Showing 42001 words to 45000 words out of 139192 words

Chapter 15 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

886

Satan kallon Fadila, Kamal yace "kufita daga gidannan kuna tsoratar min da mata" kiran megadi yayi yace afitar da su, Unty ce ta d'aga Fadila Baby ta tayata suka nufi kofa, da kyar Fadila ta iya cewa "Allah ya isa ban yafeba Amrah" tana kuka Unty tafitar da ita.

         "Abdul bayan ya tashi da Asuba yayi alwala acikin hotel d'in yayi sallah sannan yayi breakfast yanufi reception tareda biyan kud'i yafito, wurin motarshi me kyau da tsada yanufa yana tsaki yana kallon agogo ganin har 7 yayi yasashi Jan wani dogon tsaki yabud'e motar yashiga, gidan daya ajesu jiya ya tsaya a kofa yaciro waya yana kiran Baby, jiyayi wayar akashe tsaki Yakuma ja cikin ranshi yace "akan wannan kazamar ne zasu shanyani?" Headphone yaciro yasa a kunnenshi tareda kunna waka a wayarshi yanaji yanad'an kad'a kai alamar yana enjoying, kasancewar yabar marfin motar a bud'e yasa kowa na waje yana iya kallonshi, Abbansu Fadila ne yazo wucewa zai shiga gida ya hango mutum acikin mota yana rawa karasawa yayi wurinshi yayi knocking na kofar, A hankali Abdul yacire headphone d'in yana kallon Abba, cikin sanyin murya yace "good morning"

Abba kallonshi yayi daga sama har kada wannan yaron ba yaron kirki bane, daga ganin kanshi zaka fahimta yaje ya Tara gashi kamar wani mawaki, Abdul ganin yayi shiru ya kara cewa "morning"

Abba yace "nabi morning dagudu, nace nabi morning da gudu, haba ya kana d'an musulmi zaka kunna waka kana rawa a titi, tukunna ma wakake nema?"

Abdul mutumin yabashi haushi babu tantama wannan baban yarinyar can ne, yace "Wanda nakawo jiya da dare ita nazo d'auka"

Da sauri Abba yace "au saika cemin karuwarka Fadila wato idonta ya bud'e har samarai take kawowa kofar gidana ko? To ka b'ace anan kafin natara maka yara"

Abdul yafara gajiya da surutun mutumin shi bayason hayaniya ko kad'an, Mamace ta leko jin Abba yana fad'a da mutum, da ihu tace "bawan Allah ka aika gidan makwabtanmu akwai yara Wanda zasu kaika gidan Sadiya kanwarka tana can, Dan Allah idan kaje ka kula da Fadila nabaka amanarta Fadila ba karuwa bace" tana fad'an haka tashige gida tana kuka, kan Abdul ya d'aure meyake faruwane yana maganar kanwarshi suna kawo mishi maganar wata wai karuwa, Abba wucewa gida yayi yabarshi zaune yana tunani, Wani yarone Wanda bazai wuce shekara goma sha d'ayaba ya iso wurin tareda gaida shi yace "nasan gidan Unty Sadiyan zan kaika" Abdul yace "to nagode shigo muje" shiga yaron yayi sukad'au hanya da kwatance har suka iso, Abdul ne yace "shiga kace Baby tazo inji Yayanta su tafi" Yaro yace "to" tareda shiga ciki, lokacin Unty da Baby suna kokarin kwantar da hankalin Fadila wacce take kuka tanajan Allah ya isa, sallama yayi Unty tace "kashigo" yana shiga yace "wai Baby tazo inji yayanta sutafi"

Unty tace "kace yashigo inji matar gidan" yana fita yafad'awa Abdul, Abdul tsaki yaja yacire dubu biyu yabaiwa yaron tareda gode mishi, yaron yayi murna ya tafi, saida yayi sallama aka bashi izinin shigowa kafin yashiga, ganin Baby tana zaune agefen yarinyar suna kuka yasashi kawar da kanshi shifa ya tsani yaga mace tana kuka, gaisawa sukayi da Unty daganan tace "Bawan Allah zanso kutafi da Fadila tayi nisa da gida wata kila zata manta dacin amanar dasukayi mata, nasan kai musulmine kuma ansan musulmi da taimako ka d'auketa a matsayin kanwarka badan niba badan itaba saidan Allah"

