Showing 96001 words to 99000 words out of 139192 words
tsaki takumayi, kafin ta buɗe kofarta tana lekawa ko Abdul yana falo, ganin bayanan yasa cikin sanɗa tayi hanyar kitchen, frij ta buɗe taciro biyar araye (five alive) takara takawa cikin sanɗa zatabar kitchen ɗin, "ke" a rikice tajuya tana neman inda sautin yafito, a bayanta ya tsaya yana kallon yanda take waro manyan idonta tana neme neme, "sata kikeyi ne?"
Jin muryanshi a bayanta yasa takasa juyowa sai girgiza kai datakeyi, murmushi yayi tareda matsowa dab bayanta har jikinsu yana gogan juna, hannu yasa a hankali ya tara gashin data baza har goshinta ya mayar bayanta tareda sa fuakarshi a wuyanta yana kallon fuskarta, hannu yasa ya rike cikinta infact ya rungumeta ta baya sosai, numfashinta ne yafara yin sama sama jin abinda yayi, a kunne ya raɗa mata "you know what?"
Girgiza kai tayi yace "yanayinki yana birgeni musamman idan kika tsorata, kinayin abu kamar yarinya ƴar 2years" sakinta yayi ya juyo da ita tana kallonshi, murmushi yayi mata itama tayi mishi, hannu yamika mata yace "zamu iya zama abokai"
Kallon cikin idonshi tayi a hankali ta mayar da kanta kasa sannan tasa hannunta cikin nashi sukayi musbiha tace "Eh"
Murmushi yayi mata me sanyi yace "thanks"
Fadila kallonshi tayi dan ita mamaki yake bata sam bashida hali guda ɗaya watarana fishi watarana dariya watarana duka biyu, yace "tom my frnd yanzu babu wani wasan ɓuya tsakaninmu sabida abota baya bukatan haka ko?"
Cikin dariya tace "eh" sakinta yayi yace jekisha juice ɗinki, dariya takarayi mishi tace "bye"
Tsayawa yayi yana kallonta haka kawai take birgeshi.
"Kwana uku da faruwan haka Amrah bata kara magana dasu Abba ba, saide idan suna bacci ta lallaɓa tashiga idan ta gansu saita koma ɗaki, kwance take akan gado da safiya takasa tashi tun ɗazu jikinta a mugun mace ga gabanta dayaketa aikin faɗuwa, Mama ce tayi ihu daga ɗakinsu tana kiran Kulu, Kulu datake aikin kosanta dan gab take da fita taji muryan Mama tana kiranta, da gudu tayi sallama tafaɗa ɗakin ganin Mama ta rike Abba tana kuka yasa tace "lafiya?"
Mama tace "baya numfashi ku taimaka min"
Kulu dan tsabar ruɗewa tama kasa yin komai sai gaba take tana baya magana ma takasa, Amrah ce tashigo da gudu tana cewa "meya faru?"
Ganin Abba a kwance baya numfashi yasa ta tsala uban kara tayi kanshi tana girgiza shi, Hannunshi ta ɗaga ta saki sai gani tayi ya faɗi alamar babu rai a jikinshi, lululu idonta yafara a hanakali tafara sulalewa har tayi kasa sumamma, kuka Mama tafara Kulu ce taɗan daure tashiga makota takirasu, Shigowa sukayi kowa yana salati, maza sukace a basu wuri suyi wankan gawa, farawa sukayi nan danan mutane suka cika gidan makil, Saida aka gama wanka aka suturtashi sannan akace suzo suyi sallama dashi, ruwa Kulu ta watsawa Amrah a fuska kafin ta farfaɗo, mata sukace kije kuyi sallama da mahaifinki, kin zuwa tayi saida aka riketa aka kaita wurin gawan, zama tayi dirshan akasa tana kuka, buɗe mata fuskar akayi a take ta rufe idonta dan batason gani, ana gamawa aka ɗaukeshi za'a tafi, nanfa Mama da Amrah suka rike makaran suna ihu, wani mutum ne ya daka musu tsawa tareda cewa "bakusan Allah ya tsinewa mata masu kururuwa akan gawa ba? Munsan zafin rabuwa babu daɗi to amma ai Allah yasan dalilin rabaku kuma baya barin wani dan wani yaji daɗi, kuyi mishi addu'a dan a wannan lokacin yana bukatar hakan, duk mamaci idan za'a fita dashi a gidanshi yanajin zafi koda ko ɗan aljanna ne, kuyi addu'a"
Yana faɗan haka suka wuce dashi makwancinshi, saide muce Ubangiji yaji kan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya, mukuma idan namu yazo Allah yasa mucika da Imani,
dahaka Amrah sukayi kwana uku makota suna shigowa wasuma har kwana suke, ranar na huɗu kowa ya watse gidan yarage daga Mama sai Amrah da Baba Kulu, har yau babu maganar data kara shiga tsakanin Mama da Amrah.
