Showing 120001 words to 123000 words out of 139192 words
amma wani ɓangaren yanace mata ta daure tashiga, buɗe kofar tayi da sallama a bakinta, shiga ciki tayi tace "Yaya kanata inane?"
Da sauri taja da baya ganin yanda suke zaune da Nabila, "innalillahi wa inna ilaihiraji'un,Hasbunallahu wa ni'imal wakil Allah karabamu da mugun ji da mugun gani" duk ta rikice ta ruɗe batayi zaton Kabir yanason Nabila ba gashi yau ta gansu sunashan soyayyarsu, Kabir daya lura mutum yashigo yace "waye?" jikin Baby ne yafara rawa, daurewa tayi ta goge hawayen daya zubo mata tashiga ciki tana murmushin dole, kawar da kanta tayi tace "barkanku dai"
Kabir yace "Bebi! Yakika tashi?"
Baby tace "lfy ga breakfast na kawo maka" juyawa tayi zata tafi Nabila tace "Darling! Baki ganni bane?"
Baby ɗan yaƙe tayi tace "Sorry Unty Nabila good morning"
Nabila tace "Morning how are you?"
Da sauri Baby tace "am fine" buɗe kofar tayi Nabila tace "Darling zo mana"
Taso taki amma bataso su fahimci tana kishi, komawa tayi cikin ɗakin tace "gani"
Nabila tace "Baby yanajin yunwa please serve him"
Baby tace "okay"
Kabir zuciyarshi tana tafarfasa amma yayi alkawarin bazai cewa Nabila ko kala ba, dan yafi kowa sanin ɓacin ranshi idan ranshi yaɓaci koshi baya iya controlling ɗin kanshi, Baby tana gama sa mishi tafita da sauri taje wurin motarta, shiga tayi idonta baya ganin hanya amma ta daure tafara tafiya akan titi tana tuki tana sharan kwalla, data eufe ido su take gani, da karfi ta buga sitiyarin motar tace "Cheaters" a hankali kuma takara cewa "meyasa nake ganin laifinsu? Laifina ne" hakadai ta rinka surutu harta isa gida, tana shiga ɗakonta ta rufe kanta tana fasa duk abinda yashafi glass watsar da sauran take, hawa gado tayi ta rinka wulli da pillows, kamar zararriya haka tadawo,
Nabila abincin ta ɗauko tabashi, kin karɓa yayi tayi dariya tace "Are you okay"
"Ki sauka kificemin daga gida before i loose my temper"
Dariya takuma yi kafin ta mike tace "sorry Baby kasan nasaba da jikin maza banida kunya ko kaɗan shiyasa, amma idan kaji zafi zaka iya faɗawa Dady bakason auren karuwa dan nifa banajin magana wannan kaɗanne daga aikina"
Kabir cikin zafi ya mike yace "okay kece karuwan? Okay let's see"
Hannunta yariko yafara janta zuwa cikin ɗakinshi, aɗan tsorace tace "what are you doing?"
Baiyi mata magana ba yaci gaba da jan Hannunta be ajiyeta ako inaba sai kan gadonshi, kashe wutan ɗakin yayi yace "you say you're prostitude right? So let's see"
Da sauri tafara jabaya tace "kaga malam kada kamin komai"
Wani dariya yayi yace "are you scared?"
Haɗe fuska tayi tamike zata fita, rikota yayi da karfin da Allah yabashi har saida tayi ihu kaɗan, matseta yayi da jikin bango ya shake wuyarta sai kakari take tana rarraba ido, ganin zai hallakata yasashi sakinta ya zauna bakin gado tareda dafe kanshi da hannu biyu yace "please get out"
Da sauri Nabila ta mike tana rike wuyanta saida takai bakin kofa ta buɗe murya tace "Allah ya isa ban yafeba"
Da gudu tafita taje wurin motarta, shikam ko motsi baiyi ba,
Kabir ne yaɗau wayarshi yadanna number ɗin Baby, ringing kusan biyar bata ɗaga ba, hankalinahi ne yatashi meyafaru? Kara kira yayi ta ɗaga sauke ajiyar zuciya yayi yace "Bebi meyafaru?"
