Showing 72001 words to 75000 words out of 139192 words

Chapter 25 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

891

/>
Kabir yace "Okayyyy hakanefa, amma Meyasa kake Mata Tsaya dayawa?"

"haushi take bani Wlh duk sanadinta ne Dady yahadani da Wancan wawiyar Yanzu irin wautan dasuke agidannan sai kayi mamaki, dambe sukeyi ita Baby tahau kanta, ita kuma batada karfi sai shegen Baki, Ga son guje guje da wasan banza" yakarashe maganan da tsakin takaici.

Kabir yace "kaga sai Kuje kuyitayi a gidanka idan Baby batanan kaine abokinta"

"waye sa'an wasa da ita?  God forbid"

Haka sukaci gaba da firansu,

Saida Fadila tasha maganin zabzab'i Kafin tasamu tayi bacci.

*washe gari*

Yau Yakama Friday daidai da ranar da Dady yayi alkawarin yiwa Fadila da Abdul Aure, Abdul ne kwance Akan gado tinda Yayi sallan asuba be kuma mikewaba har Yanzu karfe 11:30 Kabir dake zaune da waya a hannunshi sai tsaki Yakeja tunda asuba Yake trying d'in number Fadila amma wayarta a kashe yana cikin tashin hankali sosai, kallon Abdul Yayi wanda Yayi d'aid'ai Akan gadon dagashi sai Wani karamin wando da vest, wani tsakin Yakuma ja Kafin ya d'au filo ya makawa Abdul a fuska, Abdul a firgice ya Mike yace "waye"

"wayo ne, yau aurenka amma kazo ka kwanta Akan gado kusan karfe sha biyu ake nema, dallah katashi kafara shiri"

Wani dogon tsaki Abdul Yaja Kafin yakoma ya kwanta, wayarshi ce tayi kara yana dubawa yana Yatsina fuska, ganin sunan AK yasashi Sakin fuska yad'aga yace "my maaan"

Dayan b'angaren akace "how far?  Yanzu muke hanyan gidanku Nidasu A Man Allah dai yasa kawayen amaryan hot hot ne?"

"kaga banason iskanci kannena ne bawasu ba, Ku yaushe zaku daina neman Mata? Ga Prince yadaina Yanzu Haka muna tare dashi yahad'u dawata Baby datake garashi da bango" wufce wayar Kabir Yayi yace "Karka jishi karyane sai Kun Iso"

"Dan Allah Adda Fadila kitashi kishirya bakiga kawayenmu sun fara zuwa ba? Kinaso ayimin dariyane?"

Fadila dake kwance rungume da filo tayi hamma tace "Kinga kada Ki dameni zan shirya amma sai 12 okay?"

Baby fuska tausayi tayi tafara lallab'a Fadila saida Pinky tasa Baki Kafin Fadila tamike tana kashe jikinta hartayi wanka, Wurin kwalliyama saida sukayi da kyar Kafin ta yadda akayi Mata, Ai kuwa tafito Kamar 'yar tsana Babita, tayi Kyau sosai wani leshi Baby tazab'o Mata me Kyau acikin kayan lefenta tasa sai Masha Allah aketa Fad'i duk wanda yaganta, Nabila dake kwance agado tana danna waya takira number d'in Abdul "Babyna ya kika tashi?"

Cikin shagwab'a Nabila tace "Yayana shine Baka kirani ba? Gashi yau aurenka Inason Inga kayi Kyau sosai Dan Allah kasa kaya zamuyi hoto kaji yayana"

To Babyna angama,

Dariya tayi tace "that's why I love you"

"love you too"

Yace Kafin yakashe wayar, Fadila dake gefe ana d'aura Mata Kai tana jinta batako Kalli Inda takeba danta lura yarinyar akwai girman kan tsiya da raini Ga yanga sai shegen sirka yare da turanci, ta d'au al'adan turawa ta d'aurawa kanta Kamar ba yar musulma ba Allah dai yashirya,  ita kuma Fadila bata d'aukan raini shiyasa ma ta watsar da ita, Amma kanwarta akwai saukin Kai hakama yasa suka Saba daga jiya zuwa yau Kamar 'yan uwa"

