Showing 111001 words to 114000 words out of 151781 words

Chapter 38 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2690

uwarta sai dai karta fito "wallahi zaki sani tunda kika yi silar rabamu da d'anuwanmu kema zaman gidan nan sai yayi miki zafi zamuyi addua kam ya dawo haiyacinsa amman kema zaki ci ubanki ".inji cewar aunty ."
khadija."

Aunty khadija ta numfasa tace "auta na baki wannan aikin ki tabbatar kin lakadawa wannan yar gidan matsiyatan mugun duka "ai karki damu aunty bani kad'ai zanyi wannna aikin ba tare da sister zamu ci ubanta ai wallahi adamcy ya cucemu daya auro mana wannan yarinyar aunty khadija taja hannun nana hauwa'u suka sauka suka koma parlour'n mami alokcin mami ta fito tana cewa "ai ni ba aurenta bane damuwata a yanzu kamar yadda kuka ce ubanta d'an giya ne uwarta kuma karuwa ce wallahi wannna shine babban tashin hankalina "asalinta kenan sai dai mu d'age da addua kuma muyi maganinta Allah sarki maryama kam tana can ciki tsananin tashin hankali hannunta rike da waya tana son ta kira adamcy tana jin tsoron abinda zai biyo baya jin sun wuce yasa ta sauke naunauyen ajiyar zuciya."Duk wuni ranar a storace maryama tayi sa acikin d'akin da ta d'an ji motsi jikinta zai Kama rawa har most especially kasan mararta ta kai hannu ta dafe kasan mararta da take wani irin karkarwa shiyasa bata sauka dan karta had'u dasu daga d'akinta sai parlour'n ko abu take bukata hakura take har sanda zai dawo ta kwanta flat akan kujera dafe da mararta tana zubar da hawayen cin mutuncin iyayenta da sukai ."


Karfe biyar daidai ya dawo gidan kallo d'aya yayi mata ya fahimci akwai abinda ke damunta dan ko kusa dashi bata zo ba yayi mata tambayr duniya tace babu komai kanta ke ciwo "shine ba zaki kira ki fad'a min ba?" ya fad'a yana janyota ya had'eta da jikinsa ya kai hannunsa daidai kanta normal yaji kanta sannan ya zarce da hannunsa kasan mararta yana shafawa ahankali "me kika bawa baby nah yaci ?"tai masa narai narai da idanun tana had'e fuska "nifa bana da komai "ai bazaki san kina da ba amman ni naji alamun kina da akan jijiyata "Allah bani da komai karki min mutsu mana dan rashin wayonki bazai bari ki fahimta ba, ya kai bakinsa yana tsotsa karan hancinta ta zare jikinta ta koma can nesa dashi ta tsaya ."ahankali ya taka ya sake janyota jikinsa gabad'aya ya rungumeta tare da matseta gam ajikinsa wani iri taji ajikinta nan take gabad'a ya tsigar jikinta suka mike hatta numfashinta sai daya nemi ya d'auke sakamakon irin rungumar da yayi mata "Ina son ki haifa min yara da wuri."

"Bayan kana da wata !"naki nafi so !ya fad'a yana shafa mata sansar jiki "bari na baki maganin ciwon kai kafin lokacin sallah yayi wani kallo tayi masa tana shagwabe masa fuska "naki wayon tunda ka fita kaina da marata ciwo suke "yarin yar nan fa na gano ki babu abinda ke damunki so kike ki doje min kuma baki isa ba haka yayita jagwalgwalata har sai da yaji kiran sallah daga massalaci dake cikin estate din sannna ya barta ya shiga bayi ."da daddare da misalin karfe goma adamcy na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda maryma ke zaune a tsakkiyar gado ta cigaba da karatun novel din d'azu , madadin tayi murmushi saboda kashi hamsin na damuwarta ta kau amman taki sakin fuska yanzu ma tana karatun ne dan samun sausaucin abinda ke damunta sai tayi kamar ta fad'a masa sai ta danne ."shi kuwa lokaci lokaci ya kan d'ago idanunshi ya kalleta saboda gaba d'aya hankalinsa yana kanta ."

shiru yayi na second biyar yana kallonta cikin rigar bacci fara sol iya gwiwarta ahankali ya d'auke idanunshi ya maida kansa ya cigaba da aikinsa da yakeyi ,sai dai kasa cigaba da aikin yayi ya taso daga shi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon inda take rigingine itama sai ta tashi zaune sosai tana kallonsa ya zauna a gefenta tare da ajiye mug d'in hannunsa akan bed side d'in, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannusa ya miko mata alamar tazo garesa .bata musa masa ba ta matso ya janyota gabad'aya ya had'e ta da jikinsa tare da makaleta a tsakkiyar k'afafunsa.ahankali ta zame ta kwanta ta d'ora kaina a cinyarsa daman wajen da ya fi son ta kasance kenan ya kar'bi book d'in hannuna ya ajiye a gefe, ya d'ora hannusa a saman cikinta yana sak? maimaita tambayarta damuwarta "wai meke damunki ne ?"cike da sanyin jiki ta shafa sajensa shi kuma ya d'an ciza lips dinsa na kasa "miyasa wataran kike da miskilanci ne ?"tace "ni d'in?". 'ta fad'a tana nuna kainta da kallonsa'.sai wani basar dani kike inata tambayrki meke damunki ?"..


