Showing 60001 words to 63000 words out of 151781 words

Chapter 21 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2668

baya ji baya gani ."

Yana k'ok'arin kamota karar wayarsa? ta dakatar dashi gabad'aya duk sai suka zubama wayar ido suna jin fad'uwar gaba har ta tsinke bai d'auka ba sai da wani? kira ya sake shigowa? sannan ya daga Muryarsa vary low yace, " bright yaya dai?".
Mamaki da al'ajabi ya cika bright , ya cire wayar daga kunnensa ya duba dan tabbatar da mr ata ne kuwa?, lallai shine dan haka ya maida wayar a kunnesa yana fad'in "kana? lafiyarka kuwa sir ?".
Ciza? lips dinsa na kasa yayi tare da katse wayar, dan in dai a haka zasuyi wayar nan yasan bazai fahimci komai ba kuma yasan tunda yaga kiransa akwai sako da'aka turawa maryama. ajiye wayar yayi? ya shige bathroom da? kallo k'asan idanu? kawai ta iya binsa daahi amma ta kasa ko kwakwkwaran numfashi a inda take ."

? ??
? ? ?

Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
? ?? MAR'ADAMS
? ?? =ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

? ? ? ? ?? Page 14


Adamcy kam ruwa ya kunnawa kansa had'e da dafe bangon bathroom din da hannuwansa duka,yayinda a hankali ruwan ya dinga sauka a saman kansa at the same time km sai faman ciza lips dinsa na k'asa yake da karfin dan danne karfin sha'awar dake taso masa dan shi kad'ai yasan halin da yake ciki domin ahalin da yake ciki ji yake kamar zai ci babu baya jin zai iya d'aga mata kafa na wasu kwanaki idan ma yayi dauriya to na yau ne kawai. dan idan ya cigaba da jurewa to fa komai zai iya faru wa dashi.
Jikinsa a matukar sanyayye ya soma k'ok'arin
fitowa ,a inda ya barta zaune cikin tsananin shaukinsa a nan ya fito ya isketa bata ko motsi ."kallo d'aya ya mata ya d'auke tsumammun idanunshi akanta sannan ya zauna a bakin gadon yana goge kansa da k'aramin towel bayan ya gama ya kwanta a kife yana jin wani irin zazzafan reaction da sauyin yanayi a gabad'aya ilahirin jikinsa, ahankali yasa hannuwansa duka ya dafe jijiyarsa ta karkashi tare da sake runtse tsumammun idanunshi dan harbawar da take babu sauki ."

ringing din da wayarsa ya sake yi ne ya dawo da
Maryama daga fita haiyacinta da tayi na wuncin gadi ,dake wayar tana kusa daita ta waiga inda wayar take tana sauke wani wahalallen numfashi idanunta suka sauka a akan wayar sunan amar ta ga yana yawo a screen din wayar hannunta ta Kai ta dafe goshinta tana sake sauke wani wahalallen numfashi adaidai lokacin daya juyo ya tsura mata idanunshi yna kallonta cikin tsananin sha'awarta har lokacin wannan abar tasa bata kwanta ba tana nan a mike ,tana k'okarin kawar da fuskarta daga kallonsa taga yay mata alamar ta kawo masa wayar"a natse ta jawo wayar da d'ayan hannunta ta yunkura ta mike tsaye ta nufo inda yake kwance da kyar take d'aga kafafunta saka makon idanunshi dake tsaye kyam kanta jiki a sanyaye ta miko masa wayar ya kai hannunsa ya amsa had'e da riko yatsun hannunta ya fixgota aiko nan take ta zubo jikinsa saurin d'auke numfashi sukai atare alokcin da kiran ya katse."

