Showing 24001 words to 27000 words out of 139192 words

Chapter 9 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

895

d'ankwalinta ta Ciro ta goge jinin dayabi tyles d'in ta tura d'ankwalin zuwa gefen gawan, nan ta kwanta a kasa tana kuka mecin rai, Washe gari Guyson yashigo d'akin ganin  ita kad'aice yasa yace "ina Wanda ya d'aukoki?"

Baby jikintane yafara rawa bakinta yana shaking tace "am...am..Dama yafitane yace zai dawo Dan Allah ka taimaka ka fitar dani wallahi na wahala a wurinshi" kallonta yayi daga sama zuwa kasa yanaso ya tabbatar da abinda take fad'a, ganin jini a jikinta yasa ya gaskata zancenta cikin rashin kulawa yace "ko baki rokaba ai dama yanzu zaku tafi gida sai kuma wata rana, sannan yanzu keda wannan zaku rika zama Dan naga yana sonki sosai, idan yadawoma zai bani sauran cikon kud'ina"

Rass Rass gaban Baby yabada sauti "yanzu idan suna gane ya zanyi? Nashiga uku na lalace yaya Abdul kazo ka taimakamin"

Guyson cikin tsawa yace "koba magana nake mikiba kinje kina tunaninki na banza tashi mutafi"

Baby mikewa tayi da kyar tana takawa a hankali Dan kada ya ganota, saida sukaje daidain baking kofa kafin ta juya tana kallon karkashin gado Inda ta b'oye gawan,Guyson yace "me like kallone? Zaki wuce mutafi ko sainayi ball dake nakuma sa an zanaki"

Baby da Saudi tajuya atafita, wurin motar da sukazo aka kaita shiga sukayi gaban d'aya 'yammatan a galabaice, Baby tsabar tashin hankali ko kulada lamarinsu batayi ba bale tagane halinda 'yan uwanta suke ciki, burinta kawai ta iso gida ta baiwa Fadila labari Wata kila su sami mafita, saida aka shigar dasu har cikin gida kafin aka bud'e but d'in akace kowacce yafito, fita sukayi lokacin Fadila tana tsaye tana kallonsu cikin tausayi takasa karasawa wurin, da gusu ta iso wurin ganin yanda aka wurgo Baby waje, wurinta ta nufa Rana kuka tace "ki yafemin nakasa taimaka miki am so sorry"

Hannu Baby yasa tana share mata hawayen girgiza mata kai tayi alamar ta daina kuka, Fadila rikota tayi suna shiga d'aki tana kuka ta wuce toilet yasa mata ruwan wanka, dawowa  tayi Takara rikota suka shiga toilet d'in, Fadila tana ganin yanda Baby tafita a hayyacinta amma ta danganta hakan da fyad'en da akayi matane, suna shiga toilet Baby tafad'a jikin Fadila tana kuka cikin dasashiyar murya Wanda baya fita sabida kuka da tsoro da tsananin firgici race "Adda nayi kisan kai ki taimakamin na kashe mutumin kuma na b'oye gawanshi, Adda so inmutu in barki Dan Allah kitaimaka min karsuga gawanshi" a kud'ime Fadila ta d'agota tana kallon fuskarta tace "me kike fad'ane Babyna? Waye kika kashe? Tayaya kuma?"

Baby ta rungume ta kem tafara bata bayanin abinda yafaru, jikin Fadilane yafara rawa bakintama rawa yake tarasa dawanne zataji da kisan da Baby tayi ko kuma da Kukan Baby Wanda yake d'aga mata hankali? Tasan idan suka gane Kasheshi tayi to itama kasheta zasuyi, gashi wannan kisan tayishine sabida kare kanta domin shi dama abokin gaba koya kasheka ko kuma ka kasheshi, ita tama rasa yanda zatayi da wannan lamarin, buga bayan Baby tayi a hankali tace "Relax in Allah ya yadda zansan abinyi bazasu kasheki ba, babu Wanda zai Gane kece kikayi kisan kinji?"

Baby gid'a kanta tayi don har yanzu bata cikin hayyacinta, saida Fadila taga tad'an samu relief kafin tacireta a jikinta tace "kiyi wankan da kanki tunda babu abinda ya sameki kinji?"

Gid'a kai takumayi sannan tafara kwab'e kayanta, Fita Fadila tayi ta zauna a bakin gado ta buga tagumi tana tunanin mafita, sai daga baya kafin tagano mafita amma dolene saita sadaukar da rayuwarta kafin Baby ta rayu, da wannan tunanin taji ranta fayau, dukda kasan zuciyarta babu dad'i "Amma ya zanyi? Kanwata tariga tasani cikin matsifar rayuwa".

