Showing 33001 words to 36000 words out of 139192 words

Chapter 12 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

893

hankalinshi ya tashi me akayi mata? Kodai bata sona ne? Anya ba dole aka aura mata niba? Shine tambayar dayake a zuciyarshi, d'an  buga bayanta yayi alamar rarrashi yace "its okay kidaina kuka"

Amrah cikin kuka tace "Yaya Kamal idan banyi kuka ba me zanyi?"

Kamal yace "banaso ñnaga kina kuka meya sameki?"

Cikin kuka tace.

         "Yaya Kamal jikina yana bani Adda Fadila zata dawo idan ta dawo kuma nasan zatamin kallon maciya Amana, kuma idan taganni dakai kishi zaisa tafad'i abinda ranta yaso zata iyamin sharri a wurinka kuma zata iyamin sharri a wurin Iyayena, shiyasa nake kuka"

Kamal tausayi yarinyan takuma bashi Fadila wace irin Yaya ce me son zuciya?

"Kidaina kuka kowa yariga yasan halinta kuma koda tayi miki sharri akanta zai koma, zanyi kokarin ganin na fahimtar da Abba da Mama kinga ba wani Matsala ko?"

Amrah ta gid'a kai, yace "to kiyi dariya in gani"

Dariya tayi tana sunkuyar da kanta, Yace "tashi ki shirya na kaiki wurin shan ice cream" kallonshi tayi tanajin kamar tashigar dashi cikinta tsabar so, da murna tamike tashiga toilet Dan akwaita Dason outing, murmushi yayi ganin yanda take murna Dan yace zai kaita wurin shan ice cream indai hakan zai sata farin ciki to babu shakka zai rinka squeezing na time nashi yana kaita wuraren shakatawa, wata kila zai rage mata rad'ad'in dayake ranta.

        "Bayan tashirya cikin abaya pitch color da mayafinshi sai d'an karamin jaka baka data rataya agefe kafarta sanye da flat shoe, tayi kyau sosai fuskarta d'auke da light makeup, Kamal ne yafito rikeda makullin mota ya kalleta tayi mishi kyau, yace "Kanwata mayafin nan yayi karami ko za'a canja please?"

Amrah turo baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "Ayya Yaya Kamal nifa banason abinda zai takuramin jiki mayafi babba takuramin yake"

Kallonta yakeyi yanajin sonta a zuciyarshi jiyake kamar karta daina magana tsaban yanda muryanta yayi mishi dad'i, Lumshe ido yayi yace "please mukoma kiyita min magana da shagwab'anan na tabbata bazan gaji da kallonki ba"

Dariya tayi sosai kafin tace "nikam mutafi ai tareda kai zamu fita bani kad'ai ba, watakilama kishine yake damunka..." Da sauri tasa hannu tarufe bakinta jin SUB'UL DA BAKA datake shirin yi, murmushi kawai yayi yariko hannunta suka nufi parking space, Ummace ta leko ta window tana kallonsu jitayi kamar tabisu ta tsayar amma idan tayi haka zasu tuhumeta kuma batasan amsa dazata basu ba, a hankali ta koma cikin bedroom ta kwanta akan gado, "meyake shirin faruwa? Nashiga uku!" Shine abinda take maimatawa a zuciyarta.

      "Kamal da Amrah wurin shan ice cream na Imbru garden sukaje, kujeru masu kyau suka zauna akai sai kallonsu mutane keyi, Kamal ya kurawa Amrah wacce take zaune kusa dashi ido, "Kallonfa?" Murmushi yayi yace "idan ban kalli kyakyawar matata ba wace zan kalla?"

Murgud'a baki tayi tace "ai bankai Adda Fadila kyau ba"

Da mamaki ya kalleta yace "ai kinfi Fadila kyau nesa ba kusa ba hasalima banason kina had'amin kanki da Fadila dukda nasan Fadila 'yar uwarki ce dole kiji zafi idan aka fad'i abinda babu dad'i akanta amma yazama dole in fad'a Fadila muguwace batada tausayi batada Amana kuma Wanda aka bashi amana yaci shi munafiki ne Allah ne yafad'i haka, kinga Fadila munafuka ce"

Amrah kawar da kanta tayi gefe tanajin dad'ine ko haushi ne, maganan yayi mata dad'i batason taji Kamal yna yabon wata halitta koma bayan ita, Kamal yace "kiyi hakuri idan ranki ya b'aci"

juyawa tayi tace "kadaina bani hakuri babu komai Allah yana kallo"

Yaji dad'in maganarta gata yarinya amma ta iya tsara zance kamar babba "wani kalan flavor  gimbiyata takeso?"