Abdul kallonta yayi na tsawon lokaci yajuya yaga yanda Baby take kallonshi tanaso ya Amince, sauke numfashi yayi yace "to ba matsala Baby zata baki address namu dakuma number wayarta zaki iya kira koda yaushe" yana fad'an haka ya mike yafice, Unty tace Baby tarike Fadila sutafi in Aah ya yadda watarana zata kawo musu ziyara, saida Fadila ta rungumeta sosai sukayi kuka kamar karsu rabu, kafin Baby ta janyeta suka tafi, azaune suka sameshi a motar ya had'e gira yana danna waya, Baby ce ta zauna a gaba, kallonta yayi yace "koma baya" babu musu ta mike sum sum takoma baya wurin Fadila, key yasawa motar suka d'au hanya har yanzu Fadila da Baby basubar kuka ba, daidai bakin titi yayi parking tareda juyawa yana kallonsu bud'e motar yayi yace "duk wacce bazatayi shiruba taficemin a mota" tsitt kakeji ko tari babu Wanda yakarayi, haka suke tafiya kamar wasu kurame, Sai Fadila datake magana da zuciyarta.

           "Amrah jikinta Sai rawa yake taki sakin Kamal, shikuma ganin haka yazata ko tanajin nauyin 'yar uwar tata ce, da kyar yasamu ya lallab'ata bayan yakaita d'aki, bakinta yana rawa tace "yaya Kamal ina tsoro wallahi"

Kallonta yayi yace "bakiyi komai ba Amrah karkiji tsoro"

Rungumeshi tayi tana kuka tace "karsu rabani dakai yaya karka gujeni dannAllah ina sonka wallahi"

Ganin bata hayyacinta yasashi rungumeta shima, d'ago kanta tayi bakinta yana rawa tanaso tafad'i magana amma takasa ganin haka yasa yahad'e bakinshi da nata, tsitt tayi tana sauke ajiyar zuciya saida yaga tad'an dawo hayaccinta kad'an kafin yacireta daga jikinshi ya kwantar da ita akan gado ya rufata da blanket, ya rage hasken wutar kafin yafice yaje wurin megadi yaje "idan wad'annan suka kara dawowa kayi musu duk abinda kaga dama ka had'asu da yara suyi musu duka kana jina"

Megadi yace "eh yallab'ai" daga haka ya juya.

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

*ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 30*

~Mama yau tayi kuka kukan data jima batayi irinshi ba, har kanta yafara ciwo bargo ta lullub'a jikinta dashi ta kwanta lub tana zubar da hawaye, Abba ne ya leko yace "gara fa ki warware sabida Fadila bazata zauna a gidannan ba tom" ko kulashi batayiba taci gaba da kukanta, babu abinda yake d'aga mata hankali kamar yanda taga Fadila ta rame tayi baki, Fadila meson Ado da kwalliya yau itace fuskarta babu komai tayi fayau haka? Idan ta tuna sai kukan yakara karuwa.

"Fadila da Baby shiru sukayi a motar Abdul ya kunna waya yanaji, saida yaga 1 yayi kafin ya tsaya a wani restaurant yafita, Baby ce tariko hannun Fadila tace "kiyi hakuri da halin yayan namu wlh da Bahaka yakeba nayi mamakin yanda ya sauya a lokaci d'aya bansan meya sameshi ba, yanzu nikaina tsoronshi nake" kuka ne ya kwace mata, Fadila tace "Kidaina kuka Amrah karki damu zan hakura da duk halinshi mudai tayashi da addu'a idan wani abinne ya sameshi Allah ya yaye mishi" Baby tace "shiyasa nake sonki Adda Fadila kinada saurin fahimta" daga haka sukayi shiru babu Wanda ya kara cewa komai, ta b'angaren Fadila kuma tana cikin damuwa sosai ita har yanzu tana Addu'ar Allah yasa mafarki take,

Abdul ne yashigo motar hannunshi rikeda ledoji manya guda biyu mika musu yayi Baby takarb'a tana kallon Fadila, bud'ewa tayi taga abinci ne acikin take away da drinks, mikawa Fadila d'ayan tayi, Fadila takarb'a ta aje a gefe Dan ita bata sha'awar komai a halin yanzu.

"Sunyi tafiya me nisa kafin suka shigo garin Abuja, lokacin Baby da Fadila har sunyi bacci, sun shiga cikin gida Abdul ya juya yana kallonsu ganin suna bacci yasashi fita yarufe marfin motar tareda shiga gida, Mommy ce zaune a falo itada Kaka, ganin Abdul shikad'ai yasa kaka tambayar ina Amrah, Abdul yace "suna cikin mota bacci suke"

Waro Ido Kaka tayi tace "itada wa ka bari a mota?"

