Showing 18001 words to 21000 words out of 139192 words

Chapter 7 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

899

hannun marasa imani mugu me halin mugaye" a hankali hawayen suka daina fitowa sai zuciyarta dataji yana kokarin bushewa Allah yasani taso Amrah iya so, ta nuna mata kauna irin na 'yan uwantaka, Amma Amrah taci Amanarta ta cuceta.

    "Kamal yana zuwa gida yayi parking riko hannun Amrah yayi yakaita har part nasu, suna shiga ya zaunar da ita akan gado yana kallonta yace "to bud'e fuskar mugani"

Amrah sai a lokacin taji wani irin tsoro ya ziyarceta tama manta shaf akan dole saiyaga fuskarta, hawayene yafara fita daga idonta yana sauka a hannu Kamal, da sauri ya d'ago yana kallon hannunshi ganin tana kuka yasashi jin ba dad'i a zuciyarshi Dan ya tsani yaga mace tana kuka balle ma Fadila dabayaso yaga koda rantane ya b'aci balle ayi maganar kuka, a hankali ya janyota jikinshi yana jin kamar ya maidata ciki, d'ago kanta yayi yasa hannunshi a hankali yafara zame mayafin data rufe fuskarta dashi, da sauri ta kankame hannunshi taci gaba da kuka, murmushi yayi domin ya lura Fadila tana tsoronshi tun ranar kamu, janye mayafin yayi da karfi yana dariya da sauri yayi baya a tsorace ganin fuskar Amrah yayi shab'e shab'e da hawaye, gyara riganshi yayi muryanshi yana d'an rawa yace "Am sorry nazata Fadilace" da sauri yanufi hanyar fita danshi a zatonshi Irin d'an shirmen da akeyine na Amaryar karya Wanda za'a kawo da farko daga karshe akawo Amaryar, jiyayi Amrah tarike hannunshi tana kuka kamar ranta zai fita, saurin janye hannunshi yayi yace "kiyi hakuri wallahi na zata Fadila ce shiyasa nayi hakan"

Cikin kuka ta tashi ta kankame shi kamar za'a kwaceshi, tace "yaya Kamal nice matarka ba Fadila ba, dani aka d'aura Auren Fadila taci amana ta gudu"

Kamal sakin bakinshi yayi yana sauraron maganar kamar Almara, ci gaba tayi da kuka tace "sun had'u da wani saurayi ya rinjayeta da kud'i shine tabishi suka gudu" tureta yayi daga jikinshi cikin zafin nama tayi baya baya ta fad'i kanta ya bugu da jikin gado atake wurin ya tashi, cikin tsawa yace "me keki fad'ane? Ya kike anbaton wani namiji tareda Fadila kuma baniba"

Amrah ganin haka yasata mike a firgice tahaye kan gado tana jin mugun tsoronshi, Kamal jikinshine yafara rawa yana kallon Amrah, turo kofar akayi Umman Kamal ce tashigo hannunta d'auke da juice tana murmushi, ganin Kamal tsaye ranshi a b'ace ga Amrah zaune a karshen gado tana kuka yasa taji zuciyarta ya kusayin bindiga, sakin kofin tayi tareda juice d'in suka tarwatse akasa dafe kirji tayi tace "dafatan bakayi mata komai ba, domin wasu al'adar haka sukeyi sai an kawo amaryar karya kafin akawo ta asalin daga baya"

Hawaye tagani a idon Kamal da sauri taje wurinshi tana tambayarshi lafiya? kuka yasakan mata sosai yana kallonta Jikinshi yana rawa, janyoshi tayi jikinta tana buga bayanshi a hankali tace "relax"

Saida yayi kukanshi me isa kafin ya bud'i baki yace "Ummana My Deelah ta gudu tabarni" d'ago kanshi tayi tace "me kake fad'ane Kamal kafi kowa sanin halin Fadila bazata iya gudu tabar dabba bama balle mutum, mutumin ma Wanda takesonshi kayi tunani mana my son"

Cikin muryan kuka yace "Umma tunanina ya toshe kitafi dani d'akinki bazan iya zama anan ba" Umma tama rasa me zatayi zaunar dashi tayi a gefen gado tana bashi hakuri akan yad'an tsaya zuwa gobe idan mutane sun watse sai Asan abinyi, da kyar ta lallab'ashi ya daina kuka sai sauke ajiyar zuciya dayake, A hankali bacci ya d'aukeshi tana mishi bargo kafin tafita ko kallon inda Amrah take batayi ba,

