Showing 48001 words to 51000 words out of 151781 words

Chapter 17 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2663

kuka "my princess you must eat well kalli yadda mararki ta shafe ."?
"to ai Ina cin abinci sai dai ba koda yaushe ba tayi maganar tana shagwabe masa fuska alamun zatayi kuka "kina son ki kasa d'aukarta ciki da wuri ne "?
"me kuma ya kawo wannan maganar ?"ta fad'a tana had'e fuska a dole karya kawo mata maganar lumshe idanunta tayi tace "wai dan Allah kai baka jin kunya ne "?kunya for where ?" "dole fa zaayi maganar ciki tunda dole .."dan girman Allah karka k'arasa maganar ."

Shiru yayi tare da kamo laulausan tafin hannunta cikin nashi yana murzawa hannunta da jikinta tamkar ba diyar talakawa ba ,yan'uwanta suka shigo dakin tai saurin zare hannunta cikin nashi dan muddin tayi sakaci to kuwa ita zai barwa abun kunya umma subai'a har ma da yusura suka dinga jero mata sannu.byn sun fita ne taji tamkar kar su fita dan bata son abarta daga ita sai shi a d'akin hakan na sake frigita zuciyarta dan zan tutt'ukansa babu sauki komai nashi dabam salon soyayyarsa mai matukar tafiyar da kuzari da ruhi ne sai data shanye tea tas sannan ya soma bata abinci kad'an taci tace "ta koshi bai wani takurata ba tunda ta sha tea sosai ya ballo magani ya mika mata, ba musu tasa hannu ta kar'ba ta sha dan tasan halinsa ciwonta ba zai hanashi matseta ya bata ba ko dagula mata lissafi ba har sai yaga ta sha dan gabadaya a tsorace take dashi ."


sosai Idanunshi ke cikin nata yayinda hannunsa ke tsarke cikin nata "ki tashi daga wannnan ciwon naki domin a samu damar kawo min ke pls nan take ta had'e fuska "kinsan Allah idan na bar gidan nan kuma kikayi abinda yasa ba'a kawo min ke ba a yau ba bazaki sake ganin kafafuwana a inda kike ba "sai me ai na ma huta da takura." "tayi maganar acikin ranta k'aramin bakinta yake kallo yana son ya Karanci abinda ke ranta itama shiru tayi tana tunani bata ankara ba taji ya kamota ya sanyata ajikinsa yana shafata cikin wani yanayi na tsananin sha'awrta "ni zan wuce amman masu zuwa d'aukar ki suna zuwa ni wallahi da umma zata barni dana wuce dake an hutar da kowa kwace jikinta tayi tana masa wani kallo "sai kace wata yar kaza zaka ce zaka wuce Dani kamar bani da galihu "meye marabanku."


Tai shiru tana kallon kafin ahankali tace "bani da maraba da kaza kake nufi ?"yes gabad'aya jikinta babu kwari kamar pepper Allah kina shigowa hannuna double abinci zan dinga tura miki ga abinci ga spam dan kiyi saurin .."saurin kai hannunta bakinsa tayi ta toshe tana kallon cikin kwayar idanunshi shima cikin idanunta yake kallo cike da matsanancin shaawarta kallon juna suke kamar zasu cinye juna" Ina sonki s?sai bazan ta'ba son wata halitta sama dake ba."yayi maganar acikin ransa sake had'ata yayi da jikinsa yayi runguma mai kyau sannan ya zareta yana duba agogon hannunsa" nan da wasu yan mintuna zasu karaso har juya ya sake dawowa yayi kissing din foreign head dinta lumshe idanunta tayi batasan lokacin daya fice ba sai bud'e idanunta tayi taga wayam baya d'akin."