Yau da safe Amrah ce tasa dogon hijabi ta nufi ɗakin mama, tayi sallama kusan sau uku ba'a Amsa ba, ganin haka yasa tashiga kawai, Unty Sadiya datake tara kayanta awata karamar jaka ta gaisar, ko kallonta Unty batayi ba tace "lafiya" daganan tagama shirinta tayiwa Mama sallama tareda yi mata nasiha kafin ta tafi, Mama tashi tayi zatabar ɗakin Amrah tace "Mama inason yin magana dake"
Mama cigaba tayi da tafiya batace komai ba, Amrah takara cewa "Mama magana fa nake, nace inason yin magana dake"
Mama tace "dan Allah kitashi kibarmin ɗaki"
Amrah tashi tayi tace "zan bari amma saikin amsamin tambayar dazanyi miki"
Kallonta mama tayi da mamaki tace "banida lokacin amsa miki tambaya"
Amrah tace "yazama dole ki amsamin tambaya"
Juyawa Mama tayi zata fita Amrah ta rufe kofar ta jingina da jikin kofar tana kallon mama, Mama tsabar Mamaki takasa cewa komai, ita tama fara tunanin mutuwar Abba ya juyawa Amrah hankali, tace "miye tambayar da zakiyimin?"
Amrah tace "Mama shin kinada sa hannu a ɓatar Yaya Khalil?"
Tambayar tayiwa Mama bambarakwai, ɗago kanta tayi tace "kina zargina ne?"
Amrah tace "Eh"
Mama da Amrah tafara bata tsoro tace "to bazan faɗa ba tunda naga kinyi kauri yanzu saiki sani faɗan dole kinji uwata?"
Amrah tace "yazama dole ki amsamin wannan tambayar Mama"
Mama tace "nace bazan Amsa ba"
"Mama dolene fa ki amsa dahaka zan cika alkawarin danayiwa Abba"
Mama tace "indai dahakane to kin daɗe baki cika alkawari ba".
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 63*
~"Mama dolene nacika wannan alkawarin kuma nayiwa kaina saina cikashi"
Mama bangajeta tayi ta fice a ɗakin, kwafa Amrah tayi tace "Mama wannan amsar yazama dole kibani"
Kullum sai Amrah tazo tayi mata wannan tambayar, da ran mama ya ɓaci tace "Idan kika karayimin maganar nan wallahi saina ci miki mutuncin da bazaki kuma shigomin ɗaki ba" hanyar waje ta nuna mata cikin zafi tace "fita!!!"
Amrah baki ta buɗe zatayi magana Mama takuma cewa "Fita!!"
Sumsum takama hanya tayi waje Dan bataso tsana yakara shiga zuciyar Mama, ammafa ta kudiri aniyar gobe sai Mama tafaɗa mata kota halin yaya ne,
Ɗakin Kulu tashiga tace "Baba Kulu akwai taimakon danakeso kiyimin"
Kulu tace "ina jinki"
Amrah tace "nasan kinsan komai namu kinsan sirrin mu, inaso ki taimakamin yanda zan gano gaskiya, gobe da dare inaso kije ɗakin Mama kuyi fira sosai har kisa ta manta kulle kofarta, sannan idan kin koma ɗaki takira wayarki ta tambiyeki ina nake kice ganinan a kwance a gefenki koda ko bana ɗakin kinji?"
Kulu tace "miye fa'idar yin hakan?"
Amrah tace "basai kin sani ba ni kawai shine taimakon da zakiyimin"
Kulu tace "to amma idan cutarwa zakiyi fa?"
Amrah tace "kin taɓa ganin inda ƴa ta cutar da uwarta?"
Shiru Kulu tayi kafin tace "Tom shikenan zan taimaka miki"
Asuba tagari.
"Fadila ce zaune abakin gado tanashan tea dukda yana kona bakinta hakan be hanata daurewa tasha ba, sauri take dan yanzu aka kirata ana nemanta cikin gaggawa, saida ta shanye ta mike jikinta sanye da uniform riga da wando fari, sai hijabi guntu da fask mask datasa da glass fari a fuskarta, tayi kyau sosai, jakan baya tasa ta ɗauko wayarta da makullin mota, cikin sauri tafita, har gudu gudu take danta iso da wuri, karo sukaci da Abdul wanda yake sanye da jallabiya da alama a bacci ya tashi, kallonta yayi yakara murza ido ya ganta da kyau kafin ya sakar mata murmushi, kasa tayi da face mask ɗin tace "good morning frnd"
Matsowa yayi kusa da ita yamika mata hannunshi, gaisawa sukayi yace "morning, saurin me kike?"