Baby datake sheshekan kuka tace "babu kaina ke ciwo"
"Hmm Bebi zanzo anjima zamuyi magana kinji"
Giɗa kai tayi sannan ta kashe wayar,
Da mangrib ya shirya yaje gidansu, gaida Momy yayi sannan yaje ɗakin Baby, sallama yayi yaji babu amsa saida yayi sau uku kafin ya murɗa handle ɗin yashiga, Baby datake bacci cikin kayan data watsar ya tsaya yana kallonta, a hankali yafara tattara kayan yana maidasu mazauninsu, saida yagama yasamu wuri ya zauna yana kallon yanda take bacci hankali kwance, a hankali tafara buɗe idonta tana turo baki, ganin Kabir zaune a gefenta yasa ta tashi da sauri tace "Yaya yaushe kazo?"
Murmushi yayi mata yace "tashi kije kiyi alwala"
Tashi tayi tanaɗan rufe jikinta dan kayan yaɗan riketa, ɗauke kanshi yayi yafara danna wayarshi, saida tayi alwala tazo tayi salla kafin ta zauna a gefenshi tace "gani yaya"
Ajiye wayar yayi yana kallonta yace "Bebi! Inaso ki faɗamin gaskiya banaso ki ɓoyemin komai kinji?"
Giɗa mishi kai tayi, yace "Bebi kina sona?"
Jin tambayar tayi bambarakwai da sauri ta dukar da kai kasa, riko hannunta yayi yace "kada kiji kunyana kifaɗamin gaskiya kinji?"
Baby saida tayi shiru sosai kafin tace "Eh" tareda rufe fuskarta, Murmushi yayi yace "zaki aureni?"
Kallonshi tayi tace "Yaya to ai kana auren Unty Nabila"
"Forget about her zaki aureni?"
Baby tace "Eh"
Sakin hannunta yayi yace "kinsan naso Fadila amma hakan beyi ba Allah besa zata aureni ba, amma na tabbata ke zaki zama matata da yaddan Allah"
Murmushi takeyi kanta akasa yace "Baby zan tafi gobe zanzo wurin Dady nayi mishi magana dan Allah kada ki bani kunya a idon Dady kifito kifaɗa musu gaskiya kinji?"
Baby tace "tom"
Tashi yayi zai fita, hannunshi ta riko ya juyo yana kallonta, dukar da kai tayi tace "Um..yaya bakace kana sona ba"
Dariya kaɗan yayi yace "idan kikaga idona zaki fahimci komai"
Tace "ban ganeba gaskiya"
Yace "i love you so much Bebi"
Sakin hannunshi tayi, nan yafita Baby tafara tsalle acikin ɗakin tanajin daɗi, waya ta ɗauka takira number ɗin datayi saving da Darling! Fadila tana ɗagawa Baby tayi tsalle tace "Adda kina gida Gobe?"
Fadila da muryan bacci tace "ai babu aiki gobe ina gida, meyasaki murna haka?"
Baby tace "Adda sai nazo zan faɗa miki,
Kabir beji wani daɗi ba danshi soyayyar dayakewa Fadila me yawa ne.
"Kamar yacce kwanaki suke tafiya haka cikin jikin Amrah ma yake girma yau yazama saura wata biyu ta haihu da yaddan Allah, tana rainon cikin ne cikin kunci da tunani wannan ma Kulu tana yawanyi mata nasiha akan tarage yawan tunani kada ya haifo mata damuwa,
Haka dai take zama tayita tunani duk ta rame tayi baki.
"Kabir yaje wurin Dady yace shi gaskiya bayason Nabila yafison Baby, da farko Dady yaki yadda amma dayaga Baby tafara kuka shima Kabir ɗin kamar zaiyi kuka yasa yace ya yadda nan aka yanka biki nanda wata biyu,
Kabir da Baby suna soyayya yayinda Fadila tafara son Abdul sosai, shima Abdul yanaɗan sonta amma yafison yarinyar daya yi raping ɗinta tun tana karama, acikin kwanakin yaje yola a ɓoye batareda ya sanarwa kowa ba, ya nemeta ya nemi Km amma bai samu hakan ba, haka ya hakura yadawo gida yana cigaba da tunaninta.
"Kwana karewa suke, rayuwa canjawa yake, mutuwa kusantowa yake, kamar yacce akasa date na auren Baby da Kabir yau yakama saura sati ɗaya ɗaurin aurensu, shirye shirye ake bana wasa ba dan Dady yanaso yafitar da ƴaƴan nashi a kunya, a halin yanzu Fadila tana iya tsayawa da Kabir har suyi magana, kowa yana ɓoye son dayakewa ɗan uwanshi,
Baby sai dilki take da gyara me kyau, Fadila ce zaune akan sofa kusada Baby ta tsareta tace "Saifa kinshi maganinnan Momy ce take bani nima inasha magananin Mata ne"
Baby tana yamutsa fuska ta karɓa tanasha jin bauri yasa tace "Adda Fadila babu daɗi wallahi"
Fadila tace "badan Daɗi akesha ba, momy tabani yakai gora biyar yanzu haka akwai gora biyu a ɗakina ga wannan ki shanye sai nakara miki wani idan yakare kada kibari kowa yagani kinji?"