a parlour'n kuwa adamcy yayi wa umma sallma yana k'ok'arin fita ta biyo bayansa tana masa magana ya tsaya cak ."adamu kana ganin bazaku dade a gidan mahaifitarka ba?"shiru yayi kawai yana kallonta "wai saboda Kayan amfanin maryama ne "umma sau nawa zamuyi mganar nan gidan da zata zauna babu abinda babu acikinsa amman tunda kuna raayi zaku iya kai wa zan turo zuwa jibi akai ku gidan sai ku Kai mata."
ya fad'a haka ne saboda baya son suga ya raina matsayinsu "to shikenan hakan yayi ya sake yi mata sallama ya fice yana kiran direbansa yaji ko Sun taho "alright!"kawai ya fad'a atakaice Karfe biyar daidai umma da subai'a tare da kawayen aunty suka shirya maryama cikin wata hadadiyar atamfar super exclusive puppy toch of white and black ajiki ,dinki riga fitet da zani ne aka mata duk da tafi son dinkin doguwar riga amman dinki ya kar'bi jikinta sosai tare da lullubeta da lifaya shima fari toch of pupply sukai mata wanka da ruwan turare kala kala suka fito da ita umma tace akaita gurin aunty suyi sallama sannan idan an fito daita akaita wajen baba gali shima tai masa sallama ."


Allah sarki maryama durkushewa tayi a gaban umma sai kuka ya kufce mata tana kiran umma !!"shine kawai abinda bakinta yake iya furtawa itama umma hawaye ne ya cika mata ido ta goge da sauri tana cewa "ki daina kuka kin dai san baki da lafiya Allah yasa kin shiga a sa'a Allah yayi miki albarka Allah yasa wannan gida da zaki shiga ya zamo silar samun kwanciyar hankalinki Ina miki fatan alkhairi arayuwarki aurenki tashi kinji lokaci na tafiya ta mikar da ita tsaye tana kuka umma na kuka dan zatayi kewar diyarta
aka nufi bangaren aunty daita itama dai da kuka suka rabu tana sa mata albarka tare da fatan alkhairi sannan suka shiga bangaren baba gali shima dai babu yabo babu fallasa yayi mata addua da fatan alkhairi suna fito iyayen adamcy na shigowa mutun uku ne kawai suka zo d'aukarta hajiya zulfa'u da matar baba babba sai zabiba sun baro matar baba k'aramin da matar uncle jay a gidan mami da sauran jamaa batare da 'bata lokaci ba aka shedawa umma zuwansu ."


inda tace subaia tayi maza ta fito da akwatin data shiryawa maryama na kayanta na sakawa guda uku mutun biyar ne ta bangaren maryama zasuyi mata rakiya umma,da kawayenta aunty guda biyu sai aunty fatima da aunty hassana sai kuma kawayenta mutun uku a natse umma ta fitar da maryama daga lungunsu tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya tuni fuskarta ta sake canzawa aka sakata motar da hajiya zulfa'u take ciki gefenta umma ce sauran mutane suka shiga mota suka bar unguwar ,cikin mintuna talatin da wani abu suka k'arasa abdullahi estate Kai tsaye bangaren mami aka nufa daita alokcin duk suna zaune a babban parlour'n har mami dan tun kafin su karaso hajiya zulfa'u tayi wa aunty shahida text message akan lallai suyi kokari mami ta zauna a parlour'n dake sun san shiru su akan maryama batare da bata lokaci ba suka bukaci mami ta dawo parlour'n tace "me zanyi bayan gasu zulfa'u dasu hajiya baseera da kyar dai suka lallabata ta fito cikin wani hadadden lace red toch of gold haka mayafin data lullube jikinta dashi da talkami duk gold ne ga wasu awarwaron zinariya a hannunta haka ma wuyanta sarkar gold ne ."


kana kallonta kasa tun asalinta ba daga gidan babu ta fito ba daman kuma ga kyau ga jiki mai kyau Allah ya bata bazaka ce itace ta haifesu ba hajiya zulfa'u rike da hannun maryama bata tsaya a koina Ina ba sai a gaban mami fuskar d'auke da murmushi tace "Aunty ga surukarmu maryama ta kamo hannunta ta sanya maryama ai maryama na Jin hannunta cikin nata jikinta ya Kama rawa sai dai cike da girmamawa da ladabi maryama ta zube a gabanta kanta na sunkuye a kasa cikin tsananin jin kunya da fargaba dan har lokacin kuka take mai ban tausayi tunda mami ta rike hannunta taji komai ya sauya agareta wani irin tsanarta kawai take ji yana bin jinin jikinta cikin sakonnin da basu wuce goma ba ta saki hannunta tana kirkiro murmushin dole inda zabiba ta karaso gaban maryama ta soma k'ok'arin bud'e? mata fuska cak mami ta dakatar daita ta hanyar take mata kafa ."


muna sai da ingantaccen maganin mallaka sai dai baa bawa mai kishiya saboda karfinsa ga masu bukata zasu iya tuntubata ta wannan number 09136918331 ."