Abdul tashi Yayi yai wanka yashirya cikin tsadadden shadda Kalar Sama "sky blue" takalmi yasa me tsadan Gaske da hula d'inkin Borno shima sky blue, sajen fuskarshi ne ya kwanta Lub, sai Wani shek'i Yake Kamar ba gobe, turare ya fesa me kamshi Saide fuskarnan babu alamar Dariya Ko kad'an ya tamke tamau Dan Sam baya cikin farin ciki yana b'oye damuwarshi ne kawai danshi kad'ai yasan me yake ciki, haske yakara sosai sakamakon rama dayayi na kwana biyu, Yarima daya fito daga toilet yana tsane kanshi da towel ya Kalli Abdul daga Sama har kasa, ba karya Yayi Kyau sosai yafito Kamar Mijin Novel, "kaga Angon yau bada kanka asare kaje Wurin Amarya kace ya Fad'i"

dad'a turmusa fuska Abdul Yayi bece komai ba, yarima ne yakaraso Wurinshi ya rungumeshi yace "kayi Kyau Saide kamanta agogo" janye jikinshi Yayi taku kad'an ya Iso Wurin akwatinshi bud'ewa Yayi yaciro Wani Leda, d'auka yayi yabude saiga Wani kwali me Kyau, bud'e kwalin Yayi yaciro Wani rantsatsen agogo yana haske Kamar ya d'auke Ido, Wurin Abdul yanufa yariko hannunshi sannan yasa mishi agogon yace "Dude wannan shine Gift nawa"

Kallon agogon Abdul Yayi yace "wannan agogon bana diamond ba? Haba Dude kanaso ayi kidnapping Nawane? Ko a yankemin Hannu? Ai wannan agogon Saiku 'ya'yan sarakuna, hasalima basai Kabani gift ba a aurena zuwankama  ya wadatar dani"

Dariya Kabir Yayi yace "duk wanda yasaci agogon nan Nayi maka alkawarin da kafarshi zai kawo maka batareda kawani damuba, nidai inaso kaso agogon nan sosai sabida Nina Baka kyautarshi kaji? "

Rungumeshi Abdul Yayi yace "nagode kuma zan kula dashi Nayi maka alkawari"

Kabir yace "bari Nima nashirya"

Muryansu MK sukaji acikin gida da sauri Abdul yabude musu Kofa suka shigo ban hira ya b'arke tsakaninsu aka fara tuno da da, Sallama Baby tayi Abdul yace "waye?"

Baby tace "nice"

Yace "tsaya awurin Ina zuwa"

Tashi yayi yaje ya sameta, "me kuma?"

"Dady ne yace kufito za'a d'aura Aure"

Wani uban tsawa ya daka Mata har saida jikinta yafara rawa zaro Ido tayi tana kallonshi yadda Yake nunata da yatsa yana Mata tsawa, "me zanyi musu?!!! Kece uwar Shishigi da kirana Ko?  Zaki barnan Ko sainaci Ubanki banza munafuka"

Dukar da kanta tayi kasa tana murza yatsunta Wani tsoron shine ya dirar Mata fiyeda na kwanakinnan "Kibar nan"

A tsorace tajuya tafara tafiya daidai bakin Kofa yace "Baby"

Tsayawa tayi bata juyoba Dan Idonta yacika da hawaye tana Kokarin mayarwa, a hankali ya tako zuwa Wurinta Hannu yasa a kafad'arta ya juyo da ita, dukar da kanta tayi Dan batason kallon idonshi jira kawai take taji saukan Mari a fuska, rungumeta Yayi yana Sakin ajiyar zuciya, cikin mamaki take kallon bayanshi "lafiyanshi kuwa?"