Amrah ta tsorata sosai ganin yanayin Kamal Dana mamanshi da farko tazata abin zaizo mata da sauki sai kuma yanzu take ganin kamar abin zaifi karfin ta, a hankali ta mike tareda gyarawa Kamal bargon dayake lullub'e dashi, zama tayi a kasa tana kallon fuskarshi tana murmushi shafawa tayi a hankali tace "Insha Allah saika zama nawa gaba d'aya zan jure duk wani wulakanci dazakayimin sabida ina Sonka, zansa ka manta da wata halitta wai Fadila, saika manta da Fadila kamar baka tab'a sanin wata me irin sunar ba, sainasa ka tsani Fadila Wanda ko maganarta akayi Maka Bazaka saurara ba, Kamal Baku dace da Fadila ba dani ka dace" tana fad'an haka hawaye yana wanke mata fuska tarasa hawayen menene, saida tagaji Dan kanta kafin ta mike tashiga toilet tayi Alwala tazo ta tada sallah tanayi tana kuka.

_Jiddah Ce....✍️_

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 13*

    ~Bayan ta idar da sallan ta d'aga hannunta sama tace "Ya Allah Kaine ka halicci Amrah sannan kai ka halicci Fadila kasa soyayyar Amrah a zuciyar Fadila sannan kasa soyayyar Fadila a zuciyar Kamal sannan kasa soyayyar Kamal a zuciyar Amrah, Allah Kasan inason Kamal idan har Fadila zata dawo ya Allah kacire mata soyayyana a zuciyar ta banason Fadila ta rab'eni da mijina dan nasan tabbas akwai soyayyar Fadila a zuciyar Kamal, Allah ka bani ikon cire wad'annan soyayyar ka bani ikon cire soyayyar Fadila a zuciyar Kamal sannan kabani ikon cire soyayyar Fadila a zuciyar Amrah sannan kabani ikon cire soyayyar Amrah da Kamal a zuciyar Fadila, kodai nayi laifi ne? Nayi laifine? Me nayi?"

Tafad'a cikin kukan da ake kira kukan bakin ciki, shafe addu'ar tayi a fuskarta tanajin wani irin karfin gwiwa yana zuwan mata, tashi tayi taje wurin Kamal ta rab'a ta gefenshi ta kwanta tareda janyo bargonshi itama ta lullub'a ciki.

       ~Baby tafarka tunda jimawa amma tayi shiru tana jinsu lokacin da sukazo, jikinta rawa yake sosai, Fadila ma mikewa tayi cikin tashin hankali ta kalli sauran 'yammatan dasuketa kuka, wasu sunayine domin an tafi da 'yan uwansu wasu kuma sunayine domin yunwa, share hawaye tayi tace "bamuga ta zamaba a wannan gidan zasu zalincemu kuma babu Wanda yasani dolene mugudu"

Mikewa sukayi a gigice sunason sugudu wasu ko takalmi basu d'auka ba, Babyma tariko hannun Fadila gam suna Addu'ar Allah ya kub'utar dasu, cikin sand'a suke tafiya har suka isa bakin kofa bud'ewa Fadila tayi tace "muna fita kowa yayi gudu sai inda karfinmu ya tsaya"

Gyad'a mata kai sukayi tariko hannun Baby Gam, suka bud'e kofar kowa ya d'iba da gudu, basuyi nisaba sukaga wad'annan kartin sunabin bayansu, da d'aid'ai suke kamasu har suka kamosu duka, bulala suka Ciro suka fara dukansu dashi tako ina, Baby ta galabaita ga kishi ga duka abin yayi mata yawa, Fadila ma ta daku sosai domin jikinta duk layin bulala amma dukda haka tana kokarin tarewa Baby dukan, jansu sukeyi a kasa har cikin gidan, sauran yammatan da sukazo tare sai kallonsu suke cikin tausayi gashi ba halin karb'a musu, saida kowa yakasa motsi kafin suka daina dukan, guyson ne yakira dukka 'yammatan yace sufito, suna fita kowacce ta durkusa akan gwiwarta suna sauraron hukuncin daza'ayi musu, cikin muryan mugaye da b'acin rai matuka yace "Wad'annan 'yan iskan da iyayensu basu damu dasuba sunyi niyan gudu a gidannan nasan kece kika fad'a musu Ku gudu ko?"

