda da zancena"
Kabir badan yaso ba yace "to Dady"
Albarka Dady yasa mishi kafin yace "munyi waya da me martaba yace yau zaka tafi wai ko?"
Kabir yace "eh Dady"
Dady yace "to ga wannan"
Makullin mota yabashi tareda cewa "nace drivern yazo a motar haya sai ku koma da sabuwar motarka"
Mikewa Kabir yayi ya rungume Dady tareda cewa "nagode"
Dady yace "ba komai"
Daganan yafita,
Yana fita Kabir yamike yasa key a ɗakin, jikin wardrobe yaje yafara buga kanshi, ganin hakan bazeyi mishi ba yasa ya buɗe jakar kayanshi yafara watsarwa idanunshi sunyi jaa, da karfi yace "I am looser"
Watsar da sauran kayan ɗakin yayi, ya kwanta aciki ranshi kamar ze fita.
Sauri take tahaɗa break fast kwai take soyawa amma sai tsaki take dan yakiyi da wuri, tahaɗa tea tun ɗazu da dauran kayan karin kumallo soya kwan ma jitake kamar tabari dan yakiyi, tasan yanzu Yarima yana jin yunwa be saba da zama har iwar haka be karya ba, saida tagama ta shirya komai akan plate kafin taje ɗakinsu da Fadila tayi wanka tareda sa wani atampha riga da skirt yasha cutless ajikin, hoda ta shafa me kyau wanda yakara fito mata da haskenta, sai lip balm tayi kyau sosai tayi ɗaurin Ture, gyalle tayafa kalan kayanta kafin ta fesa turare me kamshin gaske, ganin kanta tayi a madubi tayi kyau sosai, kallon kan gado tayi a hankali taji jikinta yayi sanyi tunawa da Adda Fadila wacce take tsokanarta idan tayi kwalliya, gashi wai yau tayi kwalliyan sabida wanda Adda Fadila takeso, "oh Allah kai kasanyamin son Yarima a raina ya Allah kasan dalilin dayasa kayi hakan" bayan gama tunanin taɗau hanyar kitchen, breakfast ɗin ta ɗauka tayi hanyar ɗakin Abdul, abakin kofa ta tsaya tanajin kunya sosai amma ta dake tayi knocking, da sauri ya share hawayen dayake fuskarshi tareda fara tattara kayan dan bayaso Dady yaganoshi, saida yaɗan kintsa kafin yaje bakin kofar a hankali ya murza key ɗin ya buɗe, karo yaci da fuskar Baby tana sakar mishi murmushi me tsada da jan hankali, shima murmushin karfin hali yayi mata kafin yajuya yakoma ciki, a hankali take tafiya harta shiga cikin ɗakin, bin ko ina take da kallo yanda ya lalace ba kamar yacce tasani ba, komai a tarwatse ga kwalban turare dasuka fashe, anan ta lurada kanshi yanaɗan fitar da jini, cikin sauri ta ajiye plate ɗin ta nufi wurinshi, taɓa wurin tayi tace "meya sameka yaya?"
Hannunta yariko ya zaunar da ita akan katifa tareda zama a gefenta, duk ta rikice sai tambayarshi take meya sameshi?
Tashi tayi da sauri taɗauko first aidbox, tazo wurinshi, shiru yayi yana kallonta, a hankali taciro auduga da spirit, dangwala audugar tayi da karamar xesos tasa acikin spirit ɗin, kanshi tariko tasa audugar, ihu yayi yana rike hannunta dan yaji zafi sosai shi a rayuwarshi bayason wahala ko zafi ko kaɗan,
Baby leko fuskarshi tayi tace "yaya kaine da ihu?"
