Showing 129001 words to 132000 words out of 139192 words
riganshi yayi ya juya musu bayanshi, Amrah ganin tabon a inda Abba yafaɗa matane yasa ta ware hannunta murya baya fita tace "pls hug me"
Kallonta kawai yake baiyi yanda tace ba, hawaye yana fita a idonta tace "Yaya Khalil"
Kallonta yakeyi yana ganin kamar ta taɓu, Fadila tace "tana maka magana"
Matsowa yayi a hankali ya rungumeta rikeshi tayi tace "kaine yayanmu Khalil"
Da hannu tayiwa Fadila alamar ta matso, matsowa Fadila tayi ta rungumesu duka biyu tana kuka tace "Allah nagode maka daka haɗani dasu kafin na mutu, nabaku amanar ƴata kuma inaso asa mata sunan FADILA"
Kulu ce suka shigo ɗakin dasu kaka da Ahmad da Umar dakuma Minal da Bilal, Bilal da Minal ne sukayi kanta suna murna sukace "Momy kin siya mana sabon Baby?"
Rungumesu tayi tace "eh nasiya muku sabon Baby kuma zan tafi nabar muku ita, ku kula da kanwarku kunji?"
Minal tace "Momy garinku zaki koma?"
Amrah hawaye taɗan share a ɓoye tace "Eh garin mu na asali zan koma"
Ɗago kai tayi takalli Ahmad daya sunnar dakai tace "Ahmad yau ba harara ne? ban taɓa iskanci da Umar ba, Nasiha nakeyi mishi amma ka gafarceni kuma inaso ka rinka lura da lamarin kaninka karinka yimishi nasiha"
Kallon Umar tayi dayake zubda hawaye tace "Kanina? Yau bazaka cemin Unty bane?"
Umar yana kuka yace "Unty"
Kallon Kaka tayi tace "kaka tsohuwa yau ba matsifa ne"
Kaka tace "kaniyarki"
Ɗan murmushi tayi ta mikawa Kulu hannu, da karfi kulu ta rungumeta tace "zaki tashi Amrah bazan koma Yola ni kaɗai ba tare zamu koma"
Amrah cikin ciwo tace "bazaki koma yola ba, inaso ki Auri Ahmad"
Kulu tace "Aa Amrah ke zaki aureshi"
Hannu tamika Ahmad jikinshi duk amace ya matso hannunshi tariko tahaɗa dana Kulu tace "ka aureta idan na mutu"
Sakin hannunsu tayi ta rungumo Fadila sosai tana kuka tace "kinyi zaton na zalinceki ne? Amma nasan kinsan bazan cutar dake ba, nayi hakan ne dan in tsiratar dake daga halaka, ki gaidamin Kamal kice ina sonshi domin sharri akayi mishi"
Fadila tace "no bazaki mutu ba"
Amrah cikin kuka tace "kicemin Kanwata ko zanji daɗi"
Cikin kuka Fadila tace "ƘANWATA"
rungumeta tayi sosai tace "Yaya Khalil kacemin kanwata"
Khalil daya shiga ruɗani baisan lokacin dayace "ƘANWATA" ba, Murmushi tayi musu tace "ku gaida Mama kucewa Unty Sadiya ta daina fishi dani"
Daganan tafara shakuwa tana furta "La'ilaha illallah muhammadarrasulullah sallalahu alaihi wa sallam"
Shakuwa takeyi sosai, da Gudu Baby tafito tana kiran nurses ɗin, atare suka shigo sukayi kan Amrah, Hannunta Baby ta ɗaga taga ya saki, da sauri tace "ta mutu"
Fadila ɗago ido tayi takalli Baby da idanunta wanda suka koma jaa suka kara girma tace "sabida ba ƴar uwarki bace shiyasa zakice ta mutu, da yayanki ne bazaki faɗi hakan ba"
Abdul ne ya matso ya ɗaga hannun Amrah ganin bata motsi yasashi sa hannu ya shafe fuskarta a hankali ya furta "Allah ya karɓi ajiyarsa"
