Showing 51001 words to 54000 words out of 139192 words

Chapter 18 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

888

lullub'eta rungume papern tayi ta rufe idontajin dad'i, wayrata taciro daga aljihunta tafara d'auko number d'aya bayan d'aya saida tagama kafin tadanna call, kusan 5 miss call ba'a d'aga ba, haushi taji sosai taaan ya manta da ita a halin yanzu, koda ya d'auka ba lalle yaganeta ba, tana cikin tunani taji wayarta tana ringing, d'agawa tayi tana kallon number ajiyar zuviya ta d'auke ganin number Yarima ne, Kore ta danna Takara a kunnenta "hello" shine abinda tace, ta d'ayan b'angaren akace "ayi hakuri Yarima yana tsaka da aiki zaki iya kiranshi anjima" kitt aka kashe wayar, wani sabon kukane yazo mata tasan da batayi mishi rashin mutunci ba da yanzu ya Aureta, baccine ya d'auketa tana cikin kukan.

     "Amrah tana shiga gidan mama tanufi kitchen shinkafa da wake tagani acikin Tukunya roba ta d'auka tad'iba aciki zama tayi a kitchen d'in tafara ci kamar wacce tayi shekara bataci abinci ba, saida yafara shake mata wuya tamike da gudu tanufi randa mamace tafito daga d'aki ganin mutum yana gudu yasa ta rafka salati tana shirin komawa d'akin, Amrah tace "nice mama" mama tace "Amrah shine zaki shigo babu ko sallama ai sai ki tsorata ni"

Amrah tace "Mama abinci nakeci wlh yunwa nakeji sosai"

Murmushi Mama tayi Dan ta tabbata cikine da Amrah, saida Amrah takoshi kafin tasamu tana ganin hanya me kyau, Mama tariko hannunta suka shiga d'aki tace "sannu" Amrah tana rab'e baki tace "yawwa Mama"

Mama tace "ya naga kin rame? Once dai ba tunanin Fadila kike ba?" Cikin dauriya tace "mama.." Kuka ne ya kwace mata, Mama ta janyota jiki tace "banda kuka fad'amin meyafaru?"

Amrah cikin kuka tace "Yaya Kamal bata sona shi mugune mama bashida imani wallahi har giya yanasha"

Mama tace "innalillahi wa inna ilaihiraji'un, me kike fad'ane Amrah?"

Amrah tace "Wallahi gaskiya nake fad'a miki mama har dukana fa yake kinga tabon jikina" riganta tad'agawa mama saiga shatin bulala kamar wacce aka daka da karfe, Mama cikin kukan tausayin 'yarta tace "baisan kinada cikin bane?"

Amrah tace "banida cikin mama hasalima sau d'aya Abu yashiga tsakaninmu"

Mama tace "ga alamun ciki  sun bayyana ai koda sai d'ayane ciki zai iya shiga yaushe rabonki daganin period d'inki?" amrah tace "gaskiya Mama na dad'e nifa banma kulaba Dan tashin hankalin danake ciki"

Mama tace "to cikine dake amma idan kinaso mu tabbatar tofa dolene muje asibiti yanzu ma kuwa"

Hakan ko akayi suka tafi asibiti, saida akayi wake gwaje kafin aka gano tanada ciki, result aka basu suna nufi gida, Mama tace "idan yasan kinada ciki to zai biki a hankali kina zuwa kinuna mishi kinji?"

Amrah tace "to" saida tawuni kafin ta koma gida bayan mama tabata kud'i,

Tana zuwa wayi Wanka  ta cab'a ado Dan tasan yau dolene su shirya da Kamal nata, Allah ya taimaketa yau bai shigo mata a bige ba lafiya lau yashigo, saida yayi Wanka ya kwanta akan gado kafin tabishi ta rungume tana murna, tureta yayi a jikinshi yanajan tsaki, Amrah tace "nasan daga yanzu kadaina tureni kenan ajikinka, sanyi maka albishir Wanda zaisaka farin ciki"

Kamal yace "menene dallah kifad'amin Dan fita zanyi"

Cikin shagwab'a tace "yaya Kamal inada ciki d'azu mukaje asibiti da Mama suna tabbatar min dahaka gama result d'in" Tamika mishi karb'a yayi yakaranta yace "congratulations Allah yaraya muku cikinku natayaki murna dake da Wanda yayi miki cikin lalle zai zama uba"

Kallonshi tayi da mamaki tace "ban ganeba yaya kamal"

Kamal yace "okay ina nufin bani yakamata kinunawa wannan takaddan ba uban yaron yakamata kinunawa"

Mikewa tayi da matsifa tace "banason rainin hankali Kamal kana nufin ba Kaine uban yaron ba to waye yamin cikin?"

