Showing 108001 words to 111000 words out of 139192 words

Chapter 37 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

871

son Amrah sosai, Kulu kuwa sai yawo dason zuwa wurin shakatawa shi kuma Ahmad a ɓoye yake ɗawainiya dasu Amrah dan bayaso mutane su fahimta.

             "Pinky ce acikin ɗaki sai kai kawo take, Muryan Daddy ta jiyo abin yakara bata tsoro, Nabeela ta jima bata dawo ba gashi Dady zeyi tayiwa Pinky faɗa, bata kara tsorata ba saida taji Dady yana kiran sunanta da ihu, fita tayi jikinta yana rawa tace "gani Dady"

Dady yace "Ina Nabila?"

Pinky tace "am.. am tana wanka"

Dady kallon Pinky yayi yace "tana wanka kikace?"

Pinky tace "eh dady"

Dady yace "okay muje ɗakin naku ai zata fito ko?"

Jikin Pinky ne yafara rawa tace "to.to"

Gaba dady yasata suka nufi ɗakinsu Pinky sai rarraba ido take tasan Nabila bata cikin toilet gashi tayiwa Dady karya yau idan ya gano gaskiya me kwatanta saiya shirya, Hawaye ta share a ɓoye dan tasan Nabila bata nan, kamar a mafarki taji Nabila tana kiran sunanta, da sauri ta juya tana kallon Nabila data fito daga toilet daga ita sai towel, Nabila murmushi tayi tace "Darling meya tsorataki haka?"

Pinky cikin jin daɗi ta rungumeta, Nabila tace "Welcome Dady"

Dady kallonta yayi yace "me gadi yacemin kin fita da mota yaya akayi kika dawo banji horn ba?"

Nabila cikin murmushi tasaki Pinky ta matso wurin Dady tace "come on Dad yaushe zan fita a gidannan kamar jail?"

Dady yace "Nabila banaso ku lalace yaran zamani ba abin yarda bane"

Nabila face ta kwaɓe sannan ta faɗa jikin Dady tace "Dad Babu fa inda naje ina nan kwance ka tambiyi Darling mana"

Dady yace "na yadda sabida Pinky bazatayi min karya ba, ku kama kanku ku rike mutuncinku kunji"

Nabila tace "come on Dad kasan halinmu ai kasan abinda zamu iya kasan wanda bazamu iyaba"

Dady yace "hakane ina tsoron barinku agida dagaku sai mahaifiyarku mamanku batada hali ko kaɗan kuyi kahuri bawai ina zaginta bane, naso ace ɗan uwanku yana nan amma Allah baisa hakan ba Allah shi kaɗai yasan dalilin rabamu dashi tun yana yaro"

Pinky tace "Dady Allah zai bayyana shi mu cigaba da addu'a"

Kallon banza Nabila ta watsa mata sannan ta wuce wurin shafa manta, Dady fita yayi yana share hawaye, yaso ace ɗanshi nafari yana tare dashi amma hakan baiyi ba, tunaninshi idan ya mutu waye ze kula da wannan uban dukiyar daya bari, "Allah ya bayyanaka khalid"

Nabila Dady yana fita bata kalli Pinky ba tace "Darling meyasa kike addu'ar Allah ya bayyana yayan mu? Kinsan fa idan ya bayyana bamuda kaso me yawa acikin dukiyan Dady, kaso ɗayafa za'a raba mana mu biyu shi kuma yaɗau ɗayan"

Pinky tace "meyasa bazan damuba? Ɗan uwafa ba wasa sannan kina maganar dukiyar Dady idan mun rigashi mutuwa kumafa?"

Nabila tashi tayi cikin takunta na isa da raini tariko hannun Pinky tajata zuwa bakin gado, zama itama tayi tace "Darling ke yarinyace bazaki ganeba bakije kinga duniya ba, bakije kinga yanda turawa suke rayuwar ƴanci ba, infact bamusan shi bama kila muganshi da shegen muni kinga gara dai mu kasance mu kaɗai ɗin"

Pinky tace "komaifa zaki faɗa Unty Nabila saide ki faɗa nikam bazan daina addu'a ba"

Nabila tace "oh Hello naganoki kinaso ya bayyana me daganan sai yasamu abokai idan sunzo gidannan sai suyita baki kuɗi suna cewa ke kanwarsu ce ko?"

