Showing 54001 words to 57000 words out of 139192 words
Baby ce take taimaka mata akan duk abinda zatayi dukda Babynma tana cikin matsala amma haka take daurewa tana yiwa Fadila hidima, d'agota tayi da mug a hannunta "sannu Adda, ki daure kisha tea d'in ko kad'anne zai taimaka miki amma tun safe kike zaune haka ciwon cikin zai iya yin tsanani"
Yamutsa fuska Fadila tayi cikin yanayin ciwo tamikowa mata hannunta a hankali Baby ta d'agota gaba d'aya tasa mata filo a bayanta, mug d'in ta d'aura mata a baki a hankali Fadila take sipping tana yamutsa fuska Dan tea d'inma jinshi take kamar mad'aci, Mommy ce tashigo d'akin tana kiran sunan Baby, kawartace tadawo daga Dubai da kaya shine takeso tasiyawa Baby, Ganin Tana baiwa Fadila tea ga Fadilar kamar ba lafiya yasa tace "lafiya kam?"
Baby cikin yanayin tausayi tace "Mommy tin safe Adda Fadila bata da lafiya bataci komai ba sai yanzu takeshan tea shima badan dad'iba' hawayene yataru a idonta da sauri tasa Hannah ta goge, Mommy hararan Fadila tayi ta kara murtuke fuska tace "meyake damunki?"
Fadila tace "ciwon cikine" mommy tace "Baby biyoni ki karb'a mata magani"
Da mamaki Fadila ta d'ago tana kallon Mommy wai yau itace zata bata magani? Cabd'i za'ayi ruwa da kankara yau a garin Abuja, Fita sukayi itada Baby ba'a jimaba saiga Baby da kwayar magani a hannunta cup na ruwa ta d'auko tace "kisha" ansa tayi tasa a bakinta runtse Ido tayi Dan ta tsani magani da allura da kyar dai ta had'e, a hankali tariko hannun Baby tace "Baby Jiya Daddy yace yanada magana damu kije kisanar mishi banida lafiya kar yaji shiru"
Baby tace "to" tareda fita, d'akin Daddy tanufa lokacin yana bacci murmushi tayi Dan tana matukar son baban nata, tunawa tayi da lokacin datake yarinya idan zata tasheshi, dariya tayi tanufi gadon ta d'auko filo ta maka mishi, a firgice Daddy ya farka yana cewa "waye?" Dariya takeyi harda rike ciki, binta yayi zai kamota da gudu ta fara zagaye d'akin saida yagaji kafin yafad'a kan gado yace "ina jinki meya kawoki?"
Tace "Daddy dama Adda Fadila ce ba lafiya kuma kace yau akwai maganar daza kuyi shine tace na sanar maka"
Daddy ya d'ago kai da alamar ya tausayawa Fadilar yace "muje naganta"
Da gudu tafice dan tana tsoron karya kamata, dariya kawai yayi yabi bayanta, Abakin kofa sukaji kakarin aman Fadila da sauri Daddy ya karasa har cikin bedroom ganin yanda take wahalane yacewa Baby "Kiramin mommyn Ku"
Baby tace "to" tareda fita da gudu, d'akin mom taje tace "kije inji Daddy yana d'akinmu" da matsifa mommy tamike meyasa zai kirata a d'akinsu?
Saida tashiga taga Daddy ya rud'e akan Fadila, ciwon cikin mata shine yake wani zufa yana mata sannu haka? Lalle akwai bala'i a gidannan "gani" shine abinda tace, kallonta Daddy yayi daga sama zuwa kasa yace "bakiga yanda take bane zakicemin gaki?"
