Showing 9001 words to 12000 words out of 139192 words
Unty Sadiya tagane, Fadila tace "Unty ba komai kawadai halinta ne ya motsa"
Unty Sadiya murmushi kawai tayi don tasan akwai matsala b'oye mata kawai sukayi, riko hannunsu tayi tace "muje Ku gaida Abbansu Aisha saimu shiga daga ciki ko?"
Karasawa sukayi duk suka gaidashi yace "yammatan mama yaushe rabonku da zuwa gidannan? Kodai munyi muku laifi ne?"
Amrah tace "eh laifi kukayi mana shiyasa bama zuwa"
Yace "To Allah ya huci zuciyar Autar Mama"
Dariya dukayi duka suka wuce cikin d'akin Unty, Amrah suna shiga tafad'a akan gado domin har yanzu ranta bai gama warwarewa ba, tana dakewa ne sabida kar Fadila tashiga damuwa, Wayarta ce tayi ringing tana d'agawa taga new number d'auka tayi ta kara a kunnenta "hello"
Shine abinda aka fad'a, itama tace "hello, dawa nake magana?"
"Kabir ne daga GRA"
Amrah tace "ayya sannu"
Yace "baiwar Allah idan bazi damuba inason inje gidanku muyi maganar Fahimta dake"
Amrah tayi mamaki wai yau ace namijine yakirata har yanason zuwa gidansu?
"Baiwar Allah kinyi shiru"
Amrah tace "ba komai kasan gidanne?"
Kabir yace "eh nayi kusan 3weeks ina bibiyarki saida nagano gidanku"
Amrah tace "ok Amma saida yamma domin yanzu ina unguwa"
Yace "ok ba komai" d'it ya kashe wayar,
Amrah murmushi tayi tanajin dad'i domin bata Ganshi bama taji muryarshi tayi mata daga gani yanada nitsuwa, sai a lokacin taji damuwarta tad'an gushe, "Karya kike Inna Falmata dole akwai masu sona". Tafad'a cikin zuciyarta, Fadila ce taga Amrah tana dariya cikin murna tace "meya faru Kanwata naga kina dariya"
Amrah tace "babu komai Adda"
Nan suka shiga hira da Unty Sadiya har su Aisha suka dawo daga makaranta, Amrah ce tayi musu wanka Fadila kuma tayi musu girki, Saida sukaci abinci da juice wanda Unty Sadiya ta had'a da kanta kafin sukayi mata sallama zasu tafi, kud'i taciro a poss nata nabasu dubu da d'ari Biyar biyar nasu, godiya sukayi mata kafin suka tafi, bayan sun koma gida Amrah tasakeyin wani kwalliyan ta fesa turare a jikinta tana cikin sa d'ankunne taji karar wayarta, murmushi tayi kafin ta d'auka tace "ka iso ne?"
'Dayan b'angaren akace "eh"
"Ok ganinan fitowa"
Fadila tana kallonta kuma itama taji dad'in hakan,
Tashi Amrah tayi tace "Adda ina zuwa"
Kashe mata ido d'aya Fadila tayi tace "ayi hira lafiya"
Rufe fuskarta tayi da hannu tana dariya kafin ta fice.
"Wata farar motace kirar Bugatti tagani pake a kofar gidansu, saida ta karewa motar kallo ta karance numbar kafin ta iso, tana zuwa tayi knocking, bud'ewa akayi taji wani kamshin Turare me sanyi ya bugi hancinta, cikin muryarshi me nitsuwa yace "shigo mana gimbiya"
Amrah tace "aa kafito dai"
Murmushi yayi tafito daga motar taganshi wani chocolate colour ne dogo, kyakkyawa, d'auke kanta tayi don batason had'a ido dashi, murmushi yayi yace "ina take?"
Cikin mamaki Amrah ta d'ago kanta tace "wace?"
Shima kallonta yayi yace "Fadila Mana yayarki ai itace nakira"
Amrah wani irin bugawa zuciyarta tayi, kallonshi take batako kifta idonta "yayata?"
Cikin sakin fuska yace "eh"
"Juyawa tayi idonta ya rufe bata ganin komai sai bakin duhu, Kabir yace "jimana Kanwata" juyawa tayi idonta yayi ja, kud'i ya Ciro a aljihunshi yace "ga wannan kisiya chocolate"
Amrah jikinta ne yafara rawa a hankali ta zuba mishi manyan idonta cikin wata irin murya tace "chocolate?"
