Showing 81001 words to 84000 words out of 139192 words
/>
Nabila tace "waya sani? Ko haɗa baki kukayi dashi kuzo ku cutar da zuri'armu, shi ai bazai faɗa ba kema bazaki faɗa ba nasan tabbas akwai alaƙa tsakaninku ku kukasan me kuke ƙullawa kuma nima mind you ilimin sanin ɗan Adam nayi a kasar london kinga babu abinda ze gagareni sani acikin jama'a wawiya ƙazama matsiyaciya"
Tass kakeji a fuskar Nabila Fadila ce ta wanketa da mari, cikin tsiwa Nabila tace "ni kika mara..." kafin takarasa Fadila takara ɗauketa da wani marin, cikin riƙe ƙunci tace "ni kika mara ba..." wani marin takuma ɗauketa dashi, sannan tace "kina buɗe bakinki ina kara danna miki wani marin ba kince ke bakida kunya ba? To ni Fadila nafiki rashin kunya ba garani ba Matsiyaciya ce ke kumafa? Karuwa ballagaza me kuɗi"
Nabila tace "niba karuwa..."
Wani marin Fadila takuma bata wanda yasa tayi baya baya zata faɗi da sauri ya tarota yana riketa, Abdul ne daya shigo ɗakin yanaso yakira Baby yatarar da Fadila tanata wanke Nabila da Mari, ranshi idan yayi dubu to tabbas ya ɓaci, cikin hasala yayi kan Fadila yafara wanketa da mari, Baby se janshi take tana kuka da bashi hakuri, juyawa yayi ya saukewa Baby ma marin da saida tafaɗi da baya tayi kan gado, Fadila takiyin ihu dukda marin yana shiganta amma ta busar da zuciyarta takiyin koda motsi ne, saida yagama marinta kafin yarike kunnenta yace "idan kika kuma taɓamin ƴar uwa saina kasheki" yana sakinta tayi kan Nabila da gudu atake ta zubar da ita akasa tafara naushinta da iya karfin da Allah yabata, Nabila sai ihu take ita kuma Fadila tana dukanta ne da haushin dayake tare da ita, Abdul ne yayi kanta yana ƙoƙarin janye Nabila datake ta ihu, shi yarasa a ina yarinyarnan tasamu ƙarfi haka, janta yake amma ina sai dukan Nabila take, Baby ma tazo tana janta sun kasa janyeta, hakuri Nabila tafara bata amma Fadila akwai bakin zuciya idan ranta ya ɓaci kamar me jinnu, saida numfashin Nabila yafara yankewa kafin Abdul yasa iya karfinshi ya tureta, gefe tafaɗi tana sakin numfashi da ƙarfi sannan tasake yunƙura zatayi kan Nabila da Abdul ya rungume, ganin haka yasa Nabila sakinshi da gudu tayi waje, Fadila ma a zuciye ta juya tawuce Bedroom ranta a mugun ɓace, Baby ce tabi bayanta da tsawa Fadila tace "Fita dan Allah!!!" ganin yanda idonta yayi jaa yasa Baby juyawa jiki a sanyaye tabar ɗakin gashi lokacin walima yayi tarasa yacce zatayi, tana zuwa falo taɗau wayarta tayi dialing number ɗin Dady, gaisawa sukayi sannan tace "Dady kayiwa Adda Fadila magana taki zuwa wurin walima"
Dady yace "meyasa?" Baby tace "Dady rantane kawai a ɓace"
Kashe wayar Dady yayi sannan yayi dialing number ɗin Fadila, Fadila dake zaune a gefen gado ta kwantar da kanta akan filo sai kuka take rabzawa magangun Nabila sun mugun ɓata mata rai, taji wayarta yana ringing, sharewa tayi dan batasan me kiraba a halin yanzu bazata iya magana ba, kusan miss calls biyar Dady yayi mata bata ɗaga ba, Dady ya ruɗe ganin yana kiran Fadila miss call biyar bata ɗaukaba, bata taɓa yimishi haka ba, number ɗin Abdul yakira bugu ɗaya ya ɗauka, "hello Dady" cikin ɓacin rai Dady yace "meya samu Fadila?"
