Showing 78001 words to 81000 words out of 139192 words

Chapter 27 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

869

ya girgiza kanshi kafin yace "kaji kunya wallahi kana namiji da halin mata? To Allah ya shiryeka kadai rinka kiyayewa kada kazo kanayiwa yarinya karama kuka sabida tsaro badan tsoro ba"

Kawar da kanshi yayi yaci gaba da wanke fuskarshi dan har Kabir d'inma haushi yake bashi, Kabir yace "in fact yau zamu mika ka hannun yarinyar sai yanda tayi dakai" wani kwandon soso Abdul ya d'auko da gudu yayi kan Kabir dashi ai kabir ganin haka yasa ya bud'e kofar yafara arcewa, sai zaga d'akin suke da kyar Kabir ya tsere yana dariya.

_bayan isha_

Sun zagayeshi gaba d'aya sun sashi agaba suna lallab'ashi ya tashi suje wurin amaryar kada tace an wulakantata, kememe Abdul yaki yadda hasalima kwanciya yayi yaja bargo yafara neman bacci, Kabir dayake tsaye ranshi idan yayi dubu to ya b'aci yace "Abdul wallahi idan baka tashi ba yau zan tafi kafin na irga uku, d'aya, biyu, uku.."

Abdul be tashi ba, Kabir ranshi ab'ace yamike ya d'auko properties nashi yayi hanyar fita dan yariga yasa aranshi ze tafi d'in, Abdul dayake kwance yazata da wasa Kabir yake atake yamike yace "tsaya mutafi"

Kabir dayake dab da murd'a handle ya tsaya yana murmushi yana d'aya daga abinda yasa yakeson Abdul shine bayason b'acin ranshi,  juyowa yayi yakoma cikin d'akin, Abdul yafara shiri a hankali kamar bazeyiba,saida yaja lokaci da dama kafin yagama duk suna kallonshi amma ba wanda yayi mishi magana, Kabir ne ya rungume Abdul kad'an yace "kayi kyau dude na tabbata yau idan taganka saita rud'e"

Turmutse fuska yayi yaki magana.

Fadila da Baby ma hakan ta kasance tsakaninsu, Saida Baby ta tashi zata tafi kafin Fadila tamike tasa atamfa dogon riga wanda aka cire pattern d'in akasa ajikin gyale tayi kyau sosai dan yanzu saida sukayi mata make up, saide fuskar kamar an aiko mata da mutuwa ko alaman murmushi babu, suna cikin fesa mata turare Nabila tashigo d'akin hannunta rikeda leda alamar daga shopping ta taso, zama tayi a gefen gado ta bud'e ledan shawarma taciro tafara ci, sai ice cream me chocolate aciki, tanaci tana danna wayarta ko kallon inda Fadila take batayiba, Fadila ma hakane kallo d'aya tayi musu ta watsar, Pinky ce tace "Unty gida kikaje"

"Eh kinsan bamuda nisa da kafama naje"

Baby tace "shiyasa naji dad'i wallahi pinky zaki rinka shigowa Adda Fadila koba komai zaki d'ibe mata kewana"

Pinky tace "eh mana kullum ai ina nan saita gaji dani kin sanni dason gidan amare"

Dariya sukayi banda Fadila da batama saurarensu me kyau, Abdul ne yakira Nabila tana d'agawa tace "Yayana ina kakene? Gani acikin gidanka amma ban ganka ba, nayi kewanka sosai"

Abdul yace "ki sanar musu yanzu zamu shigo"

Kai da waye?..."

Bata karasaba yakashe wayar, kallon screen d'in tayi sannan takalli pinky tace "Wai ki sanar musu Yayana ze shigo yanzu suda abokansu nakega"

Tana fad'an haka taci gaba da shan ice cream nata, Baby ce tarufewa Fadila fuskarta sannan ta juya ta tafi bedroom, itada pinky tabi bayanta dan su ba kawayen amarya bane kannenta ne, yarage daga Fadila sai Nabila dataketa aikin shan icecream bata damu data gyara d'aurin kanta da kuma wandonta daya bayyana ba, harkan gabanta kawai take, sallama akayi a hankali Fadila ta amsa sannan ta maida kanta cikin Mayafin ta sunkuyar, Abdul ne da Kabir sai abokansu guda hud'u, zama sukayi suka gaida Fadila bata amsa ba dan alokacin kukane yaci karfinta, Kabir ya kalli Amryar yace "da farko dai ni abokin Abdul ne kuma amininshi" dim gaban Fadila yafad'i jin muryan kamar na wanda tasani.

