Showing 69001 words to 72000 words out of 139192 words
tamike tashige toilet, cikin mamaki Fadila tabita da kallo, to me Nayi Mata tamin wannan kallon?" d'aga kafad'ar tayi ta Tab'e Baki alamar oho, Baby ce ta kalleta tace "Adda Fadila wad'annan yaran kanwar Momy ne wannan sunanta Pinky Wancan kuma Nabila, Pinky inace Mata Baby girl sabida ita pally nace, babansu shine Governor na garinnan ban tab'a zuwa gidansu dakeba sabida Nasa gari suna karatu a London ita Nabila tagama this year ita kuma Baby girl sai next year zata gama"
Fadila tace "Yayi Kyau gaskiya Sannunki Baby Girl"
Tashi pinky tayi ta rungumeta tayi Mata kiss a kumatu tace "yawwa untynmu"
Baby tace "muje falo duka"
Fadila tace "to" Wurin wardrobe taje ta d'auko Wani dogon Riga Baki da Ado dayawa ajiki tasa tayane kanta da karamar d'an kwalinshi sannan tashafa Hoda ta feshe jikinta da turare mai kamshi tad'au wayarta kallon Baby tayi tace "Ku muje"
Pinky tace "Wow Dan Allah Ko Tsaya Nayi snapping d'inki wallahi kinada Kyau kuma kinyi kyau"
Tsayawa Fadila tayi tana Dariya suka ta d'aukanta hoto da wanda sukayi Gaba d'ayansu da wanda itada Baby sai kuma itada Pinky yanda suka rungume juna Kamar Dama can sun Saba, Fadila ce tace "ya Isa ko"
Pinky tace "Ki tsaya muyi miki d'aya a snapchat pls"
Tsayawa Tayi zasu d'auke, Nabila ce tafito daga toilet ta bangaje Fadila Kafin ta rab'a ta gefe tawuce, kallonta Fadila tayi batace komiba suma su Baby ba Wanda yace kala Haka Baby taja hannun Fadila suka tafi falo, zama sukayi suna fira su uku ita kuma Nabila ta d'aura Kafa d'aya Akan d'aya tana Danna wayarta sai chatting take da kawayenta turawa tana voice da Turanci tana Dariya kad'an kad'an, Fadila Ko tsabar hira batasan lokacin data cire d'an kwalinta ba tana basu labarin Makarantarsu, Abdul ne Yayi sallama a hankali taja Sanye da bakin Kata Riga da wando kanshi da picap Baki, fuakarshi luwai luwai sajenshi ya kwanta Lub, sai kamshi Yake zubawa, Nabila ce ta Mike da d'an Saurinta taje ta rungumeshi tana Dariya, shima rungumeta Yayi yana Dariya yace "yaushe akasa?"
Cikin shagwaba tace "Bana kiraka kaki d'auka ba"
Lakuce hancinta yayi yace "sorry Baby na kinsan Ina busy ne"
Zama Yayi Akan Sofa ya d'aurata a cinyarshi tana zuba mishi shagwab'a shikuma sai lallamata Yake yana biye Mata, Pinky ce tace "Hi Yaya Abdul welcome"
Dariya Yayi yace "Baby girl I love you"
Dariya tayi tace "love you too"
Fadila Ido tazuba musu tana kallon ikon Allah takasa ganewa iskanci ne Ko kuma wayewa ne, gashi Nabila sai narkewa take ajikin Abdul, ita wannan wayewar yana bata haushi basu San zunubi suke d'iba ba? Gyalenta ta yafa tamike tabar falon ranta Ab'ace, Pinky tace "lafiya dai Ko?"
Baby tayi murmushi tace "kyaleta Kishi ne"
ita kuma Fadila tana Barin Falon taje d'akinsu tafad'a kan gado, "Toma miye damuwana? Meya shafeni dasu? Ba 'yar uwarshi b'ace ba suyi tayi zunubi akansu baniba garama na daina nuna damuwata Dan wad'annan ba islamiya suke zuwaba bale Susan me Kyau da Mara Kyau Halan ma ace Kishi nake"
Rufe Idonta tayi tafara bacci cikin konciyar hankali.