Abdul yace "ban saniba Dady"
"Allah yasa kada kasani kaje yanzu kace mata taɗau kirana zamuyi magana" "To Dady"
Hanyar ɗakinta yabi yaje ya sameta tahaɗa kai da filo tana kuka, jikinshi ne yaɗanyi sanyi, amma tunawa da dukan datayiwa Nabila yasa yajima baya tausayinta, akanta ya tsaya yace "Ke!!!" ɗago kanta tayi da idanunta da sukayi jaa ta zuba mishi, wani rass yaji gabanshi yayi, saida zuciyarshi tabada sauti dum kafin ya daure yace "Dady yace kiɗau kiranshi yanzu yanzu saura kuma ki faɗa mishi abinda yafaru"
Share hawayenta tayi taɗau wayarta, daidai da lokacin da Dady yakirata, ɗauka tayi taɗan sauka kasa tace "Hello Dady"
"Lafiyana kalau bacci nakeyi shiyasa"
Dady yace "to tashi ki shirya yanzu za'a fara walima kinji"
Giɗa kanta tayi taɗan share hawayen nata tace "to Dady yanzu ma kuwa"
Dady ne yafara janta da hira harta warware tana dariya kamar ba itaba, Abdul dayake tsaye yanata kallonta yayi mamakin yacce ta sake tanata zubawa Dady surutu kamar babu abinda yafaru, Dady ne yace "To ranar litinin zaki fara zuwa aiki"
Daka tsalle tayi ta sauko kasa tana murna, ganin haka yasa Dady yace "to tashi dai ki shirya yanzu kinji" da murnarta tafara shiryawa tana gyara kwalliyarta daya cakuɓe da hawaye, kallonta Abdul kawai yake sannan yajuya yafice batareda yace mata komai ba, leshi tasa me tsadan gaske ta ɗaura kanta tasa ɗan kunnen gold da Dady yasa mata acikin akwatinta, Alkyabba taɗaura golding color tasa wani takalmi high hill cover, posa ta ɗauko wani karami me yalƙi da ado ado ajikin, tarike a hannunta turare ta feshe jikinta dashi sai kamshi take zubawa, kyau kamar ze zuba a wurin, cikin fara'a ta ɗauko wayarta tayi hanyar Falo, Ihu Baby tayi ta rungume Fadila ganin yacce Fadila tayi kyau kamar asace a gudu, Fadila ma rungumeta tayi suna dariya, Pinky dake zaune tasha pink ɗin dogon riga da dark blue na gelle tayi makeup me kyau itama sai murmushi take dan tanajin nauyin tashi taje itama dan tana ganin kamar Fadila zata daketa itama tunda yayarta taja musu, Fadila ganin haka yasa ta ɗagawa Pinky hannu alamar tazo, pinky mikewa tayi a hankali itama taje Fadila janta tayi itama tafaɗa jikinsu suna dariya, Baby ce taɗan ɗago tace "Amma miye sirrin dariyannan? Naga dai yaya yashiga ɗakin kuma yafito yana dariya kodai..."
Bugin bakinta Fadila tayi tace "jekisa anko kizo muje an fara walima"
Da sauri Baby taje ta shirya itama cikin Pink ɗin dogon riga da dark blue ɗin gelle kyau tayi sosai kamar kasace ka gudu, wayoyinsu iphone suka rike a hannunsu kafin suka nufi wurin walima fuskar Fadila rufeda Alkyabba, wurin zamansu aka tanada musu, Abdul ne suka fito shida sauran abokanshi suma sunyi anko cikin blue ɗin shadda, manyan mata sunyi dressing na atamfa pink da gelle blue wurin yayi kyau sosai, Nabila ma data shirya cikin Dogon riga pink ta ɗaura kanta da blue ɗin ɗan kwali, ko gyalle bata yafaba, sai fuskarta datayi jaa sosai dukda tashafa hoda amma be ɓoye ba, gefe tasamu ta zauna, badan Dady ne yace tazoba wallahi da babu abinda ze sata ta tsaya anan, taro yayi taro an fara gudanar da walima, Abdul ne yaciro wayarshi yakira Kabir "meyasa baka fito ba har yanzu?" Kabir yace "Wallahi dude haka kawai zuciyata take tsinkewa inaji kamar wani abu yana shirin faruwa dani"
Abdul yace "Addu'a ai itace maganin komai"
Kabir yace "to babu komai ina fitowa"
A hankali yake takunshi me ɗauke da sarauta harya karasa wurin Abdul ya zauna a gefe jikinshi duk amace, Abdul ne ya sakar mishi murmushi shima yamayar mishi, Dady da momy sun karaso wurin an fara wa'azi wa Amarya da ango dakuma nasiha da karatun alkur'ani me girma, Baby datake sauri ga drinks a hannunta ledan yaɗan yage sai kokarin tarewa take amma ina drinks ɗin ya zube daidai bakin kofa suka fara watsewa, Kabir daya mike yana amsa kiran me martaba, saida yagama yanufi hanyar komawa, da gudu tabi big colan daidai gabanshi ya tsayar da kafarshi, a sunkuye tazo zata ɗauka da saure ya ɗauke yabuɗe, buɗe bakinshi yayi yaɗaga sama yafara sha, mikewa tayi tana kallonshi, yana sauke goran ta waro ido waje, shima ido yawaro yana kallonta, sunkai minti biyar suna kallon juna, bakinta yana rawa tace "ya.ya.yariiimaa"
Cikin murna shima yace "Amrah. Kece?"