Kabir yaci gaba dayi mata nasiha dakuma yi musu addu'an fatan alkhairi, yana gamawa Abdul yamike yace "to muje ko"

Kabir yajashi yace "sai sauran sunyi magana tukun"

Zama yayi badan yaso ba, suka fara da d'ad'd'aya har suka gama, shafewa sukayi da addu'a, sannan Ak yace "gobe akwai walima harna kagu nafara wa'azi"

Tsaki Kabir yaja yace "inde kaine zakayi wa'azin to wallahi a fasa walimar"

Ak yace "Hahaha ni kasan ilimina kuwa? Idan nafara karatu saikace Sudais ne wallahi"

Gaba d'aya suka d'auke kansu dan sun san halin Ak banda neman mata babu abinda ya iya, Nabila kuwa tazuba mishi ido tana kallonshi yaron akwai son wasa, Fadila datake jinta a mugun takure tayi shiru tana kallon kasa, saida aka gama kafin Kabir suka mike zasu tafi yace "ah nayi mantuwa ban tambayi amaryar tamuba ya sunanki?"

Fadila jitayi kirjinta ya buga a hankali tace "Fadila!!!"

Kabir yace "banjiki ba amarya kodai kinajin kunyana ne? Ki warwarefa dan ni babban abokin mijinki ne, Fadila a hankali takara cewa "Fadila"

Dukda be jita me kyauba amma yaji tace "Nabila"

Kallon Nabila yayi a zuciyarshi yace "sunansu ma iri d'aya sede wannan batada kunya"

"Oh nice name Allah yabaku zaman lafiya da abokina haihuwan fari asamin takwara"

Fadila wani kunyane ya lullub'eta dukda kanta akasa yake, Ak yace "nidai asamin kaga sai su samu alaramma"

Kabir yace "alaramman 'yan iska ba"

Dariya sukayi gaba d'aya suka fice a d'akin, Abdul suka gani jingine da mota yana ganinsu yace "to oya kowa yatafi saida safe nima gidan Dady zanje"

Kabir yace "okay matsa to sufara shiga saimu tafi daga baya"

D'an matsawa yayi suka shiga tareda yimusu saida safe, Kabir ne yakalli Abdul yace "wallahi idan ka tafi saina kira Dady nafad'a mishi, sannan wannan yarinyar innocent ce kada kashiga hakkinta dan babu wani asara daya wuce mutum yashiga hakkin wanda yake shiru shiru, nabarka lafiya saida safe"

Abdul rike hannunshi yayi yace "dan Allah kada katafi mu kwanato anan"

Kabir jan hannunshi yayi yace "kaga yanzufa ka girma ka daina yin abu kamar wani d'an goye ko ita Nabilar nasan bazatayi kuka kamar haka ba"

Abdul yace "ina ruwana da Nabila da ita zanyi rayuwane?"

Kabir yace "sorry amma rayuwa da ita yazama maka dole"

Abdul yace "kamar ya rayuwa da Nabila ze zamomin dole?"

Kabir ganin Abdul ya fara maganganun da babu kansu yasa yace "sorry kaje ka kwanta saida safe zanzo tinda za'ayi walima kaji"

Badan yasoba ya sakeshi yatafi, juyawa yayi yakoma site nashi wanda akayi mishi gini kamar a aljanna kyau iya kyau gidanshi yayi, yasan Dady yana sonshi amma yarasa meyasa Dady be barshi ya nemo wacce yakeso ba, dukda dai yabashi damar yakara aure amma hakan beyi mishi dad'i ba dan ko kad'an beyi niyar ze had'a sarauniyarshi da wata, dahaka ya kwanta yanata tunanin irin zaman da zeyi da yarinyar acikin gidan.

Baby se had'a kayanta take tana sauri, Fadila ce tariko hannunta tace "dan Allah ku kwana sai gobe ku tafi kiyi hakuri ki yafemin kada kitafi yau wallahi zuciyata zata buga please sister me"

Baby datake ninke kayan data cire ta d'ago kai ta kalleta tace "Adda wallahi idan na kwana Dady zemin fad'a bakiji yace kowa yadawo yau ba?"

Fadila tace "zan kirashi please"

Ganin Baby bazata yadda ba yasa taciro waya tayi dialing number d'in Dady, sawa tayi a hands free "Hello daughter?"

Fadila tana kuka tace "Dady ka taimaka kabar Baby ta kwana a gidannan gobe saisu koma"

Dady yace "wannan shine damuwarki?"

Fadila tace "Eh"

To shikenan ta kwana sai gobe sudawo ko?"

