Showing 15001 words to 18000 words out of 139192 words

Chapter 6 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

896

atake yaji notikan kanshi sun fara kwancewa jin irin muryar datayi mishi a wannan tsohon Daren da kyar ya had'a murya yace "Kanwata meya sameki?"

Kara langwab'ar da murya tayi tace "Yaya cikina kemin ciwoooo"

Kamal yace "sorry ina Fadila kice mata tabaki magani"

Wani siririn ihu tayi Wanda yasa tsikan jikin Kamal yatashi, take yaji idonshi yafara rufewa, kashe wayar yayi gab'a d'aya ya kwanta rub da ciki yana sauke numfashi, Amrah dariya tayi tace "Saima kashigo hannu bazaka kara anbatar sunan Fadila a wurina ba" kwanciya tayi bacci yatafi da ita cikin in dad'i, Kamal kuma tashi yayi yaje kitchen yafara Neman lemon tsami a cikin drawer yasamu yad'auko cup da ruwan zafi ya matsa lemon tsami a ciki, Umma ce tayi sallama domin d'aukan snacks zata baiwa kawarta, ganin mutum a kitchen ya juya bayanahi yana matsa lemon tsami a cup yasa ta tsaya tana kallonshi, Juyawa yayi zai koma d'aki yanad'an runtse ido, ganin Umma yasashi fara b'oye cup d'in, Kallonshi Umma tayi tace "me zakayi da lemon tsami a wannan tsohon Daren?"

Sosa kanshi yayi yarasa mema zaice mata, cikin jin kunya yace "Mommy nakira wayar my Deela bata d'aukaba"

Umma dariya tayi Dan taganoshi, tace "ok kayi hakuri ai gobe za'a kawo maka itako my son"

Murmushi yayi Wanda yake ara mishi kyau ya rungume Umma yace "I love you my Mom"

Shafa kanshi tayi tace "gud nyt my son, karka sha lemon tsamin dayawa zai iya kawo maka illah kayita sallah kawai kaji"

Wani irin kunyan Umma yaji a hankali yarab'a ta gefenta yawuce baice komai ba.

_jiddah ce...✍️_

08144818849[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 11*

    ~Yana shiga d'aki ya d'ura cup d'in a bakinshi saida yayi tass kafin ya sauke, Runtse idonshi yayi yace "Astaghfurullah" kwanciya yayi ya jawo filo tareda d'aura kanshi ya lumshe idonshi yana tunanin Fadila har bacci me dad'i ya d'aukeshi, baiyi nisa ba yaji ana d'an bubbugashi bud'e idonshi yayi Wanda ya kankance sabida bacci yana kallon wanda ya tasheshi daga bacci Abdul yagani yarike ciki yana dariya "kai are you mad?"

Abdul kara tsuntsurewa yayi da dariya yace "yanzu tsabar jaraba saida kasha lemon tsami kafin kayi bacci? Kai Allah dai ya shirya yaran zamani, gobe da safe zamu kawo maka ita kaga sai ayi till down" sake kwashewa yayi da dariya kafin ya kwanta akan gado, Kamal kallonshi kawai yakeyi idonshi harya fara kawo ruwa kuka yafarayiwa Abdul kamar karamin yaro, Abdul jinshi yana kuka yasashi tashi yana tambayarshi lafiya?

Kamal kuka yakara fashewa dashi hankalin Abdul yatashi ganin Kamal yana kuka, janyoshi jikinshi yayi yana lallashinshi a hankali Kamal yafara sauke ajiyar zuciya har bacci ya d'aukeshi, saida Abdul yaji yayi nauyi kad'an alamar bacci yasashi d'agoshi ya kwantar ya rufashi da bargo yana mamakin meya sashi kuka, shima kwanciya yayi a gefenshi har bacci ya d'aukesu.

_Fadila_

       ~Bacci take sosai a cikin jirgin da aka kwashesu, saida suka iso wani kasa kafin tabud'e idonta Wanda sukayi mata nauyi, a hankali tajuya tana kallon wata kyakkyawar yarinya wacce bazata wuce sa'ar Amrah ba tana kuka kamar ranta zai fita, cikin mamaki Fadila tace "kukan me kikeyi Kanwata kema kimzo Aurenane? Yanzu muka taso daga wurin dinner ina Yaya Kamal nawa yake?"