Ɗan yamutsa face tayi tace "wallahi yanzu aka kirani wai ana nemana da gaggawa"
Ɗan dariya yayi yalakaci kumatunta inda yaɗan lotsa sannan yace "shine zakibar frnd naki agida shi kaɗai?"
Fadila datake sauri tace "sorry zan dawo da wuri bye"
Riko hannunta yayi yana kallonta, tace "me?"
Beyi magana ba ya matso da bakinshi kan kumatunta yayi mata kiss tareda cewa "bye"
Dariya kaɗan tayi tace "thanks you bye"
Da gudu tafita kamar wata ƴar yarinya, kallonta yayi yana murmushi, a ranshi yace "badai yarinta ba"
Daganan yaje yasha tea ɗin shima ya shirya yatafi office.
"Yau da dare Amrah ta tura Kulu ɗakin Mama tayi kamar yacce tafaɗa mata, saida suka gama hira kafin Kulu tafito tareda kashe wutan ɗakin, Mama kuwa akaci sa'a bata tunada kulle kofa ba,
Amrah data shirya cikin wani Farin kaya tashafa farar hoda a fuskarta yanda bawanda ze ganeta, tashafa bakin kwalli a hakoranta, daidai idonta tashafa kwallin tayi zagaye dashi idan ka ganta zaka rantse fatalwace, gashi rigan yayi mata tsayi sosai, wani farin yadi ta yaga ta ɗaura kanta dashi, sannan ta ɗaure daidai cikinta da kafarta dashi kamar de yacce ake ɗaure gawa, wuka ta ɗauko tafito a hankali, Kulu data shiga toilet tayi fitsari yanzu tafito danta sanar da Amrah yanda sukayi da Mama, cin karo tayi da mumunar fatalwa acikin ɗaki, jikintane yafara rawa tace "ku gafarceni wallahi bansan komai ba, innahu sulaimanu wa innahu bismillahi..." warwas tafaɗi akasa sumamma, Amrah ganin zata ɓata mata lokaci yasa ta tsallakata ta wuce, a hankali ta buɗe ɗakin Mama tareda rufe kofar gau, Mama taɗan firgita tace "waye?"
"Hindu ce"
Juyi ɗaya Mama tayi tafaɗo akan gado jin muryan kamar na larabawa, a tsorace ta ɗago tana neman ta kunna wuta, da kyar tasamu ta kunna, neman inda maganar yafito take, "gani tanan"
Tana juyawa ta hango fatalwa yanayi mata dariya, ihu tayi takara kashe wutan, "me kikeso dan Allah meya kawoki?"
"hahahahahaha kinji tsoro ne?"
Mama tace "Eh..eh..eh..."
"Shiru!!!! Nazo ki faɗamin gaskiya shin kinada sa hannu a ɓatar ɗana?"
Mama tace "wallahi wallahi...."
Wuƙa Amrah taciro tayi kanta da gudu ta shaƙe wuyanta sannan tasa wukar a wuyanta tace "idan baki faɗamin ba zaki bini inda kukayi sanadiyyar zuwana"
Mama tace "eh inada..inada masaniya amma banice na ɓatar dashi ba, Maman Mijinmu ce ta ɓatar dashi amma tafaɗamin kuma ranar data faɗamin nayi farin ciki sosai, dan nasan ze mance da Khalil yafara son yarana, kinsan uwa tanaso aso ƴaƴanta sosai"
"Kamar yacce nima nakeso yaso ɗana sosai, awace duniyar kuka kaishi?"
Mama tace "ban sani ba ranar da Mama zata mutu taso ta faɗamin amma zafin ciwo ya hanata faɗa har Allah ya ɗauki rayuwarta"
Amrah jikinta yayi sanyi amma dukda haka bata karaya ba takara matso da wukan dab wuyar Mama tace "Meyasa kikaki faɗawa ƴarki gaskiya?"
Shiru taji babu amsa, dubawa takarayi taga Mama ta suma, fita tayi da sauri tagudu ɗaki tareda cire kayan ta ɓoye awata leda ta jefe acikin wardrobe sannan tashiga toilet ta wanke jikinta, tazo tasa kayan bacci, ruwa ta ɗibo a roba ta watsawa Kulu a fuska, Kulu tayi ajiyar zuciya tana salati tace "fatalwa"
Amrah tace "dalla tashi aina kikaga fatalwa?"