Baby tace "tom"
Fadila tace "kimin alkawarin zakisha"
Baby tace "nayi alkawari zansha amma bazaki karamin ba"
Dariya Fadila tayi tace "tashi muje ki tayani girki"
Baby tace "Aa gaskiya ina dilki kuma tunda nasha maganin naji marana ya kulle"
Fadila tace "yafara aiki zakice, tom bari nakira Kabir yazo dan kinga nan ba kowa saina fita nabaku wuri"
Baby duka takaiwa Fadila ita kjma ta ruga zuwa kitchen tafara aikinta.
(Idan zaka gina ramin mugunta ginashi daidai dakai, momy ta baiwa Fadila magani dan hana haihuwa ita kuma Fadila ta baiwa Baby a rashin sani)
Saida suka ini kafin Baby taɗau goran maganin ta ɓoye a jakarta kafin ta tafi gida.
_Jiddah Ce_
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 77*
~Kamal yana cikin damuwa baya iya bacci kullum cikin tunani yake ada tunanin Fadila ne ya dameshi saide yanzu tunanin Amrah yake bada wasa ba, Umman shi ce tayi sallama jin muryanta yasa yaɗau bargo ya rufawa kanshi dan bayaso yanayi mata magana tunda taki faɗa mishi mahaifinshi, Umma tasan idonshi biyu hakan yasa tace "Kamal tashi zamuyi magana"
Tashi yayi yana kallon Umma daganan ya ɗauke kai, Umma matsowa tayi tariko hannunshi tace "nasan kana fishine dan naki faɗa maka dangin mahaifinka, to Kamal kasani nice na haifeka, saide ina neman gafaranka ka yafemin Kamal"
Kuka tafara da sauri ya matso wurinta dan akwai ciwo ace mahaifiyarka tanayi maka kuka, "umma kiyi shiru"
Umma tace "Kamal nasan zakaji zafin abinda zan faɗa na haifeka ne bada aure ba, lokacin danake budurwa nayi yawo aduniya sosai amma mahaifinka yana garin Abuja kuma nayi maka alkawarin da kaina zan kaika ko kuma idan bakaso naje zanyi maka kwatance nabaka number ɗinshi idan kaje kace kaine Kamal ɗanshi daya haifa batareda aure ba"
Kuka ne yaci Umma, Kamal dayaji ruwan jikinshi ya daina tafiya yasa yazubawa Umma ido, ganin irin kukan datake yasa ya danne damuwarshi yace "Umma babu komai kaddara ce tazo ahaka kuma ni ban tsaneki dan kinyimin hakan ba yanzu burina shine nasamu Amrah nayi rainonta da cikin dayake jikinta idan kin bani daman yin hakan"
Umma share mishi hawayen dataga yana zuba tayi tace "idan hakan zai saka farin ciki na amince ka ɗaukota ka raini cikin jikinta dan nasan itama yanzu zatayi hattara"
Kamal rungume Umma yayi yace "nagode Umma na"
Umma batace komai ba dan yaron nata yana bata tausayi sosai.
Washe gari ya shirya yatafi gidansu Amrah, sallama yayi mama ta amsa yashiga ya gaidata kamar babu abinda yafaru haka ta amsa mishi fuska aɗan sake, Kamal sunnar da kai kasa yayi yana sosa kanshi, yarasa waye aciki zai fara cewa ita tasa yazo gidan Fadila ce ko Amrah? Mama ganin shirun yayi yawa yasa tace "Kamalu! Meyafaru?"
Kallon Mama yayi saiga hawaye suna sauka a idonshi, Mama tace "Haba Kamal kana namiji amma kana kuka? Meya faru? Umman takace ba lafiya?"
Kamal cikin hawayen yace "Mama inason cikin jikin Amrah wallahi ina sonsu"
Kuka yakara fashewa dashi, Mama ɗan murmushi tayi tace "hmm Kamal kace ba cikinka bane ya akayi yanzu ka yadda naka ne? Kuma Amrah tace tunda kukayi aure sau ɗaya ka kusanceta"
Kamal cikin Hawaye yace "Mama wallahi ba sau ɗaya bane inasa mata maganin bacci kullum a juice bata saniba, kuma nine na lalata ta tun farko"
Mama tace "Kamal kada ka ɗaurawa kanka laifi itama Amrah tanada laifinta, amma meyasa kace kaine ka lalata rayuwarta tun farko?"
