Showing 30001 words to 33000 words out of 151781 words

Chapter 11 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2643

zama dasu? "karka wani samu? damuwa wannan abu ne mai kyau Allah yasa hakan ya zama alkhairi maryama bazata ki zama tare da mahaifiyarka ba ."



Yaji dadi sosai daman kuma yayi masu kyakkwan zato yasan bazasu ce a'a ba "cikin 'ya'yan gidan nan kaf Allah yayiwa mryama baiwar hakuri kuma yayi mata baiwar ilimi da? hankali da nutsuwa, zakayi mamaki yadda zata zauna lafiya da mahaifiyarka ,da ba dan kar na baka labarin irin rayuwar data fuskanta da irin qaddarorin da suka fuskanceta cikin ikon Allah ta cinye jarrabawarta ba ,to zaka d'auka ko dan maryama tana tawa ce yasa haka, amman gashi tsananin hakurin datayi yasa taga karshen komai? wa ma zai ce ta taba fuskantar matsi da Kunci maka mancin wanda ta tsinci kanta "basani ba kota fad'a maka wanda ta fara aure ?mr ata yayi shiru yana dubanta a tsanake yana saurronta "d'an cikina? maryama ta aura ?"kana ganin idan bansan nagartata ba duk yadda suke dashi? zan yarda ne ?"amman hasalima nice da kaina na had'a auren saboda kyawawan hala??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????iyanta amman dake auren ba mai daurewa bane Allah ya kar'bi abunsa dubanta kawai yake kafin ahankali yace "Allah ya jikinsa !"ya fad'a? a fili yayinda a boye yace "ai mutuwarsa Itace alkhairi arayuwata daman sai wani ya rasa? wani yake samu ." "ameen !"umma ta amsa tana sauke numfashi ."


Suna zaune suna tautauna yadda zuwansu baba babba zai kasance a gobe maryama ta shigo sanye cikin dogon hijab har kasa kawai taga mutun zaune ,ta tsura masa ido tana kallonsa da mamaki akan fuskarta ,yayi kyau sosai cikin shigar? da yayi ,shima ya d'ago ya kalleta sai daya ji wani abu ya caki zuciyarsa ,ahankali ta d'auke idanunta akanshi tana gaishesa"yallabai barka da zuwa" mr ata yana jinta yayi mata banza ."ta d'an juyo ta kallesa jin bai amsa ba taga idanunshi baya kanta yana kallon wayarsa ne yayinda? fuskarsa a d'aure, maryama ta d'an tsorata amman ta danne tsoron da taji ta kalli umma "sannu da gida umma!" yauwa maryama sannu da zuwa ya firddausi take ?"tana lafiya tace a gaisheki ,ina amsawa firdausi amarya maryama ta d'an ja tsaki tana cewa "nifa umma ina ganin bazan iya kwawance nan ba dan bazan iya fita kullum ba ,gashi wai sai anje wajen agwane a ajibose bazan iya ba gsky ba ."
umma tai murmushi tana duban adamcy dake zaune yana sauraronsu dan tasan za'a rina karshe bazata yi ba ."sai dai bata ce mata komai ba ."
"Ina yini yallabai ?"ta sake gaishesa "lafiya !"ya amsa atakaice maryama tayi shiru tana tunanin laifin me kuma tayi masa daya canza mata ya wani had'e rai kamar yaga mutuwarsa har ma zai zo gidansu batare daya kirata ya sanar daita zai zo ba sannan yazo yana wani cika yana batsewa ".