Fadila sakin Amrah tayi ta tashi ta rike kwalar rigan Abdul, naushi tafara kaiwa kirjinshi kamar mahaukaciya, tana kuka tace "mugu azzalimi to bazata mutu ba idanma so kake ta mutun"
Ganin bata hayyacinta yasa Abdul ya janyota ya rungume, mutsu mutsu tafara danta kwace jikinta, riketa yayi gam yace "ki dawo hankalinki"
Luff tayi a jikinshi, Nurse ɗinne suka ɗauke Amrah suka sata a motar Ahmad, Fadila ganin haka yasa ta kwace jikinta da karfi gashi ko ɗan kwali babu akanta,da gudu tayi kan gawar tana tutture mutanen wurin, Kabir alokacin yaji wani mugun tausayinta, shima da gudun yaje ya riketa yana janta, ganin zasu rabata da ƴar uwarta yasa tafara tsala ihu kamar zata fasa asibitin, Kabir baisan lokacin daya rungumeta ba, Abdul ganin haka yasa yaje yana kokarin janyeta a jikin Kabir ɗin, da tsawa Kabir yace "baka ganin yanayin datake cikine? Ka kyaleta"
Da mamaki Abdul yace "matata ce fa"
Kabir yace "nikuma Kanwata ce"
Kallonshi Kowa yakeyi awurin, Baby ce ta matso tarike yayan nata ta rungumeshi tace "calm down Yaya komai zaiyi sauki"
Gidansu Ahmad ne suka ɗuru a motar suna kuka suka tafi,
Kabir ne yarike Fadila yasata a motarshi sukabi bayansu Ahmad ɗin, Abdul ganin haka yasa shima yariko hannun Baby suka shiga motarshi sukabi bayansu Kabir,
Agida an nemi amarya an rasa, Momy dukta ruɗe ganin Babu Fadila babu Abdul babu Kabir kuma Babu Baby,
Momy kiran Dady tayi tace "babu lafiya fa"
Dady yace "meya faru?"
Tace "ba Amarya ba ango ba Abdul ba Fadila"
A rikice Dady yace "kun duba ko ina?"
Momy tace "eh"
Da sauri Dady yakashe ya lalubo number ɗin Baby ringing biyu taɗaga yace "kuna inane?"
Babay tace "Dady anyi rasuwa nan tayi musu kwatancen gidan"
Dady ne yakashe yacewa me martaba da Dadynsu Nabila dasu Momy yace sutafi, nanfa aka kwasu hankali tashe dan sunyi zaton ko kabir ne ya mutu ko Abdul ko Fadila, Nabila da Pinky ma sun bisu, mota uku aka cika aka nufi gidansu Ahmad,
Kulu ce takura mama daga yola tace "Mama kihau motar Abuja yanzu kizo"
Mama tun safe dama takejin bugun zuciya tasan akwai abinda zai faru wanda babu kyau, da sauri tace "Amrah ko?"
Kulu kashe wayar tayi dan batason ta tayarwa mama hankali,
Suna isa gidansu Ahmad Fadila ta buɗe motar yanakan tafiya, faɗiwa tayi hannunta yaji ciwo amma bata kula ba, tashi tayi tashiga gidan da gudu, a lokacin aka fito da gawa, ciki aka shiga dashi, su Baby ma sun karaso, nan suka shiga cikin gidan duka, kan kace me har mutane sun fara taruwa, Ruwan wankan gawa aka haɗa aka shiga da Amrah ciki, su Kaka ne sukayi mata wankan gawa aka suturta ta, ganin Mangrib yayi yasa akace sai gobe dasafe za'a birneta, nan aka ajiyeta a ɗakin kaka, Fadila zama tayi a gefen gawan bakinta ya mutu sai ido datake bin duk wanda yayi magana dashi, Baby ce ta matso ta zauna a wurinta a hankali tariko hannunta, da karfi Fadila ta wubce tana kallon Baby, shiru Baby tayi, su Nabila sun karaso matanne suka shigo masan kuma suka tsaya a waje, Fadila tana kallonsu amma batayiwa kowa magana ba, Momy tace "waya rasu?"