         "Kamal zaune yake a office ya tara files a gabanshi bai tab'a ko d'ayaba, gashi aikin ya taru yayi mishi yawa sabida hutun daya d'auka sabida bikin gashi wannan mayaudariyar ta gudu ta barshi, sannan zasu had'ashi dawata kanwarta Wanda shima a matsayin Kanwa ya d'auketa shi ta inama zai fara rayuwar Aure da Amrah yarinyar data zama kamar Kanwarshi, had'e kanshi yayi da jikin desk yanajin kamar yayi kuka, turo kofar akayi cikin tsokana yaji muryan Abdul yana cewa "ango kasha kamshi, irin wannan tagumin hala tunanin Amarya kake ko? To ai idan matane basu fara saka cikin tunaninm ba yaro sai sun kware da harkar zakajima kamar ka zauna a gida karka fita ko ina"

Sai a lokacin Kamal ya d'ago kanshi da idonshi Wanda yayi jaa da sauri Abdul ya kalleshi sannan cikin mamaki yace "Abokina are you okay?"

Kamal kallonshi yayi yace "ba lafiya Abdul Fadila ta cutar dani taci amana kuma bazan tab'a yafe mata ba, ta gudu tabarni tabi saurayi sun tafi, nikuma tabarni da kanwarta wai a matsayin mata yarinyan Dana d'auketa a matsayin *KANWATA* Ta ina zan farayi mata zancen soyayya har muyi zaman Aure da ita, nikam na yanke shawarar sakinta ma zanyi ko domin idan ina kallonta dolene in tuna Fadila, nikuma banson ina tunata sabida abinda tayimin"

Abdul yace "Kasan yanzu al'arshi ya girgiza dakayi maganar saki? Saki itace Kalamar da Allah ya halatta amma bayason jinshi, Allah ya halatta sakine sabida ya baiwa bayinshi sauki, Idan ka daure kayi biyayya zakaga da sauki a rayuwarka, miye banbancin Amrah da Fadilar?"

Kamal kallonshi yayi da mamaki yace "banbanci kake tambaya my foot? Ai kaima kasan akwai banbanci sosai ma"

Kafin yakarasa yaji wayarshi yana ringing, d'agawa yayi cikin sanyin murya yace "hello" d'an tsayawa yayi sannan yace "Dan Allah Ku kyaleni nace muku kuyi duk yanda zakuyi dasu nidai kawai inji Alert"

Katse wayar yayi Abdul yana kallonshi, Kamal yace "shikenan bazan saketa ba amma babu abinda zai shiga tsakanina da ita harta gaji da kanta ta tafi"

Abdul dariya ya kwace dashi yace "kaine zaka iya zama d'aki d'aya da mace kace idan ta tagaji zata tafi? Ahh Lalle Alkiyama ta kusa Kamal ya shiryu"

Harara Kamal ya banka mishi sannan yace "sabida nine sarkin jarababbu ko?"

Abdul toshe bakinshi yayi yace "Allah ya huci zuciyar Oga"

Kamal hararanshi kawai yayi.

_jiddah ce...✍️_

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 16*

    ~Fadila ta rasa yanda zatayi ta kub'utar da Baby cikin wannan halin, Amma da wannan tunanin yazo mata sai taji sauki a zuciyarta, da dare kamar yanda aka saba yauma haka suka shigo da babbar mota zasu kwashi 'yammata, Fadila ganin haka yasa tacewa Baby "idan aka tambayeki Abu kice bakisan komai ba, kinji?"

Baby cikin kuka tace "to Adda karki bari su kamani" dafa kafad'arta Fadila tayi tace "ba komai" zuwa wurin motar tayi itama tashige ciki wurin sauran Addu'a take Allah yasa taci wannan jarabawar, saida suka iso har Hotel d'in aka bud'e musu mota kowacce aka nuna mata d'akin dazata shiga, Fadila da sauri tasha gaban wata yarinya wacce take kokarin bud'e d'akin da Baby tafad'a mata, cikin muryan tausayi tace "Dan Allah kitaimaka kibarni nashiga d'akinnan wallahi Sam hankalina bai kwanta da mutumin da suka had'amu ba"

Kallonta yarinyan tayi da Alama bata yadda da maganar ba, komade menene ai duk d'ayane, a hankali tace "ba komai kishiga ni sai nashiga wancan d'in"

