Showing 117001 words to 120000 words out of 139192 words

Chapter 40 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

868

ɗaya jikinshi ya mutu Kabir yana matukar bashi tausayi, Kabir ganin haka yasa ya zauna akan gado ya kwantar da kanshi a cinyar sarki yace "Abba kayi hakuri nasan bakaso ina irin wannan maganar amma yazama dole nafaɗi abinda yake raina kodan gudun kamuwa da cuta"

Abba yace "ba komai Kabir kaci gaba da addu'a Allah yana tare da kai kaji?"

Kabir yace "eh Abba amma zanyi missing ɗinka"

Abba yace "nima haka"

Daganan ya tashi yaci gaba da shirinsa harya gama yayi sallama da kowa kafin driver yajashi sai Garin Abuja.

       

            "Baby yau kitchen tashiga tana girki tun azahar, Momy tana kallonta danta fahimci girkin wa Kabir takeyi taso tafaɗawa Dady amma shi Dady sam baya fahimtar abu, Baby waya ta ɗauka takara a kunnenta, "Hello Darling"

Fadila tace "meyasa tun ɗazu nake kiranki bakya ɗauka ina kika ajiye wayarki ne?"

Baby tana yanka albasa idonta duk hawaye tace "girki nake"

Fadila da mamaki tace "girki? To ina ƴan aiki suke?"

Baby tace "Aa wannan special ne dan inayiwa Yaya Kabir ne yakirani jiya awaya yace zaizo yau shiyasa nazo inayi mishi abinci kinsan menake dafawa?"

Fadila da mamaki tace "Aa ina zan sani"

Baby tace "jellof rice ne da cowslow da banana and coconout juice sai fruit salat nasan zaiso ai ko? Ko zaki zo ne?"

Da sauri Fadila ta kashe wayar danji tayi wani abu yataso mata wanda takasa gane ko menene shi, Baby sai lokacin ta tuna ashe da Fadila take waya jikintane yayi sanyi tasan yanzu Fadila tafara zarginta, sharewa tayi taci gaba da aiki dan gaskiya zata iya karɓan duk wani ɓacin rai akan Kabir saide Fadila ta yafe mata,

Saida tagama ta shirya komai tayi wanka tareda cancaɗa kwalliya tasa leshi baki da adon jaa, ta ɗaura ɗan kwali ture kaga tsiya, kallon Kanta tayi a madubi nan ta tsaya taɗau hotuna masu kyau, shiga watsapp nata tayi, tayi sa'a kuma Fadila tana online da sauri ta tura mata hoton tace "kiga hotona nayi kyau?"

Fadila tana ganinta tace "gaskiya kinyi kyau ina zakije haka?"

Baby reply tayi mata da "babu inda zanje yaya Kabir yana zuwa"

Da sauri tayi delete for every one abinda bata saniba shine Fadila tariga tagani, Fadila sauka tayi a watsapp ɗin batace komai ba,

Baby rike baki tayi tace "meyasa nake son zama wawiya akan yaya Kabir ne? Bana iya controlling ɗin kaina"

Rufe Data itama tayi ta ajiye wayar, ɗan kwanciya tayi wai kafin yazo taɗan huta, bata saniba wani nannauyan bacci ya ɗauketa,

Kabir yazo ya sauka agidan Dady Momy da gangan tabashi abincin ƴan aiki bata bashi na Baby ba so take yau Dady yasan abinda yake faruwa, ci yayi yace "nagode Mom Dady yabani makullin gidana wai jiya Baby taje ta sharemin ta goge komai a gajiye nake bara naje naɗan huta"

Momy tace "to Kabir ka huta lafiya"

Kabir yace "Momy ina Baby?"

Momy tace "Baby tana bacci tun ɗazu kona tasheta?"

Murmushi yayi kaɗan yace "Aa barta kawai natafi"

Tafiya yayi, yawuce gidanshi yana shiga yaga komai kala ɗaya dana Abdul ga wurin shakatawa da lambu masu kyau, buɗe ɗakin yayi yashiga, wani kamshine ya bugi hancinshi, hawa sama yayi yaga ɗakin komai a kimtse toilet yashiga yayi wanka yazo yasa kaya marasa nauyi saida sukayi waya da sarki kafin ya kwanta ya rufa jikinshi da blanket nanfa bacci me daɗi ya ɗaukeshi,

Baby kusan awa huɗu tana bacci sai bayan mangrib ta buɗe idonta tana hamma tareda kallon cikin ɗakin nata, da sauri ta ɗauki wayarta taga 7:5 yayi, dirowa tayi daga kan gadon tana salati, da sauri ta fito tana kallon yanda gari yayi duhu, "oh Allah ina yaya Kabir ɗin?"