Da dare kowa Yayi sallar isha sai suka hallara duka a falo Kowa hira Yake da 'yan uwan Momy da 'yan uwan Dady Fadila takasa sakewa ta zauna a takure wata kanwar Dady ce ta matso Wurinta tarike hannunta tace "Ki saki jikinki amaryarmu kinji?"
Cikin Kunya Fadila tace "Tom nagode"
Dahaka Matar take janta da fira har suka Saba, kallon cikin falon tayi bataga Nabila da Abdul ba, ganin sunacan suna ta iskancinsu da sunan wayewa mtswww, bata gama tunanin ba taji sallamar Abdul d'ago Kai tayi suka had'a Ido atare suka watsar ganin Nabila rungume a gefenshi yasata Cigaba da hirarta, shima zama Yayi yanata hira da 'yan uwanshi har dare yaraba, watsewa akayi aka Barsu daga Baby sai pinky sai Nabila Abdul da Fadila manyan duk sun tafi, Fadila jingina kanta tayi Akan Kafar Baby, Nabila ce tace "Yayana zansha ice-cream"
"Babyna Ina zan samo miki ice cream a darennan Kibari gobe dai"
Kukan shagwaba tafara yimishi rungumeta Yayi yana bata hakuri Kamar zai maidata ciki, Pinky ce tace "my love kaida zaka angwance gobe Ai babu kanka yaushe kakeda lokacin Unty Nabila Ga Unty Fadila nan"
Satan kallon Fadila yayi wacce tafara lumshe ido alamar bacci ta narke Akan kafar Baby Kamar wata karamar yarinya, Kawar da Maganar Yayi yace "Baby na tashi kije Ki kwanta Wallahi na gaji"
Nabila Kwanciya tayi ta d'aura kanta Akan cinyarshi tace "Anan zanyi bacci"
Dariya kawai yayi yafara shafa kanta yace "Baby Kin girma ma Baki daina rigima ba"
Turo Baki tayi kawai,
Fadila mikewa tayi tace "Allah ya tashemu lafiya"
Pinky ce tariko hannunta tace "dan Allah Ko zauna Kagama bamu labarin Nasan gobe ba kanki, Kin tsaya a inda kanwarki ta nemi tsokanar mahaukaci"
Fadila tace "Kibari sai Gobe"
Pinky tace "Dan Allah" ganin haka yasa Fadila ta koma ta zauna tafara basu labarin.
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*K'ANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 50*
~Pinky tace "dakata Unty Fadila kanwarki akwai neman tsokana to amma tanada karfi kuwa?"
Fadila tace "Eh tanada shi Yanzu ba labarin KANWATA zan bakuba labarin Garinmu zan baku sabida na KANWATA yakare"
Pinky tace "Aa Dan Allah Nikam Wlh Inason kanwar taki kihad'amu kawance da ita"
Shiru Fadila tayi tace me kikace?