umma dai bata ce komai ba ta zuba masu ido sai dai ta lura yanayin maryama kamar bata so zuwansa ba,shima kuma yayinsa ya nuna bai ji dadin fitar da tayi ba ,jiki a sanyaye ta nufi? d'akinta ."ahankali ta cire hijab dinta ta ninke ta zauna abakin gado tai shiru idanunta na kokarin zubar da hawaye tayi saurin gogewa ita kam wannan? halin nasa yana matukar damunta dan dai Allah yasa tana da dauriya ne, data yarda ta bayyana? masa yadda take son shi da bata san irin wulakancin da zata sha a hannunsa ba a yanzu ma da shine yake bukatarta yana mata iskancin daya ga dama Ina ga ita ke bibiyarsa ."shi kam mr ata bayan ya kar'bi number baba gali tashi yayi bai nemi maryama ba yyiwa umma sallama? ya wuce .sosai maryama taso tasan me ya kawosa dan har dare tana tunanin umma zata yi mata magana akan zuwan? shi amman ta share ta kasa hakuri ta tambayeta "umma wai zuwan me mr ata yayi d'azu?" umma tace" babu komai zuwa yayi mu gaisa "gaisawa kuma umma "?eh mana? ko akwai wani laifi ne ?"aa "!maryama ta fad'a tana girgiza mata kai sai dai tai tsai da ranta tana tunani dan a lissafinta ya kwana biyu bai kirata ba gashi yau yazo yayi mata banza "to ke me zai dameki tunda Allah ya saukaka miki idan ma fasa aurenki yayi ai kin huta ,amman kuma ya zakiyi da son shi da sharadin yan'uwansa har washegari ranar laraba mr ata bai nemeta ba canji da mr ata yayi mata shi ya kara d'aga mata hankali ya kusan haukatata dan gabad'aya ta gama amincewa zuciyarta ta rasa shi ."

******
A yau? ne su baba babba zasu? samu ganawa? da baba gali tare da malam mustapha a babban masallacin malam mustapha dake kan sabon titin agege had'add'un motoci? jeep guda biyu tare da motocin masu tsaronsu guda hud'u wad'an da daman sun san unguwarsu maryama mr ata ya had'asu dasu ,karfe d'aya daidai suka baro estate dinsu mota d'aya baba babba ne tare prof lawan shu'aib aminin mahaifin mr ata yayinda d'ayar motar baba k'aramin ne tare da uncle jay zaune aciki sai motocin masu tsaro biyu a gaba biyu abayan da jiniya suka karaso unguwar diribobin suka yi parking a gafen titi inda mutanen unguwar suka zubawa motaocin ido suna kallon jami'an tsaronsa dake cike da kowannesu rike da bindiga .kai tsaye? baba babba ya soma neman number baba gali, daga baba k'aramin har baba babba da uncle jay har ma prof lawan zance zuci suke acikin ransu da mamakin a irin unguwar da adamcy ya kawosu nema masa? aure wata hargi tsatsiyar unguwa,mai cike da adarawa kala kala? da 'yan cirani iri iri da 'yan sikiraf, shi kam prof lawan kasa hakuri yayi yace "kaddara aure kenan babu inda bata kai bawa,shi kuma adamcy duk tarin ya'yan manya mutane dake cikin kasar nan birjiki bai ga wacce tayi masa ba sai anan kaddararsa take ?"


numfashi baba babba ya sauke kawai dan bai san ma me zai ce ba sai dai ya shiga cikin wani yanayi mai tsarkakkiya babu abinda yazo zuciyarsa kamar nuzlarsa yadda tai kulafucin son shi haka ma hindu wacce har yauzu tana mutuwar son shi dan ko bayan fitowarta daga kurku sai data samesa da maganar ya shiga cikin lamarin sai dai? hakuri ya bata tare da bata misali da nuzla da yana da wannna karfin ikon to tabbas da tun lokacin da nuzla ta haukace akanshi ya dace ya bashi umarnin ya aureta .""ubangiji yasa albarka "!prof? lawan ya fad'a yana jinjina kai baba babba ya amsa da"ameen !"daga haka bai k'ara cewa komai? ba ya kai hannunsa baki yana shafa farin gemunsa batare da 'bata lokaci ba baba gali ya turo ataho dasu suka fito a natse kowannensu cikin shiga ta alfarma suna taku ahankali kallo d'aya zaka masu ka tabbatar da cewa wad'an din? manya mutane ne ."
baba gali dake tsaye a bakin massalaci cikin tsananin tashin hankali da firgici tsayuwar jiran karasowarsu tun daga nesa yake kallonsu tare da yaron daya tura idanunshi ya zuba masu gaba d'aya kwakwaluwarsa motsin kirki bayayi tun kafin su Kai ga karasowa inda yake ya tabbatar da lallai ba komai yasa maryama tayi wannan babban kumun ba sai hasaadar da suke mata hawaye ne ya cika idanunshi yayi saurin daukewa? ahankali suka karaso yayinda jami'an tsaron ke biye dasu ."