Saida yakai minti biyar ahaka Kafin yace "you are my sweet sister, I love you so much, banason abinda ze saki cikin damuwa, ke yarinyace har Yanzu bazaki gane halinda nake ciki ba,  hawayene yafara bin fuakarshi yana Sauka zuwa wuyanshi, Baby niba Mugu bane Kin sani, bansan Meyake damuna ba Wlh, nazama Kamar mahaukaci Ina Kwance ma Ina surutu ni kad'ai" KANWATA? Na'am tafad'a a hankali, beyi magana ba kawai ya saketa, juyawa Yayi ze tafi tace "Yaya kayi hakuri"

Murmushin karfin Hali Yayi sannan yace "ba kiyimin komai ba Kicewa Dady muna zuwa"

Gid'a kanta tayi, yajuya yatafi, shiru tayi tana tunani, dafa kafad'arta akayi da sauri tajuya ganin Fadila ce yasa tayi murmushi itama Fadila murmushi tayi mata "tin d'azu Dady yace Nazo na dubaki amma na tarar kuna magana da Abdul shiyasa najiraki a Kofa saida kuka gama"

Kallonta Baby tayi tace "Adda Fadila da Gaske Kinason Yaya Abdul yanzu"

Fadila jitayi Kamar ruwan zafi Baby take watsa Mata amma babu dadi tace Mata Aa Dan akwai Kunya Koba komai ta taimaka Mata, A hankali tace "Eh Ina sonshi"

Murmushi Baby tayi tace "to kiyimin alkawarin zaki kula dashi bayan kunyi aure"

Fadila kawar da kanta tayi tana Kokarin maida hawayen dasuke shirin zubo Mata tace "Nayi miki alkawari"

Ta baya Baby ta rungumeta tace "nagode"

A hankali ta zameta tace "muje"

Tafiya sukayi zuwa side Nasu.

Pinky ce tazo Wurin Fadila tace "Unty Fadila Kicewa Yaya ayi dinner please, Wlh yaki yadda amma Nasan idan Kece ze yadda"

Fadila kallon kasa take tana tunani me zata fad'a Mata Yanzu?

Wani idea ne yafad'o Mata tari tafara tana Rik'e kirjinta, Baby ce tarikota da sauri ta zaunar da ita taje da gudu yadawo Mata ruwa, karb'a Fadila tayi tace "nagode"

A hankali ta kurb'i kad'an Kafin ta aje, Pinky tace "sannu"

yawwa Yawwa Fadila tace, daganan Maganar Dinner ta b'ace, suka fara sabgoginsu.

karfe biyu cif aka d'aura aurensu Akan sadaki dubu d'ari wanda Dady yabada, tunda aka d'aura aure Abdul yafara ciwon Kai da kyar Su yarima suka shigar dashi mota Dady yana ankare amma bece komaiba.

Jiddah Ce

08144818849[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *K'ANWATA*

  🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 52*

         ~Kabir acikin mota yace "Haba Dude ka warware mana me hakane? Kanaso mutane su fahimci abinda ake ciki ne?"

Abdul Rik'e kanshi Yayi Dan yana Mugun Sara mishi, driver ne yazo yakaisu gida, Yarima yace "muje ko"

Abdul kasa fita Yayi Dan bayajin karfi Ko kad'an, Kabir ne ya rikeshi suka fita a hankali suka fara tafiya da kyar Abdul Yake ganin abu biyu biyu, Momy ce zaune acikin 'yan uwanta, sai fira suke suna cin snacks da drinks momy tana cikin farin cikine sabida tasan meta taka, Dady ne yashigo d'akin yana Sanye da Babban riga sai Baby dake gefenshi tayi Ado cikin swizz less pink tayi Kyau sosai da sosai sai zuba murmushi suke da ganinsu Kasan suna cikin farin ciki, hannun Baby rikeda Jakar Dady, babu wanda ya amsa musu sallaman Dan dukansu sun maida hankalinsu Akan fira Dacin snacks, Dady ne yakalli Baby yace "Kin Gani Ko? 'yan uwanta idan suka samu abinci to ba magana Yanzu duk hankalinsu Akan drinks da snacks d'innan basu Ko jimu ba, Kafin dare saina karayi musu order na drinks Dan Nasan babu abinda wannan zeyi musu sai Anyi Magana suce anayi musu gori"

Dariya Baby takeyi tunda dady yafara zancen, abin yabata Dariya "Ke dariyan uban wa Kikeyi?"