Baiyi maganaba yawuce ciki, da sauri kaka tamike zuwa wurin motar tana zuwa ta bud'esu tareda tashinsu, a firgice suka mike Dan sunyi zaton Abdul ne, Kaka tace "lafiya naga kun dawo tareda ita?"

Baby tace "muje ciki zanyi miki bayani"

Fita sukayi a motar duka suka nufi cikin gida, ganin Mommy a falo yasa jikin Fadila yafara rawa ganin farko datayiwa matar tazata tanada hankali to amma data rab'eta saita Nuna mata asalin kalanta, Kaka ce tace "kuzauna kubamu labari"

Zama Fadila tayi a kasa ta sunne kai, Baby ce ta zayyana musu duk abinda yafaru ta d'aura dacewa "Dan Allah Mommy badan halina ba kisa Daddy yabar Adda Fadila ta zauna agidannan" mommy kallonta tayi tace "zan sashi amma akan sharad'i guda d'aya"

Da sauri Baby tace "kifad'a Mommy wlh zanyi"

Mommy tace "saidai idan zata zauna tayi aiki a gidannan ma'ana tazama 'yar aiki"

Da sauri Baby ta d'ago kanta tana kallon mommy jin maganar data fad'a ganin ko kallonta batayi yasa ta juya tana kallon Fadila, Fadila gid'a mata kai tayi alamar tace tayadda, hawayene yafara bin fuskar Baby tayaya Fadila zatayi aiki agidansu kamata mommy tad'auki Fadila amatsayin 'ya bazata iya ganin Fadila tana aikatau agidansu ba, Mommy ce ta katseta dacewa "kin yadda ne ko kuma?"

Fadila sai gid'awa Baby kai take, ganin Babyn bazata iya fad'a ba yasa Fadila cewa "Eh mommy na yadda"

Kallonta tayi daga sama har kasa tace "sunana ba mommy ba sunana Hajiya kuma haka zaki rinka kira kinji?" Fadila tace "to Hajiya"

Mommy tace "sannan duk ranar dakuka sake kuka nunawa Daddy Cewar aiki take agidannan wallahi ranar zatabar gidan, Dan haka ma a d'akinki zaku zauna tunda kece kika d'ibota" tana fad'an haka ta mike tabar wurin, Kaka ce ta kallesu taga yanda jikinsu yayi sanyi tace "kuyi hakuri ganin farko danayi muku atare na fahimci akwai shakuwa sosai a tsakaninku, to Amma kinsan halin maman taki sai a hankali kuyi yanda tace sai a zauna lafiya kunji?"

Baby cikin kuka tace "to amma Kaka tayaya zatace Adda Fadila tazama 'yar aiki agidannan itafa ta taimakamin lokacin danake bukatar taimako, gaskiya saina fad'awa Daddy yasan abinyi"

Kaka tace "kus karki kuskura idan kikayi haka zata kori yarinyarnan ke kinsan tsakanin mata da miji kuwa?"

Shiru sukayi Baby tamike tariko hannun Fadila tace "muje muyi salla muhuta"

Fadila dama bame yawan magana bace gashi kuma tahad'u da wannan kaddarar sai shirun yamaidata miskilar dole, duk maganarta yanzu baya wuce tace eh Aa shikenan bata wani dogon hira, Baby abun yana daminta tayi tayi taga Fadila tafiya a wannan damuwar amma takasa, haka ta hakura tabarta.

"Amrah ganin Fadila bakaramin tsorata tayi ba saida tayi kwana uku kafin tadawo hayyacinta shima da taimakon Kamal ne, zaune take akan sofa na d'akinta data rufe Ido Fadila take kallo haka jiya tayi mafarkin abun tsoro da Fadilan, wayane a hannunta a hankali tadanna numbern Kamal takira, lokacin Kamal yana office yaga kiran Amrah da sauri ya d'aga yana tambayarta lafiya? Kuka tafashe mishi dashi hankalinshi dukya tashi tattare takaddun yayi yahad'asu a jaka ya kulle kofar yanufi gida, yana zuwa yaganta a kwance jikinta yana rawa shima yanzu yafara zargin Fadila anya bada wani abun tazoba? Tunda tazo Amrah takasa samun nutsuwa, karasawa yayi wurinta yariko hannunta tanajinshi tarikeshi tana kuka, d'aukanta yayi yawuce bedroom da ita, yana zuwa ya kwantar da ita akan gado shima yahau gadon tareda rungumeta itama rungumeshi tayi, a hankali yafara saukar mata da wasu zafafan kiss runtse Ido tayi tana karb'a, daganan yafara kokarin core kayan jikinshi danata sai a lokacin tadawo hayyacinta ta tureshi da karfi, lumshe Ido yayi yakara rikota, tana kokarin tureshi amma takasa, yauya tabbata saiya maidata matarshi ta asali, saida yad'au lokaci mai tsayi kafin ya saurara mata itakuma Amrah tafita a hayyacinta sai sauke numfashi take, Kamal shiru yayi yana tunanin ya akayi haka, waya yaciro daga aljihunshi ya lalub'o number wani abokinshi doctor yana d'auka yace "ya ake gane mace virgin?"

