Showing 21001 words to 24000 words out of 139192 words

Chapter 8 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

898

gama jinin daya fito a jikinmu suka shafa akan kyallen sannan suka juya sukayi tafiyarsu babu tausayi ba imani, wad'annan mugayen masu gadin suka fara dukanmu da bulala akan mu tashi mutafi, da mukaji dukan yayi mana yawa shine muka mike amma banda Amina wacce bakinta yake motsi, a hankali nakai kunnena daidai bakinta Dan naji me zata fad'a sai naji tana cewa Dan Allah idan Allah ya kub'utar damu a hannun wad'annan mutanen mu taimaka muje Kano unguwar Rimi muce wayene malam Hamisu muyi mishi bayanin abinda yafaru damu sannan muce mishi 'yarshi Amina ba guduwa tayi ta barshi da ciwo ba wasu mugayen mutanene suka kamata daganan naji Amina tana salati bansan lokacin Dana kurma ihu ba ganin jikinta ya sake idonta ya rufe, ina kuka sauran 'yan uwana suna tayani Amma wannan marasa imanin yasa akayita dukanmu har muka fita mukabar gawan Amina" tsit d'akin yayi bakajin karan komai sai kukan da sukeyi babu shakka suma watarana mutuwa zasuyi a hannun wannan mugayen, Fadila idonta yayi ja, jitayi babu Wanda ta tsana a duniya kamar Kanwarta wato Amrah, wannan wani irin kiyayyane Amrah ta nuna mata a fili haka? Kukan zuci da kukan fuska duk saida tayisu, Baby ma kukan take ba sassautawa tunawa datayi da yayanta Wanda yake matukar sonta dayasan halin datake ciki babu shakka dasai zucuyarshi ta buga ya mutu, Fadila ce ta lura da kukan da Baby keyi, ita a halin yanzu batason ganin kannen mytum ma, ta tsani sunan Kanwa a rayuwarta domin abinda kanwarta tayi mata, Kawar da kanta tayi bata yiwa Baby magsna ba, matsowa Baby tayi kusa Da ita tace "Adda meyasa bazaki rarrasheni ba yau?"

Fadila kallonta tayi na 'yan wasu lokuta kafin cikin siririn muryanta tace "Baby Dan Allah kada kikara kirana da Adda na tsani wannan Kalmar banaso kicemin Adda kuma banaso kicemin Yaya ki kirani da Fadila kai tsaye"

Cikin mamaki Baby ta kalleta tace "Adda lafiya kuwa me nayi miki?"

Cikin tsawa Fadila tace "nace miki banason sunannan na tsani Kanwa a rayuwata idan kincemin Adda hakan yana nufin ke Kanwata ce, nikuma na tsani Kanwa banaso!!! Banaso!!! Banaso!!!!"

Jikin Baby ne yafara b'ari domin bata tab'a ganin Fadila a wannan yanayin ba, a hankali tace "shikenan naji bazan kara kiranki da Adda ba Fadila zan rika kiranki amma kisani badan zuciyata taso hakan ba"

Fatima sai kallonsu take cikin mamaki tacewa Fadila "Dama ba kanwarki bace?"

Fadila gid'a kai tayi cikin hawaye batace komai ba, Baby tace "ni daga Abuja nake ita kuma daga Adamawa"

Fatima itama tace "nikuma daga Gombe nake GRA gidan Adviser na gwamna babana shine adviser na gwamna, Kallonta Fadila tayi tana mamakin yanda akayi yarinyar tazo nan, Fatima cikin dariya Wanda yafi kuka ciwo tace "nasan kunada tambaya ya akayi nazo nan ko? Hmmm wannan guyson d'inne yayimin magana ta Instagram tun bana kulashi harna fara kulashi a haka muka kulla soyayya dashi na tsawon lokaci har yacemin zaizo ya Aureni nikuma na sanar da iyayena, babana tunda yaji wannan maganar yace shikam bai yadda ba, nikuma da giyar soyayya ta d'ibeni a take naje nasamu yayanshi daga karshe dai akasa Babana dole ya amince, shine guyson yazo yayi gaisuwa yayuna duk basaso amma ni na tirje nace saina Aureshi, dahaka akasa Date na Aurenmu, saura sati d'aya bikinmu shine yace na shirya muje siyan kayan laife, nikuma na shirya mukayi sallama da Mamana Ina shiga motarshi naga ya nufi airport dani, dana bud'i Baki zan tambayeshi ya zabgamin mari yaciro bindiga yace idan nayi magana saiya kasheni haka yasani ina dariya har muka shiga jirgin dahaka nazo kasarnan"

Fadila da Baby sun mugun tausayawa yarinyar, cikin kuka Fatima tace "Idan zaiyi inason mu kulla kawance daku don bamusan Wanda Allah zai kub'utar ba anan"

Fadila tace "insha Allah dukkanmu zamu kub'uta" cigaba sukayi da kukansu babu me lallashi.