Amrah tace "Vanilla Yaya Kamal"

Kallonta yayi yace "Nima nafison Vanilla kinga ra'ayinmu yazo d'aya"

Dariya tayi tace "eh kam"

Zuwa yayi ya karb'o musu ice cream yazo ya zauna ya bud'e d'ibowa yayi a spoon yakai bakinta, babu kunya babu tsoron Allah Amrah ta bud'e baki tana murmushi ta karb'a, itama d'ibowa tayi tasa mishi a saman hanci, ganin haka shima yad'ibo yashafa mata a fuska, dahaka suka fara har suka b'ata kayansu da ice cream saidai Amrah tafi b'aci Dan Kamal gaba d'aya ya shafe mata, ganin kayanta yafi b'aci yasa ta zauna a kasa ta turo baki tana zuba shagwab'a kamar karamar yarinya, Kamal yanayin yayi mishi kyau waya ya ciro yana dariya yafara d'aukanta photo harda video, saida yagama kafin yazo yafara rarrashi da kyar ta yadda yasiya mata wani harda su chocolate da sweet yabata tarike a hannunta, suka Shiga mota har yanzu bakinta a gaba, baiyi magana ba suka tafi gida, suna shiga gida Amrah tad'au ledanta ta bud'e motar tafice, Kamal ne yazagayo da gudu yariko hannunta, cikin sanyin murya yace "Am sorry Kanwata"

Hararan wasa ta banka mishi taja hannunta da karfi zata wuce shima da karfi ya fizgota ta fad'a jikinshi ad'an tsorace ta rungumeshi tsam tana sauke numfashi a kunne ya rad'a mata wata magana da karfi ta tureshi yana dariya yafara gudu tana binshi daidai bakin kofa tasamu tarikoshi ta baya ta rikeshi gam yana dariya yana kwace jikinshi, Unty Sadiya ce ta waro do tana kallon ikon Allah, ranta ya b'aci sosai ganin Moment na Amrah da Kamal ita tanacan tana kokarin nemo Fadila sukuma sunzo sunayin wata 'yar Makauniyar Honeymoon wacce za'a kirata a fili da Cin Amana, rai b'ace tanufi wurinsu da karfi taja Amrah kafin Amrah tagano ko wayene harta d'auketa da wata zazzafar mari, Star tafara gani suna yawo a idonta tsabar zafin Marin, d'ago hannu tayi zata kara mata Kamal yayi carab yariko hannunta yana huci kamar zai mari Unty Sadiya, cikin mamaki Unty take kallonahi bakinta bud'e, Umma ce ta koma cikin gida da sauri ganin abinda yake shirin faruwa,  cikin d'aki tashige tana ekawa ta window, Amrah ta durkushe kasa hannunta tikeda kuncinta inda Unty ta mareta jitake kamar ta tashi ta rama amma idan tayi haka Kamal bazai yadda tana da hankali ba dole ne tad'au mataki akan matarnan.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 22*

        ~Huci kawai yakeyi hannunshi rikeda na Unty yau badan taci darajar Aure ba wlh dasai ya wanketa da mari sai tayi Dana Sanin Marin datayiwa matarshi, Unty cikin mamaki tace "Me hakan yake nufi Kamal?"

Kamal Wanda ranshi yagama b'aci yace "me kika gani da idonki?"

Ba Unty ba har Amrah wacce take durkushe saida ta d'ago ta kalleshi jin maganar daya fito daga bakinshi "Kamal ni kake fad'awa bakar magana Dan na mari Amrah?"

Kamal yace "badan darajan Auren dayake kanki ba dasai na zabga miki mari kema kiji idan akwai dad'i"