Da mamaki doctor yayi mishi bayani, "nagode" shine abinda yace ya katse wayar tareda mikewa yashige toilet ko kallon Inda take baiyi ba, saida yayi wanka me had'eda Alwala yafito ya shimfid'a sallaya ya idarda azahar, fita yayi agidan gaba d'aya kanshi a kulle, Amrah sada yafita tamike tashiga toilet d'in tana mamakin meyasa Kamal yafita yabarta haka? Babu ko tausayi, da kyar dai tayi wankan itama mai had'eda alwala tayi sallarta a d'aki ta kwanta akan sallayar tareda rufe jikinta da hijabinta tana tunani meyasa Kamal yabarta a wannan halin ba tareda ya taimaka mata ba, Kodai har yanzu yanason Adda Fadila ne? Saurin kawar da maganar tayi tunawa da yanda ya wulakantasu ranan ta tabbata bayason Fadila, da haka har bacci b'arawo ya saceta tana sake sake.

"Fadila tana aiki yanda Mommy tasata idan Daddy yana nan batayi idan bayanan kuma tazama jaka zatayita aiki kenan, yau ya kasance Saturday duk 'yan gidan suna gida kasancewar ba aiki, Fadila ce take goge jikin TV ta manta shaf akan mommy tace kartayi aiki ranarda daddy yake nan, ta maids hankalinta sai gogewa take Daddy ne yashigo d'akin da sallama d'auke a bakinshi, kallonta yayi da mamaki yace "aa my daughter ina 'yan aikin gidan suke kike aiki da kanki?"

Fadila ta rud'e sosai tana tsoron kada mommy tafito da sauri tace "Eh Daddy naga yayi kura shiyasa idan nagama bazan karayin komai ba" daddy yace "yawwa ina Mamana take?" (yana nufin Baby)

Fadila tace "aita koma bacci tinda tayi breakfast"

Yace "okay to kishirya ranar Monday Abdul zaije yayi miki register a makarantar su Mamana"

Wani irin garin cikine ya ziyarci Fadila batasan lokacin datayi tsalle ta rungume Daddy ba, kamar zata kayar dashi tana dariya Daddy ma dariya yake sosai Dan yanaganin yarinyar har yanzu akwai yaranta, mommy ce tafito daga b'angarenta hannunta rikeda cup na shayi Turus tayi ganin Fadila rungumeda mijinta, Cup d'inne ya sub'uce mata jikake tass yafashe akan tyles, da sauri suka juya suna kallonta Fadila ganin Mom yasa ta karasa da gudu Batama lurada fasashen cup d'inba taje ta rungume mommy tana murna, da sauri mommy ta tureta, sai gata akan glass d'in jikinta yafashe, ihu ta tsala jin zafin daya ratsata, Abdul daya fito Dan yagaida mom da Dad yaji ihunta da sauri ya karasa Inda yaji tashin ihun ganin mutum kwance acikin glass daya tarwatse yasashi zuwa da gudu ya d'agota a hankali ya kwantar da ita a gefe, cikin tausayi yafara cire mata glass d'in aduk Inda ya soketa, sai kuka take tana rike hannunshi, cikin sanyin murya yace "sorry tsaya na cire miki saura kad'an kinji?"