Momy tace "yana gidanshi mana yazo kina bacci ai"

Baby tace "meyasa baku tadani ba?"

Momy batace mata komai ba tawuce awurin, Baby da sauri takoma ɗaki tashiga toilet ta wanke kwalliyan daya ɓaci tayi alwala tayi salla kafin takarayin wani sabon kwalliya ta canja kaya zuwa wani pencil gown wanda yaɗan kamata kaɗan, ɗan kwali ta ɗaura ta ɗauko gyalle tasa baki tayafa, wayarta da makullin motarta ta ɗauka, saida ta leka taga ba kowa kafin tawuce dining taɗau babban plate ɗin data jera abincin akai, hanyar parking space ta nufa ta, motarta tashiga ta ajiye babban plate ɗin sannan ta zagayo ta zauna tayiwa baba me gadi horn, daganan tafice agidan bata tsaya ako inaba sai gidan Kabir dayake Zone 2, da kanta tafita tabuɗe get ɗin tashiga da motarta, parking tayi takara rufe get ɗin sannan taɗau plate tashiga daga ciki, tasan ɗakinshi hakan yasa ta wuce sama direct, abakin kofa ta tsaya tana tunani a hankali tasa hannu ta buɗe kofar, sallama tayi sau uku bai amsa ba, shiga tayi ta ajiye plate ɗin ta nufi bedroom ɗinshi, ganinshi yana bacci yasa ta sauke ajiyar zuciya haɗida yin murmushi, zuwa tayi ta zauna a gefenshi taɗanja blanket ɗin kallon fuskarshi, wani daɗi taji a ranta ganin yanda yake bacci kamar innocent child, Hannu tasa tana shafa sajen daya kwanta a fuskarshi, Kabir cikin bacci yasa hannu ya rike ɗayan hannunta, murmushi takuma yi tana kallinshi, saida yayi kusan awa ɗaya yana bacci tana zaune a gefenshi, a hankali yafara buɗe idonshi ganin kamar mutum a gefenshi yasa yakara buɗewa sosai yana kallon Baby datakeyi mishi murmushi,

Da sauri ya mike yace "Bebi!!! Yaushe kikazo?"

Ɗan turo baki tayi tace "tin 7:30 ina nan nazo kana bacci shiyasa na zauna saika tashi"

Wayarshi ya ɗauka yana kallon agogo yaga yanzu 8:29 da sauri ya kalleta yace "meyasa to baki tadani ba?"

Farfar tayi da ido tace "naga kanajin daɗin baccin ne shiyasa"

"To tashi na kaiki gida yanzu fa 8:30 yayi"

Make kafaɗa tayi tace "Um Umm nikam anan zan kwana"

Ido ya waro yana kallonta da sauri yace "Anan?"

Baby tace "um nakawo maka abinci tashi muje kaci" jan hannunshi tayi da sauri ya janye yace "wayasan kinzo agida?"

Baby tace "Momy tasani Dady ma yasani abinci nakawo maka please kada kace min natafi yanzu kaji?"

Jan hannunshi tayi ya saukko daga gadon toilet ta kaishi tabashi sabon brush tace "gashi yi brush kayi alwala idan kayi salla sai kaci abincin ko?"

Kallonta yakeyi baice komi ba, makilin tasa a brush ɗin ta matso wurinshi tace "haa"

Karɓa yayi yace "jeki falo zanyi"

Baby bashi tayi tace "okay saika fito"

Da tsalle tsallenta tafita yana kallonta a zuciyarshi yace "yaranta yanacin kan yarinyarnan gaskiya"

Brush ɗin yayi sannan yahaɗa da alwala saida yayi salla kafin yacanja kaya zuwa dogon wando da riga polo, taje kanshi yayi kafin yafita zuwa falo, Baby datasa wani Comedy tana kallo sai dariya take harda zamewa akan sofa, Tsayawa yayi yana kallonta da sauri ta ɗago tace "Yaya ka idar da sallan? To taho kaci abincin"

Ajiye wayar tayi ta ɗauko karamin plate tayi serving ɗinshi, Zama yayi ya harɗe kafa a gabanta yana kallonta ta ɗibo a spoon tace takai bakinshi tareda cewa "Haa"

Karɓan spoon ɗin yayi yace "zanci"

Ganin haka yasa ta haɗe fuska ta juya mishi baya alamar tayi fishi, juyo da ita yayi yace "sorry Bebi gashi to bani naci da wuri dan banaso kiyi dare sosai"

Karɓan spoon ɗin tayi tafara bashi abincin har saida ya kawar da kanshi alamar ya koshi, turo baki tayi tace "saifa ka kara"

Runtse idonshi yayi yace "cikina zai fashe"

Dariya abin yabata cup ta ɗauka ta tsiyayo juice ɗin tabashi shima saida ya shanye yamike yace"muje nakaiki gida gobe sai kituro driver yakai miki motarki kinji?"