Fadila tace nagode, tura kofar tayi tashiga zuciyarta yana bugawa sai a lokacin tafarajin tsoro wata zuciyar tace kartayi wata zuciyar kuma tace tayi, runtse idonta tayi tanufi karkashin gadon, ta zaro bargon da sauri taja da baya ganin fuskarshi ta kumbura suntum ga bakinshi yana fitar da jini gakuma wani uban wari daya bugi hancinta, rufe hancin tayi da gefen hijabinta tasa hannu taja gawar, lokacin har jinin yafara bushewa, ruwa ta d'ibo daga toilet tazo tasa akan gawar jinin yad'an jika dukawa tayi tashafo jinin, a hankali ta runtse idonta tareda shafawa a jikinta da wukar dayake hannunta, tana gamawa tamaida ruwan ta d'auke kwalbar da Baby tayi anfani dashi jiya ta bugashi da kasa ya tarwatse, kwanciya tayi akan kwalbar jikinta yafara tsagewa, ihu tayi ganin ba Wanda yashigo yasa takara sakin wani ihun, saida ta jera ihu yakai sau biyar kafin taji karan bud'e kofa, Guyson ne yashigo yana hura hanci cikin tsawa yace "ke bakida hankaline? Zaki tsaya kina yiwa mutane ihu"

Ganin yanda suka kwanta acikin jini yasashi karasawa da sauri, bubbugasu yake amma ina basa motsi Fadila kam ta suma, amma mutumin ya mutu, hannu ya d'aura aka domin bayason kowa yasan Alhaji Mudi ya mutu a hannunshi ya tabbata sai an kamashi kuma ayi mishi d'aurin rai da rai, da sauri ya d'auko ruwa ya watsawa Fadila firgigit ta mike tana haki kamar da gaske, wani gigitaccen Mari Guyson ya d'aureta dashi, rike kuncinta tayi tace "me nayi maka?"

Wani Marin Yakuma d'auketa dashi, Marin daya gigita kwakwalwan Fadila tunda take a rayuwarta bata tab'a karb'an mari ba sai yau yau d'imma me zafi, Guyson cikin matsifa da bala'i yace "meyasa kika kasheshi?"

Fadila kukane ya kubce mata hannu tasa a bakinta ta toshe tana kuka, cikin tsawa yakuma cewa "ba tambayarki nakeba? Meyasa kika kasheshi?"

Fadila tana kuka tace "shine ai ya janyo harna kasheshi, fyad'e yayimin shiyasa nikuma na rama da kisa....shiru tayi jin wani irin azaba a wuyanta, Guyson ne ya shake wuyanta kamar zai kasheta ya zazzaro ido waje yace "bakida hankali kinsan matsayin wannan mutumin a kasar Nigeria kuwa? idan baki saniba barini nafad'a miki, Alhaji Mudi shahararren d'an kasuwa ne Wanda ya shahara a fad'in duniya,  kinsan nawa nake binshi? Ina binshi naira Miliyan 30 tin akan wasu 'yanmata Dana kwaso tun shekarar 2017 shine zaki kasheshi ba tareda ya biyani kud'ina ba? Kinyi babban kuskure kuma zakisan bakida hankali Yarinya"

Fadila ganin yanda ya rud'e sai itama taji duk ta rud'e harma tafara Dana sanin yin wannan taimakon, wata zuciyar tace taimako ba'ayi mishi dana sani, janye gawan yayi ya tura karkashin gado shima da niyar gobe zaije ya binne idan ya faki idon mutane, Jan Farida yafarayi har zuwa waje saida yakaita tsakiyar hotel d'in kafin yaciro bulala yafara zabga mata kota ina, kiran wad'annan kartin yayi suka d'aure hannunta a baya, da bulalan yaci gaba da dukanta kota ina, fuskarta ta farfashe jikinta duk yayi tsami mutane sai kallonsu suke babu me iya taimaka mata Dan tabbas sunsan halin Guyson, Fadila ruwa take bukatar sha a hankali da kyar take iya furta kalmar "Ruwa, Ruwa" amma wannanmugun bai dainaba saida yaga numfashinta yafara d'aukewa kafin ya kyaleta a baiko kunceta ba. Har garin Allah ya waye Fadila tana zaune a cikin Hotel babu me taimaka mata.

      "Baby kwance take tana kuka sosai Dan tasan Fadila zata iya d'auka alhakin kisannan a kanta, ita kuma tasan bazata tab'a barin Fadila haka ba, Bazata yadda Fadila tafad'a halaka sabida ita ba, share hawayenta tayi tana tuno yayanta me sonta, Wanda bayason ko kad'an yaga kukanta, kuka takeyi sosai data tunoshi, Fatimace zaune a gefenta tanakan bata hakuri.