Murgud'a baki mom tayi tace "nagani wannan ai tsakaninku ne wayasan meyake faruwa yanda naga ka rud'e ai kafi kowa sani" waro Ido yayi yace "me kike nufi?" Tace "abinda kaji da kunnenka shinake nufi"
Wani mahaukacin mari ya d'auketa dashi rike kunci tayi ta zabga ihu, hannu tad'aga zata rama yariko hannun nan suka fara kokawa kamar yara, Fadila miko hannu tayi tanaso tarabasu amma ina ciwo yaci karfinta kuka kawai takeyi Baby kuma sai Jan Daddy take tana bashi hakuri, Abdul ne yashigo d'akin jin ihun Mommy ganin suna kokawa ga Fadila tana murkususu tana kuka yasashi karasawa wurinta ko magana baiyi ba yasa farin hannunshi me d'auke da kwantaccen gashi ya d'agata cak tareda rungumeta yayi hanyar waje da ita, Baby ganin haka yasa tabisu tana sharan kwallah duk sukabar Mommy da Daddy sunata fad'a, parking space yanufa da ita Fadila sai Kallon fuskarshi take shikuma ya had'a gira da Ido ya murtuke fuska amma duk da haka bai hana kyawunshi fitowa ba, bud'e motar yayi ya shiga da ita a cinyarshi ya kwantar da kanta sannan yasa key, da gudu Baby tazo tabud'e baya Dan tasan halinshi mad'au yanzun nan zai tafi yabarta ba abinda yadameshi, tuki yake a hankali yana Kallon fuskarta yanda take yamutsa fuska alamar ciwon yana damunta, ga hannunta tasa a maranta da alama wurinne yake mata ciwo, d'ayan hannunshi ya d'auko yasa akan nata a hankali yacire Natan yamayar da nashi a wurin, shafa mata cikin yake kamar dawasa taji numfashinta yana shirin d'aukewa b'oye fuskarta tayi tana jin yanda yakeyi kuma cikin yanad'anyin sauki, shikam ko Kallon fuskarta bayayi burinshi kawai su iso asibiti a dubata, Baby ce tad'an leko tana son ganin halinda Fadila take ciki, da sauri tayi baya tana maida numfashi ganin hannun Yaya Abdul nasu a cikin Fadila yana shafawa, sai waro Ido take tana kawar da kanta, Abdul ya fahimci ta Ganshi amma shikam ko ajikinshi saboda baiyi da wata manufa ba zuciyarshi fess, a bakin wani katafaren asibiti suka tsaya Wanda aka rubuta "Specialist hospital"
Parking yayi yaciro hannunshi ya d'agata sai cikin asibitin mutane sai kallonsu suke wasu su birgesu wasu kuma suce rashin kunya ne, office na doctor yanufa kasancewar yasan doctorn abokinshi ne, Baby ce tabud'e mishi kofar ya shiga, mikewa doctor yayi yana waro Ido ganin Abdul rike da mace kuma ga Baby nan lafiyarta lau, tsaki Abdul yaja yace "dallah kabamu gado na kwantar da ita"
Gefe yanuna mishi a hankali Ya kwantar da ita, doctor ne yafara dubata yana mamaki ko dai Abdul yayi aurene gashi yarinyar kyakkyawa kamar ita tazana kanta, Kallon Abdul yayi yace "kud'an bamu wuri" harara Abdul ya zabga mishi yace "babu inda zanje kayi a gabana" Baby ce tajuya tafice, gefen gadon Abdul ya zauna, saida doctor yagama dubata yayi rubuce rubuce sannan yace "wannan ba maganar ka bace maganar manya ce"
"Me kake nufi?" Cewar Abdul, yace "inaso nayi magana da babanta ko mamarta"
Abdul yace "duk maganar dazakayi dasu Nima zaka iya dani sabida ni yayanta ne"
Doctor yace "to anji yaya babba, gaskiya ba maganar wasa maganar gaskiya zan fad'a maka wannan yarinyar daso samune ayi mata Aure sabida auren shine zaisa tadaina wannan tsananin ciwon cikin, idan kuma tanada Aure to gaskiya mijin nata sai anyi zama dashi Asan menene matsalar"
Abdul shiru yayi itakuma Fadila ta runtse Ido kamar bacci ya d'auketa duk da cikin yana mata ciwo to amma dolene ta daure dan maganar yayi mata nauyi, doctor yace yanzu zamuyi mata allura zata samu sauki zuwa yamma to amma zamu kwantar da ita tayi kwana uku sabida ta warware, Abdul yace "okay ba Matsala"
Allura doctor yaciro yazo wurinta yace "yawa gashima tana bacci sai ayi mata ba wani gaddama kasan mata dakin allura"
Mikewa tayi a firgice tana kallonsu tace "wallahi idona biyu Dan Allah kar kamun allura" yace "allura yazama dole ayimiki, juya kadan lokaci naja akwai patients dazan duba"
Kin juyawa tayi tana rokanshi, Abdul ne yadaka mata tsawa yace "zaki juyane ko kuwa?"