Unty tazama statu zuwa yanzu tarasa abun fad'i bakinta yana rawa tajuya tana kallon Amrah ta nunata da yatsa tace "Amrah kinyi Asara kin cuci 'yar uwarki Allah bazai barki ba Amrah saikin fuskanci wulakanci a rayuwarki...." Kafin ta karasa Kamal ya tari numfashinta dacewa "karki sake ki zageta sabida batada laifi, meyasa zaki d'aura mata laifin yayarta? Taji da wanne? Da b'atan yayarta ko kuma da tashin hankali? Yarinyarnan fa 17 years ce tayi karama da d'aukan wasu matsalar kinaso takamu da low BP ne? Ita Fadilan dataje yawon duniya taje karuwanci waye yayi maganar rashin dacewar abun? Sai wannan wacce ta rufawa iyayenta da yayarta asiri ta Aureni bata bari kowa yasan halinda ake cikiba bata yadda mun shiga kunya a idon duniya ba itace zakisa Agaba kina zagi kina tuhumarta da laifin daba nata ba, to last warning karki sake ki kara shigowa gidannan idan kinsan matata zakizo duka" yana fad'an haka yariko hannun Amrah ya d'agota tareda share mata hawayenta ya janyota jikinshi yana bata hakuri da kalamai masu dad'i saida tad'an sassauta kukan kafin yacireta ajikinshi yariko hannunta suka wuce cikin gida anan sukabar Unty Sadiya tsaye baki bud'e ido a waje kamar Walidation taga nama (lols) ga ledan Ice cream a gefe, Amrah kallon Kamal tayi tace "Yaya Kamal ka tsaya in bata hakuri kar tace na rainata"

Kamal jiyayi kamar yayi mata kuka tsabar tausayin data bashi d'auke kanshi yayi ya had'a rai yace "babu hakurin dazaki bata kamata ai ace itace zata baki hakuri"

Amrah wani sanyi taji a zuciyarta ganin yanda Kamal yanuna yana sonta a idon Unty dama aya barta taje bata hakuri da waahi saita kwancewa Unty Notikan dasuke d'aure akanta Wanda suke sata shiga harkar daba tata ba, saida Unty ta gaji da tsayuwar kafin tajuya zata fita, kallon ledan Ice cream tayi dasu chocolate da sauri tajuya tad'au ledan cikin b'acin rai tace "baku ba ice cream saidai kusha ruwan zafi da Lipton kuma insha Allahu ko madara bazaku samuba".

      

          "A kwana a tashi ba wuya yau saiga su Fadila kusada boda sunyi kwana d'aya a wurin amma sun rasa ta ina zasu bi, Sunyi murna sosai ganin koba komai zasu mutu a kasarsu ta haihuwa, zaune suke akarkashin bishiya wacce take nesa da boda, Fadila ce tace "yanzu yaya zamuyi? ta ina zamu fara bi?"

Baby tace "nimadai bansan yanda zamuyi ba Adda Fadila sabida ina tsoron karsu kamamu"

Fadila kwarai kuwa amma inada mafita d'aya saidai akwai hatsari sosai"

Duk suka amsa da "kifad'a mana mun yadda" Fadila gyara zama tayi tace "Meze hana da daddare muje bakin Bodan muga yanda abun yake?"

Kowacce taji tsoro da wannan maganar sukace "ta Yaya?"

Fadila tace "idan munje ke Fatima kece zaki karasa wurinsu kice amma ki b'uya idan kinji alamar tafiyan mutane sai kiyi mana alama da kukuruku kinji?"

Fatima tace "to Amma idan sun kamani fa?" Fadila tace "Yanzu bazaki iya sadaukar da rayuwarki akan 'yan uwanki musulmai ba?"

Fatima tace "zan iya  Kuma nasa a raina zanyi Fadila zama dake akwai d'aukan darasin rayuwa zanyi fatan karsu kamani sabida banason rabuwa daku inajinku kamar 'yan uwana ada banason shiga cikin mutane sabida girman kai da nuna mahaifina yanada kud'i amma yanzu na tabbata mutum rahama ne"

Shiru sukayi sunajin maganarta kowada yanda yakeji a ranshi.

       "Da dare sun shirya su Biyar Fatima saida ta roki tuba a wurin kowa tabaiwa kowa hakuri sabida yanayin zama gashi batada tabbacin zata dawo, suna kuka suna cewa ba komai har suka rabu tana juyawa tana kallonsu, saida suka iso bakin boda Fadila ta rungume Fatima tace "All the Best" Fatima janye jikinta tayi tawuce daidai bakin bodar tana lekawa akwai haske awurin amma ba sosai ba zaka iya hango masu zirga zirga a wurin dukda bazaka gane fuska sosai ba, Fadila da sauran 'yammatan lab'ewa sukayi sunason kallon hanya amma basu ganin komai, saida suka kai minti Talatin har sun gaji zasu juya sukaji sautin tafiyar mutane, a hankali suka koma Inda suke suka lab'e, Wasu mutane ne sun rufe fuskarsu da alebo sun kai kimanin mutane arba'in sukazo wucewa ta wurin wani wuri suka d'aga suka dirka dukansu aciki suka sannan d'ayan ya rufe, waya yakira yana magana a hankali yace "wannan sun samu sun tsallaka ba Wanda yaganmu gobe zasu zaka jisu a Nigeria"

Wani Hamdala su Fadila sukayi tareda rungume juna suna toshe bakinsu gudun karsuyi sub'utar baki suyi ihun murna.