Muryan momy suka jiyo a bayansu, da sauri Dady yakarb'i jakarshi yawuce Sama Dan yasan abinda ze biyo baya, Baby tace "magana muke Nida Dady ba dake bane"

"Eh Ai najiku ba cewa Yayi 'yan uwana mayunwata bane? Basa ganin abinci su Kyale Koba Haka yaceba?"

Baby tace "Momy gaskiya kannenki beji Daidai ba ba Haka yaceba"

Rank'washi momy tayi Mata aka tace "nice Banji Daidai ba?  Ke yara Mata suna d'aurewa uwayensu Mata gindi Ke kuma kinabin Ubanki, to idan abinci ne sai munci Harda sud'e kwano Saide a koremu a gidan kuma 'yan uwanama zasuci su koshi Wallahi"

Baby saida tad'anyi Gaba tace "Momy bagasu Ga abinci ba waya hanasu ci Allah yabada Ai suci kawai su gode Allah" kasa tayi da murya tace "Abinka da Babu a House"

Momy tace "Dan ubanki me kikace"

Gudu tayi tabar Wurin "zan kamaki ne".

        "Sorry" shine abinda Kabir yake fad'awa Abdul, Abdul sosai yakejin ciwon Kai, saida suka Iso d'aki Kabir ya sakeshi babu wanda yagansu Dan ta kofar baya sukabi, ruwa da paracetamol Kabir yabashi a hankali ya karb'i ruwan, Wurin had'iye magani ne sukayi tayi da kyar Abdul Ya amsa yasha, Kwanciya yayi Akan gado bacci yanaso ya d'aukeshi amma tunani Yayi mishi yawa, Kabir ne yazo ya zauna a gefenshi yariko hannunshi yace "Dude! ka cire damuwa a ranka ka rungumi kaddara, zaka sawa kanka Hawan jini a banza"

Abdul shiru Yayi Dan yana bud'e Baki kukane ze sub'uce mishi kuma bayaso yasaba kukan Dan kada Watarana yazo ya sakarwa Fadila tazo ta rainashi, Rik'e Hannun Kabir kawai yayi ahaka har bacci Yayi gaba dashi, Kabir yana kallon abokin nashi cikin tausayawa a hankali yashafa gashin kanshi me tsantsi da yalki yace "Allah ya cireka cikin wannan damuwar Ameen"

Cire hannunshi Yayi yad'au wayarshi Kiran number Fadila yayi har Yanzu akashe addu'a Yayi Allah yasa lafiya, dukda shima yana cikin damuwa amma Yana b'oyewa Dan kada hankalin Abdul yarabu biyu Gara yabarshi shima yaji da abinda Yake damunshi.

      "Fadila ma kanta yana ciwo tun d'azu amma ta daure sabida mutane zasuyi ta tambayarta, tana zaune ta dafa kanta dansu Baby da Pinky sun dameta da surutu ita kuma uwar Girman kan tana gefe tana kallon series film na India a wayarta, Baby ce tace "Amarya lafiya kuwa?"

d'an tsaki Fadila taja tace "Kalau"

"Kodai kina tuna zamanki Ke kad'ai da yayana ne?"