Dariya yayi yace "eh Kanwata"
Da gudu tashige cikin gida bata karb'i kud'in bama, tana zuwa taga Fadila zaune tana waya da Kamal, kallon Fadila takeyi tanajin wani yanayi a cikin zuciyarta, da kakkausan murya tace "Adda Fadila ke akewa magana baniba".
_jiddah ce_
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 7*
~kallonta Fadila tayi tace "nikuma?"
Cikin fushi Amrah tace "wa kikaji nace?"
Mikewa Fadila tayi tariko Amrah da mamaki tace "me kike fad'ane haka Kanwata?"
Kwace jikinta tayi tawuce d'aki batace komai ba,
Fadila hijabi ta d'auka tafice zuwa waje, tsaye taganshi jingine da motarshi yana ganinta ya saki murmushi, d'aure face tayi tamau takarasa wurinshi, "sannu malam me kayiwa kanwata tashigo gida ranta a b'ace?"
Kabir cikin sakin fuska yace "Babu abinda nayi mata kud'i kawai nabata tasiyi chocolate daganan takiramin ke"
Harara ta banka mishi tace "bani kud'in chocolate d'in"
Kud'in yaciro a aljihunshi ya mika mata, rarraba kud'in tayi ta watsa mishi a fuska tace "shine hukuncinka sabida ka b'atawa Kanwata rai kuma ina gargad'anka da karka sake zuwa gidannan idan ka kara zanyi maka abinda yafi wannan"
Tana fad'an haka ta juya a fusace, yana kiran sunanta ko kallonahi batayi ba, shima cikin b'acin rai yashige motarshi ya busa kura yabar kofar gidan, yarane suka fara warwaso akan kud'in.
"Amrah kiyi hakuri na koreshi bazai kara dawowa ba"
Amrah da fuskarta yayi ja ta d'ago kanta tace "kin koreshi kuma Adda?"
Fadila zama tayi a gefen katifar tariko hannun Amrah tace "kiyi hakuri hakan bazai kara faruwa ba..."
Wayantane yayi kara tana d'agawa taga numbar Kamal, murmushi tayi ta d'auka tace "hello"
"Ina kikaje?" Shine tambayar da Kamal yayi mata, cikin mamaki tace "ban gane ba"
Shima tsawa ya daka mata yace "ba wurin wani d'an iska kika fitaba yanzu? Ko kin zata babu Wanda zai fad'amin ne, to an kirani an fad'amin yanzu kin fara biye biyen maza, to inaso in fad'a miki idan har wannan rayuwar kike son d'aukawa kanki kiyi gaggawan saukewa" d'it ya kashe wayar.
bin wayar tayi da kallon mamaki "me yake nufi?"
Amrah tana jinta batace komai ba saima tashi datayi tafice a d'akin zuwa kitchen domin tafara jin yunwa,
Fadila kiran Kamal tayi kusan 4 miss call bai d'auka ba, tashiga damuwa iya damuwa domin yabarta da tunani.
"Kamal zauje yake akan kujerar office nashi, ranshi ya b'aci sosai, shi a rayuwarshi babu abinda ya tsana kamar mace me biye biyen maza, gashi Fadila tana nema tafara hakan, ba sau d'ayaba ana kiranshi ace ta had'u da wani a wuri kaza, idan ya bincika kuma saiyaga da gaske taje wurin, ya yadda da Fadila hundred percent, to Ammafa d'an Adam Tara yake bai cika goma ba, kuma yasan 'yar uwarta bazatayi mata sharri ba"
Dafe kanshi yayi da hannunshi biyu, wani tunani yayi kafin ya mike yad'au makullin motarshi, hanhar gidansu Fadila yanufa, yana isowa yakira wayarta data d'auka yace "kifito zamuyi magana"
Fadila fita tayi da sauri, tana zuwa ta bud'e motarshi tashige lokacin ya kwantar da kanshi jikin sterin motar, d'an bugashi tayi tace "gani na iso"
Yana jinta ya lumshe idonshi duk matsifar daya kwaso saida yaji jikinshi ya mutu yarasa ta inama zai fara, hakan yasa motar yayi shiru bakajin komai, Fadila ganin bashida niyan magana yasa tace "yayana meyake damunka ne?"
Sai a lokacin yasamu damar d'ago kanshi, zuba mata kasalallun idonshi yayi, kasa jure kallonshi tayi ta dukar da kanta kasa, saida ya gaji Dan kanshi yace "why? Meyasa kikeyin haka? Ni a yanda nasanki kinada nitsuwa bakya kula maza, sai kuma gashi har samarai yara kanana kike kulawa, yau kin baiwa samarai biyu numbern ki, gashi kuma kin gayyaci wani yazo wurinki why?"