Wayarta taciro ta gyara zama tace "babu inda zanje anan zan kwana kai saika kwana a bedroom ɗinka"

Dafari yazata wasa take amma saida yaga ta kafe yasa ya zauna a gefenta tareda riko hannunta yana murzawa ya sanyaya muryanshi yace "Bebi? Be kamata ki kwana a gidana ba kinsan akwai sharrin shaiɗan"

Da sauri cikin tsoro tace "ina shaiɗan ɗin?"

Ganin ta tsorata yasa yace "eh akwai shaiɗan agidannan ɗazu ina kwance akan sofa ɗinnan nagansu sun fito da kaho da bakaken kaya dana tsorata saina gudu cikin ɗaki"

Baby waro ido tayi ta matso wurinshi tace "to muje cikin ɗakin kan"

Yace "dana kwanta kuma a ɗakin naga matar shaiɗan tafito tarike wuyana da kyar na dinga ihu, sai naga sun fito dayawa acikin toilet daganan suka matso wurina suka rinƙa tsorata ni"

Baby da sauri ta gyara ɗaurin kanta ta ɗauko mayafinta tace "to dama Dady yace nadawo da wuri gobe da safe zanzo nakawo maka breakfast kayita karanta ayatul kursiyyu idan bazaiyi ba saika koma gidanmu ɗakin Yaya Abdul zaifi maka kwanciyar hankali amma ni yanzu zan tafi"

Yanaso yayi dariya amma bayaso tagano cewar karyane sai yace "ki kwana mana to kawai"

Baby da sauri tace "no no no bawai banason kwana bane aa momy ce nake tunani zatayita kewana basai ka kaini ba zan tafi da kaina dan Dady zaiyi faɗa shikam ma baisan nazo ba itama Momy bata sani ba"

Makullin motarta da wayarta ta ɗauka, tace "Good Night"

Fita tayi ya rakata zuwa wurin motarta yace "bye"

Buɗe mata get yayi tana fita yayi dariya sosai ganin yanda take gudu da motar yasan ta tsorata, rufe kofar yayi yakoma ciki daganan fa yakasa shiga bedroom dan tsabar tsoro gani yake kamar da gaske shaiɗanu zasu fito mishi, "wayyo Allah nida nakeso na tsoratata gashi yanzu nima na tsorata kaina"

Ɗan rufe ido yayi da sauri ya buɗe yace "nashiga uku bazan iya bacci ba"

Baby tana isa gida ta tarar da ba kowa acikin gidan hakan yayi mata daɗi cikin sanɗa ta nufi ɗakinta ta buɗe a hankali takuma rufewa hamdala tayi tace "nagode Allah"

Juyawan da zatayi taci karo da Dady da Momy zaune suna kallonta, da auri tafara kaikaya wuyanta tana kallon kasa, Dady ne yatashi yace "ina kikaje da daren nan?"

Baby tace "babu"

Da tsawa Dady yace "ina kikaje nace?"

Da sauri cikin tsoro tace "ina gidan yaya Kabir nakai mishi abincinshi ne"

Dady kallonta yayi sosai sannan yace "ya dace kije gidan namiji a wannan lokacin?"

Da sauri ta girgiza kai, Yace "buɗe baki kimin magana"

Da sauri tace "Aa Dady amma ai Yaya Kabir ne ba gidan wani naje ba shi ai kamar Yaya Abdul yake a wurina ko kwana nayi agidanshi ai ba komai"

Dady yace "akwai kuruciya akanki har yanzu to bari kiji shaiɗan baisan wani Yaya ko ɗan uwa ba ki rinƙa kula"

Juyawa yayi yakalli Momy datayi wiki wiki da ido dan ita tahaɗa duk wannan gurmin, yace "kinji zahiri ai? a matsayin Yaya ta ɗaukeshi amma kinje kina kawo kananan magananku na mata"

Momy tashi tayi tace "bazaka taɓa fahimta"

