Showing 120001 words to 123000 words out of 151781 words

Chapter 41 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2675

ya koshi daita ba ."
bai barta ta goge kasanta ba ya makaleta yana shafa bayanta "sannu na gode sosai Allah yayi miki albarka"ai jin furucin dake fita daga bakinsa yasa taji wani sanyi ya mamayeta taji duk wani radadi da take ji alokcin ya kau domin bata ta'ba expecting zai furta hakan ba ta sake shige masa tana makale ajikinsa bacci ya d'auketa har kusan karfe takwas da rabi bata motsa ba saboda gajiya ya gyara mata kwanciya ya sauko ya shiga d'akin motsa jiki bai fito ba sai wajen karfe goma ya sha wam water da zuma sannna ya dawo d'akin har lokacin bata tashi ba wanda kusan adaidai wannan lokacin tuni ta tashi ta had'a masa abun kari bai tasheta ba ya shiga wanka byn ya fito ya hada tea da kansa dan baya son yayiwa mami magana ta fad'a masa bakar magana ya kunnan TV yana shan tea yana kallo dan bazai fita zuwa koina ba saboda da tafiyar da zai yi zuwa uk ya haura kan bed din inda maryama take kwance ya janyota jikinsa ya kwantar daita kan fadadden kirjinsa yana shafa sumar kanta wani irin zafi yaji yana fita daga jikinta 'ckin bacci ta rungumeshi tare da shigewa jikinsa tana mika ".

Ahankali ya kai bakinsa kunnenta "dadina jikinki zafi lumshe idanunta tayi tana jin wani irin kasala dan gabadaya ilahirin gabobin jikinta ciwo suke mata yayinda kasanta ke mata wani irin radadi mai had'e da dadi dadi .ahankali ta bude idanunta gbdy ta kai ga agogon dake manne da bangon d'akin karfe goma shabiyu saura ta gani dan haka atsorace ta zabura zata mike tsaye ya maidaita jikinsa yana cewa "Ina zuwa kuma ?"zanje na had'a maka breakfast" tai maganar cike da shagwa'ba"Ina maganar jikinki yayi zafi kina maganar wani breakfast hannunta ta kai daidai wuyanta taji zafi sosai numfashi ta sauke tace "wallahi bana jin zazzabi sai dai kasala kasala nake ji amman may be dan.."sai kuma tayi shiru ta kasa k'arasa maganr "dan me !?share nasan zuwa anjima zan dawo normal sarai ya fahimci abinda take nufi" ko dai zafin shigar ciki ne !?"ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanun shi haba yalla'bai wani irin ciki wai haka ake samun cikin da sauki ne?"sosai kuwa tunda kin had'u da cikakken namiji ,to bani dashi "ni naji ajikina tun aranar farko kin d'auka"ya fad'a yana shafa mararta "karki yarda ki sha kowani irin magani batare da izinina ba har naje na dawo ". tace "angama yalla'bai "no no!! acire min sunan nan bana so ,to shikenan naji zumana yace "woww sunan yayi min sosai a cigaba da kirana dashi ".ya fad'a yana kissing din foreign head dinta ."

Tsayawa tayi shiru tana kallonsa a duk sanda ta ga yana mata abubuwa haka mamaki yake bata sai ta dinga ganin kamar bashi bane "ya'akayi!? Ya tambayeta yana matseta numfashi ta sauke da karfi tace"wasu lokutan sai na dinga ganin kamar mafarki nake "kamar bani ba ko ?"tayi murmushi tana kai hannunta daidai idanunta ta shafa "Ina sonki ne sosai, na sameki da wahala ba kuma zan yarda nayi sakaci ba"bari naje na had'a maka breakfast ta zare jikinta ta sauko ta sanya doguwar riga tare da k'aramin hijab ta sauko zuwa downstairs kitchen ta shiga ta soma had'a breakfast sai dai yau din ma batayi mamakin yadda masu aikin suka zuba mata ido batare da Sun Kama mata komai ba tana tsaye a kitchen din ya sauko ya shigo yaga tana ta faman aiki ita kad'ai amman masu aiki na tsaye suna kallonta ganinsa yasa suka soma k'ok'arin ficewa daga kitchen din ,ya karaso yayi hugging dinta ta baya ya sumbaci wuyanta yana cewa "sannu da aiki dadina mai yasa bakya barin sun dinga kama miki aiki ?"da fari suna kokarin taimaka min daga baya kuma naga sun daina to ma aikin guda nawa ne zanyi abuna "okay yanzu mai zan kama miki "no no!! ba sai ka kamin komai ba zan iya ." " aa ai bana son ki gaji dayawa ne bare ki wahalar min da kanki dan may be anjima zan kara kafin na wuce apart that ma bai kamata abarki ke kad'ai kina aiki haka ba bari na kama miki muyi tare ."