Tab'e baki yayi yace "I don't know kinsan gidan naku ba'a gane muku watakila ma sunada yawa" yana fad'an haka yabar mata d'akin, sulalewa tayi akasa ta zauna dab'as "me Kamal yake nufi? Yana nufin ni karuwace inabin maza? Na shiga uku niban tab'a bin wani namiji ba Allah yasani".

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 37*

        ~Tunanin duniya tayi amma takasa gano ya hakan yafaru waya ta d'auka takira number d'in Zee ringing d'aya aka d'aga "Amarya agidan Kamal Sai yau kika tuna dani?"

Amrah tace "ba maganar tunawa ake yanzu ba magana nakeso muyi dake wlh ina cikin matsala gobe idan kinada lokaci please kizo"

Zee tace "lokaci kam inadashi meyasa bakya zuwa school kinsan zamu fara Exam"

Amrah tace "ba maganar school nayi miki ba maganar zuwa gidana nayi miki idan zakizo kizo idan bazakizo ba shikenan"

Wani dariyan 'yan bariki Zee tayi tace "gidanki ko gidan Yayarki ki rinka gyara zancenki mana 'yammata"

Amrah katse wayar tayi Dan zee tana nema ta kunnata dayawa, kwanciya tayi tanajin babu dad'i har bacci yayi awon gaba da Ita, Kamal ne kwance a falo yana tunani "wato wannan yarinyar batada kunya ace har cikin datazo dashi take kokarin lak'a mishi? Ai bata isaba" ganin tunanin zaiyi mishi yawa yasashi nufan frij yad'ibo kwalaben giya guda biyu yazo ya zauna yafara sha, atake yafara buguwa harya shanye, Amai yafarayi awurin ahaka har yayi bacci cikin Aman, Washe gari Amrah ce tafara tashi falo tafita "subhanallah" shine abinda tace ganin Kamal kwance cikin Amai, Hawaye taji yafarabin fuskarta "meyasa? Meyasa run farko nafara?"

Da kyara ta kwashe aman tayi mopping nacikin d'akin, rigan jikinshi tacire taja hannunshi zuwa toilet, saida tahad'a mishi ruwan wanka kafin yadawo hayyacinshi, amma har yanzu idonshi ad'an juye Sai kallonta yake yana mata murmushi itama da kyar take daurewa tana mayar mishi hannu yakai zai riketa da sauri taja baya tana share hawaye, ta tabbata Dan baya cikin hayyacinshi ne yake kokarin tab'ata amma dazaran yadawo hayyacinshi to har dukanta zai iya amma itama Allah yasani tanaso ta rab'eshi tanaso ta rungumeshi ko zataji sauki a ranta saidai hakan babu dama, kayan jikinshi yafara cirewa a hankali tajuya baya tarufe idonta, tanaji yafara wanka harya gama abun mamaki sai taji yace "nagama"

Da mamaki tajuya tana kallonshi yad'aura towel kanshi a jike hakan yasa gashin ya kwanta a goshinshi, karasawa tayi wurinshi tasa hannu a fuskarshi tanason mayar mishi da gashin baya, da sauri yabige hannunta yafice, durkusawa tayi ta toshe bakinta da hannu biyu tana kuka, sallama taji a falo da sauri tamike ta wanke fuskarta tagoge, tafice itama, Zee tagani tsaye a falo tana kallonshi ko ina tarike kwankwaso da hannu biyu sai tab'e baki take, da gudu ta rungumeta tana murna, da mamaki Zee tace "yau ni kika runguma?"

Amrah tace "idan ban rungumeki ba wa zan runguma? Bama wannan ba muje bedroom kiji dalilin kiranki danayi, hannunta tariko suka wuce bedroom gudun kar Kamal yazo yayi musu rashin mutunci.

        "Fadila ce zaune da waya a hannunta tana faman kiran layin Yarima amma Sam ba'a d'agawa tashiga damuwa sosai domin takamu da soyayyarshi bana wasaba, Baby ce tashigo d'akin ta kalleta tace "lafiya Adda?"

Fadila tace "ba komai"

Zama tayi a gefenta  tariko hannunta tace "mun dad'e muna tare dake nasan zuwa yanzu mun fahimci juna kinsan halina nima nasan naki to meyasa zaki b'oyemin sirrinki?"