Mmn Sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Page 11


Ahankali zabiba ta durkusa agaban maryama ta riko tafin hannunta cikin nata tana kallonta cike da matsanancin farinciki ,yayinda sauran 'yan uwanta kuwa takaici da 'bacin rai ne suka dabaibaye zukatansu suka? dinga jin tsananin tsanar maryma na sake shiga lungu da sako na gangar jikinsu,ahankali zabiba ta waiga bangaren da sauran 'yan uwanta suke,wani irin mugun kallo suke aiko mata dashi ,hajiya baseera dake zaune kusa da mami itace ta kai hannunta ta d'an bud'e fuskar maryama wacce ta gama canzawa tsabar kuka,ahankali ta saki murmushi tare da rungumota da hannuwanta duka tana sawa auren albarka kowa a parlour'n albarka yake sawa auren banda su aunty khadija wad'an da sosai suke jin haushin masu sakawa auren? albarka sai dai a zahiri murmushin yake kawai suke dan kar mutane su gane sannan aka gaigaisa cike da farinciki da mutunta juna "hajiya zulfa'u tasa akayi ma su umma tarba mai kyau inda hajiya fatima ta fara magana fusakarta cike da tsananin farinciki tace "ga maryamarmu nan mun kawo maku ,a yanzu ta tashi daga hannunmu ta koma hannunku dan Allah dan annabi duk abinda tayi ba daidai ba ku tsawata mata ."


? ? ? ?? "ke kuma maryama ga iyayenki nan kiyi masu biyayya, Allah ya baku zaman lafiya Allah ya kade dukkanin sheidan a tsakaninku." babu abinda dangin adamcy ke cewa sai "in sha allahu amman banda su aunty khadija "Allah ya tabba tar mana da alkhairi Allah ya basu zaman lafiya? da zuria masu albarka."kowa yace ameen daga dukkanin bangaren stil ban dasu aunty khadija Jikin umma yayi sanyi da yadda taga mami ta kar'bi masoyiyarta kuma diya mafi soyuwa acikin zuciyarta ,dan duk wanda yake tare daita ya san irin? tsananin? k'aunar da take wa maryama kauna ce ta mussaman ,kauna ce wacce babu mahad'inta ko uwa da 'ya sai? haka ."ganin yana yinsu aunty khadija yasa hajiya zulfa'u tace "maryama ga yayyen mijinki nan suma kiyi masu biyayya kinji, Allah yasa albarka in sha allahu kinzo gidan da zakiyi farinciki acikinsa "umma ta kalli bangaren wad'an da ta gani a zaune a waje d'aya wad'an da hajiya zulfa'u tace? yayyensa ne ko bata fad'a ba alamunsu ya nuna yan'uwan adamcy ne saboda kamar da suke dashi suma babu wani alamun sunyi maraba da shigowar maryama cikinsu dan tunda suka shigo ta fahimci haka ."


? "bayan wasu mintuna sai ga adamcy? ya shigo parlour'n? da sallama sakamakon wayar da hajiya zulfa'u tayi masa ,sanye yake cikin wata dakiliyar shaddar,yana shigowa yanayin cent din parlour'n ya sake canzawa ,kamshin turarensa da kuma kamashin turaren jama'ar dake zauen a parlour'n da air freshener da akayi amfani dashi aparlour'n?
Ya gauraye waje d'aya, ahankali ya d'aura kwayar idanunshi akan masoyiyarsa wato sweetheart dinsa ,sai dai? fuskarta babu yabo babu fallasa yanayin daya ga fuskarta ba kamar d'azu da safe ba,wani boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya soma taku a natse har ya k'araso kusa daita? alokcin da zabiba take k'okarin mikewa tsaye domin bashi guri."durkusawa? yayi ya zauna yana kallonta kafin ahankali ya maida kallonsa ga?? maryama wacce kanta ke kasa a sunkuye cikin tsananin tashin hankali da fargaba mara misal tuwa ."manya dake zaune a gurin suka sake had'esu gabad'aya suka masu nasiha sosai a karshe? hajiya zulfa'u tace ayi? hotuna duk wani abu da'akayi na alada su hajiya zulfa'u sunyi
sannan umma da hajiya zulfa'u suka? nufi hanyar sama da maryama"