Kulu daka tsalle tayi ta rungume Amrah tana nuna mata bakin kofar bedroom tace "acan..acan wallahi"
Amrah tace "kiyi addu'a kije ki kwanta" ranar kulu a wurin ta kwana, ita kuma Amrah yanda taga rana haka taga dare,
Washe gari Kulu ce tafara shiga ɗakin Mama tana ganinta a sume tayi sauri tasa mata ruwa, buɗe ido Mama tayi tace "gaskiya nafaɗa"
Kulu tace "lafiya Mama?"
Mama kalle kalle tayi tace "eh" mikewa tayi tana cikin tsoro tayi alwala tazo tayi salla, tana cikin addu'a kulu tace "lafiya Mama?"
Mama tace "eh"
A ranar wuni Mama tayi kamar me zazzaɓi a daren jiya tayi mugun tsorata, da yamma ta tashi taje kitchen, indomie take kokarin dafawa tagama haɗa komai ta ɗauko Albasa zata yanka amma bataga wuƙa ba, neman wukan tayi sosai babu, shiru tayi tana tunanin to ina wuka zeje? Kulu takira tace "ina wuka?"
Kulu tace "kinsan anyi taron mutuwa dolene wani abin ya ɓata"
Mama tace "jiya da rana nayi anfani da wuka yanzu kuma ace babu? Ki tambiyi wannan yarinyar"
Kulu tace "to"
Ɗaki taje tace "Amrah inji Mama wai ina wuka?"
Amrah kiɗimewa tayi tace "wuka kuma? Bansan inda yakeba"
Kulu tace "tom"
Fita kulu tayi taje tacewa Mama wai batasan inda yakeba, Mama tace tom tareda tsayawa tana tunani sosai, Fita tayi tafara neman wukan acikin gida, a wurin wanke wanke tagani, ɗagawa tayi takara kallo sannan tace "yawwa ga wukan"
Kulu tace "ok"
Amrah hamdala tayi tana sauke ajiyar zuciya, datacewa Kulu batasan inda yake ba, kulu tana fita ta buɗe wardrobe da sauri taciro wukan tafita da gudu tabayan kofa tabi ta ajiye wukar a wurin wanke wanke, da gudu takara dawowa ɗaki ba wanda yasani.
"Fadila tiyata sukayiwa wata mata saida komai ya daidaita kafin tafara tara kayanta zatayi gida cikin gajiya, murmushi take dan zataje suyi fira da frnd nata, Baby tace "Adda Fadila naga kinata sauri kinata murmushi miye sirrin ne?"
Fadila tsaki tayi tace "Sirrin bana masu gulma bane ƴan sa eyes"
Dariya Baby tayi tace "nagano wato Yaya Abdul ne sirrin" Fadila dun dum ta sakar mata a baya, mutane sunata kallonsu acikin asibitin saida suka gama yarintarsu kafin kowa yayi hanyar gida, wani chocolate Fadila tasiya ɗaya wa ita ɗaya kuwa wa frnd ɗinta, murmushi tayi ta nufi gida, me gadine ya gaidata taciro ɗari biyar tabashi, yayi mata godiya sosai tareda fatan alkhairi, parking ɗin motarta tayi sannan tashiga ciki, takalmin mace ta hango daga bakin kofa saida kirjinta ya buga, dakewa tayi tayi sallama saida aka amsa kafin tashiga, Nabila ta hango zaune akan cinyar Abdul, sai shagwaɓa takeyi mishi shikuma yanata tsokanarta yana dariya, idan ranta yayi dubu tofa duk sun ɓaci yanzu, Kallonsu tayi batace komai ba tawuce ɗakinta, Abdul ne ya sauke Nabila daa jikinshi yace "excuse me"
Ɗakin Fadila ya nufa yaga ta zauna ta ɓare chocolate guda biyu tanasha, ɗan dariya yayi yace "frnd ba bismilla ne?"
Wani tukukin bakin cikine yakara turniketa, batace komai ba ta turo baki gaba taci gaba dacin chocolate ɗin, zama yayi dab ita yaɗansa hannunshi a gefenta yarike, yace "nima inaso"
Fadila tace "to sakeni"
Make kafaɗa yayi yace "oh oh kibani ahaka"
Tsaki taja aranta tace "Sai kaje Nabila tabaka"
Kanshi ya kwantar a kafaɗarta yace "bani to"
A hannu tasa mishi yaki karɓa, tace "gashi"
Kallon cikin idonta yayi sannan ya buɗe bakinshi alamar tasa mishi, wani katon ta gutsira dan mugunta ta cusa mishi, rikewa yayi yana kallonta, ba zato taji ya riko fuskarta yahaɗa bakinshi da nata, sa mata yayi a dole ta gutsira itama saida suka cinye kafin ya saketa yace "thanks you frnd"
Ko kallonshi batayi ba, tamike tafice, dariya yaɗanyi kafin yabar ɗakin.
