Showing 93001 words to 96000 words out of 139192 words
tayi tana kallonshi, akan gadonta ya kwantar da ita, blanket yaja ya rufata dashi rufe idonta tayi ba zato taji ya hau gadon ya kwanta a gefenta, janyota jikinshi yayi ya rufasu da blanket ɗin, waro ido tayi tafara kiciniyar kwace jikinta, a hankali ya raɗa mata "pleassse a kunnenta"
Fadila tarasa dalili duk lokacin dayace mata please sai taji tausayinshi sosai ya kamata, shiru tayi tana kallonshi yaɗan lumshe ido dahaka har bacci yayi gaba dashi, ido ta tattara ta zuba mishi tana kallon fuskarshi, haka kawai taji inama ace auren soyayya sukayi dashi? Dako zata kula dashi har sai ta mantar dashi wannan princess dayake yawan ambatonta, bataga yarinyar ba amma wallahi har zuciyarta taji ta tsani yarinyar, hannu tasa akan gashin daya tara akanshi kuma yake gyarawa sosai, a hankali take cusa yatsunta ciki tana fitarwa, Abdul daɗa rungumeta yayi yana sakin ajiyar zuciya a hankali cikin bacci, itama dahaka bacci ya saceta.
Asuba tagari.
"Amrah sunyi kwana uku basu magana da Mama ko kallonta mama batayi albarkacin Abba ne take zaune agidan da Mama ta koreta, Abba daya fara magana kaɗan kaɗan yakira Mama yace "kiramin Amrah"
Mama kallonshi tayi tace "me zakayi mata?"
Abba yace "gaskiya zan faɗa mata"
Mama tace "bakaga cutarmu datayi ba? Har zaka faɗa mata gaskiya? Ka kyaleta dama Fadila ce kafaɗawa gaskiyar dayafi akan wannan yarinyar, banaso ina yawan zama ina kallonta sabida zanzo nayi mummunar magana akanta wanda ze hanata gamawa da duniya lafiya shiyasa nake nesanta ta damu"
Abba yace "kiramin ita yau inajin jikina sosai bansan ko zan kara kai gobe a raye ba, tunda Fadila batanan yakamata nafaɗa mata"
Mama tace "haba Kai kuma wani..."
"Ki kiramin ita nace"
Mama taɗan tsorata kafin ta fice zuwa ɗakin Kulu, Shayi kulu ta ɗibo baki tana baiwa Amrah wanda tasha kaɗan ta ture cup ɗin, kulu tace "kwana uku fa bakici komai ba idan bazakici dan kanki ba kici dan ɗan dayake cikin cikinki mana"
Amrah tace "idan banci ba ze iya mutuwa ko?"
Kulu tace "tabbas ze iya rasa ranshi idan bakicin komai"
Amrah tace "to Allah yasa ya mutu kada yazo duniya da rai indai hakane bazan kumacin komai ba"
Kulu tace "bakida hankali ne kisan kaifa zakiyi kuma ai wannan yaron shine ze zame miki gata dan bazeso yaga uwarshi acikin halin kunci ba"
Amrah tace "zeji tausayina kafin yaji labarina amma dazaran yaji labarina tofa labari zesha bamban"
Mama ko sallama batayi ba tace "Abban Fadila na kiranki"
Zuciyar Amrah ne yabada wani sauti me ban tsoro jikinta yafara rawa, kulu ce taɗan riketa tace "yi ahankali"
Mama juyawa tayi tafice, Amrah tace "Kulu bazanje ba wallahi bazanje ba Abba ze kasheni a ɗakin can"
Kulu tace "idan bakijeba shine babban Matsala ki daure kije zan tsaya a bakin kofa Idan naji yana dukanki zan shiga"
Amrah tace "kiyimin alkawari"
Kulu tace "nayi alkawari"
Da kyar ta mike ta ɗauko wani riga takara akan na jikinta tasa hijabi biyu sannan tasa rigan sanyi asaman wai acewarta bulalar bazata shigeta sosai ba, duk abinda take Kulu tana kallonta, gishiri ta ɗibo tashafa a hannunta dan bulalan ya karye idan an daketa (har natina da Walidation da Maamah idan munyi laifi akace bayan mangrib za'ayi mana hukunci ranar gishiri kamar anyi ɓarinshi a jikinmu yarinta daɗi)
Saida tagama kafin tanufi ɗakinsu Tayi sallama a hankali, ganin Abba zaune akan kujera yasa ta zauna abakin kofa tayi redin gudu, Abba yace "tashi kizo nan" tashi tayi ta zauna a gefe, Mama ma na zaune da gyaɗa a hannunta tana ɓarewa, Abba yayi shiru kusan na minti goma, Amrah tace "Abba dan...."