Zaune kawai umma take? a parlour'n adamcy amman gabad'aya ranta bai mata dadi ba dan bata san wani irin rayuwa mryamarta? zatayi acikin wannan gidan mai cike da girman kai da izza ba , fitar hajiya zulfa'u daga parlour'n ne ya bawa maryama damar durkushewa ta zauna a gaban umma? tare da kifi kanta akan cinyar umma tana wani irin? kuka mai matukar ta'ba zuciya "numfashi umma ta sauke a yanzu ta sake fahimtar mai yasa maryama take yawon kuka ."tasan kuka wannan tashin hankalin da take hangowa kanta ne yasa ta rasa sukuni da walwala tare da kwanciyar hankali."
umma ta kai hannunta zata kamota domin maidaita inda ta tashi sai ga? adamcy ya shigo parlour'n dan haka ta zaunar daita a gabanta shima daya karasa shigowa durkusawa yayi a gaban umma? tare da tankwashe kafafuwansa kamar yadda maryama tayi sai dai shi zuciyarsa cike take da farinciki sa'banin maryama da zuciya da gangar jikinta suke cikin rauni,ba dan namijin kokarin da take ba tuni da zuciyarta ta buga tun a parlour tsabar firgici ."


Umma tayi shiru tare da zuba masu idanuwanta da suka gama canza kala saboda itama kuka take son tayi tsawon lokaci tana zaune ta tasu gaba so take ta mikawa junansu amana sannan ta tashi ta iske su aunty fatima a k'asa? su wuce gida cikin sanyi murya ta kira sunan mr ata "adamu!"
Ahankali ya d'ago tsumammun idanunshi daga kallon maryama ya zubawa umma tare da amsa mata da "na'am!"dan bazai iya kin amsa mata ba matsayinta a wajen mryamarsa da kuma irin mutuntashin da take ya wuce yayi ignoring dinta sai dai yadda ta kira sunansa ya sanya gabad'aya gabobin jikinsa sun yi sanyi sakamakon muryarta sosai ya tattara hankalinsa gareta dan jinta yake tamkar mahaifiyarsa? ".
"adamu ga maryama matarka nan na kawo maka ita ,adamu ga maryama nan na baka ita amana
Ita din marainiya ce ka rike min ita amana zanji matukar farinciki da kwanciyar hankali idan na ganta cikin tsananin farinciki a gidanka"kayi hakuri daita kayi hakuri daita, duk da nasan ba lallai tayi maka abinda zata kureka ba kasance war tana da tsananin hakuri wanda kai ma kasan da haka, idan kuma har tayi maka ba daidai ba dan Allah kayi hakuri daita saboda har yanzu tana da karancin shekaru."


kuka sosai maryama take umma ta riko hannun maryama ta damka a tafin hannunsa tana danne hawayen dake k'ok'arin wanke mata fuskarta ."
"Kukan ya isa haka maryama kiyi wa mijinki biyayya karki cutar da mijinki,ki rikesa amana duk runtse duk wuya kiji maganar mijinki duk abinda ya umarceki matukar bai sabawa sharia ba kiyi masa,aure ibada ne duk abinda akace ibada ne lallai sai an jajurce akanshi maryama adamu ku rike amanar junanku abinda umma tayita jadda masu kenan dan idan basu rike juna da amana ba komai zai iya faruwa atsakaninsu makiya zasu yi tasiri arayuwarsa ."shiru adamcy yayi yana dubansu yana jinjina girman kaunar dake tsakanin umma da maryama? jikinsa yayi sanyi tausayinsu ya kamashi domin gabad'aya yanayinsu ya nuna basa son rabuwa da juna ."