Baby tsabar murna jitake kamar ta rungumeshi amma tasan hakan be hallata ba... Kafin takarasa tunanin taji ya rungumeta tsamm yana dariyan farin ciki, shiru tayi itama a hankali tasa hannunta ta rungumeshi, saida yakai minti biyar ahaka kafin yaɗan saketa tareda riƙo hannunta yace "meya kawoki nan?"
Baby tace "Auren yayana ake"
Kallonta yayi sosai yace "nima auren abokina nazo ai Abdul"
Dariya tayi tace "to ai shine yayana"
Daɗa rungumeta yayi yace "amma meyasa bansan hakan ba Amrah? Na nemeki ban sameki ba, nasan dana sani dana haɗu da Fadila"
Rass gaban Baby yafaɗi, a hankali ta janye jikinta ta sunkuyar da kanta ƙasa, Yarima bakinshi yana rawa yace "Please karki faɗamin maganar da babu daɗi karki cemin wani abu yafaru da ita, kinsan bazan iya ɗauka ba mutuwa zanyi please"
Baby da takeji kamar zuciyarta ze faɗo tsabar tsorata yasa taɗan sunkuyar da kanta again, Yarima baya baya yafara yana girgiza mata kai, "dan Allah kada kicemin wani abu mumuna ya sameta"
Baby hawayene yafara bin ƙuncinta ɗago fuskarta tayi tana kallon cikin idonshi, tasani zeji zafi sosai idan tace mishi Fadila tayi Aure to amma ya zatayi? Dolene tafaɗa mishi gaskiya, da sauri yariƙo kafaɗarta yana girgizata yace "Dan Allah kifaɗamin meya samu Fadila ta?"
Baby cikin kuka tace "Adda Fadila tayi Aure Yarima kuma itace ta Auri Yaya Abdul"
Tana faɗan haka tayi hanyar cikin gida, fizgota yayi da iya karfinshi, waro ido tayi ganin zata faɗi da sauri ya tarota yariketa gam har tanajin zafi, girgiza kanshi yake kamar mahaukaci sabon kamu, Baby data tsorata tafara kokarin ihu, rufe bakinta yayi da hannunshi da wani murya me amo yace "Impossible"
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 55*
~Baby data tsorata tana waro ido tace "wal..wallahi da gaske nike itace ta auri yaya Abdul" cilli yayi da ita gefe, taga taga tayi tafaɗi kasa, a hankali ta miƙe tana kaɗe jikinta daya ɗanyi ƙura, Yarima da idonshi yayi jaa sosai jijiyoyin kanshi suka mimmiƙe sai safa da marwa yake a wurin, juyowa yayi ya kalli Baby waro ido tayi ganin hawaye yana kwaranya daga idanunshi, da sauri ta matso wurinshi tana bashi hakuri, ɗaga hannunshi yayi sama yace "Stay away from me please"
Baby batama saurareshi ba ta matso wurinshi tana goge mishi hawayen da suka ɓata mishi fuska, ɗan tureta yayi yace "Is Okay ba komai amma bakuyimin daidai ba, meyasa baku faɗamin ba koda ta wayane?"
Baby tace "Nayi zaton ta faɗa maka dan itama ba son auren takeba shima yaya ba son auren yakeba, dady ne yahaɗa"
Yarima cikin kuka yace "kiyimin alkawarin abu guda ɗaya"
Baby tace "insha Allah nayi maka alkawari koda banji na menene ba"
Riƙo hannunta yayi yace "kiyimin alkawarin bazaki faɗawa kowa abinda yake faruwa ba"
Baby shiru tayi naɗan lokaci tana tunani kafin tace "harda Dady?"
Yarima yace "Eh"
Tace "Tom nayi maka alkawari babu wanda zan faɗawa"
Ɗan dariyan karfin hali yayi yana goge idonshi, yace "tashi to muje ko?"
