Showing 9001 words to 12000 words out of 151781 words

Chapter 4 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2648

dafo min ne a mota in sa a kawo min inci ?"ni kaje kaci abinci kuma ai kasan naka ne tunda Kai ne kace a dafa maka ?"k'aramin bakinta yabi da kallon? yadda take motsa shi ahankali kamar
bata so ,ko da yake da gani maganar ma a dole take yinta ."wani farin abu ya danna bayan kamar minti biyar akayi knocking ya tashi yaje ya bud'e kofa ,wani yaronsa ne tsaye cike da girmamawa "? "umar kaje bayan motar dana shigo dashi yanzu ka d'auko min? jakar abinci" da sauri umar ya juya ya barshi tsaye a bakin kofa tsayuwar? jiran dawowarsa bai jima ba ya sake dawowa cike da girmamawa ya mika masa ya amshi jakar abinci ya maida kofar ya rufe ya dawo ya zauna akan kujera ya d'aura jakar akan dining table yana dubanta ."



"dan Allah kayi sauri kaci muyi maganar da zamu yi dan dare ya fara bana son Ina yin dare a waje "baki yi min yadda zanji dadin cin abinci bane ".
ya fad'a tare da mikewa ya karaso inda take zaune ya kamo hannunta tayi hanzarin zata fizge hannunta yace "stop maryama kinsan banason kina hanani ta'ba abinda ya kusan zama halal dina "ai sai ka jira har lokacin yayi tukun bawai ka maidani? kamar wata sakariya ba "karki damu lokaci yayi "a ranta tace "idan wannan uwartaka ta bari ba ."wallahi na matsu naji na d'aura miki marata kiji..."ai tun kafin ya k'arasa maganar ta fixge hannunta tana hararrasa ya mike tsaye yana murmushin gefen baki "matsoraciya kawai ."
Wata hararar ta buga? masa "ki san ban ta'ba biyanki komai ba amman akan kallon nan naki mai sa ki? kara min? kyau karki sa a yanzu nace zan biya "wata hararar ta sake masa ".okay in zo na biya? kenan ?ya fad'a yana tahowa ai ko ta canza fuska? zatai masa kukan shagwaba? bai san sanda ya sake murmusawa ba "I really like all you maryama ya fad'a yana kashe mata idonsa d'aya sannan ya koma ya zauna kamar yadda yayi d'azu ."


A daidai wannan lokacin da mr ata yake zaune yake cin lafiyayyen kuskus din da maryama ta dafa mashi mami na can tare da yaranta suna tautaunawa akan waya "inda aunty khadija tace "mami ki barshi yayi auren sai ki kafa masa duk sharudd'anki idan kina dasu "haka ne khadija maganarki? tayi amman ni zan so mami tasa shi? ya maida maryam ya had'esu duka "inji cewar aunty shahida "anya shahida kina ganin hakan zai yuwu kuwa ?"mami ta fad'a cike da zullumi "zai yi mana a yadda ya matsu da yarinyar nan ai kina fad'a masa zai amince "to kina ganin ita maryam zata yarda ta koma masa ne dan kwata kwata banga alamun zata koma ba ?"idan dai zan bar shi kawai zan barsa yayi aurensa shikenan yayi galaba akaina "mami ta k'arasa maganar cike da rauni "ai mami halin adamcy ne sai shi inda kika san ba mutun ba "ki bar shi din yayi auren amman karki d'aga masa kafa idan ma da hali yarinyar ta tare agidanki duk abinda zaayi kina gani "kuna ganin haka yayi ace ta tare a cikin gidan nan alhalin akwai tarin gijaje muna dasu ?".