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 64*
~kwana biyu da faruwan haka Amrah ce zaune akan tabarma ta buga tagumi tana tunani ga cikin jikinta dayake matukar bata wahala, Kulu ce tayi sallama da robar kosanta sau biyu tana kiran Amrah amma tayi nisa a tunanin batama jinta, bugata tayi a firgice ta kalli kulu, Kulu tace "Kinsan tunani zai iya haifar miki matsala a wannan lokacin? Kinada ciki ya kamata ki rinka yiwa kanki adalci"
Amrah tace "to ya zanyi? Koda banyi niyan tunanin ba sai nayi, rayuwa tana zuwan mana babu sassauci amaikon na yau yafi na jiya sauki aa sai dai na jiya yafi na yau sauki, dubi yanda Mama ta shareni a gidannan kamar ba ɗiyarta ba"
Hawaye ta share, Kulu zama tayi a gefenta tace "Kidaina damuwa Mama bazatayi fishi dake me tsawo ba zata sakko vary soon kinji?"
Amrah giɗa kai tayi tace "Babban matsalata yanzu shine ta ina zan fara neman ƴan uwana? Awane duniyar zan nemesu? gara Fadila nasan fuskarta amma Khalil bansan fuskarshi ba, bansan kamanninshi ba"
Kulu tace "tabbas saida abu biyu zaki samu ƴan uwanki"
Amrah tace "menene wannan?"
Kulu tace "na farko sai kinyi suna a duniya na biyu kuma sai kinyi kuɗi dahakane zaki raba gidan jaridu da radio"
Amrah tace "hmm Bab kulu kenan ta ina zan farayin kuɗi kina ganin talaucin da muke ciki"
Kulu tace "akwai Allah idan kikasa Allah a ranki to zakiyi nasara"
Amrah tace "to Allah yasa"
Sallama akayi Amrah ta amsa, wani karamin yarone yace "wai anayiwa Amrah magana"
Amrah ɗago kai tayi tace "waye?"
Yaron yace "wani me mota ne"
Amrah tace "kaje kace batanan"
Kulu tace "Aa kace tana zuwa"
Amrah kallonta tayi tace "meyasa?"
Kulu tace "bakisan dame bako zezo miki ba"
Amrah kwafa tayi tace "tom" mikewa tayi tasa wani dogon hijabi sannan tafita cikinta yaɗan turo kaɗan, Leke tafara ko zata hango waye, ganin bazata hango kowa ba yasa tafita, "barka" juyawa tayi taci karo da mutumin da sille watarana, ɗan murmushi tayi tace "barka dai"
Yace "kinyi mamakin ganina ko?"
Tace "babu abin mamaki a wannan duniyar yanzu komai possible ne"
Dariya yayi yace "Amrah baiwar Allah"
Tace "ya jikin matar taka?"
Shiru yayi be bata amsa ba, ganin haka yasa jikin Amrah yayi sanyi, Tace "kayi hakuri"
Yace "ba komai dama Allah yayi mata rasuwa ne"
Amrah tace "innalillahi wa inna ilaihiraji'un, Allah yaji kanta da rahama"
"Amin"
Daganan yace "nazo wurinki ne da babbar magana"
Hanklinta ta mayar kanshi sosai tace "tom ina jinka"
Yace "Aurenki nakeso nayi amma naganki da ciki kuma baki cmin kinada aure ba"
Shiru tayi batace komai ba, yace "kiyi hakuri"
"Ba komai nayi aure inada ciki mijina ya sakeni kaga kenan maganar aure bazeyi tsakaninmu ba har saina haihu"
Yace "nasani amma dafari sunana Ahmad ina rayuwa da matata da mahaifiyata dakuma yarana guda biyu a garin Abuja, Matata Allah yayi mata rasuwa, idan babu damuwa zanso na kaiki wurin mahaifiyata harki haihu acan daganan sai muyi aure, dan tun ranar dana ganki nakasa samun nutsuwa"
Amrah tace "Gaskiya bazan iya binka ni kaɗai ba dan zamanin yanzu ba'a yadda da mutum kuma saika nemi izini awurin mahaifiyata"
Yace "ba