Baby tace "Tom"
A hankali suke tafiya Baby tana riƙe da drinks ɗin shikuma jikinshi duk a sake jiyake hajijiya yana neman kada shi, wuri yasamu yaɗan zauna tareda dafe kanshi, ɗan durkusawa tayi tace "Kada kasa damuwa a ranka please"
Murmushi yayi mata wanda yafi kuka ciwo kafin yaɗan girgiza kanshi alamar tom sannan yace "dan Allah kije ki buɗemin fuskarta nayi mata kallon ƙarshe"
Baby bata kawo komai ba tace "tom"
Wurin Fadila tanufa, fadila tana ganin itace tace "ina kika shiga?"
Baby tace "buɗe fuskar taki ai walimar takusa karewa ko?"
Fadila tace "kunya nikeji wallah"
Janye hulan alkyabban Baby tayi atake fuskarta me sheki da ɗaukan hankali ya bayyana, kokarin jan hulan take amma Baby tahana.
Ido yazuba mata daga inda yake yana kallon yacce tayi kyau harma tafi da kyau da murjewa, wasu zafafan hawayene suka cika mishi ido hanki yaciro ya goge a hankali,
Fadila tace "bakida hankali ne?"
Baby tace "kalli can"
A hankali Fadila ta ɗago kanta tana kalle kalle, Baby tace "ba nan ba can nace"
Ɗago kanta tayi takalli inda Baby take nuna Mata, a kiɗime ta waro ido tana kallon Yarima daya zuba mata ido yana murmushi, saurin rufe idonta tayi, Baby tace "meya faru?"
Fadila tace "Ghost"
Ɗan Dariya Baby tayi tace "ke dalla shine ba Ghost ba"
Fadila mikewa tayi zataje wurinshi da sauri Baby tarike hannunta tace "kadafa kimanta yanzu kinada aure"
A hankali takoma ta zauna saide har yanzu idonsu a sarƙe yake dana juna"
Jikintane yayi sanyi sosai "to meya kawoshi aurenta?"
Baby tace "abokin yaya Abdul ne ashe yayi sati a gidanmu bamu saniba"
Kallon mamaki Fadila tayi mata a zuciyarta tace "wallahi dana san yana gidanmu damun gudu dashi munje munyi aurenmu amma ƙaddara tariga fata"
Baby tace "nasan tunanin dakike a zuciyarki amma fa kirinƙa tunawa kinada aure yanzu, haramun ne ki tsaya kina tunanin wani can daban"
Shiru tayi.
Nabila a hankali tamike taje wurin Abdul riƙo hannunshi tayi tace "Yaya Abdul ya sunan Wancan yaron?"
Abdul yace "ok Kabir kike nufi?"
Tace "Koma menene nikam sunanshi nakeson sani dakuma labarinshi"
Abdul yace "banida time yanzu kibari saina samu time amma dai shi ɗan sarki ne"
Da mamaki tace "ɗan sarki?"
Abdul yace "kinga banida time yanzu"
Sakin hannunshi tayi takoma wurin zamanta, tasani ɗan wani matsiyaci bazai wulaƙanta ta haka ba, tabbas yasan meya taka, amma dukda haka ai MULƘI YAFI SARAUTA.
"Dan Allah kayi hakuri ka kyalemu koda kwana ɗayane muyi idan yazo zuwa gobe da safe saimu nemi wani gidan mukoma"
Amrah ce ta durkusa da gwiwowinta tana rokan mutumin daya riko casbi a hannu yakafa rawani dawani dogon ashwaki yana bada odan a fitar da kayansu zuwa waje, sai watsar da kayan ake kamar na mahaukata, Abba daya kwanta agefe Mama sai fifita shi take dan hawan jininshi ya tashi, yace "kira Amrah banaso tana rokanshi haka ba sauraranta zeyi ba kuma tanada ciki abin ze zame mata damuwa"
Mama a hankali tamike jikinta a sanyaye tanufi wurinda Amrah ta durƙusa Ta ɗagota, Amrah cikin muryan kuka tace "bakada tausayi ne? Inafa da ciki na durkusa maka ina rokanka, ina kakeso mu kwana dan Allah hasalima gidanfa namune ba naka ba meyasa kazama mugu..."