Yarinyan ta d'ago kanta idonta yayi ja kamar gauta fuskanta shab'e shab'e da hawaye cikin muryar kuka tace "Nima ban sanki ba a cikin jirgin naganki kuma mutanennan mugayene tun d'azu suke dukan mutane a cikin jirginnan  nima sun hanani magana satoni sukayi" ta karashe maganar tana kuka sosai, Fadila rikota tayi cikin tashin hankali da tsananin mamaki tace "ina zasu kaimu? Nifa daga wurin kamun Aurena na tashi baki ganni da kayan Amare ba?"

Wani mutum ne baki kato ya iso wurin yana washe hakwara yace "yammata kin tashi kalau? Ai tun d'azu kike bacci, oga yace abaki kulawa me kyau sabida zaki kawo kud'i daga ganinki" wani abinci yamika mata a cikin bakar leda, Fadila cikin tashin hankali tace "bawan Allah ina zaku kaimu?"

Washe hakwara Yakuma yi yace "idan oga yazo saiki tambayeshi kinga bake kad'ai bace ga mata sunfi dubu a jirginnan" waigawa tayi ta kalli yanda yammata suke kwance a cikin jirgin fuskokinsu duk ya bushe da hawaye sun jiggita sosai kowa ya lankwane sabida wahala, wani irin sauti zuciyarta tabata, cikin tsananin firgici ta mike da gudu zatabar cikin jirgin, yarinyar gefentace tariko ta tace "karki tafi kibarni Dan Allah ban saba da kowa ba saiki, please ki taimakamin ni Kanwarki ce"

Jikin Fadila ne yayi mugun sanyi jin tace mata ita Kanwarta ce, tsayawa tayi tama rasa me zata farayi, ganin batada mafita yasa ta zube a cikin jirgin tana ihu sai kiran Amrah da Kamal kawai takeyi, jin muryan mutum a kanta yana mata tsawa yasata d'ago kanta Dan ganin ko wayene, guyson tagani ya had'e gira yana zuba mata harara da sauri ta share hawayenta tace "Guyson Dan Allah kafita dani a wannan jirgin ka kaini wurin Amrah"

Wani mugun kallo ta zuba mata kafin cikin tsawa yace "wace Amrah kike nufi? Wancan kanwar taki ai tana can sunacin Amarci da Kamal kuma itace ta bani kud'i akan inyi duk yanda naso dake burinta kawai ta auri Kamal sabida tajima da sonshi a ranta, kuma idan bakyason in kasheki karki kara bud'emin wannan bakin naki domin banida imani kasheki zanyi in binneki babu Wanda ya isa ya kamani" Ciro wata 'yar karamar bindiga yayi ya nuna mata yace "kin gani ko? Akwai bullet aciki sosai guda d'ayama ya isheki"

Fadila ganin bindiga yasa jikinta yafara rawa a hankali ta juya ta rungume yarinyar datake gefenta tana faman sharan kwalla,

Guyson yace "nasan kinason kisan me zamuyi daku ko? Kiduba nan kigani 'yammatane sunfi dubu zamu akwai yaran masu kud'i musamman wannan na gefen naki sannan akwai yaran talakawa zamuyi Sana'a ne daku, domin zamu kaiku kasar Sudan akwai alhazawa da sauran masu kud'i suna zuwa su zab'i wacce sukeso, sabida haka ki kama kanki"

Yana fad'an haka yabar wurin fuskarshe sak na mugaye,

Fadila kankame yarinyar tayi kuka ma yaki zuwa mata, sai ware ido kawai take tanajin zuciyarta kamar zai fasa kirjinta yafito, a hankali yarinyar tafara kokarin zame jikinta, Fadila da sauri ta dad'a rungumarta muryanta yana rawa tace "please kibarni a jikinki karki cireni idan kin cireni kirjina zai fashe, kitaimakamin ki rungumeni ko zanji dad'i"

Wani irin kuka ne yazo mata Wanda babu sauti, yarinyar ganin haka yasa itama ta rungume Fadila tana kuka, a hankali tafara taping na bayanta har taji bugun zuciyarta yafara raguwa.

     "Amrah!! Amrah!!!" Shine kad'ai abinda Fadila take fad'a, da sauri yarinyar tace "na'am waye yafad'a miki sunana? Kodai kin sanni ne?"

Fadila ture yarinyar tayi a jikinta tace "meye sunanki?"