_Jiddah Ce....✍️_

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi



*Chapter 23*

        ~murna sukayi sosai suna cikin jin dad'in sun samu mafita sukaji ana cewa "heyy!!! Heyyy!!! Kubita"

A firgice suka juya sunason ganin waye za'abi ganin Fatima tana zabga gudu wasu mutane suna binta yasa suka tsaya a gefe d'aya tana zuwa wurinsu suka janyeta tareda toahe mata baki gudun kartayi ihu, haki takeyi kamar ranta zai fita sunajin mutanen sunata haske haske da dogon toci me zooming sukayi tsitt har saida suka daina jin motsi kafin suka fito cikin sand'a suka koma makwancinsu a nesa da bodan, Daren yau basuyi bacci ba suna shirya yanda zasu gudu gobe".

     "Amrah ce a kitchen tana soya plantain tunani ire iri takeyi amma tafi tunanin Fadila sabida tana tsoron kada Fadila tadawo tarabata da masoyinta Kamal, Kamal ne yashigo kitchen d'in da rigan bacci a jikinshi rungumeta yayi ta baya ya kwantar da kanshi a bayanta cikin muryan bacci yace "kiyi hakuri da abinda Unty tayi miki jiya insha Allah zan d'auki mataki" cire hannunshi tayi daga waist nata tajuya tana kallonshi kankance ido tayi ta tab'e baki kamar wata baby mayar da muryanta tayi irin na maza ta kwaikwayi maganarshi, dariya yayi sosai yace "keba? Zanyi maganinki ne"

Itama dariya tayi tace "da paracetamol ko Flajin?" Jan kumatunta yayi yace "da kowanne ma, me kika shirya mana?"

"Delicious" tace.

Cikin tsokana yace "Kamar ta iya girki"

Shiru tayi mishi Dan tasan idan ta biye mishi zasu wuni anan batayi komaiba domin akwaishi da surutu kamar (Walidation)

Tayata aikin yafara sunayi suna hira tareda tsokanar juna saida suka kammala kafin Kamal ya kwashe abincin yakai dining itama Amrah tattare wurin tayi ta goge kafin tabi bayanshi da jog na Banana and Water melon juice, Sai murmushi takeyi ganin yanda Kamal yake sakin jiki da ita zata iya rantsuwa Kamal baya tuna Fadila yanzu itakuma shine babban abinda takeso a rayuwarta, tana zuwa wurin dining ta sameshi ya zauna yana jiranta zata zauna agefe ya janyota ya d'aurata a cinyarshi a firgice take kokarin kwace kanta amma ta kasa da tsoro a fuskarta tace "Yaya Kamal su Umma fa suna zuwa please ka saukeni"

Lumshe ido yayi Dan yanajin dad'in yanda take zaune a jikinshi bayaso ta tashi ta barshi koda na second d'ayane, kara matseta yayi ajikinshi ya kwantar da kanshi a kafad'arta da murya kamar me bacci yace "please kizauna banason kitashi kinji?" Yafad'a yaba shinshina wuyarta kamar mage, Lamarin Kamal yafara bata tsoro da iya karfinta take kokarin sauka amma yahana hawayene yafara bin fuskarta a hankali tace "Dan Allah ka saukeni idan su Umma sunzo sunci abincin na yadda zan zauna amma yanzu ina kunyar su ganmu haka"

Kamal ganin tana hawaye kuma baya son yaga tana kuka yasashi fito da harshenshi yafara lashe hawayen nata cikin wani irin salo, Itama shiru tayi Dan yanayin yayi mata dad'i, Umma da Hajiya Turai ne suka shigo d'akin daidai lokacin Kamal yakai bakinshi kan na Amrah lumshe ido sukayi gaba d'ayansu suna shakar numfashin juna Wanda yake saukar musu da kasala musamman Kamal Wanda yakeji kamar ya had'iyeta kozaiji sauki, bakinta yake sucking cikin kwarewa yana sauke ajiyar zuciya, Da sauri Umma tayi baya baya tana Neman hanya amma kofan ma bata ganiba Dan wani irin duhu take ganin ya mamaye hanyar, Hajiya Rufe idonta tayi tana cewa "Lahaula wala kuwwata illa billahi Allah karabamu da mumunan gani"

A hankali suka sulale batareda sun bari yaran sungansu ba, d'akin suka koma zama sukayi akan sofa jigim Umma har wani zazzab'ine yake shirin kamata.