Baby tace "Amrah ce kanwar Adda Fadila"
Momy tace "dama suna garinnan ne?"
Baby tace "momy labarin yanada tsayi kibari sai an nutsu"
Zama momy tayi a gefe itadasu Nabila,
Kabir yana ganin me martaba sun karaso yaje yaja hannunshi suka nufi gefe, cikin tashin hankali yace "Abba kaine ka haifeni?"
Abba da Mamaki ya kalleshi yace "Wani irin magana kakeyi Kabir?"
Kabir tsunkuyawa yayi zuwa kasa yasa hannunshi akan kafar me martaba hawaye yana fita a idonshi yace "dan Allah Abba kafaɗamin gaskiya kai ka haifeni ko ba kaiba"
Abba jikinshi ya mutu sosai sunkuyawa yayi shima ya ɗago Kabir share mishi hawayen yayi yace "Kabir banine na haifeka ba amma na ɗaukeka a matsayin ɗa"
Kabir yana kuka yace "waya haifeni?"
Abba yace "bansan mahaifinka ba amma a yola muka tsince ka lokacin kana yaro baka iya magana, mukuma zamuyi tafiya, idan aka tambiyeka sunanka baka iya faɗa, bayan mun koma gida dakai, dama ni banida yaro Allah bai bani haihuwa da wuri ba, nida kaina nacire maka kaya nayi maka wanka, ganin wannan tabon na bayanka wanda aka rubuta K yasa nasa maka sunan Kabir, ganin hankali da nutsuwarka yasa na jaka jiki na maidaka kamar ɗan cikina, shiyasa mutane dayawa basusan banine na haifeka ba, kuma hakan ne yasa ƴan uwanka suka tsaneka, Amma waye yafaɗa maka wannan maganar?"
Kabir yana kuka sosai yace "ƘANWATA"
me martaba yace "wace kanwar taka?"
Kabir yace "Ashe Fadila kanwata ce mungano hakan ne ta sanadiyyar Amrah bayan taga tabon bayana tace nine yayansu sunana Khalil, Mahaifinmu yarasu mahaifiyata ma tarasu tun lokacin data haifeni"
Abba rungumeshi yayi yace "hakan bazaisa kazama maraya ba, kanada ni"
Kabir Kuka yake yana rungume da me martaba, Me martaba ma saida ya zubda hawayen tausayi, ɗan sakinshi Kabir yayi yace "bari naje ciki, Amrah ce ta mutu bayan ta haihu, shiyasa nakejin soyayyar Fadila a cikin zuciyata ashe soyayyar na ƴan uwantaka ne"
Tafiya yayi yana kuka, Abdul daya tsaya a gefe yana sauraren duk abinda suka faɗa cikin Mamaki yace "dama Kabir yayan Fadila ne da gaske?"
Sanin babu me iya amsa mishi tambayar yasashi zuwa cikin gidan shima.
"Mama a tasha taga Kamal da akwati a hannu, dukda bata cikin yanayi me daɗi hakan be hanata yimishi murmushi ba, tace "Kamal ina zaka da akwati?"
Kamal yace "Mama zanje nemo mahaifina dakuma Matata"
Mama tace "Allah ne mafi sanin daidai, amma a jikina inajin kamar Amrah ta mutu dukda kulu bata faɗamin hakan ba"
Kamal a ruɗe yace "me kike nufi Mama?"
Mama tace "sai munje Abuja kafin musan me nake nufi"
Nan suka shiga motar Abuja, Kamal yayi shiru abin duniya sun taru sunyi mishi yawa, Mama sai sharan kwalla take,
Sunyi tafiya me nisa kafin suka iso Abuja cikin dare, Kulu Mama takira tazo ta ɗaukesu, tun a hanya Kamal yace "meya samu Amrah?"