Fadila sunkuyar da kanta tayi tace "kayi hakuri bazan kara ba"
Lumshe ido yayi yace "ba komai amma Dan Allah karki kara, kishinki baya barina kinsan inada kishi sosai"
Cikin sanyin murya tace "nasani am sorry"
"Yawuce yanzu kibani labari Wanda zai sani nishad'i har in manta da abinda kikamin"
Kallonshi tayi tace "to Amma sai kayimin dariya, kuma saika fad'amin waye yakiraka yace maka ina kule kulen samarai"
Dariya yayi yace "gashi nayi dariyan amma bazan fad'a miki Wanda yafad'amin ba gaskiya kibani labari kawai"
Shiru tayi na wasu lokuta kafin tafara bashi labarin sai dariya yake harda rike ciki domin labarin yasashi farin ciki, cikin muryanta na shagwab'a tace "to yanzu zan Shiga gida domin dare yayi"
Kallonta yayi yace "ok amma saikin fad'amin kalamai masu dad'i Wanda zanyi bacci dasu a raina"
Cikin idonshi takalla tace "I love you Kamal, bazan iya rayuwa babu kaiba, nayi maka alkawarin zan soka koda bayan rainane ina fatan mu kasance mata da miji a duniya da kuma lahira, dafatan yau baccinka zai kasance rabinshi mafarkinane"
"Sai a lokacin Kamal ya bud'e idonshi wanda ya lumshesu yanajin dad'ad'an kalamanta Wanda take yinsu da sanyin murya"
"I love you too my deela"
Bud'e motar tayi tafice da gudu,jitayi an riko hijabinta ta baya, da karfi tace "Kamal ka sakarmin hijabi kada Abba yazo wucewa ya ganmu"
Kamal shiru yayi yana kallonta, Juyawa tayi da niyar matsifa taga Ashe Marfin motane ta rufe hijabin dashi, janyewa tayi cikin jin kunya ta ruga da gudu.
Dariya kawai yayi yaja motarshi yabar unguwar,
Fadila tana Shiga gida tafad'a kan katifa da gudu tana haki, Amrah juyawa tayi tana kallonta cikin b'acin rai tace "lafiya kuwa?"
Fadila tace "Kamal ne yazo wallahi maganar Dana fad'a mishi har kunya take bani kamar banice na fad'a ba"
Da sauri Amrah tace "fad'a kukayi?"
Fadila tace "Aa soyayya mukayi"
"Oh yayi kyau Allah yakara dankon kauna"
Tana fad'an haka ta fice zuwa d'akin Mama, Fadila kuma sai rufe fuska take tana dariya,
Amrah tana zuwa tafad'a kan gadon Mama rufe fuskarta tayi zuciyata cike da bakin ciki, Mamace tashigo da kwano a hannunta ganin Amrah kwance yasata d'an tab'a wuyarta kad'an taji zafi, tace "Amrah bakida lafiya ne naganki haka?"
Amrah shiru tayi batace komai ba, Mama hankalinta yatashi sosai ganin Amrah haka kwanon hannunta ta mikawa Amrah tace "tashi kici d'an wake to"
Amrah cikin murya kamar me bacci tace "Mama nifa bazan iyacin wannan dankwala dankwalan abin ba"
Mama jin maganarta yasa tace "shikenan yi kwanciyarki"
Shiru tayi bata kara magana ba sai tunanin datakeyi Wanda ya Dami zuciyarta.
"Kodai maganar Inna Falmata zata kasance gaskiya ne?" Tafad'a cikin zuciyarta, wani tunani tayi tamike tafice, hijabi ta d'auka tafice agidan cikin sand'a, sauri sauri gudu gudu takeyi harta iso gidan Inna Falmata, tana zuwa ta juya bayanta taga ba kowa.
_Jiddah Ce_
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 8*
~tana shiga gidan tawuce d'akin Inna Falmata, zama tayi cikin a kasa tana haki, Inna Falmata ce ta d'ago kanta cikin firgici tace "Amrah bakida hankali ne zaki fito cikin dare, Ina Mamanku?"
Amrah tace "Dan Allah Inna kiyi shiru in nitsu tukun"
Ruwa Inna ta d'ibo mata a cup tace "gashi kisha maza kifad'amin meya faru"
Sha tayi tace "Inna tambayarki nazo nayi, kuma banaso kifad'awa kowa wannan maganar tsakanina dake ne"
Inna cikin mamaki tace "ina jinki"
Amrah tace "Inna maganarki tana nema tazama gaskiya domin kuwa Nagani da idona yau, ina tsoron kar maganarki ta karshe ta kasance gaskiya, Cewar zanyi shekara talatin babu Aure kuma babu manemi, shin hakan yatab'a faruwane kika gani da idonki?"