      " Unty Sadiya kullum tanakan bincike akan Fadila Amma Sam bataga komai ba, Yauma kamar kullum suna tafiya a motar Abban Aisha daidai wurin you ton taga wasu samarai suna raba jarida da sauri ta tab'a mijin nata, tace "tsaya muga jaridar Abban Aisha"

Tsayawa yayi yace "kekam akwai son karanta jarida kamar wata 'yar siyasa" dariya kawai tayi daidai lokacin me jaridar ya tsaya, karb'a tayi mikinta yabiya kud'in suka wuce, a motar ta bud'e jarida tana karantawa taga hoton wata yarinya kyakkyawa, duba kasan hoton tayi taga an aje miliyan 50 da kyautar gida da mota dakuma visa ta kasashe guda goma na duniya, sannan kujerar makka da Umara na wata shida gaduk Wanda yasamo yarinyar, waro ido tayi ta karanta sunan "AMRAH MAMMAN ME KU'DI"

Wurin mijinta ta juya tace "Abban Aisha duba kagani irin kud'in da aka zuba akan yarinyar ai duk Wanda yasamo yarinyar nan shida talauci sai babu kai har jikokinshi bazasuyi talauci ba"

Kallonta yayi yace "wace yarinya"

Tace "Wai sunanta Amrah Mamman me Kud'i"

Dariya yayi yace "ai Indai Alhaji Mamman ne to kad'an kika gani, yanda yakeson yaranshi na tabbata idan kasamo yarinyar saiya ninka abinda yafad'a yakara maka, kinsan yanda yakeson yarinyar kuwa"

Unty Sadiya tace "Aa to Amma b'ata tayine?"

Yace "oh oh ba ba'ta tayiba kamar saceta akayi a yanda suke fad'a"

Unty tace "to Allah ya bayyanata cikin koshin lafiya"

"Ameen".

      "Kamal yana tashi daga office yawuce gida, yana Shiga yayuta sallama babu Wanda ya amsa, kwanciya yayi akan sofa yana sauke numfashin gajiya, kallon cikin d'akin yayi yaga babu alamar mutane, a hankali ya lumshe idonshi wata kila Umma shopping sukaje Dan yaji tana maganar shopping da safe, lokacin Amrah taci kwalliya cikin shadda maroon tayi d'auri Wanda yafitar da gashinta me tsayi waje, gashi yasha gyara sai walki yake, tayi full face make-up me hakan yafito da kyaunta na asali, kwance take akan gado jin karan bud'e kofa tasan Kamal ne sabida su Umma sun tafi shopping, turare takuma fesawa a jikinta, a hankali ta murd'a handle d'in tafita, ganin Kamal kwance akan sofa yarufe idonshi kamar me bacci yasa ta tsaya turus tana kallonshi, yanda manyan idonshi suke rufe sun zama sexy, gashin idonshi Zara Zara shine yakarawa idon nashi kyau, sai karamin bakinshi da dogon hancinshi, kallonta ta maida kan gashin kanshi Wanda yad'an taru kad'an alamar yana cikin damuwa shiyasa bai gyara ba, murmushi tayi tunowa da abinda yasashi Shiga damuwa, da sauri ta karasa wurinshi ta durkusa kan gwiwanta tariko kafarshi tafara cire mishi takalmin da safar a hankali Dan bataso ta tasheshi daga bacci, Kamal yana jinta yayi shiru Dan bayason tasan idonshi biyu, saida tagama cirewa ta d'auko tissue ta goge mishi tafin kafar mayar kan Sofan, d'aki taje ta d'auko blanket tazo ta rufashi dashi hannu tasa tashafa fuskarshi Wanda shi kad'ai yarage a waje, a hankali tace "sleeping beauty"

Zame hannun tayi da sauri ganin yaja numfashi da karfi, matsawa tayi ta zauna a gefenshi tana kallonshi, a hankali Kamal yafarajin bacci yana d'aukanshi, baisan lokacin ma daya faraba, ido Amrah tazuba mishi kamar ta cinyeshi, Umma ce sukayi sallama itada Hajiya Turai, da sauri Amrah ta sauna kasa ta daidai wurin Kamal ta kwantar da kanta akan cikinshi ta rufe idonta tareda riko dukka hannayenshi biyu tafara baccin Karya, Ummace ta turo kofar tana ganinsu taji kirjinta ya buga "me hakan yake nufi?"