Kulu batayi magana ba sai sharan kwalla, hakan yasa jikin Mama har rawa yake, dahaka suka iso gidansu Ahmad, Ganin mutane dayawa yasa Mama tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Kulu ganin kuka yana shirin kubce mata yasa tashige gidan da sauri tana toshe bakinta da hannu,
Mama jikinta asake tayi hanyar gidan, tana shiga zauna abakin kofa dan jirine yake ɗibanta, da kyar kulu tashigar da ita ciki, Ido Huɗu sukayi da Fadila wacce ta takure a gefen gawan tana kallon mutane ɗaiɗai, Mama tace "Fadila"
Da gudu Fadila ta taso ta rungume Mama tace "Mama ta mutu"
Daganan Fadila ta zame a wurin ta suma, Baby ce tayi ihu tafita da gudu tana kiran Abdul, Abdul daya buga tagumi yaɗago yace "menene?"
Baby tace "Adda Fadila ma ta mutu"
Har rige rige ake tsakaninshi da Kabir gurin shiga ɗakin, Kabir ne yarigashi shiga, yana zuwa ya rike Fadila yana tashinta "Fadila!!! Fadila!!! Buɗe idonki"
Mama kallon Kabir tayi da kyau tace "Khalil!!!"
Ɗago kai yayi ya kalleta da mugun Mamaki Mama tace "Allah dai yasa ba kaine ka auri Fadila ba? Kanwarka ce, meyake faruwa?"
Kabir bakinshi yana rawa yace "eh..."
Jin yace eh, yasa Mama ta sulale a wurin ta faɗi a sume, Kabir kan mama yayi yana bubbugata,
Momy dasu Nabila ne suka taso suma duk jikinsu yayi sanyi,
Ruwa Nabila ta ɗibo tazo ta zauna a gefen Fadila, shafa mata tayi a fuska, a hankali Fadila tafara buɗe idonta, ganin Nabila yasa tamike ta rungumeta, Jikin Nabila ne yasake atake taji jikinta yayi mugun sanyi, hawaye taɗan share a hankali tasa hannu tafara buga bayan Fadila, Abdul kallonsu yake shikam yama rasa abinyi, Kabir ne ya ɗibo ruwa ya shafawa Mama a fuska, a firgice ta tashi tace "kada kacemin ka auri kanwarka?"
Kabir yace "mama ban aureta ba, nine naso na aureta dai amma sai abokina yarigani, yanzu kanwar abokin nawa na aura"
Abdul da mamaki yace "itace princess ɗinka?"
Kabir cikin hawaye yace "itace"
Abdul rungume Kabir yayi yace "ina sonka Abokina nagode maka daka sadaukarmin da soyayyarka dukda hakan shine mafi alkhairi"
Kabir yace "zan iya yimaka komai sabida nine na ɓata maka rayuwa nabaka kwaya har kayiwa yarinya fyaɗe ka yafemin"
Mama tace "aina kayi mata fyaɗen awani gari?"
Abdul cikin jin kunya yace "A Yola take"
Mama tace "ya sunan yarinyar?"
Abdul yace "bansan sunanta ba amma inada hoton bayanta"
Ciro wayarshi yayi ya nunawa mama hoton cikin mugun jin kunya, da sauri mama ta ɗago ta kalleshi, tashi tayi tashake kwalar riganshi, da karfi tace "dama kaine? Kaine kayiwa Fadila fyaɗe? Wannan ƴata Fadila ce lokacin datake yarinya"
Abdul dayaji baya iya numfashi dan wuyarshi tashake tari yafara yanaso yayi mata bayani, Baby ce tazo tanajan mama tace "Shine Mijin Fadila ki sakeshi kada ki kasheshi"
Fadila ganin Baby tanajan mahaifiyarta yasa ta mike taja Baby da karfi, nunata tayi da yatsa tace "kidaina jan mahaifiya haka ba sa'arki bace"
Baby tace "tofa wuyarshi tashake bakya tunanin kada ta kasheshi?"