"aunty khadija da aunty shahida har ma da auta suka ce "haka ne kawai zai sa ki san halin da suke ciki akan zamansu dan kinsan yaran talakawan da shegen shige shige kar aje a mallake miki d'a abinda ya kamata ko auren zai yi yaje ya nemi yar gidan manyan mutane amman yaje zai kwaso mana jaraba."sarai zabiba? ta fahimcesu suna bawa mami shawarar ne dan su samu damar aiwatar da nufinsu akan yarinyar mutane ."
mami tace "to shikenan yanzu idan mun gama wayar nan zan kira maryam naji raayinta akan komawar ta "mami da dai kin? dakata da kiranta tukun har kuyi magana da shi? yaya adamcy kuji me zai ce ,dan a so samuna ne a hakura da auren nan ,kowa yaje yayi rayuwarsa kamar hakan zai fi mana kwanciyar hankali kar a sake komawa gidan jiya "haka ne zabiba kema kinzo da shawara mai kyau zan jirasa har sanda zai sake nemana da maganar dan bazan nemesa ba .""wannan yayi daidai mami karki nemesa ki barshi idan ya gaji zai kawo kansa ne "inji cewar zabiba daga nan ta masu sallama ta sauka ta barsu akan layi itama mami sallama tayi masu ta soma neman layin maryam dan taji lafiyar khaira kira d'aya tai mata ta d'aga tana gaisheta? .""maryam ya kuke ya khaira da fatan duk kuna lafiya ?"muna nan? lafiya mami ga khaira nan yau ma akayi mata allurar immunization sai rigima take "



"Dole tayi rigima yana masu zafi idan anyi masu naga kin d'aura ta a status jiya ta kara girma "wallahi mami nima girman khaira? har mamaki yake bani sai kace yar four months haka ma dazu uncle mb da ya kira mu vedio call yace wai ta kara girma "mami tai murmushi cike da jin dadi tace "ayya muhd bello Ai kuwa ya kyauta may be daga nonnki ne dan wani lokacin idan nonon uwa yana da kyau zaki ga kafin wani lokaci? ya kar'bi yaro sai kiga yaro yayi saurin girma"to ai mami kamar ma kar mu dawo abuja shikenan khaira ta daina karba nono Madara take sha batason shan nono wallahi,ikon Allah aiko bata biyo babanta ba ,adamcy ya? shan nono sosai kuma yayi kulafucin nono dan har na yayesa baya bacci batare da hannunsa yana kan nono ba ,maryam tai shiru batare da tace komai ba "Allah dai ya raya mana ita in sha allahu nima zan shigo abuja nazo na ganku "to mami sai kinzo munyi kewarki sosai "mami tai murmushi tace "baku kai ni ba maryam tafiyarku tamkar kun tafi da komai nawa ne bana jin dadin zaman gidan nan in sha allahu zaku ganni nan kusa suka cigaba da hirarsu."


bayan mr ata ya gama cin kuskus zama yayi kusa da maryama kamar d'azu sai dai yanzu lemun gwangwani ne a hannunsa wanda itama tunin ya kawo mata nata gabanta sai dai ita kam ta kasa? sha "shawarar me kika yanke ?"ni bani da wata shawara data wuce aurenka zanyi dan..."sai kuma tayi shiru ta kasa k'arasa maganarta" kalleni sosai "ta d'aga kanta fuskarsa a d'aure kamar bashi ya gama murmushi ba ta kallesa kwarjinsa ya mamayeta sosai haka ma kyawunsa ya karu alokcin d'aya wanda yasa taji son shi ya sake dirar mata a zuciyarta tayi saurin kawar da kanta gefe tare da runtse idanunwanta tana sauke numfashi ahankali "me kake son nayi maka adam....."?
"ban ta'ba jin wanda ya kira ainihin sunana naji sanyi araina ba sai ke maryama ki d'aure ki aureni saboda da Allah ta bud'e idanuwanta" ai daman saboda Allah zan aureka ta bashi amsa cikin sanyi murya" yayi gyaran murya tare da kawar da idanuwansa daga kallonta idan har na zayyano sharuddana ya zama dole ki zaba biyu aciki Ina tabbatar miki babu fashi ko tausayawa akan kowani sharadi da zaki zaba dole zaki amince tunda na fuskanci bazaki fad'a min gaskiyar da zuciyata take bukata ba "