Yafad'a yana nuna Fadila, dukar dakai tayi kasa fuskarta tayi jaa ga jikinta duk shatin bulala, "To hukuncinku shine zakuyi kwana biyar bakuci abinci ba sannan duk wayewar gari zaku fita da wad'annan Ku d'ibo ruwa harsai kun cika komai na gidannan daga gobe zaku fara, kutashi kubani wuri"

Cikin d'ingishi Fadila tamike tana tafiya, juyawa tayi tana kallon Baby wacce ta kwanta a kasa jikinta yana rawa Alamar ta galabaita, da sauri taje wurinta tarikota da kyar ta iya takawa har suka isa d'aki, suna shiga Fadila tad'auko roba babba tad'ibi ruwan sanyi a ciki takai toilet d'aukan Baby tayi takaita har bakin toilet tace Shiga kiyi wanka zakiji sauki, Baby kallonta tayi na wasu lokuta kafin cikin kuka ta rungumeta tace "bazan iya wanka da ruwan sanyi ba Adda"

Fadila jitayi yarinyar takara bata tausayi lallab'ata tayi har ta yadda tashiga tayi wankar tana fitowa tafad'a kan gadon Fadila taja zanin gado me datti ta rufa jikinta dashi, itama Fadila wankar tayi tazo ta kwanta a gefen Baby tanajin zazzab'i yana rufeta jikinta yana d'an rawa ta janyo baby jikinta a haka har bacci ya d'aukesu, sauran 'yammatan ma saida sukayi wanka da taimakon wata Zainab a cikinsu wacce takeda dauriya sosai, kowa ya kwanta batare da sunci abinciba.

          "Da Asuba Kamal ne yafara mikewa yana mutsika ido, kallon gefenshi yayi yaga Amrah ta kanainayeshi tana bacci, runtse idonshi yayi yana tuno da maganarta na jiya da sauri ya hankad'ata zuwa kasa, a firgice ta tashi tana kallonshi da manyan danunta, nunata yayi da yatsa cikin b'acin rai yace " idan kika kara tab'a jikina saikin gwammace ba'a haifeki ba, kodan kinga ina sakar miki fuska shine kika samu daman rainani, niba sa'anki bane yanzu zanyi miki dukan tsiya"

Amrah ido ta zuba mishi batace komai ba saima jikinta daya fara b'ari Dan bata ganinshi cikin b'acin rai irin na yau ba, yace "koda shike banga laifinki ba laifin iyayenki nagani sun maidani Mara wayau sun zata ni shashasha ne shiyasa suka canjamin mata ba tareda sun fad'amin ba, Allah ya isa tsakanina dasu"

Da sauri Amrah ta mike tace "Yaya Kamal bafa laifin su Mama bane laifin Adda Fadila ce nafad'a maka guduwa tayi itada saurayinta Mama kuma bataso tasa Ummanka a Kunya gaban kawayenta shiyasa akace a d'aura Auren dani, Amma meyasa zakaga laifin iyayena? Bazakaga laifin Adda Fadila ba, ka manta lokacin danake kiranka a waya in fad'a maka cewar Adda Fadila tafita dawani? Ka tab'a binceke akan hakan? To idan Baka saniba Adda Fadila har d'akin saurayi tana zuwa kuma inada video d'insu a wayana idan kana ganin karya nayi maka" ta fashe da kuka sosai takara cewa "Banason in tonawa Yayata asiri amma Yaya zanyi yazama dole, nida akeyiwa kallon Mara kunya nice aka cuta ita kuma Green snake ne under green grass idan bamai wayo ba bazai tab'a luraba, Allah ya sakamin da Alkhairi nasan mutane suna ganin Adda Fadila tafini hankali alhalin kuma ba haka abin yakeba" turo kofan akayi da karfi, atare suka juya suna kallon kofa, Unty Sadiya ce tashigo ranta a b'ace Dan taji duk maganar dasukayi, Wurin Amrah ta nufa ta zabga mata mari, Amrah d'ago kanta tayi tace "Unty me nayi...." Kara d'auketa Unty tayi da mari Wanda yasa Amrah fad'uwa Kasa, da sauri takara mikewa tace "me nayi miki dazaki bini har gidan mijina ki mareni?..." Wani Marin ta kuma d'auketa dashi kafin tagama rufe bakinta, Fad'uwa Amrah tayi kasa da dafe gefen fuskarta da hannu bibbiyu Dan Har wani star take gani, Unty Sadiya cikin b'acin rai tace "dazaki cigaba da magana yau har zuwa fad'uwar rana bazan gaji da wanke fuskarki da kyawawan mari ba, wallahi Amrah kinyi Asara duniya da kuma Lahira bazaki shiga Aljanna a wannan yanayin naki ba"