Pinky ranta ya ɓaci sosai tace "eh yafimin ai kinga hakan zesa natara kuɗinda basai na zuba ido ina jiran na gado ba"

Taɓe baki Nabila tayi alamar ba komai sannan tace "anyway ke yarinya ce"

Ran pinky ne yakuma ɓaci sai tayi tacewa Pinky yarinya ce kuma gashi itama yarinyar ce, tsaki kaɗan kawai taja sannan ta wuce ɗakin momy ɗinsu.

         "Akwana atashi shakuwa yana kara shiga tsakanin Abdul da Fadila duk da haka Fadila bata taɓa tambayarshi damuwarshi ba, duk da tana yawan ganinshi acikin damuwa amma tasa a ranta sai sun shaku sosai kafin ta tambiyeshi, kamar kullum yauma cikin tagumi taga ya zauna yayi nisa acikin tunanin dayake, tana isowa wurinshi tasa hannu tacire tagumin dayayi kafin ta zauna a gefenshi ta zuba mishi ido tace "menene matsalarka? Meyasa kake yawan sa kanka cikin damuwa idan har inada matsayi a wurinka to dan Allah ka faɗamin"

Abdul yace "be shafeki ba"

Fadila tace "ya shafeni"

Abdul yace "kamar yaya ya shafeki?"

Fadila tace "sabida kai mijina ne kuma bazanso na ganka cikin damuwa ba"

Kallonta yayi kamar da gaske wai kai mijina ne bayan kawance kawai suke, mikewa yayi zai tafi ta riko hannunshi tace "dolene ka faɗamin abinda yake daminka"

Da mamaki yace "dole kamar yaya?"

Fadila tace "kamar yacce kaji nace"

"To bazan faɗa ba bana raba damuwata da wani"

Fadila tace "to indai hakane kawancen a kwance bazan iya zama da wanda baya faɗamin damuwarshi ba"

Abdul yace "bazan kunce ba"

Tace "yazama dole ka kunce"

"Nace bazan kwance ba!!!"

Itama tace "nace an kunce ba shawara na nema ba faɗa nayi"

Cikin jin zafi Abdul yace "me kika ɗauki kanki?"

Fadila tace "matar Aure"

Daganan ta juya tabar wurin, tun daga wannan ranar basu kara shiri ba, hasalima Fadila ta daina fita lokacin datasan yana gida, abin ya dameshi sosai baisan sunyi wannan mugun saɓon ba sai data daina kulashi, ɓangaren Fadila kuma dama ta nemi su saba ne dan watarana ta janye ta barshi hakan zesa yafito da kanshi yafaɗa mata gaskiya.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 71*

         ~Fadila da Abdul sunci gaba da rayuwarsu kamar da babu wanda yake shiga harkan wani, Abdul bayama kulata dan gani yake yarinyar akwai dn karan ɓoyayyen girman kai, itama Fadila ganin girman kan nashi yayi yawa yasa tafita a harkanshi, tana zuwa aiki akan ka'ida, yau yakama sunday tun safe suna gida amma babu wanda yafita kowa a ɗakinshi yake aiki, Abdul ne yayi wanka yafito yana tsane jikinshi, tunanin yarinyar yafaɗo mishi a rai yanda tazo ranan tayita shige mishi, ɗan murmushi yayi sannan yaje wurin mirror yashafa mai, tareda taje gashin kanshi daya kara fito da kyaunshi da class ɗinshi a fili, sajen fuskarshi yaɗan shafa s zuciyarshi yace "wai inada mata"

Turare ya fesawa jikinshi yaje wardrobe ya ɗauko wandon shakatawa jaa da farin riga da picap jaa, sawa yayi yakalli kanshi a madubi ganin yanda yayi kyau yasa yayi murmushin daya bayyana kyawawan fararen hakoransa, idanunshi wanda ake kira sexy eyes yaɗan lumshe a ranshi yace "nayi missing ɗinki kaɗan"

Daganan ya juya cikin takunshi na kasaita yanufi babban falo inda yasan dolene tabi ta wurin idan zata fita, frij yaje ya ɗauko shampain da glass cup irin na wurin party ɗinnan me style a jiki, remote ya ɗauko ya kunna speaker ya jona da wayarshi sannan yasa wakar if you get a woman hold am tied oh, zama yayi akan sofa ya ɗaura ɗaya akan ɗaya yana sha yana enjoying,