Hajiya Turai salati ta sake tana kallonsu juyawa tayi tana kallon Umma wacce tarasa abinyi,  "Karima dama yarannan suna soyayya ne?"

Umma kallonta takeyi da mamaki tace "Adda inace tare muka shigo muka gansu to tayaya zan gane?"

Hajiya tace "bazaki ganeba tunda bakwasa ido akan yaranku, bazakisan meyake tafiya a kanshi ba, to Indai soyayya sukeyi dolene sudawo hankalinsu domin bazamu tab'a yadda ba, itama yaudarar d'anmu kawai zatayi"

Numfashi Umma ta sauke cikin gajiya itama tace "to Adda yaya zanyi da yaran zamani kinajin abinda yafad'a kuma gashi abinda muka gani, nifa wallahi yarinyar nan bata kwantamin ba, har yanzu inajin yayar tata a cikin zuciyata" ras ras gaban Amrah yabada sauti "me Matan nan take nufi? Dukda video danasa musu har yanzu bata yadda ba? Sainayi maganinta zatasan bata sona kamar yanda tafad'a.

_Jiddah Ce....✍️_

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸



Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 17*

      ~nan itama Amrahn bacci ya d'auketa tana kudura abinda zatayi a cikin zuciyarta, Kamal ne yafara farkawa waro ido yayi ganin Amrah kwance a jikinshi tana shekan bacci cikin kwanciyar hankali, tsaki yad'anja ya cireta daga jikinshi ya mike zuwa d'akin Ummanshi, Zaune yaganta itada Hajiya Turai, Hajiya sai matsifa take, Kamal ne yayi sallama babu Wanda ya Amsa mishi, ganin haka yawuce wurin Ummanshi ya kwantar da kanshi akan cinyarta cikin muryan shagwab'a yace "ina kika zauna Umma na tun d'azu nake jiranki har bacci ya d'aukeni"

Kallonahi Umma tayi da mamaki tace "My Son kaida kake tareda Matarka ai bazakayi kewata ba" yasan dama haka zai faru tunda sun shigo lokacin suna bacci, yasan matsifar da Hajiya takeyi ba banza ba, shiru yayi musu baice komai ba, Hajiya Turai tace "ba magana akayi maka ba zaka share mutane ka wani lafe a jikinta kamar mage"

Nanma baice komai ba, haushine yasa Hajiya Turai tashi tafice ma gaba d'aya, Umma ce ta kalli Kamal tace "my son kafad'an gaskiya dama kanason Amrah ne?"

Kamal gid'a kanshi yayi hawaye yana fitowa, Umma cikin mamaki tace "Dama kanason Amrah ne? Shinefa tambayar nayi maka ka bud'e baki kayimin magana"

Kamal kuka yafara sosai kamar karamin yaro yace "Umma na nasan zaki fahimceni, banci Amanar Fadila ba, wallahi inason Amrah so na hakika ma, dama tun farko ita nafara so"

Umma cikin kid'ima tace "ban ganeba Kamal kayimin bayani dalla dalla yanda zan gane kadaina min kuka kamar mace"

Kamal share hawayen yayi yace "Umma wannan maganar tanada tsayi, bazan iya fad'a miki ba, sirri ne tsakanin nida Fadila wallahi bazan iya fad'awa kowaba, kiyafemin" yafad'a cikin kuka, Kan Umma ya d'aure tarasa ta ina maganar Kamal ya dosa, itafa batasan mema yake fad'aba, ganin yana kuka yasata kawar da tunanin ta rikoshi ta rungume tana buga bayanshi cikin lallab'a har ya fara sauke ajiyar zuciya.

      "Fadila tun tana iya furta Kalmar ruwa har bakinta ya mutu tsabar azaba, babu abinda takeyi a zuciyarta sai Jan Allah ya isa wa Amrah, ita a hakin yanzu batason ganin kanwa ko kad'an, itafa ko a lahira batason ta had'u da Amrah, sai washe gari Guyson yazo ya d'auketa ya wullata cikin motar, sauran ma akasasu ciki suka d'au hanyar gida, bayan sun iso wasu daga cikin mazan suka riko Fadila suka d'aureta jikin bishiyar gidan, ruwan sanyi suka d'ibo suka fara zuba mata, jikinta sai rawa yake, Baby ce tafito da gudu daga cikin d'aki jin karan tsayuwar mota, ihu tayi ganin irin hukuncin da ake yiwa Fadila kuma ta tabbata ta dalilinta ne take karb'an wannan hukuncin, da sauri ta karasa wurin wata wacce aka tafi da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login