"Ke ki iya bakinki kada kikara zagina"
"An zageka kayi abinda zakayi ai nabika da lallama da girmamawa amma baka jini ba, kuma idan babba be rike girmanshi ba yaro hawa yake ya taka"
Casbin hannunshi yaɗaga ze coɗa mata rikewa tayi gam da iya karfinta saida ta watsar da casbin tace "idan ka sake ka taɓani wallahi zanyi maka sharrin da har jikokinka da tattaɓa kunnuwanka bazasu tsiraba, kaji nayi maka rantsuwa nafika rashin mutunci"
Gyara Rawaninshi yayi yace "bazanyi miki magana ba mara kunyan banza"
Amrah cikin hasala tace "kanada bakin dazaka kirani mara kunya? Gaka babban mara kunya amma kana zagin wani? Kawani kafa hula kamar tukunya"
Mama ce take janyeta amma Amrah ta dage sai masifa take, "Mama sakeni na koyawa mutuminnan hankali"
Da kyar Mama ta janyeta ta tarar musu wani keke Napep dayazo wucewa, Abba ma shiga yayi dan kanshi yana mugun ciwo, gidan Unty Sadiya mama tace suje, dafarko Amrah tace bazataje ba amma Mama ta matsa mata dole saida sukaje, Unty Sadiya dake zaune a falo tana kallo kasancewar Babansu Aisha yayi tafiya sukuma Aisha suna gidan Kakarsu taji ana buga mata ƙofa, tashi tayi taje bakin get tace "waye"
Muryar Mama taji tana cewa "mune Sadiya buɗe"
Buɗewa tayi tana dariya tace "laaa Mama da Abbba kune?"
Dariyanta ne ya ɓace ganin Amrah a bayansu, Mama tace "ba lokacin surutu bane mushiga dan Abban naku bayajin daɗi"
Shiga sukayi gaba ɗaya da Amrah wacce jikinta yazama kamar ƙanƙara tsabar sanyin dayayi, ƙafarta ma da kyar take jaa, a falo Mama ta kirga mata abinda yake faruwa, ran Unty Sadiya ya ɓaci sosai musamman da sukace an watsar musu da kayansu,
Waya takira tace aje a ɗebo kayan nasu zasu zauna a gidanta har su samu gidan haya, Abba yace "Aa baza'ayi hakaba kinada miji kuma dolene kibi umarninshi zuwa jibi zan nema mana gidan haya in Allah ya yadda, Amma nasan wannan abin yana faruwane sanadiyyar Fadila badan itaba na tabbata da muna cikin kwanciyar hankali, Amma dan Allah ku dubi wannan yarinyar yayi nuni da Amrah, Yarinyar nan tun bayan ɓatan Fadila batada kwanciyar hankali ku kalli yanda ta rame ta lalace Fadila baza kiga me kyah ba kije GAKI GA DUNIYAR"
Wani kallon da Unty Sadiya tayiwa Amrah yasa jikinta yafara rawa a hankali tace "am..am nikam bacci nakeji Mama"
Ɗaki Unty ta kaisu sannan ta nunawa Abba ɗakin daze zauna kafin sukayi hira da mama har sukaje suka kwanta.
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 56*
~Baby ya akayi bakisan cewa Yarima abokin Yaya Abdul bane? Kodai kin sani kika maidani doluwa?"
Fadila ce take tambayan Baby datake shirya kayanta zata koma gida dan Dady yakirata yace maza takoma gida yau, mutane sun daɗe da watsewa, Juyowa tayi tace "kin san ai bazan taɓa cutar dake ba"
Fadila tace "nasani amma yanayin Yarima yanuna kamar yana cikin damuwa"
Baby tace "ki tunada dai kinada aure yanzu"
Fadila tace "Aure, Aure, Aure da nayi magana sai kice inada aure tambayama sai kicemin inada aure dama nace miki ni bazawara ce?"
Baby tace "Allah ya huci zuciyarki Dady yace ranar monday zamu fara zuwa aiki a asibitinki me suna Fadilat Hospital"
Fadila taɗanja numfashi tace "babu abinda zan sakawa Dady dashi sai addu'a Amma yanzu ina cikin damuwa" hawaye ta goge da bayan hannunta sannan tace "Baby inaskn Yarima sosai kema shaidace bazan daure ganinshi acikin damuwa ba wallahi nakasa daurewa tun ɗazu sai tunaninshi nake, amma nayi alkawarin zan rike amanar da Dady yabani na cewa nakula mishi da ɗanshi dama ni bana samun abinda nakeso a rayuwa kullum faɗi nake bana tashi"
Baby ce ta zauna a gefenta tariko hannunta tace "Amma Adda kece fa kika cemin kin fara son Yaya dama karya kikemin"
Giɗa kai Fadila tayi tace "wallahi karya nake miki bana kaunarshi shi mugu ne yafison Nabila bani yakeso ba"
Baby ce takuma gyara zamanta tace "kicire wannan tunanin a ranki yaya bayason Nabila