Murmushi kawai tayi ta cigaba da aikinta ahkl taji ya turo hannuwansa duka cikin rigarta sai jin saukarsu tayi akan breast dinta "wani irin ajiyar zuciya ta sauke da karfi tare da tsayawa cak ta kasa cigaba da aikinta tana lumshe idanunta dan sakonsa ya kai inda ake so ,ta d'an waigo kad'an ta kallesa duk jikinta yayi sanyi "why !"ta fad'a tana jin tsigar jikjnta na tashi "me nayi aiki fa zan tayaki "?haka ake taya mutun aiki?"tayi magana kamar zatayi kuka

ya kashe mata idonsa d'aya yana murza kan nipples dinta wani zazzafan num fashi ta sauke "ni dai idan ba so kake na kona kaina ba ka barni naji da aikina maganarta bai sa ya cire hannun sa ba tana aiki yana makale daita suna hira cikin nishad'i duk abinda suke idanun mami wacce ta fito yana kansu aiko nan take taji kamar an caka mata mashi ne a kahon zuciya irin kyakkyawar rayuwar data so yayi da maryam dinta kenan amman dake shi din d'an ra'ayi ne yaki dogon tsaki taja ta samu waje ta zauna tana jijiga kafa tare da had'e fuska ".ya tsurawa maryama dake tsaye a gabansa idanu wacce zuwa lokacin ta jan ye jikinta " dadina kin gaji da yawa hau bayana na goyaki ki d'an huta ni kuma na k'arasa miki aikin ."

"ka rufa min asiri a ganka kana min aiki ai sai maganar ina biye biyen malam ya tabbata "to shi kenan hau sai ki d'an huta daga baya sai ki cigaba wannan ai hutun jaki da kaya akai kake son nayi ya matsota sosai yana riko kugunta "zumana ka bari nayi aikina ,no ki hau kawai ina son na jiki a bayana. "murmushi tayi har wushiyarta ta bayya na ita dai taga ta kainta ta auri karuwan namiji dogon tsaki mami ta sak? taja wanda yasa ya d'an juyo ya ganta tana daf da juyar da kanta bai wani damu ba ya cigaba da abubuwansa sai data gama ya fito ya tsare tabawa da tambaya"akan wani dalili ne yasa bazaku taya matata aiki ba ?"gbdy suka maida kallonsu ga mami alamun itace ta hanasu"a natse shima ya kalleta yana had'e fuska Wanda yasa masu aikin sukai sun sun suka bar wajen bayan sun bar gurin yace"why sweetheart!"mai yasa wannan fa ba girmanki bane "matarka ce fa abincin da zata girka maka ne wani aikin da sai antayata ?"duk da haka ai za'a iya taimaka mata dan Allah na rokeki alfarmar ki dinga barin suna taimaka mata ya k'arasa maganr adaidai lokacin da kira ya shigo wayarsa ya nufi kofar fita amsa kiran adaidai lokacin da mami tace "aure tazo yi ba ba zaman jin dadi ba ".