bakinsa dake daidai kunnenta yasa ya d'an ciza gefen kunnenta,ahankali ta lumshe idanunta tare d'an zabura zata mike ya sake maidaita jikinsa yana hura mata iskar bakinsa sannan ya danna wayar yabi kiran amar yana cigaba da hura mata zazzafan iskar bakinsa dake tsananin kashe mata sansar jikinta,ajiyar zuciya ta sauke da karfin gaske,lokaci guda kuma zuciyarta na wani irin bugud'en bugu,ringin d'aya amar d'in ya d'aga da k'yar adamcy yace "amar ya'akayi ne ?".
yanayin yadda amar yaji muryarsa yaji kmr ya kwashe masa da dariya amman sai ya samu kanshi da danne dariyarsa, yace"adamcy lafiyrka kuwa naji muryarka wani iri ?"babu komai ya akayi ne ?".amar ya toshe bakinsa gudun kar dariya ta kufce masa ya shiga uku dan yasan halin abokinsa mugun rigimamme ne yanzu zai birkice masa "idan ma ba rainin yawo irin nasa ba a hannu yake fa amman wai babu komai yace "to naji babu komai aje a haka duk da nasan ango a hannu yake dan .."amar...!" ya kira sunansa cikin wata irin kasalalliyar murya "

Amar yayi murmushi yana shafa sumar kanshi yace "nifa ban gane wa wannan muryar ba "amar fad'a dalilin kiran idan babu dalili na ajiye wayar?"kana jina daman akan batun chemical cement din da za'a shigo dashi ne wannan satin nake son muyi magana akai "Okay Ina jinka!" adamcy ya fad'a yana mikewa zaune tare da maryama ya zaunar daita akan cinyarsa yana kissing din wuyanta. wani iri felling's taji from know where yana bin kowace gaba ajikinta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa tsaye tayi kasa da kanta ta kasa had'a idanu dashi ."
Ahankali amar ya dinga masa bayani sai dai shi adamcy kwata kwata hankalinsa baya garesa yana ga gashin jikin maryama daya ga suna mikewa ."
tafin hannunsa ya kai yana kwanrtawa kafin ahankali ya maida yatsan hannunsa k'irjinta zuwa wuyata yana yawo dashi ,ita dai kmr an dasata zaune akan cinyarsa dan kasa dakatar dashi tai duk da abinda take son yi kenan amar yace "kana jina kuwa ?"adamcy yayi sauri ya fixgo numfashi ya sauke yace "hello ..!hello !! alamun baya jinsa can kuma yace "sorry amar network ba kyau kwata kwata bana ji abinda kace ba ko zaka iya sake maimaita min abinda kace ."?

ganin da gaske dai adamcy baya haiyacinsa kuma komai zai fad'a masa alokacin bazai fahimcesa ba yasa shi cewa "bari kawai zan tura maka komai sai kayi min reply kawai "okay !" ya fad'a yana rungume maryama tsam ajikinsa tare da zagayo da hannuwansa saman cikinta cikin kasalalliyar muryarsa yake mata magana acikin kunnenta "my princess karki bari yau ma nayi bacci irin na jiya batare da na samu natsuwa daga gareki ba ".
Tana jinsa tayi shiru tana jin yadda zuciyarta ke rawa "zan biki ahankali bazan miki yadda zaki sha wahala ba "a d'an rikice ta d'ago ido suna kallon juna ido cikin ido ,maryama dake zaune akan cinyarsa ji tayi kamar ta sume masa dan ita kanta tana jin kwatan kwacin abinda yake ji sai dai ita kam bazata iya wannan juriyar ba tayi shiru tana kallonsa kamar yadda yake kallonta
da idanunshi da suka gama canza kala hakan ne yasa hawaye ke shirin zubo mata ya sake kai bakinsa saitin kunnenta "kul!"karki kuskura wannan hawayen ya zuba dan zai iya canza min lissafi ."