Hannu yaɗaga mata yace "ba ke kika kirani ba nina kiraki"
Shiru tayi ta dukar dakai, Abba yace "dafari dai nayi bakin cikin abinda kika aikata sannan naji haushinki ba kaɗan ba, Amma dana zauna nayi tunani sai nayi bakin cikin haifana da akayi a duniya, duk abinda yake faruwa baku bane da laifi nine me laifi"
Mama tace "Haba dan Allah ya kake faɗan hak.."
Ɗagawa mama hannu yayi yace "Dan Allah maryama ki kyaleni nafaɗi abinnan yau kada ki katseni idan kina kaunar annabi muhammad (S A W)"
Tsit Mama tayi bata kara koda tari ba awajen.
Abba yaci gaba dacewa "Shekaru talatin da suka Wuce nataɓa auren wata balarabiya daga kasar makka, hakan yafaru ne sanadin rashin ji danayi fama dashi ina saurayi iyayena sunce kada natafi kasar dababu dangina nikuma nace sai naje, dahaka naje Kano na yanki visa natafi saudi, acan nahaɗu dawata balarabiya ƴar shekara goma sha bakwai, dashike inada kyau kuma ina ɗaukan wanka sannan inada class sosai hakan yasa Hindu takamu da soyayyata, dukda iyayena basuda wani karfi amma na nuna mata cewar ni ɗan masu kuɗin gaskene a Nigera, Hindu yarinaya ce kyakkyawa kuma batason magana sosai, akwai wani yayanta al'amin jinina be haɗu dashi ba samsam, ya lura inada karya sosai hakan yasa yafaɗawa Iyayensu a rabamu da Hindu, agida anyi mata faɗa har an hanata fita sabida ni amma ina nariga na koya mata soyayyar da bazata iya kwana ɗaya bata zauna kusa dani ba, wannan abun ya haifar da gaba me tsanani tsakaninta da Al'amin, wata rana naje bayan gidansu na ɓata wutan gidan gaba ɗaya, hakan yasa suka fara neman masu gyaran wuta, nikuma nasa face mask narufe duk wani sign dazasu gane nine naje nayi sallama agidansu, Babanta yafito yace "waye kai?"
Nikuma nace "sunana Ahmad ina bukatar taimako na ruwan sha domin ni ɗan nepa ne"
Babanta yayi dariya yace "shigo"
Dahaka nashiga suka bani ruwa me sanyi nasha sukace nayi musu gyaran wutan kafin nanda safe sukira masu gyaransu na asali, na amince amma nace saina duba duk wani glof na gidan, Al'amin ne yake nunamin ɗaki ina dubawa harya kaini ɗakin Hindu, ganin Hindu kwance yasa nayi ajiyar zuciya naduba glof ɗin ɗakin, Al'amin yace "saura na toilet" muka shiga toilet ganin dagani sai al'amin yasa naɗau sandan mopping na buga mishi akai da karfi, zaiyi ihu na rufe mishi baki na turashi gefe na cire kayan jikinshi, kanshi yana jini na rufeshi a toilet ɗin nafito waje, Hindu ganina da kayan yayanta ta buɗe baki zatayi ihu, nikuma da sauri nacire face mask ɗina, tana ganina tamike da gudu tana kuka ta rungumeni, nima rungumeta nayi, nace "oya kisa kayannan mufita yanzu"
Karɓan kayan tayi tasa nabata face mask muka fita, Babansu na cikin gida yace "ya dai?"