Juyawa tayi a firgice tana runtse Ido, Allauran yaciro ganin haka tariko hannun Abdul dukka biyu ta matse a kirjinta, ihu tayi ta rungumeshi lokacin da allurar ya shiga jikinta, da kyar aka cire alluran, tsaki Abdul yaja yace "sakeni to karki Karya ni raguwar banza"
Rufe fuskarta tayi ta kwanta a gadon bata dad'e ba bacci ya d'auketa, doctor yace "idan ta farka zamu kaita d'akin dazata zauna na tsawon kwana uku" Abdul yace "naji" saida doctor yafita kafin Baby tadawo zama tayi agefen Abdul Tariko yatsanta tana murzawa a hankali tana Kallon kasa tareda tunanin fad'an Daddy da mommy, d'ago kanshi yayi ya kalleta jiyayi tabashi tausayi sosai, a hankali ya janyota jikinshi ya rungumeta tsam yana shafa kanta, kamar jira take ta fashe da kuka, Abdul yace "shikenan kidaina kuka, kidaina sa fad'ansu a ranki kinji Babyna?"
Gid'a kanta tayi tashare hawayen "yawwa Babyna anjima zan siyo miki chocolate kinji?"
Tace "tom yaya" Wayarsa ce tayi ruri, cirowa yayi daga aljihunshi yana duba Wanda yakira sunan daddy yagani a hankali yad'aga yace "hello daddy"
Daddy tace "wani asibiti kuke?"
Abdul yace "Specialist"
Katse wayar yayi bayan wasu lokuta saiga Daddy tambayar jikin yayi sukace da sauki, shima zama yayi a gefe sukayi shiru duka.
"Kamal ka tsaya kabani kud'in Awo" Cewar Amrah datake bin Kamal babu ko d'ankwali akanta, Kamal juyawa yayi yace "kinga dallah kirabu dani shi Wanda yayi mini cikin ubanane? Da zakice nabaki kud'in awu"
Kuka tafashe dashi tace "Allah ya iso ban yafeba ka cuci rayuwata"
"Kin cuci rayuwarki dai"
Amrah cikin kuka tace "tin farko ma shaid'an ne yasani yin haka danasan haka kake daban yadda ba tin farko"
Kallonta yayi yace "babu ruwan shaid'an a wannan lamarin idan ma akwai to kece"
"Niba shaid'aniya bace saidai kai"
Mari ya d'auketa dashi "nine shaid'anin?"
Kuka tafara tanajan Allah ya isa, fita yayi yabar mata gidan gaba d'aya kuka takeyi babu mai lallashinta saida tagaji Dan kanta kafin tashare hawayen.
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 40*
~Fadila bacci takeyi sosai kasancewar Allurar yana aiki ajikin mutum, Daddy dafe kanshi yayi da hannu biyu yanajin zafin abinda mommy takeyi mishi Baby ce tajuya tazubawa mishi ido tausayi yake bata sosai hayaniyar mommy ma kad'ai ya isheshi tashi tayi daga jikin Yayan nata ta nufi wurin Daddy hannu biyu tasa tacire mishi nashi daga kanshi d'ago kai Daddy yayi yana kallonta a hankali ta girgiza mishi kai alamar yadaina tunani d'agota yayi ya rungumeta tsam da takaici yace "Mamana mommynku bata tausaya min yanzu wai zargina take da Fadila wacce na d'auka a matsayin 'ya?" Da sauri takuma girgiza kanta tace "Daddy kadaina fad'an haka tsanar Fadila datayi shiyasa take zargin ka kuma insha Allahu komai zai dawo normal"
Shiru yayi shima Abdul shiru yayi yana kallonsu baban nashi tausayi yake bashi sosai, sai kusan mangarib kafin tafara motsi da hannunta lokacin Baby tafice zata siyo musu abinci, Abdul ne kad'ai a d'akin domin Daddy ya dad'e da tafiya, ganin tana motsi da hannunta yasashi mikewa yaje dab da ita a Hankali ta bud'e idonta ganin Abdul tsaye akanta yasa takara lumshewa a hankali, tsaki yad'anja kad'an kana yace "kina buk'atar wani Abu ne?"