da sauri ta share hawayen kumatunta dan tuni sun zubo muryata a sanyaye tace "yallabai dan Allah kayi hak'uri wlhy ina jin tsoro dan nasan muddin kayi mutuwa zanyi "bazaki mutu ba !" "Allah zaka kasheni idan kuma kana son ka kashe ni ne shikenan na ma huta da wannan rayuwa gabad'aya "tayi maganar fuskarta d'auke da tsananin tashin hankali."murmushin gefen baki yayi tsumammun idanunshi na kanta yace"bazan kasheki ba my princess kawai dadi zamu jiyar da juna kamar yadda na sanar miki ahkl zan biki
ki kwantar da hankalinki kawai cikakkiyar mace zan maidake "ya fad'a yana kissing din soft lip's dinta kanta ta girgiza masa tana sake share sauran hawayen"kinsa yadda ake murza stearing mota ?"ta kasan idanunta ta d'an saci kallonsa batare data ce masa uffan ba "yadda kika ga ana murza stearing mota ahankali haka zanbi dake cigaba da satar kallonsa take .ahankali ya janye idanunshi akanta sannan ya zaunar daita cike da basarwa kamar bashi ya gama narkewa ba ya tashi ya koma gaban mirror duk uzirinsa yayi ya gama sannan ya matsa ga wardrobe ya ciro kayan da yake buk'atar sakawa .

ganin haka yasa maryama ta zame ta kwanta akan katifa ta yadda bazata gansaba dan taga alamun yana shirin sakin towel din da yake d'aure dashi ,baki kawai ya ta'be a ransa yace "duk wannan bashi zai sa na cigaba da d'aga miki kafa ba Allah dai ya kai mu gobe ."anatse ya cigaba da saka kayansa kananan kaya wando da riga army green, ya sake d'aukar kwalbar turare ya feshe jikinsa nan take d'akin ya sake gauraye wa da kamshi turarensa yayi kyau sosai .
bayan ya gama ya matso kusada ita ya kai hannunsa kan bombom dinta ya d'an matsa yana cewa "tashi ki min rakani wajen sweetheart."
Ahankali ta juyo daga kwanciyar da tayi tana dubansa sai dai fuskarta ta d'an sauya alamun bata ji dadin abinda ya fad'a ba kamar tace wani abu sai kuma ta yunk'ura ta tashi kawai dan bata son ta nuna masa bata son zuwa wajenta yayi tunani wani abu da sauri ,hannunta ya kama ya taimaka mata ta tashi zaune sanan ya fita abinsa hakan yasa ta fahimtar zai jirata a parlour kenan bata 'bata lokaci ba ta bud'e akwatinta da niyyar d'aukar mayafi hannunta yaci karo da after dress shi ta d'auka ta d'aura a saman kayanta sannan ta nad'a vail d'in rigar, fes ta fito kamar ka saceta ka gudu abinka.."

Tunda ta fito ya zuba mata tsumammun idanun shi yana kallonta ko kiftawa ba yayi shi kansa yasan mugun maye ne akanta duk basarwarsa duk ajinsa tattare da miskilincinsa basa wani tasiri akanta, haka ne yasa take d'auka jikinta yake so ba ita ba , tana gama k'arasowa garesa ya mik'e tsaye yaso ya rungumeta sai dai sanin abinda zai biyo baya ne yasa yayi gaba. a natse ta biyosa abaya tana jin wani irin mummunar fad'uwa gaba da tashin hankali mara misaltuwa shi kuwa ko ajikinsa alamun ya nuna ma hanka linsa a kwance yake dan yadda yake taka steps d'in zai fahimtar da Kai babu wata damuwa atattare dashi, komai nashi a natse yake hatta yadda yake taka step dole ne ya birgeka, duk takunsa idanunta na kai yayinda itama take binsa a hankali,babu kowa a falon, dan haka suka nufi bangaren mami a parlour'nta na biyu suka iskesu gabad'aya har hajiya zulfa'u da ya'yan mami ya sha mamaki ganisu kenan a gidan ma suka shi kam ya rasa me suka d'auki mazajensu ?.shi kam duk mutuwar da zai yi akan mace bazai ta'ba bata wannan damar ba "