        "Kamal jiyake kamar su dawwama a haka idan tana jikinshi jiyake kamar karta tashi, Amrah ma jitayi lips nashi sunyi soft batasan lokacin data fara kissing nashiba, saida tad'an dawo hankalinta kafin ta tureshi tamike da sauri, Kamal lumshe ido yayi ya kwantar da kanshi jikin dining d'in yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, Amrah saida tad'an gyara fuskarta kafin tajuya a hankali tanufi kofa saida Tasake juyawa takalli yanayin dayake ciki kafin ta bud'e kofar tanufi d'akin Umma sallama tayi cikin d'an tsoron karsu gane abinda sukayi, zaune tagansu akan sofa suna ganinta suka mayar kamar ba abinda suka gani, Gaishesu tayi tace " Umma abinci ya kammala"

Umma tace "to jeki muna zuwa"

Juyawa tayi da sauri Dan taga kamar sunayi mata wani d'an kallo kallo Wanda baya ganeba, saida tashiga d'akin Kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta karasa wurin dining bata damu data tashi Kamal ba Dan tayi zato baccine ya kwasheshi, tana cikin serving su Umma suka shigo zama sukayi tasawa kowa nashi Hajiya ce takalli Kamal tace "shi bazaiyi breakfast  bane?"

Amrah tace "zaiyi"

A hankali tad'an bugashi tace "Yaya Kamal katashi kayi breakfast"

Kamal yana jinta saidai bayaso ya d'ago su Umma dolene su fahimci halinda yake ciki, Umma ce ta bugashi da d'an karfi tace "tashi mana son ana maka magana kayi shiru"

'Dago kanshi yayi Wanda idonshi yayi jaa fuskarshi duk zufa, saida suka tsorata duk ganin yanayinshi, "bakada lafiyane son?"

Kallon Umman yayi a hankali yace "Umma marana ked'an ciwo bari naje nasha magani"

Umma kallonshi tayi batace komai ba, a hankali ya mike da sauri Yakoma d'akinshi Umma takalli Amrah wacce ta dukar da kai tace "bishi kibashi maganin da ruwa"

A hankali tace "to Umma"

Hajiya ta kalli Umma bayan Amrah ta tafi tace "yaran zamani basuda kunya wallahi"

Hmmm shine abinda Umma tace domin ita kad'ai tasan yanda takeji a zuciyarta.

Amrah tana Shiga d'akin taganshi ya kwanta rub da ciki a bayanshi ta zauna batace komai ba shima baice komai ba, A hankali ta leka fuskarshi taga har yayi bacci, blanket taja tareda rufeshi, sannan tafice a d'akin takoma wurinsu Umma, Umma kallonta tayi tace "ya yake?"

Amrah tace "yasha har yayi bacci"

Kallon Hajiya Turai Umma tayi itama Hajiya tab'e baki tayi sukaci gaba dacin abinci.

   

       "Washe gari su Fadila sunyi shirin komawa Nigeria kota halin kaka koda zasu rasa ransu ne sunyi alkawarin saisun shiga Nigeria abinci suka Nema kowacce taci sukasha ruwa dare yanayi suka nufi hanyar dasukaga Mutanen sunbi, ramine Wanda yakeda dogon hanya tafiya kawai sukeyi suna Addu'ar Allah yafitar dasu lafiya, saida suka kara kai wani Daren batareda sunga wani alaman hanyaba a halin yanzu sun fara jiggata abincin dasuka shigo dashi yakare babu hali babu hanyan samun abinci, Ga duhu kuma basuda toci ga soro, idan sunga alamar lokacin salla yayi taimama kawai sukeyi suyi sallan haka suke rayuwa acikin wannan Ramin har tsawon kwana uku, wasu daga cikinsu sun mutu acikin Ramin saidai suyi kuka acikin duhun su tona rami Susa gawan, su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login