Fadila tace "sai me dan ya mutu? Fyaɗe fa yayiwa ƴarta"
Baby tace "baki damu ba kenan idan ya mutun"
Fadila tace "ni kin damune da Kanwata ta mutu?"
Baby cikin mamaki take kallon Fadila tace "na..."
Hannu Abdul yaɗaga mata alaman tayi shiru, tsit tayi, Kabir ne yatashi ya janye mama, cikin kuka yace "koma meyayi mata nine sila, nine nasa mishi kwaya a ruwa harya fita a hayyacinshi, bansan abin akn kanwata zai faɗa ba, shiyasa akace kayi abu me domin kanka zai koma, idan kayi mumuna ma kanka zai koma, a halin yanzu shine ya auri Fadila a matsayin siriki yake a wurinki"
Mama kuka take tace "ina Amrah?"
Fadila tace "gatacan an suturta ta shikenan ta tafi tabarmu, shikenan narabu da ƴar uwata"
Mama kan gawar taje ta buɗe fuskar, ganin Fuskar Amrah yana haske kamar kace tashi mutafi yasa ta zauna tafara kuka awurin"
Momy tazama ƴar kallo yau, takasa gane mayake faruwa,
Haka suka kwana agidan kowa idonshi biyu, da safe akazo ɗaukan gawa za'aje birneta, nanfa sabon kuka yatashi Fadila rike makaran tayi tana tsala ihu, da kyar Kabir ya janyeta yakaita ɗaki, haka aka fitar da gawan aka tafi dashi, Ahmad da ƴan uwanshi suma sunata kuka, Bilal da Minal ma sai kuka suke, Kaka ce tarikesu takaisu ɗaki, duk gidan babu wanda yakai Umar kuka idan ya tuna abinda tafaɗa mishi har wani zazzaɓi yakeji, nan su Dady sukaje suka binneta,
Fadila gaba ɗaya hawayenta ma sun bushe sai kukan zuci datake, Mary ce tashigo gidan da jaririyar a hannunta, sun manta ma da yarinyar, wurin Fadila taje tace "ga Babyn"
Fadila karɓan yarinyar tayi batace komai ba sai ido data tsura mata, Ganin yarinyar tana kama da Amrah yasa ta rungumeta,
Kamal daya kasa shigowa gidan ya rakuɓe a lungu tanata kuka, ganin jama'a sunyi yawa yasa bazaima iya isowa wurin ba,
Abdul ne yazo wucewa yaji sheshekan kuka, lekawa yayi dan ganin ko waye, ganin mutum yahaɗe kai da gwiwa yasashi matsowa ya dashi,a hankali yace "bawan Allah kadaina kuka haka meya faru?"
Kamal ɗago kai yayi dan ganin wanda yayi mishi magana, ido huɗu sukayi da Abdul da sauri yamike yace "K.M, me kakeyi anan?"
Kamal dukar dakai yayi yana kallon kasa, kasa ɗagowa yayi dan wani mugun kunya ne yarufeshi, Abdul rungume Kamal yayi yace "yaushe kazo?"
Kamal yace "nazo wurin matata ce amma tarasu"
Abdul yace "Amrah ce marka?"
Kamal yace "Eh ka yafemin naci amanarka"
Abdul yace "ba komai ashe Fadilan ce ma nayiwa fyaden kuma itace na aura"
Da murna Kamal yace "da gaske?"
Abdul yace "eh"
Kamal cikin kuka yace "ka gafarceni"
Abdul yace "kada ka damu babu komai yariga ya wuce amma ya akayi haka?"