Nace "zamuje waje da Al'amin mu gyara"
Yana dariya yace "yawwa"
Kasancewar akwai duhu yasa bega fuskar ba amma yaga kayan al'amin shiyasa ya yadda dani, dahaka nasamu nagudu da Hindu, satan gold nayi awurin wani balarabe nabiya mana kuɗin jirgin nigeria nida hindu, haka muka dawo gida Nigeria, Nayi tsammanin zata kini idan tagano cewar niba ɗan me kuɗi bane, amma haka ta hakura iyayena sunki yadda muyi aure mukaje wurin ƴan hisba sukayi mana aure, Hindu yarinyace me hakurin gaske, munyi shekaru Biyar da ita banida aikin yi haka tayita hakuri dani, ganin har yanzu Hindu bata haihu ba yasa nafara juya mata baya, tarinka yimin nasiha akan nayi hakuri haihuwa Allah ne ke bayarwa, nikuma narufe ido nayita mata wulakanci, ashe mahaifiyata ce take bata maganin hana haihuwa idan nafita saita shigo gidan tabata na dole, amma hindu bata taɓa faɗamin ba, ranar danaga haka amaikon nayiwa Mamana magana saina kwashe duk wani haushi na juye akan Hindu, ita kuma tace bataso tashiga tsakanina da iyayena shiyasa ta ɓoyemin, ta manta cewar ni nashiga tsakaninta da iyayenta"
Kuka Abba yakeyi sosai, Mama tace "kadaina tuna baya"
Abba yace "kibarni nayi kuka"
"Daganan Hindu tadaina shan maganin dahaka har Allah yabata ciki, da samun cikin tazata zata samu sauki awurina amma ina nikam rashin kuɗi yasa narinka gana mata azaba wani lokacin har tana kwana da yunwa, Hindu tayi baki ta lalace idan ka ganta bazakayi zaton daga saudi takeba saidan hasken datakeda shi,
Dahaka har Cikin yakai haihuwa babu abinda yake fita daga bakin Hindu sai Allah yabiyamin hakkina, kaima sai Allah ya nuna maka bakin cikin daka nunamin, gashi batajin hausa bata iya sabo da mutane sai turanci sai Hausa, mahaifiyata tsabar shishigi saida ta koyi turancin karfi dayaji danta ɗanawa Hindu azaba, su alokacin sunaso ba auri Maryama wato Mamanku, ciki harda Maryama itama tanunawa Hindu kishi afili, Ranar da Hindu zata haihu takira sunana, nikuma na amsa da na'am dan tabbas inason Hindu sosai, Hindu tace "Ubangiji ya sakamin abinda kayimin" jikina yayi sanyi sosai amma banyi tunanin neman gafara a wurinta ba nabari wai saita haihu saina nemi tuba, amma bahaka Allah ya tsara ba, Hindu tana haifan yaronta tace "dan Allah kasa mishi sunan mahaifina Khalil ko kuma Yayana Al'amin"
Maganarta na karshe kenan daganan Hindu tace ga garin naku, nayi kuka sosai sannan nayi nadama, Kasancewar akwai gaba tsakanina da Al'amin yasa nave Mata gaskiya bazan iyasa sunan Al'amin ba amma zansa sunan mahaifinki, Hindu bata kara cewa komai ba har Allah ya ɗauki rayuwarta, a ranar nayi kuka nayi nadama mahaifiyata kuma bansan wani hali tashiga ba farin cikine ko tashin hankali? Haka nasawa ɗana suna KHALIL, Daganan Khalil yakoma wurin mahaifiyata, yaron tun yana karami yafara ganin wulakanci da mahaifiyarku da mahaifiyata suka taru suka gallaza mishi azaba, nikuma soyayyar Mahaifiyarshi na haɗa da nashi nabashi inason khalil sosai, ganin irin azabar dasuke bashi idan bana gida kuma shi bame magana bane yasa watarana nakirashi ɗakina na ɗauko aska na rufe idona na buɗe bayanshi nayi alamar K a bayanshi dalilin hakan kuwa shine koda ya ɓata zanyi saurin ganoshi, haka nayi jinyar wannan K ɗin harya koma baƙi daganan yazama tabo ajikin Khalil, shekarar Khalil biyar mahaifiyarku ta haifi Fadila ranar suna dasafe aka nemi Khalil aka rasa, na sanar gidan redio da jaridu amma shiru kakeji har yanzu babu labarin Khalil gashi inaga rayuwata takusa karewa, yanzu abinda yasa nafaɗa miki wannan maganar shine, idan kika nemo Khalil da Fadila kuka haɗa kanku to na yafe miki duniya da lahira bayan haka bansan abinda zakiyi na yafe miki ba"
Amrah datake kuka sosai tace "Abbb.." ɗaga mata hannu yayi yace "tashi kije nagama magana"
Tashi tayi tana kuka sosai tabar ɗakin, Mama da jikinta yayi sanyi itama ta share hawaye tareda mikewa tace "Ubangiji yana kallo zai maido mana da Khalil" Abba yace "tabbas da wannan tabon kaɗai zata gane Khalil"
Shiru sukayi duka.