Fadila taji ba dad'i data b'oye mata koba komai sun taimaka mata cikin sanyin murya tace "Baby wallahi inason Yarima ada nayi wauta Dana wulakantashi amma yanzu ina sonshi"

A firgice Baby takalli Fadila cikin mamaki tace "Wani Yarima? Badai Yarima damuka had'u agidan sarki ba? Wanda yabaki nombarshi?"

Fadila tace "kwarai kuwa shine"

Zufane yafara ketowa Baby "na shiga uku" shine abinda tafad'a ranta, Fadila tace "akwai matsala ne?"

Baby tace "Aa ba komai"

Tashi tayi tafita, d'akin Mommy tanufa ta d'auko wayarta data bari akan mirror wani number tayi dialing ana d'agawa ta fashe da kuka tace "Fatima nashiga uku, Ashe Adda Fadila tanason Yarima Fatima nakamu da soyayyarshi har number d'inshi na saida na bincika na d'auka ina kiranshi a waya harmun saba dashi duk da ban nuna mishi koni wacece ba amma shima ya yadda dani, Fatima yaya zanyi?"

Ta d'ayan b'angaren hakuri akayi ta bata, katse wayar tayi ta kwanta a gadon mommy tana kuka harda shesheka, Mommy ce tafito daga toilet tana goge hannunta da tissue ganin Baby tana kuka ba karamin tashin hankali tashiga ba, karasawa tayi wurinta tad'agota tana share mata hawayen tace "meya sameki?"

Da sauri Baby tafara kokarin b'oye kukanta cikin in ina tace "ba komai Mommy kaina ke ciwo" kuka mommy tafashe dashi tace "Meyasa kuke b'oyemin abune keda d'an uwanki? Kodan kunga bana takura mukune? Kuna cikin damuwa amaikon kufad'amin saikuna b'oyewa? Kunsan b'oye damuwa a zuciya yana kawo cuta karku bari damuwa tajefaminku cikin wani hali Dan Allah..." Kuka tafashe dashi sosai, Baby tace "mommy banaso kina kuka please kidaina" da tsawa mommy tace "idan banyi kuka ba mezanyi? Kuna b'oyemin Abu kamar banice uwarku ba, to har duniya ta nad'e kada Wanda yafad'an damuwarshi dagake har yayan naki, kije kiyita fad'awa wannan watsatsiyar ko zatayi miki magani"

FIFA mommy tayi a zuciye Dan yaran sunfara bata haushi, Karo sukac da Fadila saura kad'an tafad'i Fadila tayi sauri tariketa, wani mugun kallonshi tabita dashi kafin ta wubce jikinta tabar wurin, Fadila wucewa tayi cikin d'akin tasamu Baby har yanzu tana kuka, d'agota tayi ta share mata hawayen tace "ba Sai kin fad'amin abinda yake damunki ba, nidai kawai kidaina kuka tunda kinki fad'awa Hajiya nasan banida matsayin dazaki fad'amin Amma ina rokanki Dan Allah kidaina kuka, nayi kuka a rayuwata gashi batayimin maganin komai ba, kuka ba magana bane addu'a itace magani" A hankali Baby tafara share hawayenta idonta yayi jaa hakama fuskarta.

       "Abdul dake zaune a office ya mayar da hankalinshi kan wani takadda dayake gabanshi, knocking na kofar akayi bai d'ago kai ba tace "yes coming"

Wata budurwace wacce zatakai shekara 25 tashigo office d'in kayan jikinta wani material ne d'inkin dogon Riga daga kirjin an tsaga hakan yabaiwa kirjinta daman fitowa kad'an, tanada kyau sosai kuma tanada class fuskarta d'aukeda glass half face, rasa takalmi me tsini tana taunar cingum, zama tayi akan kujeran dayake fuskantar nashi tace "Barka da warhaka yallab'ai"

Bai d'ago kaiba have "barka dai"

Murmushi tayi ganin bai kalleta ba tace "yallab'ai koba komai ai bakonka annabinka idan banci darajaba ai naci darajan musulunci"

Abdul tace "kinyi magana na amsa miki me kuma kike bukata?"

Tace "hmm koba komai ai kad'ago ka kalleni"

d'ago kanshi tayi yakalleta ya watsar yace "mezan kalla? Tsiraicin baki zan kalla na d'ibi zunubibko kuma Jan bakin dakika makawa bakinki kamar karuwa zan d'ago na kalla?"