Pinky cikin Sakin fuska tace "kihad'ani da kanwarki Wallahi naji Ina sonta sosai Ina son Mutum me neman tsokana wallahi"
Fadila tace "Ai ta mutu bata Raye"
Ba Pinky Ba har Abdul da Nabila saida suka d'ago Kai suna kallonta abin yabasu tausayi yacce suka Saba da kanwar Tata ace ta mutu "Innalillahi" Cewar Pinky cikin hawaye tace "ta mutu kuma?" Nabila kawar da kanta tayi gefe labarin ya tab'a zuciyarta Saide bata nunaba dan batason raini a cewarta, Baby ce take kallon Fadila da mamaki amma Fadila taki yadda su had'a Ido, bata tab'a zaton Fadila zatace kanwarta ta mutu ba, pinky tace "Ya sunanta"
Fadila mikewa tayi tace "Sunanku iri d'aya"
Baby cikin Mamaki takara kallon Fadila amma har Yanzu taki yadda suhad'a Ido, d'aki tawuce bata kara cewa komai ba, duk d'akin jikinsu Yayi Sanyi, Abdul ne yamike ya saukar da kan Nabila daga cinyarshi yace "Allah ya tashemu"
Nabila ma mikewa tayi tanufi dakin su Baby tahau gado ta kwanta lokacin Fadila tana Kwance tana kuka, Baby shiru tayi itama ta Mike tabar dakin taje ta kwanta Akan gadonta, ita kuma Pinky kuka tayi Tayi tace "Allah yaji kanki kawata Allah yakai Haske kabarinki Ameen ya rabbil arshil Azeem"
Shafe addu'ar tayi taje tayi alwala tayi nafila raka'a biyu Kafin tayima Amrah addu'a sannan ta konta, babu wanda yacewa Wani Kala har sukayi bacci,
Abdul toilet yawuce ya watsa ruwa had'ida alwala yafito ya goge jikinshi, saida yashafa mai da turare Kafin yasa Riga Yayi nafila tareda rokawa kanwar Fadila yafiya dakai haske kabarinta, Hawa gadonshi Yayi ya konta yana tunanin labarin wayarshi ce tayi ruri yad'aga yana kallon sunan dayake yawo ajikin "Dude" yagani da sauri yad'aga yace "halloooo"
"albishir" aka fad'a a d'ayan b'angaren, da murna yace "goro"
"Ina cikin Abuja Yanzu Haka Ina special Hotel"
Wani irin tsalle Abdul Yayi yace "dude Dan Allah da Gaske? Kodai tsokanata kake?"
"Wallahi da Gaske surprise Nayi maka dama Nayi niyan sai gobe zaka Ganni a d'aura aure dani Amma Kasan Bazan iya ba Wallahi Ina sonka Inason kasancewa dakai muyi firan yaushe gamo, Dafatan kyakkyawa ka zab'o mana me kirar Coca Cola ka gane ai"
Kuka Abdul yafashe dashi acikin wayar yace "Dan Allah dude kazo Wallahi Ina cikin Matsala narasa wanda zan fad'awa inji dadi"
Cikin sanyin murya yace "Abdul Meya faru?"
Abdul yace "Kabir Ina cikin matsala zanzo na d'aukeka Yanzu"
Katse wayar Yayi Dan bayaso Kabir yace "Aa" cikin sauri ya diro daga gado yasa jallabiya ya d'au makullin mota yanufi waje cikin sand'a, saida yabud'e get Kafin yabud'e motar yana kallon Baba me gadi yana bacci, da Mugun speed Yabar layin Yayi hanyar special hotel, Fadila datake kwance tana kuka taji karar vibrating na wayarta da sauri ta Mike tana kallon wayake kiranta da daren nan, ganin sunan Yarima yana yawo yasa tayi murmushi tad'aga wayar tareda yimishi kiss, Baby tana kallonta ita tazata Ko Abdul ne yakira, "Hello tafad'a cikin Sanyin murya"
"Babyna"
Fadila hawayene ya sauka Mata a kumatu cikin Sanyin Jiki tasa Hannu ta goge, tace "Na'am"
"Albishir"
Fadila tace "Goro"
Yace "fari Ko ja?"
Fadila tace "fari tass"
Yace "Ina cikin Abuja Yanzu Haka, Nazo naganki kuma gobe Auren abokina wanda nake matukar sonshi sosai, shima surprise Nayi mishi"
Fadila tace "da Gaske?"
Kwaikwayon muryanta Yayi yace "Aa da wasa"
Dariya tayi tace "Yarima kanada tsokana dayawa"
A firgice Baby tamike danjin sunan yarima da Fadila takira har saida Fadila takalleta, Yarima yace "Yanzu yazo d'aukana gashima yana kirana awaya gobe zan kiraki tarema dashi zamuje wurinki"
Kit yakashe wayar, Fadila juyawa tayi tana kallon Baby Sauka tayi Akan gadon tanufi Wurin Baby tariketa tace "Babyna lafiya dai Ko?"