Inna kallon Amrah tayi tace "koda na fad'a miki bazaki yadda ba, domin nagani da idona akan Kanwata wacce muka taso tare kamar ke da Fadila, saidai mu munada bambanci, Muna yawan fad'a sab'anin Ku da kuke shiri, Kanwata shiru ce batada yawan magana, tafini kyau tafini tsarin komai saidai wani abin mamaki idan samarai sunzo to wurina suke zuwa Ashe abin yana bata haushi sosai"....Kuka tafashe dashi tace "Amrah banason in tuna wannan abin, maganar danake miki yanzu tana gida shekara talatin da Biyar, da kyar akayi bikina da mijina, yanzu ko wucewa nake a hanya bama magana da ita, ko gida naje batayimin magana, shiyasa nacewa Maman Ku tad'au mataki tun kafin abin yafi karfinta"
Amrah tayi shiru tana tunani daga bisani tace "Inna inason ki taimaka min nikam ki kaini wurin malamin da kikace"
Inna tace "Aa Amrah idan har mamanki bata yadda ba bazan kaiki ba, sabida idan an kamamu muna zuwa zata iya kai kara kuma dole ad'au mataki akaina sabida ke yarinya ce, shawara d'aya zan baki yanzu shine ki maida hankalinki akan karatu idan Allah yace zakiyi Auren sai Kiga anyi tashi narakaki gida"
Amrah tashi tayi tace "karki damu Inna zan tafi da kaina banaso a gane nafito, kuma Dan Allah karki fad'awa kowa"
Inna tace "bazan fad'a ba"
Amrah fita tayi ta wuce gida, tana zuwa ta tarar da Mama da Fadila zaune hankalinsu a tashe, Fadila tana ganinta ta mike ta rungumeta "ina kikaje Kanwata?"
Amrah janye jikinta tayi tace "Dan Allah idan bazaki damuba Adda kibarni inason in d'an huta banason surutu a halin yanzu"
Mama tace "ba tambayarki akayi ba?"
Amrah wucewa d'aki tayi batace komai ba, tana zuwa taciro wayarta takira Zee "Dan Allah Zee gobe ki zauna a gida inada Matsala"
Fadila ce ta wupce wayar a hannunta "ban fad'a miki kidaina kawance da Zee ba? Ko kin daina jin maganata ne Kanwata?"
Amrah tamike cikin rawar murya tace "bani wayana Adda Fadila"
Fadila tace "bazan bada ba Amrah indai Zee zaki kira kinsan inasonki bazan yadda kifad'a halaka ba"
"Ok Dan Yaya Kamal ne yasiyo wayar shine zaki nunamin isa?"
Fadila kallonta tayi tace "ta Yaya zan nuna miki isa sabida Kamal ya baki waya? Kina ganin koda gida da mota Kamal yabaki zanji haushine Amrah? Bakisan yanda na d'aukeki bane a zuciyata, idan naganki cikin damuwa nafiki shiga damuwa, Amma tunda haka kikace ba komai ba wayarki Amma please kada ki kira Zee yarinyar batada kunya"
Jikin Amrah yamutu sosai dajin kalaman Yayarta karb'ar wayar tayi ta kasheshi ma gaba d'aya ta wulla saman Gado, Alwala tayi tazo tayi sallan Isha, sannan ta kwanta tunani ya taru yayiwa zuciyarta yawa tarasa menene mafita da haka har bacci b'arawo ya saceta, Fadila ma saida tayi waya da Kamal kafin ta kwanta.
_washe gari_
Amrah ta tashi ranta watsai domin ta manta komai da haka sukaci gaba da harkokinsu kamar kullum ta mikawa ubangiji komai, Fadila taji dad'in ganinta haka,
Kamar yanda aka yanka Auren Fadila da Kamal sati uku masu zuwa sai gashi yau saura sati d'aya me zuwa, Shirye shirye sukeyi ba wasa musamman Ta gidansu ango Wanda suke shiri sosai wa bikin, Amrah ma ba'a barta a baya ba, Fadila Unty Sadiya gyara mata jiki take ba wasa jikinta yayi kyau yayi haske, bata yawan fita domin gudun kada rana ya b'ata mata gyara, Sai dare Kamal yake zuwa susha hiransu kamar kada su rabu, Yau ya kasance ranar asabar Amrah ce tadawo daga karb'ar d'inkinta ta gaji sosai, tana zuwa ta kwanta a varanda tana nishi.