Hannu Tamika mishi d'agata yayi ya zaunar da ita, "ruwa" shine abinda tace Goran faro ya d'auko ya mika mata bud'e bakinta tayi ta lumshe idonta alamar yabata kallonta yayi da mamaki sanin batada lafiya ne yasashi riko kanta yabud'e ruwan yafara bata sha takeyi kamar zata had'a da Goran daddy ne yaturo kofar bakinshi d'auke da sallama ganin Abdul yana kula da ita yasashi sakin murmushi yajuya yafice, a takaice saida sukayi kwana uku a asibiti, acan gida kuma mommy tacika ta batse ta kumbura fashewa kawai take jira tayi, ace yau kwana uku babu yaranta babu mijinta wallahi Fadila tagama da ita, a asibiti kuma Baby ce tariko Fadila dukda tasamu sauki amma har yanzu tana samun kulawa wurin mota takaita har saida tashiga kafin takoma ta tattaro 'yan kwamutsan su tasa a motar, Abdul ne yajasu har zuwa gida, suna isa Daddy yafita ya shiga gida da wuri Dan yanada aikin da zaiyi, Abdul da Baby da Fadila kuma suka jera tare suna tafiya har cikin falo, Mommy tsaki taja tace "kai Abdul zo nan" Abdul da gajiya yagama ratsa jikinshi ya huya Yakoma wurin mommy a shagwab'e yace "mommyna sannu da gida" harara mommy ta banka mishi kana tace "ba yawwa ba wato yarinyarnan tasan shirin datayi kafin tazo gidannan domin naga kaida ubanku da Baby duk kun koma gareta ni kuma kun maidani bare yanzu ace akan yarinyar nan har mahaifinku zai d'au hannu ya mareni kaima kabiye mata ka kaita asibiti Baby ma bawata kulawa nake samu a wurinta ba gashi babanku kullum yanamin gori ya kukeso nayi da rayuwa?" Takarasa maganar tana kuka Abdul tashi yayi ya rungumeta a jikinshi yana bata hakuri d'ago kai tayi tace "zan hakura d'ana Amma saika min alkawarin bazaka sake kula wannan yarinyar ba kuma zaka auri wacce nakeso" Kallon mommy yayi yabud'i baki zaiyi magana Daddy yace "bazai yiwu ba sannan yarinyar itace ta taimkawa mamana lokacin datake bukatar taimako kuma insha Allahu itace Abdul zai Aura wannan zab'ina ne kuma babu Wanda ya isa ya hana Abdul ka sameni a d'akina yanzunnan"
Cikin girmamawa Abdul yace "to" tashi yayi yabi daddy mommy ma mikewa tayi Tabi bayansu lab'ewa tayi abakin kofa tana jiyo me zasuce Daddy ne yayi gyaran murya yakalli Abdul yace "Abdulkareem" Abdul ya amsa tareda gyara zamanshi Dan yad'an idan Daddy yakira sunanshi complete to akwai magana mai muhimmanci Daddy yace "AbdulKareem inaso ka nutsuwa ka saurari abinda zan fad'a maka naga yarinyar nan Fadila? To itace nakeso ka Aura tazame maka uwar 'ya'yanka banyi niyan had'aka Aure da Fadila yanzu ba nafison saika fara Sonta da kanka Amma ina mahaifiyarka tana Neman hargitsamin gida ta hangar zargi kuma duk inda zargi yake to akwai Matsala"
Mommy dake lab'e takasa tsayuwa shiga d'akin tayi tace "wallahi bazai yiwuba bazai aureta ba idan kuma ya aureta babu shakka zan d'aga mishi Nono"
Tana fad'an haka tafice a d'akin fufu sai d'akin Baby tana zuwa ta janyo Fadila wacce takeshan juice a cup kasa ta fad'o a hankali tasaki wani siririn kara Dan kafarta ya bugu sosai, da masifa Mommy tace "kifad'amin bokan da kika ai sunan mijina da 'ya'yana inje ya karya asirin dayayi"
Kuma Fadila takeyi cikin shesheka tace "mommy wallahi ban tab'a zuwa wurin malami bama balle boka, ki yadda dani"
Mommy kanta take har tsakiyan falo Baby tana wanna jikinta da kunfa haka ta d'aura towel tafito daga toilet d'in tana kiran Mommy, amma ina mommy sai Jan Fadila take wai dole saita bar gidan yanzu ma kuwa, Daddy da Abdul ne suka zo da gudu ganin yanda mommy takeyi kamar zata kashe 'year mutane, Abdul ne ya janye Fadila daga jikin mommy ita kuma fadila a tsorace ta rungumeshi tana kallonshi mommy jikinta sai rawa yake kamar mazari bakinta ma rawa yake gefe d'aya ba zazzab'in d'aya kamata karo d'aya, Abdul sai kara matseta yayi a jikinshi yana duba jikinta wai kotaji ciwo, bakinta yagani kamar yana mini da sauri ya d'ago kanta ya Kallon bakin hanki yaciro yafara goge mata d'ana janyeta yayi yana son dubata da kyau da sauri ta fizgoshi jikinta tana kara shiga jikinshi sosai ganin mommy ta yunkuro kamar zata daketa tayi mugun tsorata, Abdul ganin haka tasa ya kyaleta bai kuma ce komai ba, Daddy ne ya Nina mommy da yatsa yace "idan tabar gidan nan kema zakibar gidan a yau d'innan"
Mommy tace "sai me Dan nabar gidan ai inada kyaun da ko yanzu ka sakeni zan zamu ma Auri"
Wani kishi ne ya tokare Wuhan Daddy wato zancen wanima takeyi tanada Aurenshi? Mari ya d'auketa dashi yace "idan zaki yi magana kirika taunawa kafin kifad'eta da aurena kikemin maganar wani kato?"