koda maryama ta gama aikinta ta fito bata gansa ba hassalima babu kowa a parlour'n dan haka ta koma sama anan ma bata gansa ba ta shige wanka kawai bayan ta fito ta shirya cikin dogu war riga tayi roling din kanta ta zauna shiru duk ilahirin jikinta a sanyaye sai dai duk ta Inda ta motsa sai taji feelings din hannun mijinta a sansar jikinta ta dan dade zaune kafin ta farga lokacin yin breakfast yana wucewa ta mike tsaye a hankali taji jikinta duk ya jike numfashi ta sauke tace "wannna mutumin ala dole sai ya maidani irinsa kai tsaye ta shiga bayi ta cire part dinta wani ruwa ta gani ta d'an tsaya shr tana kallo ruwan wanda ya tabbatar mata da ruwan sha'awa ne.tayi tsarki da ruwan dumi sannan ta fito ta canza wani pant ta fito a parlour suka had'u dashi sanye cikin kananan kaya yayi kyau sosai hanunta ya kamo cikin nashi suka jera Zuwa kasa wanda a daidai lokacin mami ta hallara akan dining table tana break suna daf da karasowa ta zare hannunta cikin nashi jikinta a sanyaye ta soma kokarin karasowa gurin shima adamcy ya karaso ya zauna tare da sak? gaishe da mami babu laifi ta sakarwa d'anta fuska sun gaisa,Cikin sanyi jiki da sanyi murya mai kashe zuciyar ma'abocin sauraro maryama tace"mami an tashi lfy ?"da kyar ta amsa mata batare data kalli inda take ba bayan sun gama breakfast suka koma sama ,jikinta a matukar sanyaye take had'a masa abubuwansa masu mahimmanci da zai yi tafiya dasu inda shi kuma yake ta faman karfafa mata gwiwar ta kwantar da hankalinta ta daina damu wa da duk abinda mami zata yi ko nuna mata "ni nake aurenki kuma kinsan Ina sonki tunda Ina sonki me yasa zaki dinga damuwa "dole na dinga damuwa fa yan' uwanka da mahaifiyarka basa sona "wannan kuma matsalar su ce ni dai ki kwantar min da hankalinki tunda ni ina sonki duk wanda bai sonki matsalarsa ce "yanzu kwana nawa zakayi ?"just one week ne zanyi na dawo ."

Ahankali ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace "zanyi kewarka! bazaki kaini ba"ko zaka kai ni gurin umma nayi kwana biyu kafin ka dawo ?"ya janyota jikinsa ya makaleta "bazan kai ki koina ba kiyi zamanki sannan ki dinga karfafa zuciyarki ki kuma rage tsoro babu abinda zai faru duk inda nake Ina tare dake kusan yini sukai makale da juna suna shan soyayya ,karfe hud'u daidai ya shiga wanka bayan ya fito ya tsaya kawai yana kallonta "tace me ya faru ?" nothing Ina sonki sosai dadina,gani nake kamar nafi kowani namiji dace dana sameki arayuwata wani irin nishad'i taji ,ranta yayi mata dadi "Ina sonki dayawa uwa uba zanyi kewar kayan marmarina ta d'an harare sa tana cewa "wallahi kafiye rigima"! to ai gaskiya na fad'a zanyi kewarki da abubuwan nan ya fad'a yana kallon k'irjinta sunkuyar da kanta tayi "am saying it rom the bottom of my heart nafi ko wani namiji dacen samunki ya riko hannunta yana tafiya daita acikin d'akin suna manne suna cigaba da soyewa" ita dai cikakken namiji ta aura romantic wanda kowacce mace take da burin aure kasance warsa attajiri bai hanashi jiyar da iyalinsa dadin dake cikin aure ba tare da bata farinciki ba ,abinda batayi tsammanin samu daga garesa ba shi ta iske shiyasa aure dace ne wani lokacin zaka tsammaci jin dadi a gidan aure sai ka iske matsaloli "wallahi duk sai taji bata son yayi tafiyar ya barta."

