Showing 24001 words to 27000 words out of 151781 words

Chapter 9 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2645

damu kanki maryama ki cigaba dama Allah ya baki duk wanda ya samu dama irin taki dole zai yi son ranshi ".


Ahankali ta runtse idanunta tana cewa "dan girman Allah ka fad'a min sannan ka fad'a min damuwarka dan muryarka ta nuna kana cikin damuwa "did i toid you something is bothering me "?"no sir amman koda baka fad'a min ba sautin muryarka kad'ai ya isa ya tabbatar min da kana cikin damuwa "wani dogon numfashi ya sauke acikin kunneta har sai data d'an janye wayar a kunnenta sakamakon tsigar jikinta da suka mike yrrrrrrr ."gyara zamansa yayi tare da yin shiru yana kallon makeken tv plazama dake manne a bangon parlour'n yana son sheida mata hukumcin sweetheart yaji mai zatace "zata amince da zamanta tare da mahaifiyarsa ko kuwa?"amman dai sai ya share ya cigaba da yin shiru ,a kalla sai daya d'auki mintuna biyar batare daya furta komai ba har sai da maryama ta cire rai da zai k'ara yin magana sannna taji yace" my princess zuciyata na cike da kewarki kuma nasan kema kinyi kewata "yayi maganar yana lumshe idanunshi kamar tana gabansa "wani irin yarr tsigar jikinta suka sake mikewa ta lumshe idanunta "Allah yasa kar mutumin nan ya kasheta da soyayyarsa "ka fad'a min damuwarka first ita nake son ji dan jikina yana bani kana cikin damuwa ".


"ki ajiye wannan maganr muyi maganr kewarki da nayi ,kinyi kewata ko kuwa har yanzu kina kan yaudarar zuciyarki ?"yallabai karka kawar da tunanina cikin sauki duk da kana min kallon yarinya ce ni amamn fa kasan Ina da wayona ."maganrta taso bashi dariya dan har hakan ya nuna a fuskarsa ,ita kad'ai ce macen da idan ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yana magana daita ko yana tare daita yakan ji sanyi a ransa kuma koda yana da damuwa yaji muryarta tabbas sai 'bacin ransa ya gushe "dan haka karka yi wasa da tunanina Ina da hankali da wayon da zan iya gane komai dan haka ka fad'a min kawai".
"maryama banason cika magana akan abu most especially maganar danasan mutun yasan da zamanta ,kinsan laifinki a wajena nace miki zan dawo washegarin ranar dana zo wajenki amman da kika jini shiru sai baki nemi ba kika shareni kika cigaba da rayuwarki cikin rashin kwanciyar hankali dan nasan duk second din da zata zo ta wuce dole sai kinyi tunanina tare da son kiji muryarta amman tsabar taurin kai yasa kika kasa kirana ."


A yadda yayi maganar bakaramin rikita mata lissafi yayi ba sannan gabad'aya ilahirin jikinta sun mutu ahankali ta motsa bakinta "kuji min mutun wa yace maka na cigaba da rayuwa cikin rashin kwanciyar hankali ?"sannan duk second din da zata zo ta wuce sai nayi tunaninka ?"kai mai yasa da ban kiraka ba kai baka kirani ba?" "okey abinda zaki fad'a ma kenan "?tai shiru tana zaro ido kar dai yaji abinda ta fad'a ahankali fa tayi mganr? ta yadda ita kad'ai zataji."
ta rasa wani irin kunnen jin magana garesa duk yadda mutun yayi magana sai yaji a wasu lokutan ma ko bakin mutun ya kalla ya kan fahimci abinda ya fad'a "maryama zai fi miki alkhairi kafin kiyi magana ki dinga tattara natsuwa ajikinki, ko da yake ada ki kan natsu kiyi magana Amman a yanzu soyayya tana son canza miki tunani ."yana kai wa nan ya katse kiran ransa a matukar 'bace.
sauke wayar tayi tana kallon screen din wayar "to menene kuma abun fushi anan daga yar wannan maganar idan ba bakar zuciyar irin tashi ba kai dai matarka ta gida tana da aiki mutun kamar jira yake ita kam bazata iya wani kiransa ta rarrashesa ba .ajiye wayar tayi ta cigaba da lamarin gabanta shi kuwa har kusan minti goma yana zaune rike da waya yana jiran ko zata kirasa ta bashi hakuri amman yaji shiru ya kai yatsan hannunsa cikin bakinsa yana cizawa ahankali dakiyarta tana d'aga masa hankali duk tarin son shi da yake gani atattare daita amman ta kan daurewa rashin ganinsa sai dai duk yadda zata boye son shi yana nan atare daita ."