"Aa bahaka bane kaina ked'an ciwo Inason ind'an huta"

Mikewa tayi ta kwanta tana tunani ranar aurenta da Kamal ta tuna ranar Kamu yakirata da safe yayita Mata wasa Yanzu gashi yau an d'aura aurenta amma Ko Kira bata samu daga Wurin mijinba "Amrah Kin cuceni" Tunanin Kamal ba karamin d'aga Mata hankali Yayi ba, ta soshi Kamar ranta amma Yanzu yana tareda kanwarta sunashan soyayyarsu sunma manta da ita, shikuma Abba ya koreni agidanshi batareda ya saurari Hanzarina ba, Allah ne Mafi sanin Daidai amma Abba baiyimin daidai ba, saida tayi hawaye sosai Kafin bacci b'arawo ya saceta, dukda hayaniyar mutane be Hanata bacci ba.

       "Amrah tin jiya da abin yafaru bata kuma warwareba sai nokewa take tana Kin had'a Ido da Mama Dan ba karamin fad'a Abba Yayi Mata ba, Saide yau Haka kawai takejin kanta cikin farin ciki, duk bakin cikin datake ciki be hanata jin daban ba, Mama tana ankare da ita amma tasan Amrah tana farin cikine Dan Abbansu ya shige Mata, bata kulata ba Dan tayi alwashin bazata zauna da Amrah Kamar da ba sai Amrah tafad'a Mata gaskiya shiyasa ma take had'a Mata fuska,

Abba ne Yayi sallama yashigo, lokacin Amrah na zaune Akan tabarma jikinta Sanye da bakin material wanda yafito Mata da haskenta sosai, gashin kanta tayi parking wuri d'aya wanda Yake bak'i sid'ik jin sallaman Abba yasa ta zaro manyan idanunta masu Kama da kwai  Dan tasan zeyi Mata fad'an d'ankwali da sauri taja 'Dan kwalin tana d'aurawa Abba yace "kada kiji tsoron Mutum Kiji tsoron Allah, Yanzu Haka kina Kokarin d'aurawa dankin Ganni, to idan Bana nan wazakiji Tsoro?"

Shiru tayi batace komai ba, Abba yace "Shikenan Yanzu ya jikin Baki?"

Tace "da sauki Abba"

"to Allah yakara sauki Ga wannan maltina da madara na siya miki kisha zed'an kara miki karfi kinji?"

"nagode Abba" tashi Abba Yayi yafita beyiwa Mama magana ba, Amrah ce tamike ta d'auko Cup tazo tazuba Malt d'in da madaran ta Mike a hankali taje Wurin Mama, "Mama Ga Maltina"

ko kallonta Mama batayiba tace "Aa kisha abinki ni ban damu da abin duniya ba"

Wani kallo Amrah tayiwa mama kallo na mamaki amma bataga Mama ta damuba aikinta ma takeyi Ko kallo batayi Mata, a hankali takuma mikewa jikinta yayi Sanyi sosai, "to me wannan Kalmar take nufi? Damuwa da abin duniya!!!"

A hankali tad'an kurb'i malt d'in sannan ta ajiye sauran tayi tagumi, Itakam taga ta kanta yau Mamace ta juya Mata baya? Koda shike tun asali Mama tafi kulada Fadila Mama b'ata sonta sosai, ganin tunani bazeyi Mata komiba yasa ta d'ago gwangwanin Malt d'in ta had'a da Madarar ta d'aura a bakinta saida ta shanye Tass Kafin ta Sauke tace "Wallahi bade na mutu ba jini ba Ga bakin ciki Ga Rashin abu me dad'i? Kai Ina Wlh Bama zeyuwu ba, mama tana kallon ta amma ta watsar Dan tanaso saita horata da Kyau Tukun.