Baby tace "Eh mafarki Nayi"
Fadila tace "Ayya konta to Nayi miki addu'a kinji"
Kwanciya Baby tayi Fadila tayi Mata addu'a tareda Shafe Mata jikinta ta rufa Mata blanket Kafin takoma itama ta konta tana tunanin auren waye Yarima yazo, hmmm baisan itama gobe aurentaba shiyasa yace zezo wurinta, hawayen bakin ciki ne yazubo Mata a zuciyarta tace "Fadila Ke sai yaushe zakiji dadi a rayuwarki? daga wannan bakin cikin sai wannan menayiwa rayuwa Yake gasani Haka? Allah natuba ka yafemin idan ma wani abin Nayi batareda saninaba, saida tayi kuka sosai Kafin ta konta tayi bacci.
Abdul saida ya Iso kofar hotel d'in yakira Kabir awaya yace ya Iso,
Kabir ne yafito da jaka a hannunshi yakara haske dukda acikin darene zakaji Kamar ka sace ka gudu gashin kanshi sai sheki Yake, tsuke karamin bakinshi Yakeyi Dan yagaji sosai yau, Abdul ne yafito ya rungumeshi yana Dariya, shima dariyan Yayi yace "Dude I love you"
Abdul ma yace "I love you"
Dariya suka kwashe dashi suna kara Jan juna ajiki, "you are welcome Kasan de Bazan tab'a barinka ka kwana awani wuriba Kodai bakai kad'ai bane?"
Harara kabir ya watsa mishi yace "muje mota zan baka labari a hanya" mota suka shiga Abdul yace "Amma Nayi mamaki kaine ka Sauka a hotel ba mace?"
Dariya Kabir Yayi yace "Hmm duniya kenan yanada dad'i a shaideka da Hali me Kyau"
Abdul yace "kutma Kodai ka b'oye Baby a d'akin Hotel ne yanzu kake tunaninta?"
Duka Kabir yakai mishi abaya, yace "Dude Wallahi wata yarinyace ta canja ni yarinyar ta canja Babana danake Baka labari yau Abba yadaina duk wani mulkin mallaka dayake, dude I love her, Wallahi Ina sonta idan ban auretaba zan mutu, idan ba muryanta najiba Bana iya bacci me dadi"
Kallon mamaki Abdul Yayi mishi tace "Tabbas yarinyarnan tayi sa'a kaine Kafada soyayya me karfi Haka? Dan Allah kafadamin inda take da kaina zanje Nayi maka kampen"
"tananan Abuja Nakirata ma Yanzu gobe idan an d'aura aurenka zamuje"
"Allah yakaimu gobe muje Inga wannan sarauniyar amma Yaya sunanta?"
Kabir yace "Sunanta princess"
Dariya Abdul Yayi yace kace "sunan me tsada ne"
Dariya kawai Kabir Yayi, ahaka har suka Isa gida, Abdul yashiga yabud'e suka shiga a hankali suka wife site d'in Abdul, Abdul yace "shiga kayi wanka"
Kabir yace "Nayi wanka a hotel"
Zama sukayi abakin gado Kabir yace "gobe aurenka amaikon murna shine kake bakin ciki? Fad'amin Meya faru?"
"dude Ina cikin matsala Idan natuna da sai inji Kamar na bijirewa Dady, Banason wacce Yake auramin Wallahi"
Kabir ya dafashi yace "Abdul ka manta da abinda yawuce halanma Yanzu tayi aure Karka b'ata rayuwarka karike kaddara"
"mikewa Abdul Yayi yana zagaye d'akin yace "Wallahi Bazan iya mancewa ba Ina tausayin yarinyar da Dady yake auramin Ina tsoron kada nashiga hakkinta, hakki zeyi yawa akaina kataimaka Kabani mafita dude"
Mikewa kabir Yayi ya Iso Wurinshi tareda dafa kafad'arshi yace "Kasan tun muna makaranta babu wanda kake fad'awa sirrinka Saini Ko? Kuma Nima babu wanda nake fad'awa sirrina sai Kai, Kasam Bazan Cuceka ba, to shawara zan baka Kai umarnin mahifinka ka auri wacce yakeso, shine kwanciyar hankalinka"
Fad'awa jikin Kabir Yayi yana kuka tace "dude na b'ata rayuwata Ko?"