Yarinyar tace "Sunana Amrah Amma Daddynmu yana cemin Babyn Yaya, sabida yayana dayake sona sosai, sunshi Abdulkarim, sunan Daddynmu Alh Mamman me kud'i, sunan mommynmu kuma Hauwa muna Abuja da zama a unguwar GRA wannan mugun yaje wurin daddyna ya nemi aiki harya samu shine yasaceni, yanzu babu Wanda yasan inda nake a gidanmu" Fadila zuba mata manyan idanunta tayi ganin yanda take kuka abin yabaiwa Fadila tausayi yarinya arama at this age ta tsaya tana irin wannan kukan ai zai kawo mata Matsala, a hankali ta janyota jikinta tana lallashinta harta fara sauke ajiyar zuciya, bayan Minti talatin jirgin ya tsaya, bindiga Guyson yaciro yanunawa kowa yace "idan kuka nuna satoku nayi wallahi saina kasheku gaba d'aya"

Shiru sukayi kowacce jikinta yana rawa, 'yammat guda Hamsin ya nuna yace sufita sauran za'a raba musu gari, Fadila sai Roman Allah take yasa kada Surabata da wannan Amrahn, itama b'angaren Amrah hakane tanata Addu'a kamar da wasa sai aka nunasu tare, Fifa sukayi a jirgin duk jikinsu ba kwari sakamakon rashin cin abinci dasukayi, Hannun Amrah cikin na Fadila sauran 'yamnatan suna tsaye a gefe, guyson ne yafito ya yashiga dasu wani babban gida me d'auke da d'akuna manya manya da katifu biyar biyar a ciki, d'akin varanda ne babu ko albarkacin ledan d'aki, katifar wani bedsheets masu datti aka shinfida akai, sai toilet guda biyar a kowani d'akin wanda suna shiga warinsu ne yafarayi musu maraba, bindiga yaciro kafin yabaiwa kowa masaukinta, Fadila tsayawa tayi tana kallon gadon da aka nuna mata Wanda zata rika kwana akai, wasu zafafan hawayene yafara bin kumatunta "Amrah meyasa kikayi min haka? Me nayi miki?" Rife bakinta tayi da hannunta tana wani irin kuka Wanda ita kad'ai tasan irin zafin dayakeyi mata a zuciya kafin ya sauko fuskarta, dafata akayi da Sauri tashare hawayen daya fito a fuskarta tajuya, ganin Amrah ce yasa tad'anyi murmushi "meyasa kike kuka?"

Fadila tace "ba komai Babyn Yaya"

Kallonta tayi tace "karki b'oyemin komai sister kinji?"

Gyad'a mata kai Fadila tayi har yanzu hawaye bai daina fita a idonta ba, hannu Babyn tasa tana share mata itama hawayen yanabin fuskarta, Fadila ma share mata hawayen tayi ta sakar mata murmushi Wanda takejin yafi mata kuka ciwo, hannunta taja takaita daidai katifar da aka nuna mata, ajeta tayi a gefen gadon tace "zauna Babyn Yaya zan gyara miki wurin kwanciyarki domin naga baki saba da aikin wahala ba"

Murmushi Amrah tayi mata tace "zan rika kiranki da Adda kin yadda?"

Shafa fuskarta Fadila tayi tace "na yadda ke kuma zan kiraki da Babyn Yaya"

Kallonta tayi tace "meyasa bazaki kirani da Amrah ba?"

Wasu hawaye masu d'umine suka fara bin kumatun Fadila da sauri ta juya ta sharesu cikin dabara tace "banason na kiraki da Amrah sabida yana tunamin da Kanwata wacce nake sonta fiye da kaina...." Da sauri ta share hawayen dasuka zuba mata a ido, Amrah tarikota tace "shikenan stop crying"

Fadila shiru tayi tafara gyara mata katifar, tana gamawa itama taje tagyara nata sannan sukayi alwala a toilet d'in kowa ta shinfid'a d'an kwalinta sukayi sallah, bayan sun idar da sallah ne Fadila tabi duk 'yammatan d'akin tana gaidasu tareda tambayar sunayensu dakuma garinsu, kowa yayi mata bayani suna cikin haka Guyson yashigo tareda wasu mutane bakake dogaye masu jiki da jajayen idanu, tsitt d'akin yayi kowa ya maida hankalinshi akan guyson, wani roba yamikawa Fadila med'an fad'i yace ga wannan kuyi kokarin ganin ya isheku idan ba hakaba zaku zauna da yunwa sannan Ku shirya anjima da dare wasu zasuzo domin zab'an wacce tayi musu" yana fad'an haka suka juya suka tafi, da sauri Fadila ta maida hankalita kan abincin daya bata, wani shinkafa ne da aka dafashi babu ko mai balle yaji gashi kuma abincin kad'an su Biyar a d'akin tayaya abincinnan zai ishesu, juyawa tayi wurin sauran 'yammatan tace "kuzo kuci nikam a koshe nake"

      "Babyn Yaya ne tafashe da kuka tana kallon wani irin busashen abinci a cikin kwano, ita ina zata iyacin wannan abin?