Kamal yace "dogon labari ne kuma yanzu hankalina yanakan matata ta mutu amma kunya da fargaba yahana shiga naga gawant..." kuka ya fashe dashi me taɓa zuciya yama kasa karasa maganar, Abdul ne ya rinka bashi hakuri yace "muje nayi maka jagora zuwa ciki saika gaida mama"
Kamal yace "kunyan Fadila nakeji bansan dawani ido zan kalleta ba"
Abdul Kamal yabashi tausayi gashi da tarin tambayoyi amma yasan bazai iya amsa mishi a wannan hlin dayake cikin ba, da kyar ya lallaɓa Kamal suka shiga ciki, Abakin kofa sukayi sallama, Fadila na kwance daga gefe tasa dogon hijabi ta rufe jikinta duka, ga calbi a hannunta kanta yana mugun sarawa idanunta sun kumbura sunyi jaa, Sallaman Abdul ne yasa taɗan ɗago kanta, ido huɗu sukayi ta ɗauke kai takara kwanciya, Kamal ne yashigo ya durkusa wurin Mama yana kuka yace "ya hakuri?"
Mama ko kallonshi batayi ba, hakan bai dameshi ba ya mike yaje wurinda Fadila take kwance kanshi ya dukar kasa hawaye yana sauka a idonshi hannu yaɗaga sama alamar roko yace "ki yafemin"
Fadila ɗago manyan idanunta tayi tawatsa mishi wani mugun kallo, Cikin kukan yace "Ki yafemin badan niba saidan Allah"
Fadila ce tamike furr tanuna mishi hanya tace "fita!!!"
Kamal matsowa yayi yana rokanta, juyawa tayi ranta a ɓace ta hango wani butan karfe, ɗaukowa tayi tazo ta kwala mishi a goshi, nan take goshinshi yafara zubda jini, bai damuba yace "ina ƴata? Ku taimakeni na ganta kubani ita"
Sai a lokacin Mama tamike tace "ƴarka ko? Ƴarka kace ko? Tom jirani na ɗauko maka ita"
Mama cikin ɗakin tashiga ta fito dawani katon bokiti tayi kan Kamal, da sauri Abdul ya janyeshi suka fita daga ɗakin, Momy ce tamike tazo wurin Mama tace "Haba mana! Miye kukeyi haka? Gidanfa rasuwa ne kada a zagegu marasa hankali"
Mama idonta yana zubda hawaye tace "bazaki ganemin abinda nakeji acikin zuciyata bane"
Momy tace "koma menene ai sai kuyi hakuri"
Fadila tace "Momy dan ba ƴaƴanki akayiwa hakan ba shiyasa kike wannan maganar"
Momy da mamaki takalli Fadila tace "ni kike faɗawa haka?"
Fadila tace "idan bakeba to waye?"
Momy shiru tayi takoma ta zauna, Nabila da Pinky suma sunyi shiru, sai Baby datake mugun jin tsoron Fadila yanzu,
Momy ce taɗan koma gefe takira wayar Dady tace "yakamata a koma gidanmu ayi zaman makokin acan danfa anan akwai matsala"
Dady yace "eh anjima zan turo mota azo a kwasheku dan me martaba ma zasu koma gobe"
Momy tace "tom" tareda kashe wayar takoma ta zauna kamar batayi komai ba.
Nabila ce taɗau buta taje tilet dan fitsari ya dameta, a hanya taji sheshekan kuka da sauri taje wurin datakejin kukan yana fitowa, ganin yaron da aka kora ɗazu acikin ɗakin ne yasa ta matso wurinshi, Kamal ɗago jajayen idonshi yayi ya kalleta, a hankali yakuma sauke kanshi yaci gaba da kuka, Nabila ajiye butan tayi tashiga ciki, roban ruwan swan ta ɗaukko me sanyi ta tsiyaya a cup, wurinshi tanufa taje a tsaye tace "gashi"
Ɗago kanshi yayi yace "Aa banason ruwa ƴata nakeson gani" wani sabon hawayen ne yakara zubo mishi, Nabila cikin tausayi taɗan duka, cup ɗin takai bakinshi tace "sha"
Kallonta yayi kafin ya buɗe bakinshi a hankali