Tausayi yabaiwa Kabir a hankali yajashi zuwa bakin gado ya zaunar dashi yace"Aa kanada damar da zaka gyara rayuwarka, Yanzu ma kwanta kayi bacci saida safe mayi magana kaji?"
Kwanciya yayi Kabir ya rufashi da blanket Kafin yawuce zuwa Wurin flask yahad'a tea Kafin yakoma Wurin gadon yaciro wayarshi yakira Fadila, ringing biyu ya d'auka cikin Sakin muryanshi yace "Baby Nasan kanajin bacci amma ni Bazan iya bacci ba sai naji muryarki saikin cemin I love you Kafin Nayi bacci"
Wasu zafafan hawayene suka zubowa Fadila kashe wayar Yayi Dan batasan Yaya zatayi ba, Kira Yayi bata d'aga ba daga karshema takashe wayar Gaba d'aya, cikin Tashin hankali yace "Bazan iya bacci ba yau Wallahi kitaimakeni Ki amsa kirani"
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*K'ANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 51*
~Abdul daya rufe Idonshi Kamar me bacci a zuciyarshi yace "Tabbas wannan princess d'in ta canja dude, jibi yacce Yake magana shi kad'ai, shida Ko a school be fiye magana ba sai yazama dole shine Yake surutu Akan mace? Ikon Allsh"
Kabir Kiran layin Fadila yayitayi baya shiga, hankalinshi ne yatashi sosai, a hankali yajuya yakalli Abdul, d'an bugashi Yayi kad'an yace "tashi Dan Allah akwai matsala"
Abdul tashi Yayi ya zauna yana mutsika Ido Kamar me bacci yace "Meya faru kuma? "
Kabir cikin alamar damuwa yace "Dude yau princess takashe wayarta Bata jira mukayi hiraba Kasan ina sonta sosai Wlh Ina gudun kada Wani matsala yafaru"
Abdul cikin tausayi yace "Nasan wanda baya soyayya idan yafara to yana matukar wahala amma Kai wannan soyayyar dakakewa yarinyarnan tayi yawa Ai, watakila wayarta ce Caji yakare kayi Mata Uzuri, ka godewa Allah ma tana Sanka Kaima kana Santa amma Nifa? Yarinyar dana tsana Dady yake auramin tun ranar datazo da KANWATA gidannan nake fad'a maka kanwata tadaina Yimin magana sosai sai ita, duk wani shakuwa dake tsakanina da kanwata yarinyarnan ta kwace, dan ita kanwarta tarasu shiyasa take Kokarin kwace tawa"
Dariya Kabir Yayi sosai har yana Rik'e ciki, da kallon harara Abdul Yake binshi, ni kakewa Dariya?
Kabir ya girgiza Kai yana toshe Baki, saida yad'an lafar da dariyan yace "Amma yarinyar tanada Kyau Ko?"
Abdul yace "yaushe zan tsiya Inga Ko tanada Kyau Ko batadashi? Idanma tanada Kyau dafawa zanyi Inci? Taje can takarata da idanunta Kamar na mayu d'in"
Kabir yace "Lalle yarinyarnan tashiga uku irin wannan tsanar Dan Allah Kad'an rage Ko kad'an ne please dude"
Tsaki Abdul yaja ya kwanta tareda rufe jikinshi da blanket,
Yaye Blanket d'in Kabir Yayi yace "Yawwa gobe zanga kanwarka dakake bani labari a school"
Abdul yace "Allah ya kaimu" tareda kara Jan bargon, cirewa Kabir yakumayi da fishi Abdul yatashi yace "Dan Allah ka kyaleni Nayi bacci kwana uku Bana samun bacci me Kyau wallahi"
Kabir yace "Wallahi Baka isaba Kaifa kaje hotel ka d'aukoni sannan kace zakayi bacci? Never, Ai Ance bakonka annabinka"
Tsaki Abdul Yaja sannan ta Mike yace "to inaji me zanyi maka? Badai kakira budurwarka wayar a kasheba saika kwanta kayi bacci?"