Gabad'aya kasa magana tayi ta bishi da kallon mamaki"sharadina na farko "ki janye muradin aurena dan wata manufa ,sharadi na biyu? idan na aureki ya zama dole a ranar zan kusanceki .""ki zaba d'aya idan kuma bazaki zaba ba in fad'a miki d'ayan wanda ya zama dole shi? ki zabeshi ."
"Wai duk me ya kawo wannan maganar ki zaba idan kinsan babu komai acikin zuciyarki "daman ance maka zan aureka ne dan wata manufa ko me yasa duk kake irin wad'an nan maganganun?"amsa nake bukata kafin? lokacin da sharadi na uku zai zo"zan aureka ne dan Allah sai dai batun kusanta wannan ne gaskiya ..."is okay na rigada na gane dan wata manufa kike? son aurena "ka shiga zuciyata kasan menene aciki ?"tayi maganar jikinta na rawa "muje sharadin na qarshe,sharadi na karshe tunda baki zabi biyu acikin sharadina ba zan kashe mu nida ke acikin gidan nan ."



"Ban fahimci abinda kake nufi ba baki san mutuwa ba kenan ?"nasan mutuwa mana kashemu fa kake nufin zakayi ?"ashe zafin zuciyar ka? har ta kai ka? iya kisan kai ni dai gsky ban tashi mutuwa ba Ina son na cigaba da rayuwa tare da mahaifiyata ,kai idan ka gaji da duniyar zaka iya kashe kanka amamn bayan na fita a gidan nan "ya isa ya isa !!"shikenan to ki bani kanki a yanzu? na sanki ya mace shikenan zan samu natsuwar cewar ba aurena zakiyi da wata manufa ba "gabanta ya fad'i hantar cikinta ya kad'a nan take taji jiri na dibarta ,da kyar ta samu taja baya ta mike tsaye tana tangadi da baya manufar hakan da tayi shine ta samu ta gudu ."ta dan kalli fuskarsa taga? babu wani annuri akanta nan kuma dukkanin alamu sun nuna da gaske yake zai iya aikata abinda ya fad'a,take taji hankalinta ya sake tashi matuka yayinda gumi ya shiga tsatsafo mata ganin har ya cire rigar shan iskar dake sanye ajikinsa ya wurga a saman kujera shine abinda ya sake tsoratata ta juya a guje tana ihu azo aceceta ."


hankalinta bai sake tashi ba sai data karasa bakin kofa ta ta'ba tajita a kulle gam tayi tayi kofar ta bud'e taki bud'e wa tana cikin wannan halin na tashin hankali taji ya karaso gareta yana kokarin ta'bata
tai saurin gocewa ta koma jikin window parlour'n amman babu motsin mutane sai data zagaye parlour'n? tass yana biye daita amman bata samu hanyar fita ba "ki tsaya mana ki daina 'bata min loakci idan nayi bashi zai sa na fasa aurenki ba zan aureki ,kanta kawai take girgiza masa tana taresa da hannunta dan maganar ma taki fitowa daga bakinta hankalinta gabad'aya ya gama tashi kallo d'aya zaka mata ka fahimci bata cikin haiyacinta sauran kad'an ta bashi dariya dan bakaramin rikicewa tayi ba ,da gudu tabi wata doguwar hanya da tai tunanin zata fitar daita zuwa kofar waje."
bashi da tabbacin kofar a rufe take aiko taga ya biyota a guje wata irin fixge yayi mata ya had'ata da bango ,shi yayi daidai da fasa ihu da tayi wanda bai razana shi ba sai ita kanta datayi kayanta ta razana shi kuwa tsumammun idanunshi har sun canza kala ya matseta da bango yana sauke numfashi yana kokarin had'e bakinsu adaidai lokacin tasa iykar karfinta ta turesa sai dai ko gezo bai yi ba ji tayi ma kamar dutse ta ta'ba ,tana jinsa ya sake matseta ajikinsa "kayi ..kayi hakuri dan giraman Allah? karka sadu dani babu aure ,wallahi gara ka bari idan ka aureni kayi duk abinda kake so kayi dani "okay yanzu acikin sharadin farko kin zabi d'aya kenan ?"tai saurin gyad'a masa kai tana haki ."