******
da misalin k'arfe 4:50 na yammacin ranar mr ata ya yanke shawarar da zaman da yake yaje gurin mami ya sameta yaji yadda sukai da yar gwal dinta ko zai ji sanyi acikin ranshi dan haka ya fara shirin zuwa wajenta sun iso abdullahi estate adaidai kofar gidan mami direbansa da masu tsaronsa suka yi parking cike da natsuwa ya fito bayan an bud'e masa murfin mota fuskar nan nashi a had'e sai dai hakan bai hana kwarjinsa fitowa ba ,ahankali yake taku har ya shigo babban parlour'n mami bakinsa d'auke da sallama sai dai bai iske mami a parlour'n ba dan haka ya nufi kofar da zata kai shi inda take cikin muryarsa mai sanyi yayi sallama a bakin kofar d'akinta wanda tun kafin ta amsa masa sallamar ta jiyo sanyayyen kamshin turarensa dake shirin fitowa take daga d'akin ta amsa masa sallama sannan ta koma ta zauna a bakin gadonta tana jiran shigowarsa ."


Ya shigo a natse ya rusuna ya gaisheta ta amsa masa cikin rashin sakin fuska ya samu waje ya zauna yana jin bugun da zuciyarsa ke yi gefe guda kuma yana jin haushi daga dokin takura masa data hau ,bayan kamar minti goma yace "sweet heart nazo ne naji yadda kukayi da wacan yarinyar dan naji shiru baki nemeni ba "au wai maryam kake nufi ?ya kalli mami kawai batare da yace uffan ba har sanda mami ta cigaba da magana "Alhamdulillah yanzu kam maryam tasan ciwon kanta dan cewa tayi bazata iya komawa tayi rayuwa da mai bakar zuciya irinka ba ,wanda babu komai acikin zuciyarsa sai tarin mugunta da zalinci akan ya'yan mutane, bazata iya rayuwa da mutun kamarka mara yafiya ba shiyasa kaga ma ban kiraka ba yanzu dai a sauka lafiya sai kaje kayi aurenka da yar gwal ku cigaba da iskancinku da kuka saba dan bazan tursasa mata komawa gidan mutun mai bakar zuciya mara imani da tausayi ba ."tsayawa adamcy yayi tare da bin mami da kallo sakamakon jin bakar maganar data fad'a masa dan har ga Allah sai yaji aransa cewar duk fad'ar ta ce maryam bazata ta'ba bud'e bakinta ta fad'a mata haka akanshi ba yaji zafi kuma yaji sanyi acikin ranshi da bata amince ba jin farinciki rashin amincewrta ya goge tarin haushin da yaji na maganar mami ya basar da maganar kai tsaye yace "to yanzu yaushe ne su baba babba zasu je gidansu mryama so that sai na sanar mata da zuwansu "?



mami ta hararesa tana kwabe baki tace "babu ruwana da batun aurenka ka tsara komai da kanka dan yanzu kaine uwar kanka kaine ubanka kanka "inna lillahi shi kam daman mami fake love take masa ne shi bai sani ba sai a yanzu ne manufarta ta fito fili ?"ahankali ya d'ago tsuma mmun idanunshi da suka gama canza kala tsabar tashin hankalin abinda maganarta ta jefashi."
ya zubawa sweetheart yana kallonta ganin haka yasa mami ta sake had'e rai dan bata son ya kawo mata rainin wayonsa daya saba sannan ta cigaba da dubansa "sweetheart ki min adalci duk abinda kike so koda banaso haka na kan yi hakuri nayi miki shi domin farincikinki shine nawa ,lamarinki lamarin ya'yanki ban ta'ba juya miki baya ba dan Allah kada kiyi min haka alokacin nawa farinciki?"menene akayi maka na rashin adalci yanzu?"ba'ayi min komai ba abinda nake so dan girman kiyi hakuri ki yafe min sannan ki fad'a ma baba babba da kanki suje su nema min auren maryma" yayi maganar cikin wani irin yanayi mai cike da ban tausayi."