"Fadila tana zuwa aikinta asibitinta yana karɓuwa sosai kasancewar tana kula da patients, Dady yana yaba kokarinta sannan itama Baby tana bada kyakkyawar gudumawa a asibitin, Abdul kullum saiya kara tunatar mata da ze kara aure tun abin yana damunta harta kwashe ta watsar taci gaba da abinda yake gabanta,
Zaune take akan kujera tana duba files na asibiti sallama Abdul yayi hannunshi rikeda makulli, amsa mishi sallamar tayi tace "sannu"
Zama yayi batareda ya amsa ba, yace "akwai maganar danakeso muyi"
Fadila ajiye files ɗin tayi ta tattaro hankalinta tasa akanshi, yace "am naje gida yau nacewa Dady zanje Adamawa ranar jumma'a zanje mu sasanta da yarinyar kafin iyaye sushiga cikin maganar"
Kirjin Fadila ne yafara bugu da karfi jin ya ambaci Adamawa, taso ta ɓoye tashin hankalin data shiga amma takasa, "lafiya!" Abinda Abdul yafaɗa kenan,
Fadila zufa ta share tace "Adamawa kuma?"
Kallonta yayi yace "me kikaji nace?"
Fadila tace "Kamar Adamawa"
Yace "eh Yola jimeta Adamawa"
Kallonshi tayi tace "Nima ƴar Adamawa ce"
"Nasani sabida mun taɓa kaiki nida Baby ko kin manta ne?"
"Aa.aa.aaa ban manta ba"
Tashi tayi tabar wurin bata kara cewa komaiba, Tsaki yaja yace "wai tana kishi tayi tagaji"
Yana faɗan haka yamike yatafi ɗakinshi.
_jiddah ce_[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 62*
~Kabir kwance yake a gefen me martaba ya ɗaura kanshi akan cinyar sarki, Mai martaba yace "Kabir naganka cikin damuwa sosai tunda kadawo daga Abuja faɗamin meya faru?"
Kabir shiru yayi bayason yafaɗi karya kuma bayason me martaba yaji gaskiya, Sarki yace "Kabir tun kana yaro babu abinda kake ɓoyemin to yanzu danka girma banaso ka ɓoyemin komai"
Kabir shiru yayi yana kallon sarki, Mai martaba yace "faɗamin abinda yafaru"
Hawayene suka cika a idon Kabir yace "Abba Fadila tayi aure na rasata abba itace ta auri My Dude"
Jikin mai martaba yayi sanyi sosai a hankali yace "kayi addu'a Allah yasa hakan shiyafi alkhairi a rayuwa akwai wani abu, munason abu to Allah besa hakan ne alkhairi a garemu ba saikaga ya hanamu, sannan wani kuma bamason abu sai kaga Allah yasa hakan shiyafi alkhairi saikaga yabamu, kayi addu'an Allah yasa hakan shiyafi alkhairi kaji?"
Kabir yace "dama shine addu'ar danayi Amma wallahi Abba nakasa cireta araina kullum wani sabon soyayyartane yake kara ɗarsuwa acikin zuciyata jinake kamar na haɗiyeta na huta, Kuma Dadyn Abuja yace ze auramin wata yarinya batajin magana sunanta Nabila, Abba natsani yarinyar kuma wallahi bazan iya musawa Dady ba"
Abba yace "karka damu idan baka sonta bazaka aureta ba, insha Allahu saika zaɓi matar aurenka da kanka zanyi magana da Alhajin kaji"
Rungumeshi Kabir yayi yace "nagode Abbana"
Abba yace "inasonka sosai Kabir banaso komai ya dameka wallahi bakasan yanda nake jinka a raina bane"
Kabir kara rungumeshi yayi yace "nagode Abba"
Abba yace "ka daina godemin kayimin addu'a kawai kaji?"
Kabir yace "tom Abba"
Haka sukaci gaba da firansu.
"Kwance Baby take akan gado tana rikeda waya kallon number take sosai kamar tana neman wani abu, a hankali takai wayar kan bakinta ta sakar mishi kiss me zafi kafin tace "i love you Kabir, ina sonka sosai wallahi" hawaye ta share tace "amma nasan kai ka ɗaukeni ne a matsayin kanwa, bakama san ina sonka ba, Kabir ina sonka wallahi ina sonka"
"Lafiyanki kuwa Baby? Keda wa kike magana?" cewar Momy data tsiya a bakin kofa, Baby tashare hawayenta da sauri tajuya tayiwa Momy murmushin karfin hali tace "ba komai Momy"
Shiru kawai momy tayi mata, tace "ga wannan maganin ki kaiwa Matar yayanki yanzu kice tasha yanda tasaba, saura ki tsaya kinamin tambayoyi kamar jami'ar binciken sirri"
Baby tace "momy Adda Fadila fa babu ma wani soyayyar dasuke itada yaya kadama ki damu kanki wurin aika mata irin wannan"
"Me? Kina nufin zaman doya da manja suke?"
Baby tace "harma da wake a doyar"
Momy tace "okay amma ki kai mata anjima kifaɗawa dadynku kinji?"