        "da dare Dady ne yakira Fadila da Abdul zuwa falonshi, Fadila da har Yanzu kanta yana ciwo ta zurmud'a katuwar hijabi ruwan Hoda taje d'akin, shikuma Abdul Rigar daya cire yasa a hankali Yake tafiya Dan jiyake Kamar kanshi ze rabe biyu, zuwa shima Yayi Abakin Kofa sukayi Karo itama tazo zata shiga shima yazo ze shiga, kallon kallo sukayi a tsakaninsu Kafin Fadila ta janye idanunta tayi kasa dasu tad'an matsa saida yashiga Kafin itama tashige,

Dady ne zaune Akan sofa hannunshi rikeda alkurani, sallama Abdul Yayi ras gabanshi yafad'i ganin Dady da kur'ani Kadafa ace suyi rantsuwa, wuri yasamu ya zauna a gefe tareda gaida Dady "lafiya" Dady yace, Fadila ma shigowa tayi da sallama a bakinta, zama tayi a gefen Abdul Tareda gaida Dady "lafiya" itama Yayi Mata reply, shiru suka zauna na lokaci me tsawo, Gyaran murya Dady yayi yace "Alhamdllh da farko Ina tayaku murnan aurenku dukda Nasan badan kunaso bane kuka auri junanku kunyi ne sabida biyayya kuma nagode sosai da sosai Allah Yayi muku albarka, Saide Wani Hanzari ba gudu ba,  Kai Abdul Nabaka daman ka kara aure domin shi namiji Allah ya hallata mishi tin Mata guda hud'u Inda a kur'anima Allah yafad'a (Fankihu ma d'aba lakum Minannisa'i Masna wa sulasa warba'a) Ku Mata daga d'aya zuwa biyu zuwa uku zuwa hud'u saide idan bazakuyi adalciba to (Fa wahidatan auma malakat Aima nukum) Saiku auri d'aya, dan wannan ne yasa nabarka ka auri Mata biyu koda rana d'aya ne, Saide akwai sharad'i gida uku"

Abdul da kanshi Yake kasa yace "to Dady"

Dady yace sharad'in shine "idan Fadila takawomin kararka ka zalunceta bazaka kara aure ba, nabiyu idan kayi auren ka nuna bambaci to zaka saki wacce ka auro daga baya, na uku zakabar Fadila tayi Aiki batareda sata a takuraba"

Abdul Wani bakin cikine ya dameshi wannan Wani irin bambaci ake nuna mishi? Shida gidansu amma ana fifita bare akanshi?"

Dady yace "sannan zaku koma gidanku na kanku dayake zone 2 kusada asibitin Fadila da Baby, Allah Yayi muku albarka"

"Ameen" suka amsa a sanyaye, Dady yace "kutashi kuje"

Fadila ce tafara mikewa sai Abdul dayake zaune jikinshi duk a mace Dan Wlh ba karamin haushi yajiba Meyasa ita baza ace tayi mishi biyayya ba?

Dady yace "Ku dakata"

Tsayawa sukayi Dady yace "Nasan zakayi mamaki Abdul Meyasa ita Fadila Banyi Mata fad'a ba Ko? To ni kad'ai Nasan dalili, kuje"

Juyawa sukayi suka tafi, Abakin Kofa Fadila tsaya tana jiran yawuce amma Sam yaki wucewa ya tsaya yazuba Mata Ido, ganin haka yasa tarab'a zata wuce Hannunta yariko yaci gaba da kallonta, kwatan hannunta tafara Dan rikon yayi Mata zafi, "hannuna yanamin zafi ka cikani Dan Allah" baice komaiba kuma be saketa ba yafara tafiya da ita, yana gaba tana baya sai faman kwatan hannunta take, ganin yanufi sashenshi da ita yasa tafara ihu tana kiran Baby!!! danta matukar tsorata dashi, yana shiga yarufe kofarshi taja hannunta ta wurgata kasa, fad'iwa tayi Akan tiles d'in tana kuka, Belt na wandonshi yacire yafara matsowa Wurinta, baya baya tafara tana zare Ido, daidai jikin bango ta Tsaya ta manne da bangon Kamar zata tsaga ta shige jikinta sai b'ari yake, saida yazo dab da ita Kafin ya durkusa ya nunata da belt d'in yace "idan baki fad'amin gaskiya ba yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login