Ya Kai hannunsa yana shafa fuskarta yana kallon face dinta data fara 'batawa da ruwan hawaye "sauran sharadi d'aya ai daman biyu nace zaki zaba."
Shiru tayi tana son tuno d'ayan "kar dai har kin manta ?"tai saurin? gyad'a masa kai dariya ta bashi amman ya fiske "na baki minti shabiyar ki tuna "inna lillahi "ta shiga furtawa tana maimaitawa yayinda shi kuma ya cigaba da shafa fuskarta can tace "na tuna !"okay ina jinki zan aurena ba da wata manufa fa "are you sure? "tai saurin gyad'a masa kai
"kin? ta'ba mafarkin mun kasance tare acikin gida d'aya kuma a waje d'aya muna rayuwa kamar haka kafin zuwan wannan lokacin "?kanta ta girgiza masa da sauri? "karki min karya mana ."yayi mgnr muryarsa a kasalance yana zagaye pnky lip's dinta da d'an yatsansa "nasan kina? mafarkin haka dan a yadda nake kallon wad'an nan shayayyun idanun naki sun dade? cikin nitson son adam ".ta sake? girgiza masa? kai alamun "a'a!numfashi ya fixgo da karfi ya fitar ,kallon fuskarta yake cike da tsananin tausayawa tana da matukar rauni kuma daman yasan sai raunin ta ya jawo anyi mata illa kuma shine dalilin da yasa ya kasa gabatar daita ga yan'uwansa dan a yadda idanunsu ya rufe akan son wacan yarinyar sai sun nuna mata wariya abinda ya guda dai sai da ya faru shi ."



Shida zuciyarsa ke cike da tsananin muradin kasancewa daita shine za'a kafa mata sharad'i akansa ,zai ga uban da ya isa ,zai ga ta yadda wannan sharadin zai yi aiki aiko mami ce tace kar ya kusance wallahi sai dai tayi hakuri bare wasu can "maryama na sha mafarkin mun kasance tare acikin gida d'aya kuma a waje d'aya muna rayuwa kamar haka kafin zuwan wannan lokacin" yayi maganar yana sak? had'e ta da faffadan k'irjinsa tare da sauke mata numfashinsa a wuyanta,jikinta ya sake d'aukar rawa sosai duk maganar da yake mata? bata fahimta komai? amman ta'ba mata jiki da yake ji take kamar tasa ihu ko ta bashi wani lafiyayyen mari saboda bakinciki,shi kuwa gabad'aya jinta a jikinsa ya sake rikita masa lissafi da kyar ta aro jarumta ta sanyawa jikinta sannan ta soma magana cikin bacin rai "idan ka gama wulakantani ka sakar min jiki ka maidani gida dare? nayi !"tayi maganr? hawaye na zubo mata."
shiru yayi yana shafa lip's dinta yana tunanin wani wulakanci yayi mata? jikinta kawai ya ta'ba kuma daman ya saba ta'bawa kuma bazai daina ta'bawa ba har zuwa sanda zata dawo karkashinsa yanzu ma so yake ya d'an tsotsa bakinta dan yasan zai yi dadin sha ,dan haka ya sake matso da fuskarsa zai kamo lip's dinta "ban san baka da mutunci ba sai yau ... "
"cak ya tsaya ya? kasa aiwatar da abinda yayi niyya yana mata wani irin kallo ,ji yayi ma kamar maganar ba daga bakinta ta fito ba amman yasan ita tayi maganar yace "ke ki kalleni da kyau waye bashi da mutunci ?"yayi maganar yana janye jikinsa daga nata? dan yaji zafin kalmar ".