Fadila data tashi daga bacci yanzu tayi sauri ta murza ido tunawa da ko breakfast batayi ba gashi yanzu kusan 12 da sauri ta mike taɗauko wani dogon riga jaa mara hannu tasa sannan tanufi kitchen a hanya ta jiyo sauti na tashi daga falo bata kawo cewar Abdul bane kawai ta basar, Tana shiga babban falo ta hango Abdul yana zaune kamar a club, haɗe fuska tayi tawuce yana kallonta ta kasan ido harta shige kitchen, saida tahaɗa breakfast tayi brush sannan ta cinye harda siɗe plate ɗin dan bataso yaɗana ko kaɗan girman kan nashi ya dafa mishi abinci yabashi, fita tayi zata koma bedroom taci karo da Nabila zaune a gefen Abdul jikinsu yana gogan juna, tasa kanta a kafaɗarshi kome take faɗa mishi cikin shagwaɓa ne oho, Fadila idan ranta sunyi ɗari to yau casa'in da tara sun ɓaci ɗayane kawai bai ɓaci ba domin idan ɗari ne suka ɓaci to tabbas baza suyita da kyau ba, amma duk da haka saita nunawa wannan nabilar iyakanta, a zuciye ta nufi ɗakinta Abdul yana kallonta yasaki murmushi, Fadila nashiga ɗaki tawuce toilet sabon brush takumayi sannan tayi wanka da sabulanta masu kamshi, fita tayi ta ɗaura towel tanufi bedroom mai tashafa duk abinda take a zuciye take yinshi ace wannan yarinyar ce zata rainata haka? Light makeup tayi me kyau tashafa lip balm me kalar pink, eyelashes nata masu tsayi ta taje da mascara sannan ta gyara gashin kanta ta taje ta zubasu ta baya, kaɗan taɗan zubosu ta gaba, wurin wardrobe ta nufa taciro wani riga baki me adon duwatsu shiba hijab ba shiba after dress ba, daga wurin kirji aka rufe zuwa kasa kaɗan, Baby ce tabata rigan a daren aurenta, dafari taji kunya har tacewa Baby itaba ƴar iska bace dazata wannan rigan yau gashi rananshi yazo, sawa tayi ta nufi wurin nadubi, daga baya yana jan kasa daga gaba kuma an buɗe duk cinyoyinta a waje, idan ka ganta kamar Katrina cafe a wurin karɓan award, farin fatarta takara fita kamar ba ƴar Nigeria ba, zaka rantse daga india take, zubawa kanta ido tayi tacikin madubi a ranta tace "Fadila kece zaki fita haka?"

Da sauri ta kawar da tunanin tunawa da yanda take ganinsu da Nabila abin yana mugun cimata tuwo a kwarya, cingum me kamshin tomtom tasa a bakinta tana tauna, wayarta ta ɗauko ta ɗau hanyar falo tana gaba riganta yana binta abaya yana jan kasa, sakkowa take daga matattakala, tana wani taku kamar me zuwa karɓan award ɗin miss world, Abdul yana kallon wani hoton da Nabila take nuna mishi tana zaune akan cinyarshi ko akwalar rigansu, kamshi ne ya ziyarci hancinshi ɗago kai yayi yana kallon inda kamshin ya fito, ganin Fadila a wannan dressing ɗin yasa har jikinshi yaɗan fara rawa, jiyake kamar yatashi ya ɗaukota, ido ya zuba mata harda ɗan buɗe baki kamar soko, Nabila ganin ya zubawa wuri ɗaya ido yasa ta ɗago kanta ganin Fadila ce yasa ta watsar dukda taji haushin kyaun Fadila a ranta amma ta nuna kamar bataga Fadilar ba, Fadila cikin takun nata taje wurin speaker ɗin ta cire wayarshi tayi connecting da nata, waka tasa wanda sautinshi yake tashi a hankali, kashe wuta tayi ta kunna disco light anan ɗakin yafara vanja color zuwa blue da jaa, Abdul aranshi yace "how romantic?"

Wurin frij ta nufa tabuɗe taciro shampaing saida ta girgiza kafin ta buɗe nan ya tashi sama, tana dariya ta ɗauko glass cup guda biyu tasa aciki, cikin takun nata tanufi inda suke, Abdul yakasa ɗauke idonshi akanta, tana karasowa ta hura mishi iskan bakinta zuwa idonshi murmushi ta sakar mishi wanda ya bayyano ainihin kyaunta domin kumatunta ne suka lotsa ba lotsawa irin kaɗan ba irin sosai ɗinnan  "hi darling kallon fa?"