Da sauri Amrah tamike ta nuna Unty da yatsa cikin hawaye tace "Unty idan kece kike bada Aljanna ko kuma makullin aljanna a hannunki take please idan nazo shiga ki rufe ki hanani, meyasa kowa baya ganin laifin Adda Fadila sai laifina? Taimakonta nayi a idon duniya domin kada ayi mata mugun Baki ace ta gudu ranar Aurenta, sai kuma gashi abin yana nema yazamemin barazana"

"Baki fara ganin barazana ba Amrah sai nan gaba, bani kika nuna da yatsa ba?"

Amrah tace "dolene yasa na nunaki da yatsa Unty, kuji tausayina mana ku duba Abu akai, ni nafi kowa Sanin halin Adda Fadila sabida tare muka taso kuma tare muke bacci duk wani motsinta nasani duk wani sirrinta nasani" juyawa tayi taje wurin drawer tad'au wayarta, password tasa tashiga wurin video, play tayi sannan tasa wayar a rotated, Umman Kamal ce ta bud'e kofar tashigo jin hayaniya a cikin d'akin daidai lokacin Amrah ta danna play akan wani video, saiga videon yana nuna Fadila da wani saurayi Wanda fuskarshi bai gama fitowa ba suna romancing na junansu, salati Umman Kamal ta sake tareda zama a gefen gadon ta dafe kanta tanajin jiri yana d'ibanta, Kamal kurawa wayar ido yayi yana kallon Fadilarshi rungume dawani kato akan gado yana shafa jikinta, Unty Sadiya jingina jikinta tayi da bango tanajin jiri itama, ta kasan ido Amrah tabisu da kallo a hankali ta saki murmushi sannan ta kuma had'e rai tajuya tace "kun gani ko? Banaso in tonawa 'yar uwata Asiri shiyasa tun wuri ban fad'a muku ba" d'aura kanta tayi akan gadon tafara raira kuka, Kamal ne yazo ta bayanta yasa hannu zai d'agota Unty Sadiya tace "kul karka sake ka tab'ata sai mun gano menene gaskiyar lamarin"

Wani mugun kallo Amrah tabi Unty dashi ta tabbata da babu mutane a d'akin yau saita kashe matarnan, sausauta murya tayi had'i da matsowa wurin Unty dab tace "Unty bazanyi miki musu ba sabida kin girmeni, Allah yana kallo shine zai sakamin" a fusace Unty tafice a d'akin domin kanta ya kulle maganganun Amrah ya d'aure mata kai tarasa mezatayi,

Kamal ma cikin fusata yafice a d'akin shima kanshi ya kulle yarasa me hakan yake nufi, cikin tafiyarshi na kasaita yafara ratsa mutane a falon burinshi kawai yaganshi a bedroom na Umma yasamu ya kwanta akan gadonta kozaiji da saukin ranshi, yana zuwa ya fad'a kan gadon ya rufe fuskarshi da filo yana son gano gaskiyar lamarin, ganin kwanciyar baya mishi dad'i yasashi tashi a wannan yanayin yanason yajishi a jikin mutum ad'an lallab'ashi koda kad'anne, runtse idonshi yayi atake wasu hawaye masu d'umi suka fara bin kumatunshi, duk rufe idon da zaiyi Saiya hango Fadila da wannan katon a kwance suna shafar juna,

Bayan fitansu Umma ta zubawa Amrah ido tarasa me takeji akan yarinyar tsana ne ko kuma haushi ne ko kuma tausayine, karasawa wurinta tayi tareda d'agota suna kallon juna ido cikin ido, Amrah ce tafara janye idonta daga na Umma ganin yanda ta zuba mata ido tana mata kallo me wuyar fassara, Umma tadafa kafad'arta tace "zaki iya cutar da yayarki?"

Amrah tad'an juya kanta gefe kana ta mayar da muryanta yakoma slow kamar wata Innocent tace "Umma tunda kuna ganin kamar nice na cutar da ita to shikenan na yadda sabida banason musu daku"

Karo na farko da Umma taji tausayin yarinyar sakinta tayi tafice a d'akin zuwa nata, ganin mata suna shirya kayansu da niyar tafiya yasa tace "Sannunku nagode da kokari"

Sukace ba komai ai yiwa Kaine, wata yayar Umma wacce tazo daga Gombe itace tariko hannun Umma suka shige wani lungu tace "Karima yanaganki a susuce shima Kamalun yashigo d'aki a susuce ido a kumbure ko amsa gaisuwa bayayi, meke faruwa?"