      "Mutanen gidansu Kamal sun watse babu kowa sai Amrah da Kamal da Ummanshi sai Hajiya Turai wato yayar Umman Kamal wacce tace bazata tafi yanzu ba saita huta, Kamal ne yafito daga d'aki idonshi a kumbure fuskarshi yayi jaa alamar yasha kuka bana wasa ba, Umma ce ta zuba mishi ido taga yanda ya rame a lokaci guda kasusuwan wuyanshi duk sun bayyana tsinewa Fadila take a zuciyarta tana ja mata Allah ya isa datasa d'anta a wannan halin, Kamal yana zuwa yafad'a akan kushin ya lumshe idonshi yana kallon Fadila rungume da namiji akan gado, wasu siraran hawayene suka fara bin fuskarshi, Hajiya Turai ce tace "Kamalu zaka sawa Kanka Damuwa a banza, tun farko da kunyi bincike da hakan bai faru ba, iyayen yarinyar basuda kunya tunda suka kasa baiwa 'yarsu tarbiyya me kyau, nikam Ku kiramin kanwar tata in kara ganinta"

A hankaki Umma ta Mike taje part na Kamal tura kofar tayi a hankali lokacin Amrah tana zaune a gefen gado jikinta sanye da bakin dogon Riga me ratsan pink, kanta d'aure da d'ankwali pink tana danna waya tun jiya take kiran number na guyson amma swift off shiyasa yanzuma ta zauna tana kara gwadawa jin an turo kofa yasata saurin shiga wurin Game tafara yi kamar da gaske, Umma ce ta karaso d'akin bakinta d'auke da sallama amma can ciki tayi, Amrah d'ago kanta tayi ta sakarwa Umma murmushi cikin kadabi ta gaidata, Kallonta Umma tayi for a second bata amsa gaisuwan ba tace "kibiyoni Falo yayata tanason ganinki"

Tana fad'an haka ta juya tafice, Amrah binta da ido kawai tayi tana sake sake a zuciyarta "yayarta?" Shine abinda Amrah tafad'a kafin ta d'auko wata 'yar karamar gyalle ta yafa a kanta ta d'auko wayarta tafice a d'akin zuwa Falon, kallon cikin gidan takeyi ya tsaru iya tsaruwa, tanaji kamar ba ita bace a cikin gidannan, murmushi ta saki tunowa da itafa yanzu tanada 'yanci akan wannan katafaren gidan, daidai wani kofa ta tsaya tayi sallama, Amsawa akayi can kasa ta bud'e kofar tashige, zama tayi a gefen kushin ta dukar da kanta tace "gani"

Kallonta Hajiya Turai tayi daga sama har kasa kafin tace "Dama kinsan yayarki tana karuwanci kuma baki fad'awa Kamalu ba?"

Amrah ta kara dukar da kai cikin sanyin murya tace "eh Hajiya ina tsoron fad'a mishi ne sabida banaso na b'ata yayata a idon duniya"

Hajiya Turai ta kara kallonta tace "kin kiyaye martabar gidannan kuma kin tsare mutuncin yayarki dama can Allah yayi Kamalu shine zai zama mijinki shiyasa hakan ya faru, to Amma ba anan gizo ke sakar ba, shin idan yayarki taji kin Auri Kamal zata yafe miki? Kina ganin zata barki ki zauna lafiya da mijinki?"

Sai a lokacin Amrah ta d'ago kanta ta kalli Hajiya Turai, tace "Insha Allah babu abinda zai faru nariki Addu'a kuma itama Adda Fadila inayi mata Addu'an Allah ya shiryeta" hawayene yafara bin kuncinta a hankali tasa gefen mayafinta ta goge, Hajiya Turai da Umman Kamal sunji tausayinta sosai banda Jamal Wanda yaji ya tsani zuriyarsu ma gaba d'aya, cikin tausayi Umma ta mike ta d'ago Amrah wacce taketa aikin kuka a hankali tafara goge mage mata fuskarta tace "shikenan kidaina kuka babu abinda zai faru insha Allah tashi kitafi d'akinku kinji?"