Ahankali maryama ta rage takun da take ta koma tana tafiya kamar wacce bata da laka ajikinta ."Tana kallonsa har ya k'arasa kusa da mami yana kokarin zama ne idanunshi ya sauka akanta kallon second biyu yayi mata yasa ta karaso inda taga an sakar mata fuska wato kusa da hajiya zulfa'u ta raku'be kamar zata shige jikinta tana gaisheta cike da sakin fuska hajiya zulfa'u ta kamo hannun maryama cikin nata ta damke tace "lafiya kalau maryama ya kika tashi ya kuma bakunta ?"maryama kam shiru tayi ta kasa amsa mata saboda abu biyu ne suka had'e mata waje d'aya tsananin tsoro da kuma matsanancin kunya ."zabiba ma fuska a sake take dubanta tana jin lokacin da kannensa suka gaishesa ya amsa masu muryarsa a dake babu alamun wasa sannan ya gaishe da mahaifiyarsa inda ta amsa masa taja bakinta tayi shiru,dalilin da yasa maryama ta d'an d'ago a natse ta saci kallon fuskarta ,"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "wannan shine karo na biyu data sanyata acikin kwayar idanunta yau din ma fuskarta kamar ranar farko data fara ganinta ce fuska babu yabo babu fallasa bare ayi tunanin annuri yayinda idanun yan'uwansa mutun uku ke kanta sun zuba mata ido wanda babu komai acikinsu sai zallar gargadi hakan ne yasa jikinta ya kama bari ."

Adamcy ya gaishe da hajiya zulfa'u fuskarta cike da matsanancin farinciki ta amsa, bai kalli inda su aunty khadija suke ba bare su samu darajar gaisuwa daga garesa ,hakan kuwa ya bakantawa mami rai dan ta tsini wannan rainin da yayi masu ahankali maryama ta maida idanunta akan mami dake hankince cikin shiga ta kamala tana motsa bakinta taji sun kama rawa har hakoranta bata san ya'akayi taji magana ta d'auke mata ba ta d'an saci kallon adamcy ,da kwayar idanunshi yayi mata alamar ta gaishe daita ."ta sake aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "Ina kwana !".
ta k'arasa maganar jikinta na wani irin kyarma mami da duk wad'an da suke zaune a parlour'n sunji amman ta share duk da tasan ita aka gaisar adamcy ya kai hannunsa ya kamo na mami cikin nashi tare da yin kasa da muryarsa "sweetheart maryama na gaisheki "ta rike gaisuwarta tunda bata yi niyyar gaisheni ba sai da kasata ".

Maryama na jin haka ta sunkuyar da kanta kasa ta had'e hannuwanta waje d'aya ta tsarke dan bakaramin taimako hakan zai mata ba a zaune da take ,adamcy ya kai d'ayan hannunsa ya shafa goshinsa na second d'aya sannan ya maida hankalinsa ga mami "sweetheart wannan yarinyar fa matsoraciya ce , ki kalleta da kyau a tsorace take ,hajiya zulfa'u tai murmushi har ta bud'e baki zatai mgn ta tsinkayo maganar mami inda take cewa "wa take jin tsoro a nan ko kuma wake tsoratata?"shiru yayi yana duban mami yana nazarin maganarta ganin tana son juya masa magana .yaji kamar yace mata ya'yanta ke tsoratata sai dai ya danne saboda duk abinda zai fad'a mata a yanzu bayansu zata bi ,tunda yanzu bata son gaskiya ,"anan babu wani abun tsoro sannan babu maye bare taji tsoro ita dai tasan abinda ke tsoratata karka sake zuwa min daita a firgice matukar bazata samu natsuwa ba tai zamanta bana bukatar gaisuwarta ."

da sauri hajiya zulfa'u tai masa gargadi da kwayar idanunta alamar kar yace komai nan take ya runtse idanunshi gam yana danne zuciyarsa dake k'ok'arin motsawa bazai so yayi wani abu a gaban maryama ba ,dan bazai d'auki rainin mahaifiyarsa ko yan'uwansa daga gareta ba Maryama kam tashi shiga tashin hankali matuka sai dai tai ta karanto la ila a illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin wanda shi ya ba kwarin gwiwar sake d'agowa ta gaishe da yan'uwansa suka amsa mata da" lafiya !atakaice suna yatsuna fuska kamar sun ga mugun abu zabiba ce kawai ta amsa da kyau kuma ita daman tun farkon ganinta daita tasan suna da bambamci ra'ayin."
"ta sake maida kanta ta sunkuyar tana jin mummunar fad'uwar gaba ."yanayin da mami tayi kwata kwata bai ma adamcy dadi ba dan sai wani faman cika take dan haka ya mike tsaye tare da karasowa inda maryama take raku'be ya miko mata hannunsa sai dai taki yarda tayi wannan gangancin, ta yunkura jikinta a sanyaye zuciyarta na wani irin rawa dan itama Allah Allah take ta bar parlour'n idan ma da hali har gidan bata son zama acikinsa".