"waye da wuce Kai wallahi baka da mutunci "ta samu karfin halin fad'a masa haka ne ganin sun samu tazara a tsakaninsu "yanzu ni zaki fad'a wa wannan kalmar ?" ba dole na fad'a maka ba tunda ka nuna min baka da mutu..."ai wani lafiyayyen mari ne ya ratsa mata kwakwalu warta abinda bata saba ji ba arayuwarta jinshi yau kuwa sai ya zame mata wani bakon alamari sai ya zamo duk ta rude ta rasa Ina ma zata saka kumatunta taji sanyi ai ko ta zame kasa ta durkushe , ta dinga shafa kumatunta kamar mai sabon ciwon hakori sai data d'auki minti biyar tana jinyar kumatunta na dama tare da idonta da d'an yatsantsa ya d'an shafa ,ahankali ta iya d'aga kanta sai dai ta hangosa zaune yana fuskantarta sanye da Kaya ajikinsa sa'banin d'azu ,ta girgiza kanta tana son tabbatar wa kanta da gaske abinda ya faru daita kenan ?" ,kumatunta ta cigaba da shafawa dan har yanzu dai? tana Jin zafin radadin zafin marin data sha ."to a yaushe ne har yaje ya canza Kaya bata sani ba ?"ina zaki sani kina cikin gigita ."zuciyarta ta bata amsa da haka .


mikewa yayi ya nufi kofar fita jiki a sanyaye ta mike ta isa gaban mirrow dake parlour'n ta duba fuskarta a madubi ta ganta kalau babu abinda ya sameta sai dai gefen idanunta yayi ja sai lokacin taga d'an digon hawaye sun cika mata ido suna kokarin fito wa daga kwayar idanunta ahankali ta maida idanunta ta lumshe domin su karasa gangarowa taji sanyi aranta wata uwar ashar ta zuba masa wanda wallahi ta tafi karfin shekara goma batayi ashar ba dan? ba dabiar ba ce sai bayan da tayi ta dawo tana nadama duk da ba agabansa tayi ba hawaye ta cigaba da zubarwa sannnan ta tabi yo bayansa tana gunji kuka tare da nadama me yasa zatai masa rashin kunya ?tamabayr da tayiwa kanta kenan ,sai ma tazo tana? ganin laifinta da rashin kyautawarta ,a haraban gidan ta iske shi tsaye ya bud'e mata gaban mota yana jiranta kanta a sunkuye ta shiga ta zauna ya maida kofar ya rufe mata ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna ya fizge? motar da gudu uka suka bar gidan ."




Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 3


Zuciyarsa na matukar zafi yake murza stearing batare daya kalli inda take zaune ba, ahankali ta d an waigo inda yake zaune ta kallesa a tsanake fuskar nan tashi a had e tamkar zaki kwata kwata babu alamun annuri akanta numfashi ta janyo ta sauke da kyar zuciyarta cike da matsanancin tashin hankali,tana son ta bashi hakuri amman tana jin matukar tsoron abinda zai biyo baya dan fushinsa ba kyau shiyasa bata son wannan fushin nashi dan zuciyarta bazata iya d aukar fushinsa ba, kwananki baya da yayi fushi daita ta azbatu matuka. basu zame koina ba sai akan titin unguwarsu yayi parking batare daya kashe motar ba alamun jira yake ta sauka ya k ara gaba.
shiru tayi taki sauka tana kallonsa kamar zatayi kuka har acikin zuciyarta bata ji dadin rashin kunyar da tayi masa ba ,a kalla sun d auki kusan minti shabiyar suna zaune shiru acikin mota sanyi ac motar na ratsa masu sansar jikinsu yayinda kamshin turarensa wanda ya gauraye da sanyi dake ratsa cikin motar suka dinga bugar mata da zuciya .


zaune kawai take acikin motar tana ko kuwa da numfashinta da zuciyarta tana tunanin hanyar mafi sauki da zata bi wajen bashi hakuri kafin su rabu amman ta rasa, shi kuwa agogon motar ya duba a karo na kusan biyar tare da jan dogon tsaki bai san zaman me take masa acikin motar ba ,jarumtar ta aro ta sanyawa jikinta tare da kwantar da muryarta cike da girmamawa tace  yalla& . ai tun kafin ta kai k arshe taji sautin muryarsa cikin tsananin fushi .
 Get down ! .
ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login