Gid'a kai Amrah tayi kafin ta juya sum sum ta tafi.

      "Saida su Fafida sukaga babu abinda kuka zaiyi musu saidai ya haddasa musu ciwon kai yasa suka mike kowa yayi Alwala sukayi sallah ba maganar abinci saidai susha ruwa su zauna, da dare suna zaune sukaji tsaiwar mota jikinsune yafara rawa dan sunsan abinda za'ayi musu, Addu'a suka farayi kowacce tanajin zuciyarta yana bugawa, kamar jiya haka yauma yashigo dawasu manyan mutane amma daga ganinsu kasan 'yan kasar Nigeria ne, suna shiga guyson yace kowa ta mike, jikinsu yana b'ari suka fara mikewa kowacce tana Addu'an Allah yasa kada a d'auketa, saida suka kallesu tas kafin wani mutumi me jiki baki ya zubawa Babyn Yaya ido, Baby ganin haka yasa ta koma bayan Fadila ta b'uya bakinta har rawa yake tsabar Addu'a, mutumin ya saki murmushi yanuna Baby wacce ta b'uya tana kallonashi, yace "nifa ga wacce tayimin wannan nakeso"

Damke Fadila Baby tayi kamar zata mayar da ita ciki, Guyson yace "ke ba magana ake miki ba? Kinsan waye wannan kuwa dahar zai nunaki kina mishi raini"

Baby cikin Kuka tace "Dan Allah kuyi hakuri nifa ba 'yar iska bace" dariya suka kwace dashi gaba d'ayansu saida sukayi me isarsu kafin mutumin yace "to ai dama munfi son irinku sabida zamu samu kud'i masu d'unbin yasa Wanda zamuyi siyasa dashi"

Guyson ya karaso wurin ya fizgo Baby a jikin Fadila yana kanta tana turjewa sai kiran Adda Fadila kawai takeyi tana mikowa Fadila hannu alamar ta taimaka mata, Fadila ganin yanda ake Jan Baby a kasa kuma ta tuno da yanayin yanda aka kawo sauran 'yan uwansu jiya yasa taji bazata iya urewa ba dole ta taimaka mata, da gudu ta karasa wurinsu tariko hannun Baby tana janta, Guyson ganin haka yasa wani kati Wanda yake gefenshi d'auke da bulala yace yazana Fadila tunda abin nata raini ne, dukan Fadila aka farayi ba kakkautawa, tanajin zafin dukar amma burinta ta kwato Baby a hannunsu, saida sukayi mata dukan rashin Imani kafin suka janye Baby da karfi dayaji suka tafi da Ita, Fadila tana kwance tamikawa Baby hannu, babynma hannu take mika mata har akasata a bayan mota sukaja suka tafi da ita. kuka ma Fadila tana neman tayishi amma hawayenta sun kafe, jitake zuciyarta kamar wuta, wani irin rad'ad'i takeji a kasar zuciyarta, dukar da kanta tayi kasa tafara bugawa ko zataji saukin abinda yake daminta, Amma ina saima ciwo da rad'ad'ine suke kara zuwa mata "me nayi? Me nayi danake ganin irin wannan rayuwar? Amrah me nayi miki? Ki fad'amin Dan Allah wallahi zan gyara bazan karayi miki abinda nayi miki har kika kawoni cikin wannan rayuwar ba, da ace kin barni a kasata kusada iyayena wata kila zan yafe miki idan kika Auri Kamal Amma baki barni ba kin rabani da kowa bazan tab'a yafe miki ba" kukane yaci karfinta a kasa ta sunkuya tanayi kamar ba gobe, Fatima ce tazo wurin ta dafata itama tana kuka tace "Fadila dolene ki koyarwa zuciyarki da wahala, domin wannan kazamar rayuwar yanzu muka fara, bazamu tsirewa wad'annan azzaluman ba, su sunje sun b'oye iyalansu da 'ya'yansu a gida mukuma sun kawomu nan suna gallaza mana azaba suna anfani damu ta karfi da yaji, bazan Allah yace ka dubi zunubinka ba dasai muce akwai kallo ranar lahira, yanzu kiduba duk yawan 'yammatan nan akwai matar wani akwai kanwar wani sannan akwai uwar wani, kuma sun manta cewa idan kayi zina da 'yar mutane to kaima bashine dole kabiya idan Baka biya da 'yarka ba zaka biya da matarka, balle irin wannan ba zina kad'ai sukeyiba harda tsafi sunayi domin farin kyallen Dana gani a hannunsu ya tabbatarmin ba banzaba, Allah yayi mana sakayya"