ita shiryasa cikin hadadden sult blue black bayan ya gama shirinsa ya matsota kamar zai maidaita cikinsa "ni zan wuce !"ya fad'a yana kamo kuma tunta tare da sanya kwayar idanunshi cikin nata "Allah ya tsare Allah dawo min da kai lafiya dan Allah karka sha sigari har kaje ka dawo "zan sha kamar sau uku arana"ya fad'a yana had'e bakinsu waje d'aya ya d'auki kusan mintuna shabiyar yana tsotsan bakinta kamar zai cire ya wuce dashi sannan ya zare bakinsa cikin mawuyacin hali yace "muje ko !tare suka fita tana rike da wata yar karamar jakarsa shi kuma yana rike da karamar akwati a parlour'n ya ajiye akwatin hannunsa yace "muje nayi sallama da sweetheart kaje kawai zan jiranta anan bai matsa mata ba ya sa kai ita kuma ta tsaya jiran fitowarsa yayiwa mami sallama tai masa addua sosai da fatan alkhairi kamar babu abinda ke faruwa aparlour'n suka rabu byn yayi hugging dinta ta koma jikin window ta d'an yaye labulen tana kallonsa zagaye da masu tsaronsa idanunta cike da ruwan hawaye kamar ance ya kalli daidai gurin window ya hangota makale tana kallonsa suna had'a ido ta sakar masa murmushi shima murmushi yayi mata yana d'aga mata hannu yana jin kamar ya koma yace ta had'a kayanta su tafi tare itama hannu ta d'aga masa tana tsaye har sai data ga fitar jerin motocinsa sannan ta saki labulen ta koma sama cikin tsananin kewar mijinta ."


******
Wuni ranar shiru tayisa sosai tayi nisa cikin tsananin tunaninsa haka ta dinga lissafa a wanni a cewarsa five hour's zai Kai shi sai gashi har karfe shabiyu saura na dare bata ga shigowar kiransa ba sosai ta damu ta rasa abinda ke mata dadi abinci ma ta kasa ci numfashi kawai take fitarwa tana duba what's app dinta akai akai ko zata gansa online, karfe d'aya daidai sai ga kiran sa video call cike da natsuwa da zumudi ta d'aga muryarta a raunane alamun tayi kuka tai masa sallama " assalamu alaikum!"am sorry dadina !" taji sautin tautausan muryarsa ta doki dodon kunnenta"wani abu taji ya tsarga mata yana bin jijiyon jikinta ya sake kwnatar da muryar "wasu abubuwa ne suka d'an rikeni yasa bana online muryarta a raunane tace "to da fatan ka sauka lafiya?alhamdulillah nayi tunanin ko kinyi bacci?"muryarta cike da sheshekan kuka tace "na kasa bacci ! I really miss you Ina ta jin damuwa rashin ban taho dake ba nasan dole zaki damu bazaki samun natsuwa da kwanciyar hankali ba har sai kinji muryata "babu komai fa kawai dai naji hankalinta ya tashi sakama kon kace 5 hours zai kai ka sai gashi lokaci ya wuce sosai "that's means bakiyi kewata ba ?"nayi mana shiyasa hankalina y tashi "bakya son ki rasani ko ?" ta gyda masa kai tana sunkuyar da kanta."

"karki damu bazaki rasani ba Ina sonki sosai "nima haka !ya fahimci abinda nima hakan yake nufi sun dade suna video call sai faman zuba hamma take alamun tana jin baccin amman kuma bata son bacci ya d'auketa yace "kasa da alamun bacci kike ji ta lumshe masa idanunta tana d'an murmushi "ki kwanta mayi waya da safe kwana d'ayan da tayi batare dashi ba taji damuwa mai tsanani Allah bacci ma da kyar take yi sai tayita juyi a gado tana kamka me jikinta domin jikin yayi missing mahadinsa Allah Allah ta dinga yi ya dawo dan d'an kwana biyun da tayi baya nan ji tayi kamar an canzata zuwa wata halitta dabam ."bayan kwana biyu da tafiyarsa maryam ta duro nan da nan gidan ya hargitse ya'yan mami suka cika gidan taja kanta ,sai dai taje tayi mata sannu da zuwa, yadda tayi tunanin zata amasa mata babu yabo babu fallasa hakan ce ta faru sauran kam dama ko amsa gaisuwarta basu yi ba tayita kallon khaira kamar tasa hannu ta d'auketa sai dai ganin yadda maryam din ke kallonta ta kasa d'aukar ta yarinyar ta rarrafo zata zo gurinta maryam tayi saurin ta d'auketa ta riketa a hannu nta ,maryama bata wani damu ba ta share ta koma sama ."