Itama da masifa tace "Nima ai da aurena kakemin maganar wata" Baby durkusawa tayi a wurin Dan hajijiya takeji hayaniyar yayi mata yawa momy tafiye Neman rigima, Mommy tace "India ina gidannan bazai Aure yarinyar nan ba idan kuma ya aureta zan tsine mi..." da gudu Baby tamike ta iso wurin momy tareda rufe mata baki da hannunta tana zazzaro Ido, tunkud'eta mommy tayi baya baya tayi tazube akasa, Daddy yace "shikenan tunda bakyaso ya aureta ni zan Aureta ni ai baki isa ki tsinemin ba idan baki sota a suruka ba zaki sota a kishiya Dan haka kizab'a nanda sati d'aya SURUKA KO KISHIYA"
Fita yayi a d'akin mommy ta durkusa kasa ta tsala wani uban ihu kamar karamar yarinya saida suka toshe kunnensu gaba d'aya, Baby ce tazo wurin tana bata hakuri tureta tayi da karfi tace "Matsa anan munafuka duk ba kece kina janyo hakan ba? Wayyo sun kasheni na shiga uku na lalace" wannan karon Fadila ma ta girgiza sosai tayaya zatayi Aure a wannan family d'in bacin basu Santa ba bata sansu ba, gashi kuma bazata iya tsallake maganar daddy ba sabida shine uba yanzu a wurinta shine yad'au duk wani d'awainiyanta tayaya ma zata aureshi? Kuka ne ya kwace mata a hankali take zubda hawayenta masu d'umi akan kirjin Abdul, Kallonta yayi ganin tana kuka yasa tabashi tausayi share mata hawayen yayi sannan yacireta a jikinshi domin shima yana bukatar ya keb'anci yayi kukan shi, a halin yanzu yana bukatar kuma, d'aki yanufa yafad'a kan makeken gadonshi kashe wutar d'akin yayi yaja blanket yarufe kanshi a hankali yarufe kyawawan idanunshi saiga hawaye yanabin kumatunshi tun yana hawaye harya fara kuka filo yajawo ya rungume sosai Daddy yana Neman yajaza mishi aiki ya tabbata idan ya auri Fadila yayi rashin adalci yayi zalinci, gashi babu mafita da muryan kula yace "na cuceki ki yafemin Dan Allah" kuka yake mecin rai har saida yaji numfashinshi na Neman d'aukewa kafin ya dakata tareda kankame jikinshi ya runtse idanunshi yayi shiru a haka dai bacci ya d'aukeshi, b'angaren Fadila kam kuka take na fitan hayyaci sai yanzu take kara kewan iyayenta sai yanzu taji tsanar kanwarta ya kara wanzuwa acikin zuciyarta sai yanzu takeji data kashe Amrah da komai zaizo mata da sauki a rayuwarta koba komai idan Ta Tunata zatayi mata addu'a, "kaicon ki Amrah kaiconki kin cuci rayuwar 'yar uwarki gudan jininki wacce take sonki fiyeda kanta, Baby kuma tana can wurin momy tana lallashinta ganin momy ba kulata zatayi ba yasata mike taje korido had'e kanta tayi da gwiwa Dan itama tana bukatar yin kuka a wannan lokacin soyayyar Yarima yana d'awainya da zuciyarta gashi tana ganin sonshi a idanun Adda Fadila wacce ta taimaka mata a Rayuwarta, kuka takeyi na rashin mafita, Daddy yana fita yawuce sama d'akinshi ya shiga ya kwanta Dan kanshi har sarawa yake Hauwa tana Neman tasashi a matsala had'a kanshi yayi da filo yana sauke numfashi a hankali,
Mommy kuka takeyi tarasa yaya zatayi Fadila tazame mata K'ARFEN K'AFA gashi dady yanason tarwatsa mata zuciya.
"Amrah zaune take akan sallaya ta d'aga hannayenta biyu Tana kuka tace