Abdul bece komai ba sai binta dayake da ido, Cup ɗaya ta mikawa Nabila, Nabila kallonta tayi a yamutse tace "bana bukata"

Fadila cikin duniyanci tariko hannun Nabila murmushi tayi mata irin na masu shirin raina maka hankalinnan sannan tasa mata cup ɗin tace "haba Bebi yazama dole ki karɓa"

Nabila karɓa tayi tarike a hannu, Fadila tace "zaki iya tashiwa me wuri? Tunda tazo"

Nabila a banzance tace "wani wuri kenan?"

Fadila tanaɗan murmushi ta nuna mata cinyar Abdul tace "nan mana Bebi inason zama"

Nabila tace "bazan tashi ba ai anan kikazo kika sameni ko? Kuma ki sani ni ƴar uwarshi ce"

Fadila tace "oh come on Bebi nasani ke ƴar uwarshi nikuma matarshi ce"

Nabila tace "bazan tashi ba"

Fadila tace "banaso muyi na yara nafiso muyi na manya amma idan kika zaɓi na yaran sai muyi no problem"

Nabila sanin kalmar tayi sosai dan Fadila ta koyar da ita karatun tasan yanzu zatasha duka, tashi tayi Fadila ta zajna a inda ta tashi, wani shock ne ya ɗibi Abdul lokacin da Fadila ta zauna a jikinshi be taɓajin hakan ba tunda yake a rayuwarshi, Fadila kallon fuskarshi tayi tace "darling am sorry"

Bece komai ba dan bakinshi ya mutu, Nabila tace "zan tafi" riko hannunta Fadila tayi tace "oh Bebi meyasa kike sauri haka? Ki tsaya mana afara partyn"

Nabila tace "bakida abinda zaki bani koda na tsaya party ɗinne dan ban gani a jikinki ba saida kika shigo zuri'afmu"

Fadila ɗan dariyan rainin hankali tayi tace "amma ai ni farace ko Bebi? Kuma normal haka nake bana shafa na turai, Gashi na ganki agidan masu kuɗi amma fatata tafi taki hutawa wannan ya nuna ba kuɗin bane hutu kwanciyar hankali da samun iyaye masu kula dakai da nuna damuwa dakai da baka abinci me kyau shine hutu"

Nabila cikin tsiwa tace "shiyasa naga iyayen naki sun iya sun rikeki ai"

Fadila taji zafin maganar bada wasa ba amma ta daƙe tace "No no no no Bebi control your self banyi haka dan ranki ya ɓaci ba"

Nabila tace "banida lokacin zama dake har mu tsaya muna cacan baki"

"Amma ai kinada lokacin mijina?"

Nabila shiru tayi ta sunkuyo daidai kumatun Abdul ta sakar mishi kiss dan so take ta kunna Fadila, Fadila ɗan murmushi tayi ganin Nabila zata fita yasa tace "kinada damar yimishi kiss anan" nuna kumatun Abdul tayi sannan takuma cewa "amma bakida damar yimishi anan" hannu tasa tana zagaye pink lips ɗin Abdul daya zama statu, Ganin Nabila zata fita yasa ta haɗe bakinta da Abdul, waro ido yayi yana kallon yanda Nabila take hura hanci gefe guda kuma Fadila ta rike fuskarshi tana kissing ɗinshi, Nabila jin kofa a rufe yake yasa tazo a fusace taja Fadila tareda cewa "ina makulli? Ki buɗemin kofa"

Fadila data faɗo ta tashi tana kaɗe jikinta da hannunta a shagwaɓe tace "shine kika yadda ni akasa? Bakya ganin romantic moment damuke ciki ne?"

Nabila cikin fusata tace "ina ruwana dawani romantic moment ɗinku? Wancan ku ya dama"

Fadila tace "no no Bebi" ɗauko cup ɗin tayi tamika mata tace "let's dance and enjoyyyyy"