Batayi mamaki ba Dan an sanar da ita halinshi tace "yallab'ai nice nakiraka awaya akan nasamu nombarka awurin wani abokina.." Kafin takarasa maganar yad'ibi takaddun yafice, kallon kofar tayi tana jin bakin ciki ajinta ya zube, amma ahaka zata shawo kanshi, saida tad'an danna wayarta tad'an ja lokaci gudun kar ayi mata dariya kafin tamike tabar office d'in.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 38*

        ~A zuciye Abdul yaje wurin motarshi ya shiga Sai guda, yana tuki ranshi ab'ace har ya iso gida, megadi ne ya bud'e mishi get yashige ciki, saida yayi parking yaciro wayarshi yana dannawa, abakin kofa ya hango Fadila tsaye tarike jikin kofar tayi shiru alamar tayi nisa cikin tunani "kome yarinyar nan take tunawa?" Tab'e baki yayi yace "oho mata ina ruwana"

Falon mommy yanufa tana zuwa yafad'a jikinta yana nishi ala dole ya gaji, mommy tace "kai tashi karka b'allani" cikin shagwab'a yace "ayya mommy nagaji fa sosai"

Daddy ne yasakko daga up yana murmushi yace "my son kacire mata ayi maka Aure bawai kazo kana kato dakai kana kwanciya a cinyar matata ba"

Kallon Daddy yayi yace "to yau ni akeyiwa gori?"

Daddy yace "idan kaji zafi karama"

Dariya sukayi gaba d'ayansu, Mommy ce tace "Dama akwai maganar danakeso muyi daku gaba d'aya"

Daddy yazauna yace "To muna jinki" tace "dama kawata Hajiya Saratu matar honorable ce takemin maganar akwai 'yarta Fatima datakeso ta had'asu da Abdul, duba da Abdul yarone me nutsuwa da kamun kai, na duba kuma naga halin yarinyar ba laifi tanada nutsuwa sosai"

Abdul ne yakalli mommy ya had'e rai baice komai ba, Dady yace "banason yarinyar da aka tallatar ta auri d'ana saidai wacce takeda kamun kai"

Mommy tace "haba Dadynsu meyasa zakace haka? Inafa da right d'in dazan zab'awa d'ana matar daze Aura"

Daddy yace "d'anki ko kuma d'anmu? Kirinka gyara zancenki please"

Cikin b'acin rai mommy tace "bazai yiwuba wallahi dolene ya auri wacce nakeso shi baice bayason ba Sai kai zaka hana?"

Daddy yace "daga fuskarshi Nagano bayaso kuma nasan wacce yakeso wacce zasu dace dashi" a fusace Mommy tace "wace ita 'yar gidan uban waye a garinnan?"

Daddy ma cikin zafi yamike yace "meyasa sai 'yar gidan wani zaki yadda ya aura ke agidan uban wa na aureki? Har kika zama haka?" cikin kuka tace "dama nasani ai dazaran anyi magana sai kace ubana yana saida goro, goronma ai Sana'a ne, kuma wallahi bazai auri wacce banaso ba saidai in bana gidannan, idan ba hakaba zakusan halina"

Rai b'ace daddy yace "Nima idan bai auri wacce nakeso ba ZAKISAN KONI WAYE"

A fusace duk suka fice a falon, Abdul zama yayi a d'aya daga kujerun d'akin ya dafe kanshi, shikam yagaji da hayaniyar gidannan waye zaibi waye zai bari? Allah yace kabi uwa har sau uku kafin kabi uba, Amma uban nashi yanada kyakkyawar manufa shikam baisan inda zaisa kanshi ba yaji sauki, damuwar kanshi ma kad'ai ya isheshi gashi suna Neman sashi awata damuwar.

        "Amrah bayan Zee tazo tafad'a mata duk abinda yake tafiya acikin gidan, wata 'yar karamar dariya Zee tayi sannan tabata shawarwari kafin tacika cikinta da shinkafa da wake Takara mai, Amrah tana anfani da shawarar Zee akan Abu yayi mata sauki sai kara rugujewa yake domin yanzu Kamal ko kwana agida sai wataran yakeyi, idan tafad'awa Umma sai Umma tace yarintane zai daina itama da kyar yad'an shiryu mata, abun duniya yataru yayi mata yawa ta rame ta tayi haske sosoi, fuskarta ne kad'ai yayi kyau ajikinta kasancewar ita kyakkyawa ce sosai, laulayin ciki yasata agaba cikin yana bata wahala wani lokacin tayita kuka ita kad'ai babu me lallashinta idan taje gida Mama tace mata tayita hakuri lokaci ne, itafa hakurin har yayi yawa yanzu, tazama innocent batason yawan magana wahalan kantama ya isheta, number d'in Guyson baya tafiya tana ganinshi a Watsapp amma baya kulata koda tayi mishi magana, daga toilet tafito ta d'aura towel a jikinta Kamal ne ya banko kofar yashigo jikinta dukya b'aci da kura a buge yake sosai da alama ya shawu ba wasa, Kallon Amrah yakeyi tana fito mishi bibbiyu, da muryanshi na 'yan kwaya yace "Fadila ina kikaje kuka barni da kewarkiiiii?"