Fita tayi shima Dady yafita, Baby tace "oh Allah nagode maka da bansha duka ba"

Kayan jikinta tacire tasa na bacci kafin ta kwanta, wayarta ce take ringing da sauri taɗaga tana kallon sunanda yake yawo akan screen ɗin, Yaya Kabir, receive ta danna tasa a kunnenta tace "hello"

Kabir daya kasa motsi a inda yake yace "kin isa gida lafiya"

Baby tace "Eh yaya"

Yace "good" tashi yayi dan saida yaji muryanta kafin yaɗan dainajin tsoron, Bedroom ɗin yashiga a hankali Baby sai zuba mishi surutu take, hawa gado yayi yaja blanket yarufa harda kanshi dan tsoro, tace "Yaya kana jina?"

Da sauri yace "eh"

Tace "bacci nakeji good night have a nice dreem"

Da sauri yace "please kada ki kashe kibari sai nayi bacci"

Da mamaki tace "meyasa? Meya faru? Bakada lafiya ne?"

Kabir yace "lafiyana lau amma pls kibari nayi bacci kafin ki kashe"

Baby a ruɗe tace "lafiya? Meya sameka? Kodai shaiɗanun ne suka kara fito maka?"

Jin takara kiran sunan shaiɗanu yasa ya rungumi filo gam, yace "please ki daina, inajin tsoro kada ki kashe wayar sainayi bacci pls Baby"

Baby dariyane yazo mata ai kuwa tafarayi babu kakkautawa dama gwanace wajen yin dariyan asara, Kabir shiru yayi yanaso bacci ya ɗukeshi amma yaki zuwa, cikin tsokana tace "ga ɗaya ta bayanka"

A tsorace yace "Please stop it"

Baby Tace "okay yi addu'a ka shafe jikinka duka"

Addu'a yayi ya shafe jikinshi tace "to kwanta ka rufe idonka"

Kwanciya yayi ya lumshe ido, Baby tace "ka rufe?"

"Umm" ya amsa mata, tace to "kasa a ranka zakayi bacci"

Shiru yayi tace "are you with me?"

Yace "Umm"

Tace "okay kada kadamu zan baka labari me daɗi har kayi bacci kaji?"

"Umm"

A hankali tafara bashi labari tun yana amsa mata harya daina, jin saukan numfashinshi yasa tagane yayi bacci murmushi tayi sannan ta kashe wayar ta ɗaura a kirjinta har tayi bacci,

Kabir ma da wayan a kunnenshi yayi bacci.

*Jiddah Ce...✍️*

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 76*

         ~Unty Nabila menene damuwanki?"

Pinky ce zaune a gefen Nabila wacce ta buga tagumi hawaye suna fita daga idonta, Pinky hannunta ta riko tace "please ki faɗamin damuwarki jifa kanwarki ce"

Nabila ɗago kanta tayi idonta yana fitar da hawaye tace "ƘANWATA? amma baki damu da damuwata ba, kinfi damuwa da damuwar wasu akan na yayarki, kinfi son Baby da Fadila akaina"

Pinky tace "dan Allah ki daina maganar nan Unty Nabila taya zanfi son wanda bamu fito ciki ɗaya dasu ba akan wacce muka fito uwa ɗaya uba ɗaya?"

Nabila tace "Darling? Kinsan inason Abdul sosai ko?"

"Dan Allah Unty Nabila ki daina wannan tarihin yariga ya wuce ki daina wannan maganar Abdul yayi aure yanzu kema ki maida hankalinki akan aurenki da Kabir tunda Dady yace za'ayi kinga babu me canja mishi ra'ayi"

Nabila tace "akwai"

"To waye kenan?"

Tashi Nabila tayi tana zagaye ɗakin tace "shi Kabir ɗin, kinsan ance Idan kaga tunguza bata fidda mai ba to batasha matsa bane"

"Me kike nufi da hakan?"

Dafa kafaɗan Pinky tayi da hannu biyu tana kallon cikin idonta tace "ƘANWATA! jiya naji labarin Kabir yazo garinnan kuma har gidanshi nasani saida naje jiyan nagani amma ban shiga ba, tofa zanje da kaina nasashi ya ruguza auren nan batareda wani faɗa ko zagi ba"

"Unty Nabila tayaya zakiyi hakan? Kadafa kizo kina dana sani"

"Bana dana sanin komai a rayuwata sai dana sanin rashin zuwana ƴar fari da nice ƴar fari da Dady be tsaya kullum yana kawo mana zancen wannan yaron nashi daya ɓata ba, anyway shi yayanki ne Allah ya bayyana muku shi"

Pinky tace "Ameen idan da gaske kike"

Ɗan murmushi Nabila tayi sannan taje wurin wardrobe ta ɗaukko wani dogon wando crazy tasa da body hug na riga pink ta kame gashinta wuri ɗaya ta ɗaukko jakanta taciro eyelashes tayi fixing kafin tasa half cover high hill tayi rolling da gyalle karami, after dressing ta ɗaura akai, kallon Pinky tayi tace "Darling! Meyafaru?"