Muryarsa a sanyaye yace "umma ki kwantar da hankalinki in sha allahu zan rike miki maryama amana babu abinda zai faru daita babu kuma abinda zai rabamu? daita sai dai mutuwa bazan iya cutar daita ya fad'a yana murza hannun maryama dake cikin nashi ahankali cikin wani irin salo da yake sa tsigar jikinta tashi saboda tafin hannunta dake kife acikin nashi gabad'aya jikinta yayi sanyi ya soma rawa cikin wani irin yanayi maryama ta zare hannunta cikin nashi
Sosai yake jin soyayyarta na sake ratsa koina na jikinsa ,sosai yake ji? a ransa kamar zayi matukar wuya ya iya cutar daita, ita ma kuma yana mata kyakkwan zato akan shi gata da kyau ,ga hakuri , ga tsananin kunya ga talent ta kai komai a macen da mutun ya dace ya ajiye a gidansa ba? zai ta'ba had'a soyayyarta? da komai? ba ,haka zalika ba zai ta'ba son wata ba, soyayyarta? kadaice bangon da zata kara danganta shi dashi bayan ita babu wata muddin rai suna tare domin ita kad'ai ce muradin ranshi ."


"maryama kibi mijinki sau da lafa sannan kiyi hakuri da rayuwa Allah yayi miki albarka ,Allah ya dangwamar da farinciki acikin rayuwar aurenki cikin muryar kuka ta soma magana" umma na gode na gode!! da kula warki da adduarki kuma Ina sake barar adduarki? "in sha allahu maryama kullum cikin adduaoina kike kuma bazan gushe wajen yi miki ba ta mikar da maryama tsaye tana dubanta cikin tsananin kulawa shima adamcy ya mike tsaye yana duban su kafin ahankali ya nuna wa umma d'akin kwan ansa kai tsaye ta nufi d'akin daita shi kuma ya fito ."


Ahankali umma ta zaunar daita a bakin gado tana goge mata hawaye tana sake jadadata mata kalmar hakuri da kawar da kai akan duk abinda idanunta zasu gane mata? sannan da barin duk wani abinda bai shafeta ba"Allah sarki maryama kai kawai take gyad'a ma umma? dan zuwa yanzu bakinta ya sake mutuwa ko tayi yunkurin bud'e bakinta ma bazata? iya cewa komai ba umma tace "bari na kira su subai'a su shigo miki da akwatu nan kayanki umma ta k'arasa maganar tana kiran layin subai'a cikin kankanin lokaci ta jiyo sautin muryarsu? ta leko daga cikin d'akin da take tana cewa "nan zaku shigo suka shiga dashi suka jera mata a waje d'aya subai'a ta k'araso ta zauna kusa da maryama tana rarrashinta umma tace "to maryama mu zamu ce sai an kwana biyu zan lekoki ta kalli su subai'a tana masu sallama da zata wuce maryama ta riko hannun umma jikinta na wani irin rawa dole umma taja ta tsaya tana kallonta tana sake danne hawayenta dan ita kanta tana jin tsananin son yi kuka amman tasan muddin tayi kukan maryama sai yafi wanda take yi cike da jin kewarta tasa d'ayan hannunta ta zare hannunta ta juya bata sake yunkurin juyowa ba har ta bar gabad'aya bangaren ."


*****

Bayan an idar da sallah isha'i adamcy? yasa aka maida kawayen maryama tare da d'inbin alkhairi lokacin da abokansa suka bukaci suyo masa rakiya wajen amaryarsa dojewa yayi yace "ya sallami kowa ,kowa ya? kama gabansa suna dariya suka wuce dan sun san halinsa d'an raayi kanshi ne idan ya nuna bai ra'ayin abu tofa babu wanda ya isa ya canzasa ."karfe goma daidai ya shigo bangarensa bayan yaje gurin mami yayi mata sallama ahankali ya miada kofar ya rufe ya tsaya ajikin kofar tare da tsura mata tsumammun idanunshi yana kallonta tun daga kan zara zaran yatsun kafafunta da suka sha jan lalle tana nan zaune a inda suka barta jikinta lullube ."
tunda ya shigo zuciyarta ta rikice? ta dinga bugawa da sauri sauri yayinda jikinta ya sake d'aukar rawa hakan nan? taji tausayin kanta ya mamaye zuciyarta kamar yadda shima zuciyarsa take cike da tsananin tausayinta ."ahankali ya soma taku har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login