Baby tace "tom momy"
Dahaka tafara shiri, Momy tana fita tace "lalle yarannan ni sukeso su tonawa asiri? Yanzu idan Dadynsu yace baiga jika ba sai suce basuma shiri kaga sunada hujja, amma idan suna zaman mata da miji dolene yafara damuwa da jika lokacin kuma basuda hujja, bazansa bakina ba amma ita Babyn ita zatayiwa Dadyn bayani ina daga gefe ina kallon show"
Tafiya tayi tabar wurin.
Baby shiri tayi tanufi Gidan Fadila tun daga bakin kofa tafara kwalawa Fadila kira, Abdul yana zaune yanashan tea a falo yaji ana kwalawa Fadila kira, shiru yayi yanason ganin wayene, saida Baby tazo dab bakin kofa kafin yaji muryanta, Da gudu tashigo dan ita a iya tunaninta Abdul baya gida, da gudu Fadila tafito tana tace "oyoyo" rungume juna sukayi, Abdul yana kallonsu, Fadila cikin shagwaɓa ta kwaɓe face tareda turo baki gaba tace "shine aai yanzu zakizo? Amaikon kizo tun safiya?"
Baby tace "wa? Niɗin kinga yanzuma ba jimawa zanyi ba kunashan soyayyarku da mijinki inzo ina katseku ban isaba yanzu momy ce ta aikoni"
Fadila tace "metace?"
Baby taciro goran hannunta wanda tacire a ledan tace "wai nabaki wannan zakuyi magana"
Fadila da sauri ta kashewa Baby ido tana kokarin kai goran kasa, Baby tace "ke dalla ki karɓi abu batace tana baki ba dama?"
Fadila da ido take nuna mata Abdul amma takasa ganewa tace "Adda Fadila kidaina abu kamar me aljani ɗin zaki sani gudu fa"
Wubce goran Fadila tayi ta ɓoye acikin riganta, Baby zatayi magana Abdul yace "miye wannan?"
A furgice Baby tajuya tana neman inda maganar yafito, ganin Abdul a ɗakin yasa ta juya zata gudu yace "idan kika fita har gida zan biki kuma kinsan zanyi"
Tsayawa tayi cakk jikinta yana rawa, yace "kuzo nan"
Fadila ganin haka yasa tasa gudu tabar wurin, yana kiranta amma taki juyawa, tsawa ya dakawa Baby yace "miye abun?"
Baby tace "ma..ma..maganin ulcer ne"
"Ke? Ni zaki rainawa hankali? Zaki faɗamin ko saina jimiki ciwo?"
Baby tace "da gaske nake"
Socket na caji ya ciro yace "faɗamin miye abun"
Baby dama batason duka ko kaɗan ta warwaro ido tace "Maganin Wani abune Momy tace nabata"
Coɗa mata yayi, tayi ihu tace "zan faɗa"
Yace "um hmm"
Baby tace "Maganin Mata ne wai inji momy"
Tsaki yaja, yajuya yabarta a wurin, da sauri ta tashi ta kaɗe jikinta ta tafi ɗakin Fadila data kwanta akan gado tana haki tace "waye?" Baby tace "buɗe nine"
Tashi tayi ta buɗe tana lekawa, Baby tace "dama wannan mugun mijin naki yana nan? Meyasa baki faɗamin ba?"
Fadila janta ciki tayi tarufe kofar tace "inayi miki signal amma kinata zuba yanzu ya kukayi"
Hannunta dayaɗan tashi ta nunawa Fadila haɗe da turo baki tace "yasani nafaɗa mishi dole ai kinsan halinshi"
Fadila waro ido tayi tace "yanzu yasan miye aciki?"
Baby tace "kwarai nikam kinga ma tafiyata" fita tayi Fadila na kiranta amma taki saurara sai gida, Fadila zama tayi akan gado tace "wannan wani irin jujjayen mutum ne?"
Maganin ta cusa acikin wardrobe gefen ɗayan goran dan itakam bawani shama takeba, daganan ta kintsa ɗakinta tasa turare tareda zuwa toilet tayi wanka da sabulanta masu kamshi, Tana fitowa ta shafa mai da hoda kaɗan sai lip glow, wani wando buɗaɗɗe daidai gwiwa tasa baƙi da farar riga me guntun hannu, taje gashinta tayi ta sakeshi a bayanta, turare ta feshe jikinta dashi taɗan zauna kaɗan tanajin cikinta yana kara alamar yunwa, tsaki kaɗan taja ta tashi taje wurin bedroom frezer ɗinta, buɗewa tayi tana neman ɗan drinks amma taga wayam ta shanye duka,