Pinky tace "banaso mutane suna zaginki abin yanamin zafi pls ki daina irin wannan drssing ɗin kisani fa the way you dress the way people will adress you"

"Forget about them darling! Idan zakiyi abu kidaina kula mutane kiyi dan Allah badan wasu can banzaye ba"

Makullin mota ta ɗauka tace "take care"

Parking space taje tayi horn, Baba megadi yana bangida shiyasa be buɗe da wuri ba, hakan yasa dayazo ya buɗe ta dinga surfa mishi ruwan bala'i saida tagama kafin taciro dubu biyu tace "gashi kasiyi goro" karɓa yayi yace "nagode Hajiya"

Ɗaga glass ɗinta tayi ranta a ɓace taja motarta bata tsaya ko inaba sai zone 2 gidan Kabir, da kanta tafita ta buɗe get ɗin tana yamutsa fuska tashiga ciko, parking tayi ta fito tana taku ɗas ɗas harta shiga ciki, Sama tahau tana neman ɗakinshi, cin karo tayi da ɗakinshi da sauri ta cire after dressing ɗin data ɗaura ta ajiye abakin kofar, shiga cikin ɗakin tayi Kabir kwance yake akan gado yana bacci tunda yayi sallan asuba yake bacci har yanzu be farka ba, wani shu'umin murmushi Nabila tayi kafin ta cire takalmin kafarta da gyalen, a hankali ta taka har inda yake taje tahau gadon ta kwanta, yaye blanket ɗin dayake rufe dashi tayi tareda rufa musu su biyu, ta baya ta rungumeshi sosai tana shafa jikinshi a hankali, Kabir kamar a mafarki yaji ana shafa jikinshi a hankali yafara buɗe idonshi, ganin hannu da farce dogaye a jikinshi yasa yakusa kurma ihu dan yayi tunanin ko shaiɗanun ne suke fito mishi da gaske, da Sanyin murya Nabila tace "Good Morning Baby!"

Ras ras yaji gabanshi yafaɗi, a hankali tace "are you shocked?"

Juyowa yayi ya ganta tanata murmushi, da sauri ya mike yace "ke? Bakida hankali ne? Wama ya nuna miki gidana?"

Nabila dariyan gefen baki tayi tace "Come On Baby wanda zan aura amma bansan gidanshi ba? Ai da sake"

Kabir sauka yayi akan gadon ya ɗauko riganshi yasa, bai karayi mata magana ba ya wuce falo ya zauna, Nabila sauka tayi daga gadon tasa takalminta, gashin kanta ta baza sannan tafita itama zuwa falo, tsayawa tayi ajikin kofa ta harɗe hannu a kirji ta zuba mishi ido kamar sabuwar mayya, lumshe idon tayi tafara takowa a hankali, kawar da kanshi yayi yana kallon gefe, baiyi zato ba yaji ta zauna a cinyarshi tasa hannunta ta zagaye wuyarshi tana sakin murmushi, idan ya biye yarinyar nan zaiyi mata dukan tsiya gara ya barta tagama iya haukanta idan bai kulata ba zata tafi da kanta, ganin baya kulata yasa ta kwantar da kanta a kafaɗarshi tace "Baby Yunwa nakeji"

Ko kallonta baiyi ba, tasan ta kunna shi kuma hakan takeso,

Baby sauri take ta iso dan tasan Kabir yana nan yana jiran Breakfast, jikinta sanye da atamfa dogon riga purple sai mayafi karami purple da flat shoe baki a kafarta, mota tashiga ta tafi zuwa unguwar Kabir, Saida ta buɗe kofar ta hango motar Nabila, kirjinta ne yabada squtin dataji kamar zai fito, da sauri tayi parking ta ɗauko abincin ta nufi ciki dan ganin ko Nabila ce da gaske, Ganin afterdress a bakin kofa yasa takara jin kirjinta yakuma bugawa, kamar ta juya ta koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login