Sai a okacin Fadila ta d'ago kanta ta zubawa Fatima manyan idanunta Wanda suka rine suka koma jaa, cikin shakakkiyar murya Wanda baya fita sosai kamar wacce mura ya kama tace "Kinyi gaskiya Fatima Allah yana kallo bazai barmu a haka ba"

Fatima ce ta taimaka mata ta riketa har zuwa d'akinsu sauran matan sai kallonsu suke cikin tausayi sunajan Allah ya isa.

Kwanciya Farida tayi akan gado ta runtse idonta Wanda take ganin duhu duhu, saurin bud'e idon tayi ganin hoton Baby tana kuka tana mika mata hannu, Fadila haushin kanta takeji na yanda takasa taimakawa Baby, gani take kamar Baby bazata dawo da rai ba, janyo filo tayi ta toshe fuskarta akai ta saki kuka Mara sauti don bataso kowa yajita bale suyi yunkurin bata hakuri, a halin yanzu batason a rarrasheta tafison tayi kukan ko zataji da sauki a zuciyarta, ta tabbata gobe itama zasu d'auketa kuma batada zab'i dolene tabisu Dan bazata iya musu gardama ba, sabida dukan ya isheta haka.

    "Unty Sadiyace taje gidansu Farida ranta a b'ace tasamu Mama ta irga mata duk abinda yake tafiya ta kara dacewa "nifa Mama Sam ban yadda cewa Fadila gudu tayiba nafi kyautata zaton saceta akayi"

Mama tace "Sadiya da kunnena naji muryan Fadila tana cemin ita bazata iya Aurennan ba, to meye kuma ya rage Wanda banji ba?"

Abba ne yafito daga d'aki ya zauna a bakin kofa yace "Sadiya koda Fadila ta dawo gidannan bazan barta ta zaunamin ba korarta zanyi idan tay wasa saina karya kafarta, ba dunya ba? Taje zata gani gata gashi duniya Wanda baizo bama tana jiranshi bale Wanda yake ciki, ai ba sauran magana"

Unty Sadiya duk yanda taso ta fahimtar da iyayen Nasu sun kasa fahimtarta idan tashiga tanan saisu fito mata tacan daga karshema ta gaji ta tashi kawai ta tafi ranta a b'ace

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 15*

       ~ganin idan tana kwance bazata iyayin komsi ba yasata mike tafara zagaye d'akin, d'akin ma baiyi mata ba tafita zuwa cikin gida tana kai kawo tarasa mafita, Fatima ce tazo tana kara bata hakuri akan ta daina sa damuwa a ranta Fadila tace "yaya zanyi Fatima? Nakasa taimakon Baby daga hannunsu Allah ne kad'ai yasan abinda zasuyi mata yau"

Itama Fatima dauriya kawai takeyi idan bahakaba tamafi Fadila Shiga damuwa domin ita tasan abinda yafaru dasu jiya, ahaka ta b'oye damuwarta ta baiwa Fadila hakuri har suka shiga d'aki.

       "Amrah tana Fita a d'akin ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, yau tayi nasara akan Umman Kamal babu shakka gobe sai tayi nasara akan Kamal da kanshi, koda batayi nasara gobe ba zatayi Wata rana, kiran number guyson tayi suka gaisa tace "Guyson banida kud'i a kasafa Dan Allah ka turamin banajin dad'i idan babu kud'i a account nawa sabida tsaro badan tsoro ba"

Dariya Guyson yayi yace "an gama Hajiya kedai kijira zuwa anjima zakiji alert"