Fadila ce ta b'oye damuwan dayake fuskarta ta janyo Babyn Yaya jikinta tanad'an murmushi ta d'ibo abincin takai bakinta "haa"

Kallonta Baby tayi takara fashewa da wani irin kuka tace "Adda bazan iyacin wannan abin ba"

Fadila da tausayin yarinyar yashiga zuciyanta ta rikota cikin muryan lallashi tace "Babyn Yaya ki daure kici koda kad'anne banaso kizauna da yunwa kinji ko?"

Baby share idonta tayi ta rufe idonta da kyar ta karb'i abincin, sauran 'yammatan ma saukowa sukayi suka faraci cikin yunwa da gajiya, abincin ko Rabin isansu baiyi ba haka suka hakura kowacce tasha ruwa, banda Fadila wacce tayi tagumi tana tunanin gida, Mikewa tayi ta kwanta akan gado tana kuka kamar ranta zai fita a hankali cikin kuka tace "My Kamal kada kayi haka, kada kuci Amana na please Amrah ta haramta a gareka nifa yayarta ce, Amrah karkiyi Dan Allah kitasheni daga baccin danake kicemin mafarki nakeyi Amrah"  riko zanin gadon tayi da karfi tanajin zuciyarta kamar wuta, Ji tayi an fad'a a kanta ana kuka, da sauri ta juya taga Babyn Yaya tana kuka, komawa tayi ta kwanta taci gaba da kukanta Babyn Yaya tace

        "Kiyi kuka Adda kiyi kuka sabida rahamane idan kinyi kuka zuciyarki zata warke, kiyi kuka Adda" Tafad'a itama tana kuka me ratsa zuciya, Fadila jin kalaman Baby yasata kara fashewa da kukan, saida yaji zuciyarta yana Neman yin bindiga yasata fara rage kukan tana sauke ajiyar zuciya lokacin Baby har bacci ya d'auketa.

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 12*

    

       ~Washe gari kwalliya akayiwa Amrah tayi kyau bana wasa ba saidai tana d'an nuna damuwa a fuskarta sabida gudun zargi, Unty Sadiya ce tashigo d'akin jikinta a mace sosai domin ita jiya ko baccin kirki batayi ba tana tunanin Fadila idanunta sun kumbura sosai, zama tayi a gefen gadon tana kallon kwalliyan da akeyiwa Amrah, Amrah ce ta kalli Unty Sadiya tace "Unty wai inji Inna Falmata kibani maganin da ake baiwa Adda Fadila wai kada a kaini haka babu wani shiri"

Wani irin kallon mamaki da bakin ciki Unty Sadiya tabita dashi, cikin disasshiyar murya tace "Amrah bakida hankali yayarki tanacan bakisan inda takeba kizo kina maganar magani? Wallahi kin bani mamaki Amrah kuma bazan bada maganin ba kitashi ki kwata tinda naga ba kunya kikeda shi ba" Amrah turo baki tayi tana b'allawa Unty harara jitake kamar ta shaketa ta mutu, kawar da kanta tayi ta murgud'a baki, bayan Isha akazo tafiya da Amarya kowa ya tsaya yayi jigum gidansu Amrah babu Wanda zaka kalli fuskarshi kaga yana cikin farin ciki, Mama kuka take tsakani da Allah Tarasa ta ina zata fara yiwa su Kamal da Mamanshi wannan zancen, Unty ce zaune a gefenta tana tayata kuka cikin sheshekar kuka tace "ya zanyi Sadiya? Fadila ta zubar mana da mutunci gashi nafad'awa Abbansu yace insan yanda zanyi tunda nice nake zama dasu agida nice na lalata ta, Yaya zanyi Sadiya?"

Unty itama kuka takeyi tace "Mama afito afad'a musu gaskiya wata kilama bayason Amrah maybe ma ya saketa" cikin firgici Amrah ta karaso cikin d'akin tana kallon Unty Sadiya tace "Unty idan an fad'a musu mutane kowa zaiji, kuma dole zasu zagi Adda Fadila kinga nikuma bazanso a zagemin yaya ba"

Unty Sadiya tace "hakane to amma tinda hakan yafi saimu kaiki can d'in idan yaso duk abinda yafaru saimu d'au kaddara"

Wani irin miskilin murmushi Amrah ta saki daganan ta sunkuyar da kanta tana tunanin Kamal.