a mutunce ya kar'besu yana cewa "sannuku da zuwa ku biyuni ya fad'a yana juyawa da sauri sauran kad'an yayi tuntu'be dan jikinsa har rawa yake suka biyo bayansa a natse? Inda kowannen su ganin yake kamar a mafarki ne wai auren adam shararren d'an kasuwan nan da kasa da duniya tasan da zamansa? ne suka zo nema acikin unguwr irin nan kuma a massalaci irin wannan abun kamar almara , amman lamarin ubangiji kenan yafi gaban haka waje suka samu suka zauna ,doguwar gaisuwa suka yi fuskar malam mustapha cike da annuri yayinda fuskar baba gali take cike da matsanancin tashin hankali haka ma baba k'aramin zuciyarsa kuna take ganin Inda adamcy ya kawosu bayan sun gama gaisawa? suka fara da abinda ya kawosu wato nemawa d'ansu auren diyarsu maryama "baba gali ya fara magana "ni yayan? mahaifinta ne uwa d'aya uba d'aya na baku auren maryma sai dai wani hanzari ba guda ba maryama fa ta ta'ba aure kuna ganin babu wata matsala "eh to mu bamu san da wannan zance ba? amman bari mu kira shi yaron muji ko yasan da zaman haka ."baba babba ya fad'a tare da ciro wayarsa ya soma kokarin Neman number adamcy kira d'aya ya d'aga yana gaishesa? baba babba ya amsa sannan ya saka wayar a handsfree ta yadda kowa zai ji "adam gamu mun samu karasowa, gamu tare da yayan mahaifinta sai dai yayi wata magana ko kasan da zaman yarinyar ta ta'ba aure ?"adamcy yayi shiru zuciyarsa na dokawa da sauri sauri sai dai yayi matukar mamakin jin abinda yayan mahaifin maryama yayi to ma me kawo wannan maganar,?"adam kana jin kuwa ?"ina jinka baba maryama ko aure dubu tayi ina son aurenta haka "."




Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
? ?? MAR'ADAMS
? ?? =ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan? 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


? ? ? ? Page 7


baba babba yana gama jin abinda adamcy ya fad'a ya dubi baba gali a tsanake? sannan ya maida hankalin sa ga wayar da yake yace"shikenan idan mun gama zan kiraka" adamcy yace "tom!"ka ji abinda yaro yace da alamun yasan da zaman komai sai muyi fatan Allah yasa albarka, ai auren bazawara ba wani abun aibu bane yana daga cikin baiwa ta mussaman matukar zata tsare mutuncinta tasan ciwon kanta ai shikenan ." "wannan haka ne maryama kam yarinyar kirki ce wacce ta tsare mutuncin kanta ga hankali ." "Dan tana da hankalin da wata budurwa bata dashi nasan shi d'an naku shi yasan abinda ya gani atattare daita da har ya zabeta ta zamo abokiyar rayuwarsa ."inji cewar malam mustapha ."
murmushi baba babba yayi" yadda kuke da tabbas akan yarinyarku haka d'anmu adam yake domin kuwa Allah yayi masa baiwa iri iri cikin farinciki sukai murmushi hannuyensu damke da juna da malam mustapha baba gali kam zuciyarsa kamar ta buga tsabar bakinciki yaso ne lokacin daya fad'a masu ta ta'ba aure daga nan komai ya rushe sai gashi abun yazo masa da bazata "ganin baba gali bai da niyyar basu ruwan? sha yasa malam mustapha ya janyo katon din ruwan roba ya soma zarowa yana ? ajiye ma kowa a gabansa."