"Ai data d'au Wayana babu abinda zai hanani bacci me dadi amma Ina yau Nida bacci sai addu'a"
Dariya Abdul Yayi yace "ka manta sanda muke school idan Ina wannan tunanin sai kayita tsaki kace Inasa kaina a damuwa a banza, bakasan soyayya ce ba"
Kabir yace "Tabbas a da na d'auka Mata ba abin girmamawa bane, amma Yanzu Nasan darajan Mata, Ada Bana soyayya Saide duk yarinyar data birgeni Nasa anemota Ko 'yar gidan Uban Wayene sainayi abinda naga dama da ita, amma tunda princess tashigo rayuwata ta canja min shi, nadaina banzan alaka da Mata nafara basu girma a matsayinsu na iyayenmu, Allah ka gafartawa Mahaifiyata sannan ka taimaki kowacce mace a duniya da lahira, ya Allah ka taimakawa Mata a cikin sana'arsu dakuma baiwa yaransu tarbiyya"
"Ameeen" cewar Abdul, cikin mamaki Abdul Yakuma cewa "Dude Allah yasa ka auri Wannan yarinyar Dakace ta gyara rayuwarka, dukda banga hotonta ba amma Nasan tanada Kyau kuma tanada kyakkyawar hali"
Mikewa kabir Yayi yafara zagaye d'akin, cikin muryanshi daya canja zuwa rauni yace "Wallahi koda ace batada Kyau zan aureta, bakaje kaga yanda Me martaba Yake gudanar da mulki cikin ilimi ba Yanzu, koda ta kurumce ne Ko kuma ta makance Kota gurgunce na rantse zan aureta"
Dawowa Yayi kan gadon yariko hannun Abdul idonshi yacika da hawaye yace "Ina sonta Kamar Raina, I love her vary much, bhohot pyaar"
D'an murmushi Abdul Yayi yace "Nasani daga ganin idonka Ansan kana cikin soyayya me zafi Allah de yabaka sa'a"
Knocking na kofar akayi da karfi, Abdul yace "waye?"
Muryan Baby ta tsinkayo tace "Yaya nice"
Tashi Yayi ze bud'e kofar, Kabir ya kwanta da sauri ya lullub'e fuakarshi acewarshi bayaso kowa yaganshi sai gobe,
Abdul yana bud'e Mata yadawo yazauna yace "lafiya"
Kallon kan gadon tayi tace "Yaya waye wannan?"
"bakona ne"
Ajiyar zuciya tasaki lokacin data hango kafar namiji Wlh har zuciyarta takusa bugawa tazata Macece Akan gadon, harara ya banka Mata yace "me kike so?"
Tace "Yaya Nazo karb'an maganine Wlh jikin Adda Yayi zafi sosai zabzab'i ne yakamata har jikinta yana rawa"
Tsaki Yayi yace "Ina ruwana? Badai kid'auka ba gashi can, bazama Ki kirata da sunanta ba sai Adda kenan Ko? To Ko wuk'a ne kada kikara bugamin Kofa da dare akanta Kinajina? Kuma kinyi ajiyane Akan gadona dakika tambiyeni waye wannan?"
Girgiza Kai tayi, yace "zaki d'auka kifita ko saina Karyaki?
Da sauri taje ta d'auko maganin zabzab'i tafice a d'akin, tashi Yayi ya rufe yadawo, Kabir ne yamike yace "Kamar Nasan Muryan nan"
Abdul yace "ka manta lokacin danabar Wayana a wurinka takira kuka gaisa?"