    "Sai karfe tara aka fito da Amarya bayan an gama yi mata fad'a da nasiha, Maman Kamal ce tashigo da kanta ta riko hannunta takaita har cikin motar Kamal inda ya sunkuyar da kanshi tun d'azu yana jiran fitowar Fadilarshi wacce rabomshi dajin muryanta tin ranar kamu, hakan ba karamin horashi yayi ba, zama bud'e motar tayi ta zauna a gefenshi tana kamshin turare me dad'i da sanyaya zuciya, d'ago kanta tayi domin kallon meyakeyi, kallonshi takeyi yayi kyau cikin shadda brown colour Wanda yaji zubi da hula brown sai kamshi yakeyi, bin hannunshi tayi da kallo Wanda yake d'aure da agogo na diamond baki gashi kwance akai, d'ago kanshi yayi yanason ganin fuskarta da sauri ta janye gyallen ta ta rufe fuskarta dashi, kallonta yayi ya langwab'ar da kai kamar zaiyi kuka yace "My Deela please kibud'emin fuskarki in gani wallahi na horu iya horuwa, rashin kallon fuskarki ba karamin tashin hankali bane a gareni" matsowa yayi dab da ita har yana jiyo bugun zuciyarta, riko hannunta yayi Wanda yaji lalle ja da baki sai yalki yake, a hankali yake shafa hannun yace "I love this"

Amrah murmushi ta saki tacikin mayafinta, kara matsowa yayi dab da ita kamar zai shigar da ita ciki, da sauri taja a baya jin yana Neman shiga jikinta, murmushi yayi sannan yad'an matsa yana kallon yanda jikinta yake b'ari, Knocking na kofar akayi ta gefen Amrah kyawawan hannunta tasa ta bud'e, Abdul ne ya lek'o yana d'an dariya yace "ango me kakeyi ne har yanzu baka ja motar ba?"

Kamal kawar da kanshi yayi dan yasan halin Abdul tsarai yanzu kalan wani iskancine ya janyoshi nan, Abdul dariya yakumayi yace "Amarya wannan fa ba hakurine dashi ba kice mishi ya ja motar mutane sun gaji"

Amrah dad'a jan mayafin tayi batace komai ba saima zuciyarta datake bugu kamar zata fasa kirjinta ta fito, Kamal ne yarufe marfin motar yasa key ya tada sai gidansu, sauran motocin ma suka fara bin bayanshi gwanin shawa'a.

      "Fadila ganin Baby tayi bacci yasata gyara mata kwanciyar ta cire hijabinta ta lullub'ata dashi, haka kawai taji yarinyar tana bata tausayi domin daka ganta zakasan bata saba da wahala ba jikinta ma yanuna Ajebo ce 'yar gidan masu kud'i, zama tayi a gefenta tabuga tagumi tana tunani,

Bayan minti Goma saiga su guyson da wasu mutane masu kud'i manya wad'anda suka gaji da kud'i, Fadila jitayi zuciyarta ta buga da sauri ta kwanta lamo a bayan Baby tayi kamar tana bacci, guyson yace "Alhaji zaku iya zab'an duk wacce tayi muku"

Washe hakwara sukayi kowa yana kallon cikin d'akin Guyson yace "Kai duk kutashi kuzo nan" tashi sukayi kowacce cikin tsoro da fargaba, Fadilace ta riko hannun Baby sosai tanajin tsinkewar zuciya, karasowa wurinsu guyson yayi yace "ku bazaku tashi ba?" Da karfi Fadila tarike hannun Baby tana addu'a acikin zuciyarta, wani mutum ne Wanda ya zubawa Fadila ido yace.

    "Guyson karka damu wannan tashiga zuciyana ko gobe zanzo saimu tafi abata abinci da sabulai masu kyau tayi wanka dashi gobe" jikin Fadida ne yafara rawa kamar mazari, ta tsinkayo muryan wani babba yana cewa "nikam yarinyarnan karamar tayimin a gyarata itama gobe zamu tafi tare" yafad'a yana kallon Baby wacce take baccinta peacefully, Saida suka d'ibi 'yammata sunkai goma kafin suka juya suka tafi 'yammatan sai kuka suke basaso, Fadila jitayi kamar ta tashi ta kwato su amma ba hali sai kuka kawai takeyi tarasa yaya zatayi da rayuwarta, cikin bakin ciki daya taru yayiwa zuciyarta yawa tace "Amrah me nayi miki kika sani cikin wannan rayuwar? Kin rabani da Kamal kin rabani da iyayena kin kawoni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login