"Bazan ce me ka ta'ba min na kyautatawa ba kayi iyakar kokarinka akanmu amman kasani duk abinda kayi min bai kai d'aukar cikinka har haihu warka da nayi cikin tsananin wahala ba kasani adamcy har na mutu bazan manta tozarcin da kayi min ba, sannna ka mance na baka diyar danuwana ka wulakanta min ita ?ka mance maryam tayi zaman kunci a gidanka saboda tsabar bakar zuciya irinta taka da rashin imaninka ?" shine yanzu zaka ce na shige maka gaba wajen auren wata can da ban san asalinta ba "duban mami kawai yake dan ya ma rasa abinda zai ce mata "tai shiru tana dubansa har sanda ya taso ya karaso gabanta ya durkusa ya d'aura kanshi a saman cinyarta yana mai neman gafara."sweetheart !"
Ya Kira sunanta cikin wata irin murya wace bata da maraba data tashin hankali tana jinsa tayi masa banza tare da kawar da kanta "sweetheart Ina tsananin jin damuwa araina Ina jin kamar bani da kowa acikin duniyar nan, Ina ji ajikina zan iya mutuwa akowani lokacin saboda kuncin da zuciya take ciki ,ya kara makale kanshi ajikinta "sweetheart nifa amana ne a hannunki karki manta da amanar dady har dady ya cika yana sallati yana baki amanata dan Allah ki yafe min ko zuciyata zata samu natsuwa da sausauci ."


Nan take idanunta mami ya kad'a sosai ya cika da hawaye Allah sarki Tariq dinta mutun mai mutunci da son mutane da son yan'uwansa har kullum tana jimamain rashinsa Allah ya jikanka ya maka rahma kuka yaci karfin mami ya tabo mata ciwon dake zuciyarta wanda take jin bazai ta'ba warkewa ba har karshen rayuwarta tunda ta rasa wani bangaren na rayuwarta shi kuma data take ganin zai maye mata gurbin mahaifinsa yaki kwantar mata da hankali "mr ata jikinsa yayi mugun sanyi duk iskancinsa yana gudun abinda zai saka sweetheart dinsa kuka jin kuka yake kamar ana diga masa dalma a zuciyarsa ya sake matsowa kusa daita yana jin yadda zuciyarsa ke zafi da tafasa domin yasan shine silar kukanta."
"ki yafe min sweet heart "ya sake maimaitawa muryarsa na rawa "kiyi hakuri ki yafe min kuma a shirye nake da in canza in zama mai faranta miki da kaunarki ,wani sanyi dadi ne ya ziyarci zuciyar mami sai dai ji take duk dan yana son ta bashi goyon baya ne yayi aurensa ya fad'a haka ."
Ya sake gyqra kanshi akan cinyarta "sweetheart ki yafe min ko zan samu sausauci abinda nake ji araina idan ba haka ba wallahi zuciya tana daf da bugawa zaki rasa adam dinki d'an..." tayi saurin saka hannu ta rufe masa masa baki dan bata son rasashi shine fa da tilon da take dashi duk abinda take masa tanayi ba'a son ranta ba duk da ya sha mata laifi amman na kawo mata maryama yafi komai kona mata rai kuma bata jin zata manta dashi har taso yarinyar."