Gid'a kai tayi hawaye nabin fuskarta ganin azaban datakesha Ga zufa daya wanke mata fuska yasata cire d'an kwalin kanta tayi jifa dashi atake gashin kanta mai tsayi ya bazu har zuwa fuskarta ya manne, d'ago kai Abdul yayi ya zuba mata Ido karo na farko kenan daya tsaya ya kalleta ganin yanda gashin ya taru a fuskarta yasashi matsowa a hankali yafara tattare mata yana maidawa baya, Daddy ne ya juya yabar d'akin baice komai ba, Mommy ma juyawa yayi tabarsu a d'akin ranta a b'ace kamar ta bugi babu, Abdul kuma saida yagyara mata gashin yakara maida hankali wurin cire glass d'in Fadila sai kuka take kamar karamar yarinya, ganin bazatayi shiruba kuma bayason jin mutum yana kuka yasashi daka mata tsawa "zakiyi shirune ko kuma in kyaleki? Dama bakya ganine koke MAKAUNIYA CE dazaki fad'a acikin fasashen glass?"

Tsitt tayi ko hawaye bai kara sauka ba don tana matukar tsoronshi.

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 31*

        ~saida yacire mata duka yariko hannunta yace "tashi nakaiki d'akinku" mikewa tayi cikin tsoro tarikeshi suka nufi d'akin Baby, daidai bakin kofa taji wata kwalba takara shigewa kafarta ihu tayi ta durkushe awurin, kallonta Abdul yayi yaja tsaki tattare hannun riganshi yayi ya d'agata sama yashige d'akin da ita, Baby lokacin tafito daniyar d'aukar wayarta dayake ringing bakinta da brush tana gogewa, ganin Abdul d'aukeda Fadila yasa ta tsaya turus tareda waro Ido bakinta duk kumfa, Abdul ne yajuya ya kalleta cikin had'a face yace "me kike kallo?"

Da sauri ta kawar da kanta ta koma band'aki tana lekasu cikin mamaki, yana kwantar da ita yafara mayar mata da gashin baya saida yaga duk ya mayar kafin yajuya yabar d'akin, da gudu Baby tafito daga toilet d'in tafad'a kan Fadila tana tambayarta meyafaru? Fadila tace "cup ne yafad'i a kasa shine ban saniba na fad'a akai" Baby cikin tausayi tace "ayya sorry Adda barina kawo miki coffee"

Fadila batayi magana ba.

       "Amrah wuni tayi tana jinyar kanta Kodai haka maza sukeyine? To amma ai tana karantawa a Novels mazan keyiwa matan duk abinda sukeso ranan, to nata yazo da matsala hakadai tayita tunani harta kara komawa bacci, Kamal bai shigo gidan ba sai kusan karfe goma sha d'ayan dare, lokacin daya shigo Amrah ta zabga tagumi a gefen gado daga sallama bai kara cewa komai ba, saida yagama abinda zaiyi kafin ya kwanta tareda juya mata baya, Amrah abun nashi yabata mamaki kwanciya tayi a bayanshi tareda zagayo da hannayenta zuwa cikinshi cikin sanyin murya da alamar zazzab'i tace "Yaya Kamal meyafaru?, meyasa kaiyimin magana menayi maka?"

A hankali kamar bayason magana yace "please cire hannunki daga jikina banaso kina yawan tab'ani"

Da mamaki tace "Amma ni ai katab'ani kafin kafice ko?"

Yace "eh aini mijinki ne"

Itama tace "nima ai matarka ce"

Tureta yayi a jikinshi yace "Please kibarni  nad'an huta nagaji sosai"

Amrah zuwa yanzu ranta yafara b'aci tace "kai bakaga gajiyan daka d'auramin ba zakacemin kagaji?" Tsaki yaja yatashi yad'au filo zai nufi Falo, Amrah cikin zafi tarike filon tace "babu inda zakaje saika fad'amin abinda yake damunka" wani kallon baki kaiba yayi mata yaja filon ya tureta akan gadon yawuce zuwa Falo ranshi a mugun b'ace, waro Ido tayi afili tafurta "ikon Allah meyake faruwa ne? Menake gani tin yanzu? Anya Fadila batazo dawata asirin ta gogan ajiki ba?  Nashiga uku".

      "Baby ce tayi jinyar Fadil, zaune suke akan gado Baby tana nunawa Fadila wasu takaddu da akeyi a makarantarsu, Kaka ce ta leko tace "Kufito ubanku yana kira" dariya baby tayi Dan yanda kaka take cewa ubansu sai taji kamar zagi kaka takeyi, Fadila tad'an buge bakinta tace "kin raina kakan ne kike mata dariya?" Kaka tace "barta 'yar albarka ai wannan da ita da Abdule duksun rainani nibadasu zanyiba da ubansu zanyi" tana fad'a ta sakar musu labulen tabar wurin, Baby tariko hannun Fadila tace "muje ko" Fadila tace "bari na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login