Godiya tayi suka kashe wayar tanajin zuciyarta fess, d'akinta da Kamal tashige tayi wanka tareda Alwala tazo gaban dressing mirror tayi kwalliya tareda feshe jikinta da turaruka masu kamshi, wata doguwar Riga purple me hannun vest tasa, ta d'auko d'ankwali fari ta d'aura, zuwa tayi gaban mirror taciro Jan baki purple ta shafawa karamin bakin ta, hoda ta d'auko tana shafawa taji an bud'e kofar, waigawa tayi Dan ganin ko waye, Kamal tagani yashigo jikinshi a mace kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai, hanyar toilet yawuce yana shiga ya cire kayan jikinshi yazauna a cikin bathtub ya kunnawa kanshi shower lumshe idonshi yayi yanajin yanda ruwan yake bin jikinshi kamar ya dawwama a haka yakeji, saida yad'an farajin sanyi kafin yafice a ciki yad'au towel ya d'aura daidai west nashi dawani karami ya d'aura akanshi yana gogewa, fita yayi a cikin toilet d'in lokacin Amrah ta kwanta akan gado suna waya da Mama wacce taketa shiwa Amrah Albarka, Amrah sai amsawa kawai take da "Ameen" tana kallon Kamal Wanda yake shafa mai yanajin duk abinda takeyi, fuskarnan tashi a had'e Lamar bai tab'a dariya ba, saida yagama shafa mai kafin yashafa turare yaje wardrobe yad'auko suit yawuce toilet saida yashirya tsaf kafin yafito, gaban mirror yaje ya taje gashin kanshi yashafa mishi mai yasa takalmi, daganan yad'au jakarshi na zuwa office da makullin motarshi Wanda yake gefen Amrah wacce ta zuba mishi manyan idonta kamar ta had'eshi takeji, yana d'aukan makullin yajuya yafita a d'akin ko kallon inda take baiyi ba, yana fita ta sauke ajiyar zuciya "yanzu wannan gayen shine mijina? Kai gaskiya naji dad'i kamar a mafarki" d'auko filo tayi ta rungume gam a jikinta ta runtse idonta tanaji kamar ba itaba.

         "Washe gari Fadila tana kwance akan gado hankalinta duk baya jikinta idanunta sun kumbura tsabar rashin bacci yanda taga rana jiya haka taga dare, tunanin rayuwarta kawai takeyi da tunanin halinda 'yan uwanta suke ciki, sauran 'yammatan ma haka suka zauna shiru kowacce tayi tagumi,

B'abgaren Baby kuma suna fita aka kaisu wani babban Hotel nacikin garin Sudan, da kallo takebin wurin tanajin yanzu zuciyarta tafara bushewa domin duk wani tsoro tadaina ji, wani d'aki aka kaita babba saibin d'akin take da ido, bayan wasu mintuna saiga mutumin daya zab'eta hannunshi rikeda farin kyalle yana murmushi, Baby ganin haka yasa tafara ja da baya shima binta yake har suka iso wurin drawer cikin muryan mugunta yace "duk gudunki bazaki wuce d'akinnan ba"

Baby had'a hannunta tayi biyu tafara bashi hakuri amma ina Sam yayi nisa burinshi ya aiwatar da kudurinshi akanta, Baby ganin ya nufota gadan gadan yasa tajuya wurin drawer taga kwalban mirinda da ragowa kad'an a ciki, d'auka tayi ta bulbular da sauran a kasa ta buga kwalban jikin bango fass ya fashe yarage wani dogo a hannunta, nuna mishi tayi tace "wallahi idan ka tab'ani saina kasheka"

Dariyan mugunta ya kwance dashi kafin yace "babban kuskuren da zakiyi shine ki kasheni yarinya"

Baby tace "wallahi zan soka maka kwalbarnan idan ka tab'ani kaji na rantse maka"

Yana jinta yafara kokarin cire hijabin jikinta Baby ganin da gaske yake yasa ta d'aga kwalbar ta soka mishi a ciki, waro ido yayi ya kalleta Yakuma kallon cikinshi da jini yafara bi, Baby cikin kid'ima da tashin hankali ta turashi gefe d'aya ya fad'i yana mutsu mutsu yana miko mata hannu alamar ta taimaka mishi, da gudu tajuya tashige band'aki ruwa ta d'ibo tazo wurinshi tana sa mishi a baki, hannunta ya damko yana yana murzawa da karfi, jikinshi ne yafara rawa yana mika a hankali yana kallon Baby, can taga idonshi ya juya yayi fari hannunshi a cikin nata zuwa lokacin hannun ya daina motsi, ihu tayi tana jijjigashi "Dan Allah ka tashi kada ka mutu a hannuna nima kasheni zasuyi" ganin baya motsi yasa ta kid'ime tana ihu, mutane suna ta babu wanda yashigo ya taimaka mata, ganin haka yasa ta fara shafa jinin ajikin skirt nata  sai kuka takeyi ta rud'e tama rasa yanda zatayi, ganin batada mafita yasa taja gawan ta tura karkashin gado da kyar ta sake ahinfid'a zanin gadon ta rufe kafafunshi dashi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login