Rike hannunta yayi yace "a hankali pleasss akwai zafi wallahi"
Dariya ne yaso kwace mata amma ta daƙe saida tayi dressing na wurin kafin ta mayar da first aidbox ɗin, kintsa ɗakin tayi ta share tareda mopping sai kallonta yake harta gama, ta fesa turare, sannan ta ɗauko plate ɗin tazo kasa ta zauna, sakkowa yayi dan yafara jin yunwa,
Zuba mishi tayi, "nagode ƘANWATA" shine abinda yafaɗa, ɗan murmushi tayi mishi wanda ya bayyana fararen hakorinta, hannu yasa ze fara ci, ta ɗauko spoon tafara feeding ɗinshi, shiru yayi yana karɓa dan ahalin yanzu yana bukatar me kula dashi baya cikin yanayi me daɗi, yasaba idan ranshi yaɓaci momynshi ce take rarrashinshi saidai yau babu itama acikin duniyar hakan ne yasa yabari Baby tana feeding ɗinshi hakan zeɗan rage mishi raɗaɗin dayake zuciyarshi,
Kallonta yakeyi itama tana bashi tana kallonshi, "salama alaikum" cewar Momy datazo zatayiwa Kabir sallama hannunta rikeda wani kwali da alama na snacks ne wanda zeyi tsaraba dashi, baya tayi da sauri ganin Baby tana baiwa Kabir tea abaki shikuma yazuba ido sai kallonta yake harda lumshe ido, sallamar datayima basusan tazo ba, da sauri tajuya da kwalinta tabar ɗakin,
Saida ya koshi kafin yaɗan ɗauke kanshi cikin shagwaɓa Baby tace "dan Allah ka kara koda kaɗan ne"
Shima cikin shagwaɓan yace "o,o na koshi"
Dariya abin yabata saida ta dara kafin ta mike ta kwashe plate ɗin zata fita, hannunta yariko yana kallonta, a hankali takoma ta zauna, plate ɗin ya jawo shima yafara bata, kunya taji ta dukar da kanta, "ɗago kanki nifa yayanki ne"
Ɗago kanta tayi a hankali yabata itama saida ta kawar da kanta kafin ya kyaleta, tashi tayi taɗauke empty plate ɗin zata fita yace "idan kin kai kidawo zamuyi wata magana"
Baby cikin ranta wani daɗi taji "Allah kasa yafaɗa soyayya dani ne"
Saida takai kitchen kafin tadawo ta zauna a gefenshi, shiru yayi bece komai ba, yana tunanin yafaɗa mata ko kuma yayi shiru?
Baby ganin shirun yayi yawa yasa tace "ina jinka"
Kallon fuskarta yayi sosai har saida ta kawar da kanta, batayi tsammani ba taji yariko hannunta duka biyu, juyowa tayi ta kalleshi, lumshe idon yayi yace "Baby ke ƘANWATA ce, shiyasa zan faɗa miki abinda yake damuna, Dan Allah na dace da wannan yarinyar Nabila?"
Dum Baby taji a kirjinta, tambayar tazo mata bambarakwai wai namiji da suna Hajara,
"Baby Dady ne yace wai na aureta ya zaɓamin ita a matsayin mata, nikuma bazan iya musa mishi ba, sannan yau zan koma garinmu an turomin driver"
Kallon cikin idonshi take da idanunta dasuka kara girma, takai minti bakwai ahaka kafin tamike ta zare hannunta acikin nashi, da gudu tafice tayi hanyar ɗakinta tana kuka, Momy datake tsaye abakin window ɗinta tana tunanin abinda tagani, sai ta hango Baby tafito da gudu tana kuka, baifi minti biyu ba taga Kabir yafito shima fuskarshi ba alamar daɗi yanufi ɗakin Baby, saida ya buga yakai sau uku taki buɗewa kafin yajuya yakoma ɗakinshi, momy tace "oh ni Maryama me nake gani haka? Ya Allah ka kawo sauki"
Baby faɗawa tayi akan gado tafara kwance ɗan kwalin goge fuskarta tayi tafara watsi da kayan ɗakin, rigan tacire tayi cilli dashi ta kwanta akasan ɗakin tana birgima tana kuka, ganin hakan beyi mata ba, yasa ta ɗauko fillos tafara jifa dasu, zama tayi kamar mahaukaciya cikin kuka da rawar baki tace "why why meyasa hakan yake faruwa? Wannan shine kaddararmu kenan kowa baya samun abinda yakeso? Meyasa