"Sannu kanwata nasan kina gajiya sosai da bikinnan"
Amrah d'ago kanta tayi cikin gajiya tace "gaskiya Adda Fadila na gaji yanzu idan na huta kuma zanje karb'ar takalmin Dinner"
Fadila tace "Dinner ma saida kika siya mishi takalmi?"
"Dole ai kinsan Kanwar Amarya itama Amarya ce"
Fadila tace "eh hakane fa kuma nikam naso ranar kifi Amarya ma kyau wallahi kema yanzu kinayin dilki idan Unty Sadiya tazo"
Amrah tab'e Baki tayi "gyaran me zanyi nida ko saurayi banadashi"
Kallonta kawai Fadila tayi tanajin tausayinta a ranta tanajin da ace Kamal bai samu gurbi a cikin zuciyarta ba to wallahi babu abinda zai hanata ta barwa Amrah shi, "to Amma Kamal yana raina idan nabar miki Kamal banyiwa kaina adalci ba ki yafemin Kanwata anzo wurin da bazan iya taimaka miki ba" juyawa tayi ta share hawayen idonta don bataso Amrah tagani, itama Amrah shiru tayi taci gaba da hutawarta.
Kamal
Zaune yake akan kujerar d'akin Ummanshi, "Umma Dan Allah kidaina nunamin kayannan tun d'azu Abu yaki karewa? Ni wallahi yau nagaji sosai, Ummana ai kayan sunyi kyau kuma nasan sun dace da my Deela"
"Kamal d'ana kasan yanda nake ji da kai bazai bazan tab'a yiwa matarka kayan da za'a rainata ba, yarinyar tashiga zuciyata sosai tanada hankali ko ido batason had'awa da mutum, ba kamar wancan kanwar tata me idanu kamar Aljana ba, nifa kanwar tata tsoro take bani tsabar bushewar idonta batada kunya kona miskala zarratin, gara da Allah yasa ba itace surikata ba"
Kamal dariya yayi har saida dimple nashi ya bayyana tareda fararen kyawawan hakoransa yace "Umma haka yanayinta yake, idan ka ganta zakace tanada raini saika zauna da ita zakasan halinta, farkon had'uwana da Farida data zabgamin harara saida nad'an tsorata"
Umma tace "Allah dai ya kyauta, kasan me?"
Girgiza kanshi yayi,
Umma tace "Senator yacemin zaizo d'aurin Aurenku za'a Tara manyan garin Adamawa sai anyi biki nagani nafad'a, duk wasu manyan kawayena zasu gayyato wad'anda suka sani ciki harda Wanda zan Aura shima zaije dinner"
Kamal cikin murna da farin cikin jin Ummanshi zatayi Aure yace "Umma dagaske kike zakiyi Aure?"
Umma tace "ai bazanyi maka karya ba my son, babu dad'i ace inada suruka me kamun kai kuma banida Aure ba, nasan itama Fadila bazataji dad'i ba"
Kamal sauka yayi zuwa kasa yayi sujjada tareda godewa Allah daya bashi Fadila a matsayin wacce zai Aura, gashi sanadiyyanta Ummanshi zatayi Aure, mikewa yayi ya rungume Umma yana jin dad'i, Umma tace "zaku zauna a gidannan ai ko? Dan banaso Fadila tayi nisa dani"
Kamal yace "duk yanda kikace my Mommah shi za'ayi"
Umma tace nasa a gyara maka side naka nakan Up kaga zakufi sakewa a can"
Sunnar da kanshi yayi kasa alamar kunya, d'an bugashi tayi tace "kuji wai yaji kunya"
Had'e face yayi yace "kunya ai ado ce ammafa ga mata"
Dariya suka kwashe dashi.
"Ranaku sai ja suke b'angren Fadila da Kamal sai shirye shirye suke Amrah tazama busy itace rabawa kawayenta anko itace rabawa kawayen Fadila ma sabida Fadila bazata samu damar zuwa ba don tana dilki,
Kamal ma tareda Ummanshi suke shiryawa, Umma ta Dage saita had'ar da Kamal d'inta domin batason abin kunya ta gayyato manya manyan baki batason abinda zaisa taji kunya ko kad'anne,
An kawo kayan lefe Nagani na fad'a Mama saida tayi kuka sabida gani take kamar bawa 'yarta aka kawo wannan kayan ba, Amrah ma tayi farin cikin kayan da aka kawo wa yayarta, Sai aikin shigar da kaya d'aki takeyi dukda akwatin sunfi karfinta da kyar take d'agawa amma ta dage saida ta shigar d'aki.
Da dare Fadila ce ta rungumeta suna kuka domin batason rabuwa da ita,