Daganan ta wuce wurin wayarta ta sauya waka zuwa wakar i have a conversation dama Fadila tun a yola ta iya rawa sosai tana yawan yin rawa, Bin wakar take tana rawa tana baza gashinta tareda juyawa, rigan jikinta sai komawa baya yake fatarta sai haske yake cikin blue da jaa ɗin disco light, kamar hawainiya take juyawa tana karasowa wurin Abdul, daidai gabanshi ta tsaya juya kanta tayi ta watsa gashin ta baya, sannan ta kashe mishi ido ɗaya, tareda zama kan cinyarshi tana rawa, ganin baya biye mata yasa tamike ta janyo hannunshi, faɗawa jikinshi tayi tasa hannunshi a gashinta tanayi mishi dariya da karamin bakinta, ganin yaƙi rawa yasa taje ta bayanshi tasa hannu ta rungumeshi ta baya, Abdul kasa daurewa yayi dan tuni ya fice a hayyacinshi, hannunta data zagaye ta cikinshi yariko tareda juyo da ita ta gaba, yatsa ɗaya yasa yafara zagaye fuskarta dashi remote na hannunshi ya danna nan falon yaɗau sautin wakar sai tashi yake kamar a club, Fadila ganin haka yasa taji daɗi Abdul dama ta wurin rawa yafi kwarewa shi yasan rawan wakar i have a conversation sosai, ganin itama ta iya yasa yafara bin step ɗin datakeyi, nanfa suka fara rawa iri ɗaya Fadila kallon Nabila tayi taga ta runtse ido jikinta yana rawa, Abdul janyo Fadila yayi jikinshi ya riketa sosai yafara rawa da ita, ganin wakar yakare yasa ya kunna wakar "dhoom 3 wanda jarumata Katrina kaif da Aamir Khan suka hau"

Nanfa yafara rawan india da ita itakuma Fadila sai juyawa take tana watso mishi gashinta tana dariya, Abdul harda runtse ido wurin rawar yana enjoying sosai, Fadila da ihu tace "Nabilove come let's dance"

Nabila ganin haka yasa takasa daure zuciyarta ga Abdul sai ɗaga Fadila yake yana sauketa, Hawayene suka fara bin kuncinta inama ace kofa abuɗe take da wallahi bazata tsaya ganin wannan wulakanci da bakin cikin ba, saida Fadila taga hawaye a idon Nabila kafin taji hankalinta ya kwanta, hannu tasa ta saman riganta taciro Makulli Abdul yana kallonta sosai dan tariga ta tafi da tunaninshi, Da kwarkwasa Fadila taje wurin Nabila rungumeta tayi a kunne taraɗa mata "Nabilove why are you crying did i hot you? Oh am sorry nima haka nakeji idan naganki ajikin mijina enjoy it please Bebi, Bye ki gaidamin Pinky da Dady da Momy badan muna romantic Moment da mijina ba dana rakaki zuwa mota but am sorry i can't leave him alone, bye"

Sakinta tayi tabuɗe kofar, A zuciye Nabila tafita kamar zata buge Fadila, Fadila da karfi tace "take care"

Gum ta rufe kofar tareda cewa "Alhamdulillah", nan kuma takasa motsawa dan wani kunya taji ya rufeta yama zata kalli Abdul?

Abdul cikin murmushin rainin hankali yace "Baby Doll come let's continue"

Fadila tana rurrufe jiki tace "am..am bacci nakeji"

Da mamaki yace "oh no no no sweetheart don't spoiled our romantic moment please Bebi"

Fadila tace "bacci nakeji" tana rurrufe jiki tayi hanyar sama zata tafi, ta baya ya rikota yasa fuskarshi a wuyarta hannunshi yasa ya zagaya cikinta dashi "kin koreta ai saiki zauna madadinta ko?"

Fadila kwace jikinta tafara yace "Aa dolefa kibi abinda nafaɗa miki you are my wife abi?"

Fadila tace "please leave me alone inada abin yi"

Hannu yasa yana zagaye cikinta ita kuma tayi sauri ta rufe cinyarta dan wani bala'in kunya ne ya ɗibeta, da masifa tajuyo tanaso ta gudu, rikota yayi ba zato ya ɗagata sama, da kafa ya kashe speaker ɗin yayi hanyar ɗakinshi da ita, kafa tafara zillarwa tanason sauka, cikin dariyan ƴan duniya yace "nimafa na zaga duniya naje kasashe da dama"

Fadila tace "wannan be shafeni ba ka sauke ni"

Abdul yace "no no no yau kisha ɗani zan ɗan hutar dake daga tafiya kinga dressing ɗinnan yayi attracting ɗina sosai sannan kin canjamin kamar wata jarumar india sai juyamin jikinki kike kamar hawainiya, Fadila data tsorata saiga hawaye a idonta tsoronta bawai abinda yake faɗa bane Aa tana tunanin idan yayi using ɗinta to dolene yajita disvirgin sakamakon abinda yafaru dasu a kasar Sudan wanda batason tunawa koda wasa a rayuwarta, kuma tarasa virginity ɗinta ne sabida kanwarshi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login