Kamal kanshi ya dukar kasa sannan yace "Akwai wani abokina sunanshi Abdulhamid yana garin Abuja da zama amma munyi karatu anan Yola, yazomin har gida ya rokeni wani alfarma yacemin yayiwa Wata yarinya Fyaɗe karamace gashi zai bar garin dan mun gama karatu, yanaso in rika kula da ita duk wanda naga zaizo wurinta da sunan aure nayi kokari nahana, nan nayi mishi alkawrin zanyi mishi hakan, Motarshi muka shiga ya ɗaukeni ya kaini unguwar Ganye Road wato unguwar da kuka tashi, bayan mun tsaya yace muɗan jira zata fito yanzu, to a lokacin naga wata yarinya karama tana shiga gida shi baiga fuskarta sai bayanta, nikuma naga fuskarta, nunamin ita da hannu yayi yace "gatacan itace wacce nayiwa fyaɗe inaso ka kula da ita sosai kabata duk wani kulawa daya dace"
Nan nace mishi tom sabida abokin nawa ya taimaka min sosai a lokacin dabani da karfi, bayan ya tafi yana yawan kirana akai akai nikuma ina bashi information akanta, nan kullum nake zuwa na dubata batareda ta sani ba harta ɗan girma, kwatam sai ranar naga Yayarta wato Fadila, saida nayi mamakin yanda suka zama su biyu, ganin haka yasa nayiwa Fadila magana dan nasamu damar fakewa da ita na rinka kula da Amrah, da fari Fadila taki yadda muyi soyayya amma dana nace saita yadda, ina zuwa wurin Fadila muyi fira amma duk hankalina yanakan Amrah, wata rana nacewa Fadila tarakani gidan abokina, tacemin zasuje school nikuma nace idan bata yadda daniba tazo da Sister ɗinta wato Amrah, Fadila jin nafaɗi haka yasa tacemin "to"
Da uniform ɗin makaranta nazo na ɗaukesu a motata, gidana na kaisu wanda abokin nawa ya siyamin, da fari sunki shiga amma nace sam saisun shiga, shiga sukayi nikuma nakawo musu juice, sunsha kaɗan kaɗan, kafin nafito har sun fara bacci sabida maganin bacci danasa musu a juice ɗin"
Cikin kuka ya matso wurin Mama gwiwanshi akasa yace "Mama kiyafeni"
Mama shiru tayi batace komai ba sai jikinta dayake rawa, Kamal yaci gaba dacewa, "ina fita naga sunyi bacci sai nayi dariya a zuciyata nace Badai kai kaɗai Abdul zakaci moriyar ba har dani Kamal, haka na ɗauki Amrah nashiga da ita cikin ɗaki nayi raping ɗinta, saide wani tashin hankali da abin mamakin shine ba Amrah bace Abdul yayiwa fyaɗe Fadila ce, dan Amrah virgin na sameta, a lokacin na ruɗe nashiga salati a zatona itace yayiwa fyaɗe shiyasa nima zanyi mata dan koda ya aureta bazai ganeba ashe abin bahaka yakeba, doctor nakira yazo yayi treating ɗinta agida, ɗaukansu nayi da ɗaɗɗaya nasasu a mota na rufe, bayan sun farfaɗo nazo nashiga ciki ina dariya, Fadila tace "lafiya? Ina muke? Nace mata tunda muka iso kuke bacci shiyasa na rufeku gashi har Unty tafita Unguwa Kuma badama na ɗaukeki dan ban aureki ba, Nan naga Fadila tayi dariya cikin jin kunya, Juyawa nayi aɗan tsorace nakalli Amrah, Abin mamaki sai naga tanamin dariya nima mayar mata nayi nace "Kanwarmu ansha bacci"
Dariya sukayi duka naja motar naje babban shago nasiyq musu abin daɗi dayawa kowa da laidanshi, saide laidan Amrah yafi girma amma Fadila bata nuna damuwa akan hakan ba hasalima haɗa ledan tayi danata tamikawa Amrah, wannan soyayyar datake tsakaninsu yasa nafara dana sanin abinda na aikatawa Amrah, gashi nakamu da soyayyar Fadila gefe guda kuma tausayin amrah ya addabi rayuwata, hakan yasa nafara kula da dukkansu ita yayar dakuma Kanwar, tsabar kunyar abinda na aikata yasa bana ɗaukan kiran Abokina Abdul, Amma akwai babban dalilin yin