Baba babba yace "mun gode idan zai yuwu yaron yana son a d'aura auren a lahadi ta sama "ji baba gali yayi kamar ya mutu a gurin domin kuwa da zarar an d'aura auren shikenan ta faru ta kare basu da wani sauran dabara amman dai zai nemi su d'an daga masu kafa ko nan da wata biyu ne masu zuwa alabashi kafin zuwa wannna lokacin salma tayi nasarar ruguza komai sai dai kafin yayi hanzarin yin magana ya tsinkayo dariyar malam mustapha tare da cewa "ai tunda mun bada auren maryama ga adam aure kam za'a d'aura shi in sha allahu Allah ya kai mu lahadi ta sama ,Allah kuma ya tabbatar mana da alkhairi yasa muna raye za'ayi wannan auren Allah yasa auren ya zamo abun alfahari da farinciki wa zuriarku ".Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun baba gali ya shiga furtawa daga zaunen da yake ."amman dai malam mustapha da karambani tsiya yake wannan zakewa haka kamar shine shakikinta?"
maimakon ya zuba ido ya barshi yayi magana akan komai amman sai wani zakewa yake yana bare bare da rawar kai ."ameen ya hayyu ya qayyum cikin farinciki mutane dake zaune a wajen suke amsawa sannan suka ajiye wata takarda mai ruwan kasa a gabansu ".


baba babba tsaf ya fahimci baba gali kamar akwai hassada atare dashi dan a zahiri ake iya hango tarin bakincikinsa wanda Ke nuna alamun bai so faruwar wannan abun alkhairin ba ."a natse suka mikawa juna hannu sukai musabaha sannan sukai sallama baba babba ya kai hannu ya d'auki roban ruwan da'aka ajiye masa wanda hakan yasa suma sauran suka d'auka suka rike har bakin inda motocinsu suke pake? suka rakasu ."fuskar? baba gali babu yabo babu fallasa ya kalli malam mustapha dake tsaye kusa dashi yace "kai malam mustapha haka akeyi ?"da mamaki malam mustapha ya tsaya yana kallonsa "kasani ko mu a shirye muke daga jin sunce a d'aura aure ranar lahadi ta sama sai kayi tsigil ka amince halan kai zaka yi mata kayan d'aki da sauran abubuwa ?"da wani sabon mamaki malam mustapha yake dubansa sai dai yace "ayya kayi hakuri malam gali na maka shishshigi ashe ?sai dai ina mai baka hakuri tare da neman yafiya amman na d'auka kai ma hajiya tai maka bayanin komai akan batun zuwansu da kuma bukatarsu kamar yadda ta min amman dai kayi ..."fuuuuuu baba gali ya wucesa tare da karya kwana ya nufi hanyar gida hankalinsa a matukar tashe batare daya tsaya ya karasa jin abinda malam mustapha zai fad'a ba " .



Tafiya kawai yake yana surutu "ko ya salma zata yi? da rayuwarta dan tun shekaranjiya da taji batun auren nan bata sake kwantar da hankalinta ba ."?yanzu haka bata gida tun safe data fita bata dawo ba bai san inda ta nufa ba ."cike da matsanancin tashin hankali ya shigo gidan kai tsaye bangaren umma ya shiga ya samu waje ya zauna akan kujera yana mata bayanin yadda sukai da iyayen adam sannan ya mika mata takarda da suka kawo yace "kudin wata kasa ne masu yawa sosai sai dai ban san ko na wace kasa bane ga shin nan na gaisuwar iyaye ne "umma tasa ta kar'ba ta d'an bud'e ciki tace "masha Allah lallai maryama tayi kai kudi ne kuwa masu yawa nima ban san ko kudin wace kasa bane hakika yau muna cikin tsananin farinciki domin kuwa abun farinciki ya samemu Alhamdulillah Alhamdulillah umma ke jerowa tana taka rawa gabad'aya ta kasa zama waje d'aya saboda tsananin farinciki." maryma kinyi hakuri kin sha wuya yau ga irin kyakkwan sakayyar da Allah yayi miki ,gali bari naje gurin auntynta kai ma dan Allah ka kira 'yan'uwanka ka sanar masu abun alkhairin daya same mu ."maryama dake zauen a d'akinta tun awanin biyu tana zaune tana zana fuskar mr ata da shigar da ya zo daita? jiya ta jiyo maganar umma komai data fad'a ya samu kyakkwan mazauni acikin kwakwaluwarta"maryma kinyi hakuri kin sha wuya yau ga irin kyakkwan sakayyar da Allah yayi miki ta sake maimaitawa kanta? maganr "to me hakan yake nufi ?"meke faruwa a gidan nan nasu ?"