Cikin murna tace "Tnx you Dady"

Kashe wayar tayi tana tsalle tace "Dady yace ki kwana"

Baby cikin son tsokana tace "momy fa?"

Fadila tace "kinga baki isa kitafi bafa yau"

Pinky da Nabila dashike basuda wani nisa kuma da motar Nabila suka taho yasa suka shirya sukam Pinky ce tayi musu sallama sannan suka wuce"

Yarage daga Baby sai Fadila dakuma Abdul acikin gidan.

Fadila tace "Alhamdulillah yau bazan kwana dagani sai katoba acikin gidan nan"

Baby tace "wayene katon? Yayana kike nufi?"

Fadila tace "Akwai wani kato ne bayan shi?"

Baby dariya tayi tace "oho dai ahaka ake sonshi"

Tsaki kawai Fadila tayi tace "abar maganar nan ke yaushe zakiyi aure?" Baby takalli Fadila tace "sai ranar da kika haihu"

Fadila tace "bafa maganar wasa nakeba da gaske nake"

"Nima ai da gaske nake"

Wannan maganar da sukayi ya haifarwa Baby tunanin Yarima haka kawai idan ta tunashi sai taji gabanta yana fad'uwa, "lafiya kikayi shiru"

Fadila tafad'a, "ba komai"

Fadila tace "nayi missing na number me muhimmanci a rayuwata Baby, inama wanda ya sacemin sim d'ina da wayar kawai ya d'auke yabarmin Sim d'in, amma ba komai meshi yayiwa kanshi"

Baby shiru tayi tunawa da ita tasace Sim d'in, kuma tayi ne sabida dalili guda biyu na farko shine yanzu Fadila tayi aure be kamata taci gaba da waya da Yarima ba, na biyu kuma shine Tana matukar son yarima bazata iya bari number d'inshi ya b'ata mata ba"

Hakadai suka gama har suka kwanta.

Yarima tun a mota yakasa samun nutsuwa haka kawai yaga matar abokin nashi ta birgeshi tanada kunya sosai kuma daga gani zatayi kyau "ا عوذبلله" shine abinda yafad'a Dan gani yake kamar shed'an ne yake shirin yimishi hud'uba, tunawa dayayi da dogayen yatsunta yasa yarufe idonshi ya bugi sitiyarin motar bayason wannan tunanin amma ya zaiyi? Yakasa mantawa, dahaka yakoma gidansu Abdul yayi parkin na motar yafito yanaso yashiga babu wanda yaganshi sabida bayason gaisuwa, ya murd'a handle d'in ze shiga a hankali yaji Dady yace "My Son sai yanzu?"

"Kh shirt" shine abinda yafad'a dan beso Dady yaganshi ba "eh Dady"

Dady yace "yawwa to saikaje ka kwanta kaima ka nemo mata nayi maka aure ko"

Sunkuyar da kanshi yayi yace "Dady ai nasamu"

Dady cikin murna yace "a ina?"

Kabir yace "anan Abuja" yana fad'an haka ya gudu, dariya Dady yayi yace "Allah yasa abinda nake tunani yafaru, dako naji dad'i idan Kabir ya Auri Nabila sabida Mahaifin Nabila aminina ne yanason yarana kamar yacce nake son nashi yaran ga matarshi 'yar uwar matata ce, sannan Nabila taso Abdul amma Allah be kaddara zasuyi aure ba yanzu idan Kabir ya aureta ai shikenan"

Cikin murna yatafi d'aki yana addu'an Allah yasa hakane.

Abinda yafaru shine yaga ranar da Kabir ya tsaya yanata kallon Nabila, shikuma Kabir kallonta yake da wannan kayan zata fita agaban iyayenta kuma zata wuce? Shine abinda yasa yaketa kallonta ranar, ita kuma Nabila tasa kayan ne dan tabaiwa Fadila haushi sabida a lokacin tace musu zataje d'akin Abdul ne, shiyasa Dady yake ganin kamar Kabir yanason Nabila ne.