muryarta a sanyaye ta soma magana " na yafe maka adamcy dan bazan iya rikeka araina ba kuma na barka kaje kayi aurenka kuma zan fad'a ma baba babba yaje nema maka aurenta ,kullum addua nake maka dana Allah yasa kayi aure naga jikokina na gurinka to Alhamdulillah naga khaira kuma isheni domin itace jika mafi soyuwa arayuwarta "na gode sosai sweetheart "ya fad'a tare da d'ago kanshi yana kallonta ya riko hannuwanta "in sha allahu sweetheart zaki yi farinciki da zabina kuma zaki so ya'yan da maryama zata haifa min "yayi maganar da mur mushi akan fuskarsa,itama tayi murmushi kawai ba wai dan taji dadin maganarsa ba "ai an gama haifata mata jikar da zata so domin bazata ta'ba son maryama ba bare har taso abinda zata haifa masa ."


Har yanzu da yake gabanta zuciyarsa cike take tarin damuwa dan bai daina hango damuwa atare da mahaifiyarsa ba, fahimtarsa ta dai barshi yaje yayi aurensa amamn batun son maryama kwata kwata bai ga alamun haka a atattare daita ."adamcy bai bar mami ta huta ba sai daya tabbatar da ta kira baba babba tace suje masa Neman auren maryma, baba babba yace zuwa yaushe kenan ?tace "yau muna litini kuje ranar laraba ,idan yaso banda wannan lahadi lahadi ta sama sai a d'aura auren ,taki bin raayi adamcy dan shi adamcy cewa yayi a aura a wannan lahadin koda yaji abinda tace aransa yace tun dai kin amince Allah ya kai mu" baba babba yace mata "to Allah yasa alkhairi ya kai mu ranar tace "ameen ! atakaice ranta baya mata dadi da auren .adamcy ya mike ya nufi d'akinsa ya zauna shiru tare da kiran layin umma dan aganinsa ita yafi dacewa ya sanarwa ba maryama ba Kira d'aya ana biyu ta d'auka bayan sun gaisa ya sheida mata yanauwnasa zasu zo ranar laraba kuma in sha allahu lahadi ta sama za'a d'aura aure Allah sarki umma nan take ta fad'ada fuskarta da murmushi tana cewa "Allah ya kai mu lokaci Allah kuma yasa albarka Allah ya bamu ikon gani da ranmu da lafiyarmu yace "Ameen ya zarce da cewa umma maryama na kusa ne ?"aa d'azu nan taje gidansu subai'a amman nasan tana kan hanyar dawowa "okay to dan Allah umma Ina neman wata alfarma a wajenki ?tace "kayi maganar adamu !"sai daya sauke numfashi sannan yace "dan Allah karki fad'awa marayma batun zuwan yan'uwana har sai a gama komai "to shikenan an gama to ko wani abu take maka na rashin d'aa ?"yace "no no !! ai yarinyar kirki ce maryama" akwai dai maganar da nake son muyi dake ne kafin tasan komai "umma tai murmushi tace "shikenan sai kazo sukai sallama dashi yayinda fuskar umma ta kasa boye tsantsar farinciki da take ciki ta mike ta fito ta nufi bangaren aunty ."





Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
? ?? MAR'ADAMS
? ?? =ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan? 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


? ? ? ? ? Page 6

A zaune umma ta iske aunty tana kulla alawar sha ka la'be acikin farar leda? ,kallo d'aya aunty tayiwa umma ta fahimci acikin farinciki take haka nan itama taji ta tsinci kanta cikin tayata har sanda umma ta zauna fuskarta cike take da annuri batare da 'bata lokaci ba umma ta shiga karo mata batun zuwan iyayen adamcy "Alhamdu lillah kawai aunty take jerowa ,kamar ta tashi ta taka rawa dan murna haka ta dinga ji saboda? farinciki, ba shakka tana mai tabbatarwa kanta
Maryamarta tayi kyakkyawan gamo mai d'auke da dumbin alkhairai, umma? ta kasa zama waje d'aya tace "bari na shiga na sheidawa gali dan naga kamar yana gida ,daga nan zan je na sheida wa malam mustapha su tarbi bakin dashi ."
aunty tai murmushi kawai tana kallon bayanta dan tuni tayi hanyar fita "Allah sarki umma babu abinda zance miki sai dai Allah yasa kiyi kyakya wan k'arshe? Allah kuma ya barmu tare da sallama umma ta fad'a bangaren baba gali taci sa'ar samunsa shi kad'ai zaune tsikar gidansa yana jin labarai ."yana ganinta yaji gabansa yayi mummunar fad'uwa dan shi yanzu da ganinta da kiranta ba alkhairi bane a wajensa sai dai ya washe baki yace "aunty? ke? da kanki maimakon ki aiko akirani nazo ,sannu da zuwa aunty ga waje ki zauna ya tashi yana kokarin d'auko mata? farar kujera umma tace "ka bar shi ba? sai na zauna ba nazo na fad'a maka ne jibi idan Allah ya kai mu iyayen yaron nan adamu zasu zo neman auren maryama nan da sati d'aya kuma za'a d'aura aure in sha allahu ".


Wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa cike da matsanancin tashin hankali baba gali ya tsinci kanshi ciki, inda yaji kanshi yayi masa nauyi kamar an d'aura masa dutse, dishi dishi ya soma ganinta da sauri ya bud'e idanunshi sosai dan muddin yayi sakacin da suka rufe komai zai iya faruwa dashi "gali ina cikin farinciki bari na wuce dan ina son naje na sheidawa malam mustapha sai ku tarbi bakin dashi ,kai ma idan ka samu fita zuwa anjima ko gobe da safe sai kayi masa magana" tana gama fad'ar haka? ta juya da sauri ta barshi nan tsaye cikin mutuwar jiki? yana kallon bayanta. umma na fita aunty Salma ta fito da sauri ta tsaya a gabansa ganin baya cikin haiyacinsa yasa? ta d'an ta'ba shi kadan, ya maida kallonsa gareta tun dazun data? tsinci maganar yake mintsininta ,taso ta fito? taji? sosai "baban Aliyu? auren wa za'a d'aura kuma nan da sati d'aya ?"baba gali ya kalleta a sukwane? yana jin wani sabon tashin hankali na? shigarsa yace "nasan kinji komai amman bari na sake fad'a miki auren maryama za'a d'aura" idanu aunty salma ta ware sosai tana jin wani irin tashin hankali tace "amman dai ba da wannan attijirin mai kudin ba?"da shi kuwa za'a d'aura"ya fad'a mata Kai tsaye gumi na tsatsafo masa nan take jikinta ya kama rawa duk sai ta kasa furta komai,babu abinda ke yawo akanta irin maganar malaminta inda yace mata ba za'a sake tada maganar ba sakamakon aikin da yayi mata a makabarta akaje akayi aikinsa yadda idan mutun? ya mutu bazai tashi ba haka baza'a sake tada zance auren maryama da adam ba ".


"kin dai ga abinda zai faru acikin gidan nan ko kuma kina raye ba wai kin mutu ba ?"saurin bubbuga gefen kanta tayi da hannunta tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu tace "Kai kuwa ka kwantar da hankalinka har yanzu fa da sauran lokaci tunda ba'a rigada an d'aura auren ba"
"baka san wani abu ba? shi aikin zai iya tasiri aranar daurin auren? ace an fasa "kinga bazan sake kuskurena? yarda dake ba domin yarda da nayi dake ne duk yake kokarin janyo ciwon zuciya,ka kwantar da hankalinka bafa za'ayi auren nan ba "dan bakisan me nake ji ba a yanzu haka "bari? ina zuwa amman wannan auren kam tabbas baza'a d'aura shi ba sai dai bayan raina sakina da tun fara maganarsu ta fito ta girgiza kai tace "wallahi mama da kin daina wahalar da? kanki akan maryama shin dole ne sai mun taka matsayi d'aya daita ?"hannayemu kad'ai sun ishemu misali ,wallahi idan Allah yaga dama sai ya barmu muddin rai babu aure ba ita kuma tayi aurenta kuma ta dangwama cikin jin dadi ."
aunty Salma ta juyo a gigice tana dubanta tace idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login