Umma cikin bakin ciki ta zayyanawa Yayarta duk abinda yafaru, dafe kirji yayar tayi tace "lahaula Ashe iyayensu basuda hankali basu baiwa yaransu tarbiyya ba m, kai Allah ya wadaran naka ya lalace Allah ya isa tsakanin Kamalu da wancan Karuwar"

Umma tace "Ameen"

Dahaka kowa ya watse agidan suka rage daga Amrah sai Kamal da Ummanshi sai Yayar Umman Kamal wacce tace bazata tafi yanzu ba, Ummace tashiga d'akinta tana zuwa taga Kamal ya kwanta yana kallon sama idanunshi suna zubar da hawaye ya rungume filo kem akirjinshi, cikin yanayi na tausayi takarasa wurinshi tareda janye filon ta d'ago kanshi ta d'aura akan cinyarta  a hankali tafara shafa gashinshi me tsanti Wanda yasha gyara yana kanshi, Kamal har yanzu idonshi bai daina zubda hawaye ba, muryanshi yana rawa yace "Ummana please kibarni nayi kuka karki hanani kinji?"

Umma gyad'a kanta tayi itama hawaye yanabin fuskarta tace "kayi kuka my son, zai rage maka rad'ad'in dakake ji a ranka bazan hanaka ba kayi kukanka"

Rungume Umma yayi yaci gaba da kuka.

     "Fadila bacci suke me d'auke da wahala da azabar dukan da akayi musu, suna cikin bacci sukaji feshin ruwan sanyi akansu, a firgice suka farka suna kallon mutumin daya shigo da tiyo yana watsa musu ruwa, cikin tsawa yace "Ku tashi kufara aikinku"

Da sauri Fadila ta sauka akan gado sabida dukan da akayi musu jiya ya mugun tsorata ta, roba kowacce ta d'auka suka nufi wurin d'iba ruwa duk fuskokinsu babu walwala musamman Baby wacce fuskarta tayi fayau ta kumbura, Suna kan d'iba ruwa sukaga wani babban mota yashigo bud'ewa akayi aka fara fito da 'yammatan da suka tafi jiya, jikinsu jina jina kowacce tana numfashi sama sama ga wad'annan mugayen mutanen suna binsu da duka, a galabaice suke tafiya sauran ma fad'uwa suke idan aka zabga musu bulalar saisu mike, Hawayene yafara kwaranya a idon Fadila tanaso ta taimaka musu amma ba hali gashi itama tana fama da rashin lafiyan jikinta, Baby wacce ta firgice da ganin sauran 'yan uwanta cikin tsoro tace "Adda yanzu muma haka zasuyi mana yau ko gobe?"

Fadila kallon baby tayi cikin firgici itama tunawa da maganar guyson cewar zasu na canja 'yammata, samun wani dutsi tayi ta zauna ta buga tagumi indan itace babu matsala tasan rayuwarta tariga ta b'aci to Amma Baby fa? Yanda taga wannan 'yammatan sun dawo haka zasuyiwa Baby? Yarinyan ai she's under age, tayi yarinya dayawa ita kanta bazata wuce 19years ba balle Baby wacce bazata kai ba16 tausayi da tsoro sun taru sun mata yawa.

_Jiddah Ce....✍️_

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 14*

      ~A haka suka gama d'iba ruwan suka shige d'aki sauran mutanen suma suna d'akinsu babu kowa a cikin gidan sai wasu maza guda biyar da aka zubasu sabida gadi hannunsu d'auke da bulala manaya manya masu kauri, Fadila dauriya tayi ta d'ibawa 'yammatan ruwan wanka ganin yanda suka galabaita, a Hankali suka taimaka musu har sukayi wankar, Watace wacce ake kirada Fatima tafara basu labarin abinda yafaru dasu cikin kuka, tace "bayan sunzo sun tafi damu, shine suka kaimu wani babban hotel ciki harda mutanen Nigeria manya masu kud'i wad'anda ganinsu sai a jarida, wani babban d'aki suka shigar damu bamu jimaba saiga maza Alhazawa da masu kud'i sun shigo d'akin da wani farin kyalle a hannunsu, dukkanmu muka tsorata mun rasa abinyi, suna zuwa suka farayi mana fyad'e bayan sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login