  

         "Abba kada kasa damuwa a ranka in Allah yaso abinshi sai kaga ya maidaka wani cikin kankanin lokaci nikam na shaideka bazakayi wani abinda babu kyauba duk yacce akayi dawata akasa haka kurun baza'a koreka a aiki ba, ka daina tunanin inada ciki dole sai naci me dad'i aa wallahi nikam ban damuba komai ka kawo zanci kuma nayi godiya wa Allah"

Abba dayayi shiru yana sauraran Amrah yace "Amrah Allah yayi miki albarka hakika da fari nayi zaton kece zaki zama mara hakuri kuma mara hankali ashe kece zaki sharemin hawaye"

Ka daina fad'an haka Abba Adda Fadila addu'a yakamata kayi mata"

Amrah badan ance tsinuwar iyaye yanabin yaro aduk inda yakeba dana dad'e da tsinewa Fadila amma ba komai gata ga duniyar, kuma in Allah ya yadda ko aina ne saina nema miki abinda zakici wanda ze gyara miki jiki harki haihu lafiya"

Mama tana daga gefe tanajin duk abinda suke cewa, uffan bata ceba,

Sallama akayi daga kofa, Abba ne ya amsa tareda tashi yaje, suna gaisawa da meshi yace "Am ka ganeni kuwa?"

Abba yace "aa gaskiya"

Mutumin yace "Sunana Bala ni kanin me gidannan ne to ya rasu sati d'aya dasuka wuce shine muka saida gidan kuma gobe masushi zasu dawo"

Abba yace "kamar yaya? Wannan gidanfa nawane siya nayi idan karyanema in d'ebo maka takaddun kagani"

Mutumin yace "nima ga takaddun dan har koto saida mukaje aka shaida bana boge bane idan kanaso kayi tashiwan kwanciyar hankali to kafin wayewan gari kasan inda dare yama, idan kuma kanason tonan asiri to kajira gobe"

Yana fad'an haka yabar wurin, Abba ya tsaya kem yarasama abinda zeyi,

Amrah da sauri ta koma cikin gida, dama tana lab'ewa ne dan taji ko wani labari ne za'a kawowa Abba akan Fadila amma Saitaji abinda yakusan yaddata kasa, dan ta tsorata sosai hanya ma duhu duhu yake mata, Mama tana ganinta haka tace "lafiyanki?" Amrah batayi mata magana ba tawuce d'aki, sharewa mama tayi dukda ta tsorata, tana shiga d'aki tafara neman number d'in guyson, kira tayi amna switch off, sai juye juye take tarasa yacce zatayi "yanzu ina Abba ze kwashemu ya kaimu? Nashiga uku ni Amrah kada dai Abba yace kauye zamu koma? kai ina wallahi bazaniba saide ya nemi haya anan.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 54*

         ~Washe gari,  Abdul da safiya sosai yakira Yarima,  cikin muryan Bacci yace "Hello"

"Sai yaushe zaka shigo naga har yanzu shiru"

Tsaki yarima yayi yace "dan Allah ka kyaleni na huta yaushema gari ya waye?  idan naga dama mafa bazanzo ba kuma kasan halina"

Shiru kawai Abdul yayi ganin haka yasa Kabir yace "sorry zan shigo anjima kaɗan amma sainaɗan huta dan kaina yana ciwo kaji?"

Da sauri Abdul yace "Tom" katse wayar yayi,  Kabir ne yabi wayar da kallo yasan yanzu Abdul ze farayi mishi kuka shiyasa ya lallaɓashi,  tashi yayi yashiga toilet a ƙasan zuciyarshi yana tuno matar Abdul daya kasa cire tunaninshi akanta tun jiya da dare,  Wanka yayi yashirya cikin shadda ɗinkin omo yasa hula da agogo da takalminshi me kyau yaɗau makullin mota,  saida ya gaida Momy da Dady kafin yawuce parking space yabuɗe motar muryan dady yaji yana cewa "ɗan tsaya Kabiru ga Nabila nan takawo Saƙo tin ɗazu saiku tafi tare dan itama zata walimar" badan yaso ba yace "to Dady" zama yayi a mazaunin driver yasa key,  Nabila ce tafito cikin wani wando wanda ake kirada Crazy trouzer ta yane kanta da wani karamin mayafi,  Eye lashes dogo dogo tasawa idonta wanda har yake neman rufe idon, bakinta tashafa jan baki jaa sai bakin glass datasa wanda ake kira Cat Eyes manyanshi,  takalminta half cover amma high nashi, hannunta rikeda jaka baki tana taunar cingum,  ƙas ƙas take taku harta iso wurin motar ta buɗe a hankali ta zauna ɗago idonta tayi  Wanda yakusa tsorata Kabir dan yazata Jinnu ne, cikin halin ko in kula tace "barka"

Kabir daya saki baki yana kallonta me makon yabata amsa sai yace "Club zaki?"

Nabila taɗan rufe ido kaɗan tabuɗe sannan tace "Nop Walima zani"

Tsaki me tsayi yaja "tsuuuuu,  fitamin a mota"

Kallonshi Nabila tayi kallo na rainin hankali tace "kasan ni wacece?"