tun kafin yayi gaba ya barta ta nufi kofar fita
daga parlour'n ya biyo bayanta a natse suna fita babban parlour'n ya riko laulausan tafin hannun ta cikin nashi yana Jin yadda jikinta yake rawa suka haye sama a parlour'nsa ya tsaya ya janyota zuwa faffad'an k'irjinsa ya manneta tare da zagaye kungunta tana k'okarin zare jikinta ya sake rike kugunta da kyau ya d'aura kanshi a gefen wuyanta "ki rage wannan tsoron idan ba haka ba zai cutar damu." aranta tace "ka barni da tsorona idan ma kasheni zai yi ya kasheni dan muddin Ina cikin gidan nan tare da mahaifiyarka da yan'uwanka zuciyata bazata rabu da tsoroba ."
bedroom dinsa ya shige daita yana zare after dres din jikinta dama kayan jikinta ya fara wasa da sansar jikinta ita kam ta yiwa kanta alkawari ko babu sharadin yan'uwansa akanta bazata yarda ta mallaka masa jikinta ba tunda mahai fiyarsa bata sonta bata kaunar ta."acan parlour'n mami kuwa sosai hajiya zulfa'u ta rufe su aunty khadija da fad'a "gaskiya ban ji dadin tarbar da kuka wa yarinyar nan ba ,menene laifinta ?"bafa ita tace ya aureta dole ba shine yayi ra'ayi sannan kusani fa shi fa d'anuwanku ne ita kuma wacce kuke taya kishin cousins ce kuma da ta samu dama a wajensa da zaku ga sa'banin tunaninku ita dai mami bata ce uffan ba dan bata ga laifin da sukai ba ,ta gaishesu kuma sun amsa ai shikenan ."

Bangaren adamcy kuwa ahankali ya dinga rud'a jikin maryama da zazzafan romance wani fellings of excitement with love ne ya dinga shiga jikinta ta runtse idanunta gam tana amsar sakoninsa da kyar ta fixgo magana tace "yallabai bacci !"bakinsa ya kai cikin kunneta yayi mata magana cikin rada "kina jin bacci ne ?"ta gyad'a masa kai alamun "eh!"okay kiyi bacci "numfashi ta fixgo da karfi ta sauke dan tasan bazata iya ba idan tana jin tafin hannunsa ajikinta , harshensa ya zira cikin kunnenta ya fara tsotsa cikin wani irin murya tace "wayyo Allah dan Allah ka cire ganin yaki aiki tasa masa kukan shagwaba dole ya bari sai dai bai zareta ajikinsa ba ya rungumeta kawai tunda taji ya bari ta runtse idanunta bata sak? budewa ba har bacci ya d'auketa ."
ganin haka ya zareta ajikinsa ya janyo wayarsa ya soma neman layin bright yaji dalilin kiran sai dai yaji computer na cewa the number you've calling is switch off ya ajiye wayar ya d'auki nata ya shiga inbox bai ga komai ba , mikewa yayi ya fice daga d'akin ".

maryama ta dade tana bacci kafin ta tashi sai dai tayi mamakin ganinta ita kad'ai bata san lokacin da adamcy ya fice ba saukowa tayi daga kan gadon tana duba wayarta karfe uku saura ta shiga bayi ta watsa ruwa ajikinta tai alwala ta fito tana tsaka da goge jikinta taji ana knocking dan hk ta janyo hijab ta zira da sauri ta fito zuwa parlour'n ta bada umarnin shigowa mai aiki ce ta turo kofar ta shigo hannunta rike da tray dake d'auke da manya kuloli ta gaishe daita cike da sakin fuska maryama ta amsa tana kokarin amsar tray hannunta tabawa tace "a'a ranki ya dade ki bar shi !ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login