Bayan kwana biyu da zuwan maryam mami ta tashi da zazzabi ita bata ma sani ba dan itama kusan zazzabin take ji da yawon tashin zuciya dan tun jiya data sauka bata sak? sauka ba sai da mami tayi kwana d'aya da yini sannan tasani shima data sauka ne taji abakin masu aiki aiko bata 'bata lokaci ba ta nufi bangarenta da salla marta ta shiga d'akin mami gabad'aya yaranta suna d'akin sai dai ita mami bacci take tayi jam'i wajen gaishesu zabiba ce kawai ta amsa mata tace "Aunty zabiba ya mai jiki ?"fuskarta a sak? tace" Alhamdulillah taji sauki" ta d'an matso zata k'arasa gaban gadon da mami take kwance aunty khadija tace"ke ke menene haka ina zaki ?" jikinta a sanyaye tace "zan duba mami ne" tace miki tana bukatar ki dubata ne wai ke mai uwar miji uwar mijin da batasan da zamanki ba idan baki sani ba zamanki a gidan nan yasa ta kamu da ciwo oya maza maza ki kama hanya ki ficewa mutane mai shegen shishingin tsiya ko dole sai kinyi shishigi ?"wani dan iskan ne ma ya fad'a mata ?"inji cewar aunty shahida maryama dai tayi shiru ta had'e hannuwanta waje d'aya tana sauraronsu sai dai kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana tattare da damuwa "wani d'an iskan ne zai fad'a mata daya wannan kwarton nata ."

da sauri maryama ta d'ago ta kalli aunty khadija wacce kalmar ta fito daga bakinta "yanzu dan rashin imani d'anuwanta zata kira da kwarto?" "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "mami tace bata sonki bata son ko kallon fuskarki zaki wuce ne ko kuwa sai na tsinka miki mari?" ta k'arasa maganr tana kai mata duka acikinta ji kake gif wani kara maryama ta saki mai sauti tana dafe cikinta nan da nan idanunta ya cika da kwalla "wallahi kafin na rufe idona na bud'e ki bar d'akin nan shegiyar yarinya duk ma wari take ta fad'a tana toshe hanci maryama ta tsaya sanyin jiki aiko sai tasss taji saukar mari a kuncinta "oya wuce ba'a son ganinki da sauri ta fice daga d'akin tana hawaye ta koma sama tana zama kiran adamcy ya shigo bata d'aga ba har kiran ya katse wani kiran ya sake shigowa tana kokarin goge hawayenta da had'iye kukanta ta d'aga tace "hello !"dad'ina "!ya kirata da wannan sunan tace "na'am!" lafiya me ke damunki meke faruwa !?yayi mata tambayr ajere cikin tsananin tashin hankali tace "babu komai "me ya sameki kike kuka?"babu komai kefa matsalata dake kenan komai kice babu komai alhalin akwai komai ni ba mijinki bane me yasa zan dinga tamabayarki abu ki dinga ce min babu komai ".?

tai shiru tana sheshekar kuka "idan ma baki fad'a min ba zan yi bincike na gano komai jin abinda ya fad'a tace "ka dawo pls mami bata da lafiya ta k'arasa maganr tana sheshekan kuka "to kuma shine kike kuka ?"tai shiru ki fad'a me ya faru kike kuka "kawai dai ganin yanayin jikin mami ne ya sani kuka" to karki damu in sha allahu zata samu lafiya ai jikin nata da sauki dan ma munyi waya d'azu da safe tai shiru tana sauraronsa "kenan ma yasan da rashin lafiyarta shine bai fad'a mata ba? kamar ance ta d'ago kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login