Rass Rass gaban Amrah yafad'i meyake nufi?

Nufota yakeyi yana dariya da gudu tajuya zata koma toilet Dan kar yayi mata illah, carab ya cafkota yana kallon cikin idonta, ya kara cewa "My Deela kiyi magana manaaa kozanji saukiii"

Amrah bakinta yana rawa tace "to...to...kacikani"

Kara riketa yayi gem yafara shafa  jikinta ga warin giyan yana sata amai toshe bakinta tayi, shikuma sai kokarin kai bakinshi yake cikin nata, da karfi ya buge hannunta ya falla mata wani mahaukacin mari kafin yawa bakinshi anata, kakarin amai takeyi amma ba dama, saida yacimma burunshi kafin ya kyaleta da kyar a galabaice yafice yabarta sai sheka amai take ita babu abinda yake bata haushi kamar yanda tayita kiran sunan Fadila, a hankali tayi wanka da ruwan zafi tasa dogon Riga marar nauyi kanta tayafa mayafi pink tanufi b'angaren Umma, sallama tayi a hankali ta tura kofar tashiga, Umma ce zaune dawani mutum taxi kwalliya ta d'aura gwaggwaro bakinta da Jambaki tana taunar cingum, ganin Amrah tace "lafiya?"

Mutumin ne yayi dariya yace "barta mana ta zauna Hajiya ta"

Amrah kallonshi tayi stake taji mutumin baya ranta gashi kato da katon tumbi amma dagani zakasan d'ana iska ne, tace "ina kwana Umma"

Umma tace "lafiya lau ya kike?"

Sunnar da kanta tayi kasa Dan hawaye yacika mata Ido, a hankali tace "Umma inason yin magana dake"

Amtashi Umma tayi tarumiko hannunta suma nufi waje "meyasa faru?"

Amrah tace "wallahi Umma nagaji Kamal yana shaye shaye yanabin mata zama da fasiki haramunne bazan iyaba"

Harara Umma ta banks mata tace "Amrah wacece Fasika? Yanzu Dan kings Alhaji Gambo a wurina shine zaki ce mana fasikai, kifito fili mana kiyi mana wa'azi basai kin kiramu fasikai ba, wannan rashin tarbiyya ce"

Tana fad'an haka tabar wurin takoma ciki, Amrah hawayenma sun tsaya tana maganar Kamal kuma Umma tace da ita take? "Na shiga uku ni Amrah, wani irin gida na jefa kaina?"

Kuka tafashe dashi ta zauna a wurin tanayi kamar marainiya, Ummace da Alhaji sukazo wucewa sai fara'a suke gaba d'ayansu, Ganin Amrah zaune abakin kofa tana kuka yasa Alhaji Gambo yace "Hajiya ta me kikayiwa yarinyar nan?"

Umma tace "ba komai tsakaninmu ne"

Yace "haba Dan Allah yarinyar nan kamata ai kijata ajiki kisan menene matsalarta yanzu kiga yanda take kuka idan takamu da ciwo fa?" Umma cikin b'acin rai tace "wai miye had'inka da itane? Wannan tsakanina da itane babu ruwanka aciki"

Shima ranshi a b'ace yace "akwai ruwana aciki ai Nima inada yara kuma nasan yanda kikayi mata haka Nima zakiyiwa yarana gaskiya bazan iyaba na hakura dake" a fusace yabar gidan Umma tana kiran sunanshi amma yaki juyowa, wurin Amrah tanufa ta d'agota tace "dama ni tun asali baki kwantamin arai ba wallahi na tsaneki gashi kin lalatamin Auren danakeso kema daina rama abinda kikayimin wlh bazan kyaleki ba" Barin wurin tayi, Amrah tsaki taja tanajin dad'in hakan d'aya faru afili tace "kowama yad'ana bakin cikin danake d'anawa" gyara mayafin kanta tayi Yakoma kamar d'an kwali ta buga tsaki tabar wurin.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 39*

             ~Fadila yau da ciwon ciki ta tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login