Ta yunkura ta mike tsaye ta yaye labulen d'akinta ta fito zuwa parlour'n adaidai lokacin da baba gali ya mike tsaye jiki a sanyaye ya nufi kofar fita itama umma? ta biyo bayansa tare da janyo kofa maryama tayi turus tana kallon parlour'n tare da kamo yatsun hannunta tana murzawa tana tunanin abinda ya faru da har taji umma tana magana cikin tsananin murna da farinciki ,ahankali ta kai hannunta ta d'an tsutsa gefen kanta hakan nan ta tsinci kanta da jin fad'uwar gaba mai tsanani ,ta zauna akan hannun kujera tana cigaba da jin bugun zuciyarta."kusan tare umma suka jera da baba gali ya shige part dinsa ita kuma ta shiga wajen aunty fuskarta cike da tsananin farinciki mara misaltuwa ta bud'e takardar da kudin suke ciki? ta nunawa aunty "ga kudin da iyayen adam suka kawo na gaisuwar iyaye ".shiru aunty tayi tana kallon kudin domin kuwa bandir din pound's ne har guda uku acikin takardar bata san sanda hawayen farinciki ya soma gangaro mata ba" yaushe rabon tasa kudin a idanunta ?"bazata manta ba tun zamanin da take cikin gatanta da'ake kwasarsu zuwa England yawon bud'e ido daman zata sake tsintar rayuwarta haka ?"umma ta rungumota ajikinta tana cewa "bazan ce ki daina? kuka ba bilkisu domin kuwa nasan na farinciki ne kinga yadda Allah yake ikonsa ko? ".kinga yadda jinkiri ya zame mana alkhairi ko "?



naunauyen ajiyar zuciya aunty ta sauke alokcin data tuno matsalar da suke fuskanta a duk lokacin da mgnar auren maryama ya gabato ,muryarta na rawa tace "umma mu daina murnar nan? haka mu bari muga d'aurin aure wallahi zuciyata rawa take Ina cike da matsanancin tsoro da farinciki tsorona kar wani abu ya biyo baya duk da na dogara da Allah kuma kullum shi nake kaiwa kukana"ki kwantar da hankalinki bilkisu babu abinda zai faru khairan in sha allahu."aunty ta sake rungume umma ajikinta tana zubar da hawaye umma ta kai hannunta tana shafa bayanta tana rarrashinta tare da fad'a mata kalaima masu kwantar da hankali ,karki karaya da izinin allah aure kam za'ayi sa har ma sai munga jikoki alfarma manzon allah, bilkisu muna da kyakkywan zuciya ba mu kasamce azzalamai ba kuma mun dogara da allah duk wanda yace Allah to wallahi Allah ya isar masa muyi fata alkhairi da addua kawai Allah yasa auren ya zame mana alkhairi duniya da lahira in sha allahu zaayi auren nan ta fad'a tana zareta jikinta ta mika mana kudin ."aunty ta girgiza mata kai tana cewa "aa ki barsu a hannunki ai kudinku ne !"umma tai mur mushi tana dubanta shiyasa a kullum maryama ke sake shiga ranta bayan kyatatawar da maryama? take mata aunty ma na mata al kunya akanta tana nuna mata cewar maryama din diyar ce halak malak ."
"shikenan Allah yasa albarka ta fad'a tare da fitowa ta nufi bangarenta cike da murna ."


Aparlour'n umma ta iske maryama tsaye ta kamota ta rungumeta tsam ajikinta"yar albarka kinyi goshi wahalarki tazo karshe maryama yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa ta zareta ajikinta ta riko hannunta ta zaunar daita tana kallonta kamar wata sabuwar halitta ."maryama tace "umma naji kamr kuna maganr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login