hakan, dalilin kuwa shine akwai abokinmu sunanshi Kaseem amma anfin saninshi da Guyson, yanada ɓoyayyen gaba tsakaninshi da Abdul yazo yabani labarin abinda Abdul yayi mishi hakan yasa nace zan taimaka mishi nan nabashi labarin cewar Abdul yanada wacce yakeso itace Fadila, Guyson yace ba komai zai ɗau fansa akan hakan, watarana yakirani awaya yace yanaso na auri Fadila, niko nace Mishi Amrah nakeso, nan yacemin ba Auren ne zai tabbata ba dan akwai plan ɗin daya shirya, nace mishi to, nan mukazo gidanku kuka bani auren Fadila, ranar Kamu aka nemi Amarya aka rasa, Guyson yasamu Amrah yace mata ni Kamal inada sana'ar yi wanda ba kowane yasaniba, nan Amrah ta rude tace wani irin sana'a ne? Guyson yace "ina safaran mata kuma nayi musu alkawrin idan na auri Fadila zan basu ita, nan Amrah ta ruɗe tashiga kuka da rokan Guyson ya taimaki yayarta, Guyson yace ta nutsu zaiyi mata bayanin komai, Amrah tace to, nan yace mata zata iya kuɓutar da yayarta amma sai idan zata jure ta Aureni, Allah sarki baiwar Allah nan ta yadda ita tafaɗa halaka yayarta ta tsira, Guyson yace zai ɗauke Fadila sai bayan biki zai fitar da ita, nan Amrah ta amince, batasan Plan yahaɗa ba, batasan cutar da Fadila zaiyi ba, hakan yasa ta yadda dan akwai ranar daya taɓa rage musu hanya sun taso daga makaranta, basu san fakonsu yakeyi ba, Amrah bayan anyi biki tafara neman Guyson daya mayar mata da yayarta amma yace bazai mayar ba, nan fa tashiga tashin hankali duk dare idan natashi sai naji Amrah tana kukan zuci, bata bacci sai tunani, tausayi take bani hakan yasa nakasa fito mata da gaskiya dan kada ta gujeni, a ranar da Fadila sukazo gidanmu naga tashin hankali a idanun Amrah hasalima bata yadda ta haɗa ido da Fadila ɓuya take a bayana tana rokan na kori Fadila agidan, bawai dan batasonta bane aa dan kunya ne kawai Mama, bayan Amrah ta fahimci bana safaran mata yasa tafara sona nikuma tsoron kada tagano da haɗin bakina yasa na koreta agidana, Mama ki yafemin Labarin namu ba kowane zai ganeba sai mu daya faru akanmu"
Mama kallon Kamal take batasan zai iya aikata hakan ba, cikin Kuka tace "ka cuci rayuwar yarana amma ba komai"
Kamal yace "dan Allah Mama ki bani Amrah wallahi zan faɗa mata gaskiya"
Mama cikin kuka tace "Amrah tayi maka nisa yanzu dan tana garin Abuja"
Tashi tayi tashige ɗaki tana kuka me taɓa zuciya, inama ace Abban su yananan yaji labarin abinda yafaru,
Kamal ma saida ya zauna yayi kuka kafin ya mike jiki a sanyaye yatafi gida, da niyar saiya nemo Amrah dazaran yatafi Abuja.
"Bikin Baby da Kabir saura wata ɗaya cif idan Allah ya kaimu raida lafiya, Baby tanaci gaba dashan maganin da Fadila tabata, Fadila ko sai dagewa take akan Baby tasha maganin duk dan ta gyarata, yau sun shiga kasuwa sunyi siyayya sosai, suna shiga mota Fadila ta tada motar taki tashi, sunyi sunyi hakan yaki faruwa, Baby ce taciro wayarta ganin dare yanayi takira kabir, yana ɗagawa cikin muryan bacci yace "Babyna!!"
Baby da shagwaɓa tace "tashi!! tashi!! tashi!!"
Tashi yayi yace "meya faru?"
Baby tace "please kazo ka ɗaukemu motar taki tashi kuma dare yanayi"
"Ina kuke?"
Baby tace "muna kasuwa abakin get kana zuwa zaka ganmu"
Yace "okay"
Tashi yayi yaɗau makulli yaja motar sai kasuwa, Baby tana hangoshi taɗaga mishi hannu, Fadila dukar da kai tayi yana dariya ya karaso yace "ashe da bazo ba yau wasu suje gida susha bulala"
Fadila batace komai ba ta ɗebe kayan