"Ban damu da sanin ko ke wacece ba nidai nace kifita kibarmin Mota"

Nabila cikin tsiwa tace "babana shine..." dakatar da ita yayi tahanyar cewa "governor nasani ai fitamin a mota"

Cikin rashin kunya tace "kai waye dazaka koreni abmotarka?  Kai ɗan gidan uban waye?"

Cikin ɓacin rai Kabir yace "niɗan gidan Ubanki ne!!! Zaki fita ko saina fitar dake"

Kafarta tasa a waje sannan tace "wallahi ka ɗibo ruwan dafa kanka saina ɗau fansar abinda kamin kaibaɗan kowaba kaiba komaiba amma zaka wulaƙantani?"

Kabir yace "in kin fasa ɗaukar fansan baki haifu abgidan governor ba"

Fita tayi a motar takira waya daga gida aka turo mata driver,  shikuma Kabir kafin ma tagama fita ya rufe kofar motar yabar gidan,  haka kawai yaji yanaso ya zauna agarin Abuja ko dan y nunawa yarinyar nan "Sarauta yafi Mulki"

Ranshi a mugun ɓace ya iso gidan Abdul saidai tun a bakin kofa yaji hankalinshi yafara kwanciya tunawa dayayi zai gaisa da matar abokinshi, Cikin sauri yace "astaghfurullah" sallama yayi tareda shiga ɗakin Abdul shima Yasa shadda ruwan sararin samaniya yayi kyau sosai saide dariyanne har yanzu babu,  Abdul ne yasakar mishi murmushi shima Kabir ya mayar mishi,  Abdul yace "lafiya naga kamar ranka a ɓace?"

Kabir yace "share kawai"

Matsowa Abdul yayi yace "dan Allah kada kasa damuwa a ranka kamar yacce nima nasa sabida akwai illa kaji?"

Kabir yace "ba wani abu bane wannan yarinyar marar kunyar ce taɗan ɓatamin raina"

Wace kenan?  Cewar Abdul,  Kabir yace "na manta sunanta Wannan dai danaga kuna kwance ranɗin akan gado"

"Oh Nabila?"

Kabir yace "koma de menene mara kunyar dai yanzu angama shirya komai ne?"

Abdul yac "Eh tunda asuba naga sun shirya komai"

Zama sukayi suka fara fira kaɗan kaɗan, 

Fadila data turo baki tana hararan kayan kwalliyan da Baby ta jibga a gabanta tana kwaɓa mata fuska, cikin jin haushi tace "dan Allah ya isa haka"

Baby tace "Aa wallahi be isaba"

Garau sukaji an buɗe ƙofar,  da sauri suka juya ganin Nabila yasa Fadila taɗan ja tsaki kaɗan tareda kawar da kanta,  cikin ɓacin rai Nabila tace "Sister Baby yasunan wannan abokin Yaya Abdul ɗin? Waye ubanshi?"

Baby tace "wanne kenan?"

Nabila da numfashinta yake sauka da sauri sauri tace "wannan me kamada Larabawan"

Baby tace "to ai duk suna kamada larabawa ya sunanshi?"

Nabila tace "me zesa narike sunanshi daga ganinshi ɗan talakawa ne dama ƴaƴan talakawannan wallahi sun fiye girman kai da raini ga talauci ga tsiya amma sai kokarin haɗa kansu da yaran manya, wasuma su nuna sunfi yaran masu kuɗin galihu wawaye kazamai"

Fadila dataji zuciyarta tana shirin zuwa wuya da sauri ta kawar da kanta tana shafa jan baki dan bataso Nabila tasan ranta yaɓaci, Nabila tace "Kiga sunzo suna nuna maka kaiba kowa bane ƴaƴan tsiya wallahi bansan meyasa yaya Abdul ya ɗibo mana talauci ba gashi sunzo suna neman wuce gona da iri dan nasan wannan yaron dangin tsiyane sunga sunada kyau sai raini"

Baby da ranta yagama ɓaci tace "dawa kikaga yanayi miki kama? Da zakizo nan kinayi mana ihu"

Nabila tace "Yana kama da wannan karyar jini ai ya nuna"

Tafaɗa tareda nuna Fadila, Fadila mikewa tayi ta nunata da yatsa tace "duk abinda zaki faɗa ki faɗa amma kada wannan ƙazamin bakin naki yakara kirani da karya idan kuma kika kuma sainayi maganinki and mind you banida ɗan uwa a garinnan hasalima ni banada ƴan uwa tun asali kije ki nemi ƴan uwanshi ki zaga amma banda ni"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login