"Me ka gani ne kake ta faman tambayata?" yace "abubuwa dayawa"tace to babu komai kasan wani lokaci yanayin mutun yana canzawa haka dai na yini yau ban sani ba ko dan kaina da marata dake ciwo ne "ta fad'a tana gyara kwan ciyarta ajikinsa wanda yasa shi Lumshe idanun shi , ya duk'o a hankali ya manna mata kiss mai kyau a goshinta .sannan ya dauko novel d'in yana duba shafin da take kallon kasan ido yayi mata sunkuyar da kanta tayi tare da kai hannu ta Shafa sumar kanta????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ta kai hannu zata kar'bi book din ya hanata yana furta sunan book din how I love to be loved,a lokuta dadama waanan book din ke debe min kewarki most especially wannan page din ya damk'a mata book din a hannu yana shafa sumar kanta aranta tace dole kaso page din tunda iskanci ne zalla amman a zahiri murmushi ta sakar masa very interesting novel "wow!"ya fad'a da d'age mata girarsa d'aya bakinta ta turo masa tana girgiza masa Kai yace kina son ki tashi kaina kenan ?"ta sake girgiza masa kai tana mur mushi shi din ma fuskarsa a sake take ta fahimci sai lokacin ya samu natsuwa , ya jawo lap top d'insa ya cigaba da aikinsa ita kuma ta zuba masa ido yana cigaba da aikinsa batare da ya kalleta ba, idonsa na kan system d'insa yace, "kallon fa ko kina bukatata ne ?"

ahankali ta d'auke idanunta tana tabe baki a ranta tace "aikin ka kenan!"shima ta'be baki yayi alamar me yayi . karatu ta cigaba shima ya cigaba da aikinsa yana shan coffee time to time yayi aiki mai tsawo kafin ya saki wani ajiyar zuciya, ya kalli maryama da barci ya kwasheta hannunta rike da novel fuskarta ya shafa yana sake sakin ajiyar zuciya bayan ya gama ya duba camerorin gidan shiru yayi tare da kai yatsan hannunsa kan hakorinsa ahankali yaga duk abinda ya faru a gidan mamaki ya cika zuciyarsa hankalinsa yayi matukar tashi ganin irin gudun da maryama tayi domin ceton kanta daga nana hauwa'u ya ALLAH wannan irin tashin hankali ne haka ?"ya furta a fili yana kallonta baiwar Allah shiyasa yanayinta ya sauya zuwa damuwa amman kuma taki fad'a masa abinda aka mata "nan take zuciyarsa ta dinga masa tuttukin bakinciki ya duba agogon wayarsa karfe d'aya da wasu mintuna ta wuce Amman bazai iya hakuri har garin Allah ya waye ba number mijin aunty shahida ya kira kiran na shiga ba'a d'aga ba haka zalika ta mijin aunty khadija kira uku yayi ana na hud'u ne ya d'aga cikin bacci yace "adamcyn .."adamcy ya katse shi da sauri ta hanyar furta sunansa "kabir!wanda aka kira da haka ya mike zaune yana damke wayar hannunsa da kyau "kabir!! sau nawa na kiraka ?" yace sau biyu "ka jawa matarka kunne ta fita a hanyar matata idan ba haka ba zan d'auki mummunar mataki akanta yana gama fad'ar haka ya katse kiran ya kira hisham shima cikin sa'a ya d'aga abinda ya fad'a wa kabir shi ya fad'awa hisham ya katse wayarsa yana dafe goshinsa yana furzar da iska mai zafi ."

Ya d'auki kusan mintuna talatin yana dafe da goshinsa sannan ya cire hannusa yana ciza lip's dinsa ahankali ya soma motsa bakinsa "idan kunsan wata baku san wata ba idan na daukeki muka bar kasar gabad'a ya zan ga yadda zakuyi ya k'arasa maganar yana sumbatar goshin maryama,kwanciya ya gyara mata ya ja bargo ya lullu'ba mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala kamar yadda ya sabar ma Kansa kafin ya kwanta sai yayi alwala bayan ya fito ya kwanta a gefenta zuciyarsa na cike da tausayinta addu'a ya musu sannan yasata a jikinsa yana shafa jikinta tana jin motsinsa a jikinta ta share ta cigaba da baccint"Washegari bai nuna mata yasan komai daya faru ba sai dai bayan yayi breakfast ya gargad'eta da karta sake ta fita duk abinda take so da zarar ta danna bell masu aiki zasu zo su kawo mata ."
tai shiru tana jin bayaninsa har ya gama ya riko hannunta suka fito tare zuwa bangaren mami koda suka shiga tana bayi tana wanka wankata kuma yana d'aukar lokaci amman haka ya zauna jiranta ,itama haka ta zauna ya riko hannunta cikin nashi yana murzawa yace "ko dai zan tafi dake ne !"kamar tace masa!eh!sai kuma ta girgiza masa Kai ."

"me yasa yanzu bakya son cigaba da zane naga ko a gida bakya yi ?"zan cigaba mana hutun wata nawa aka bani domin nasan ranar komawa aiki ?""ba maganar komawarki aiki nake yi ba ai aiki kin gama dashi har abada sai dai idan ina bukata zaki min a gida"ya fad'a yana kissing din hannunta yana matseta da jikinsa tare da kai bakinsa daidai kunneta tayi saurin zame jikjnta daga nashi "yalla'ba mami fa karta fito ya sake matseta yana harararta yace"ni fitowarta nake so ai "naunauyen ajiyar zuciya ta sauke ita dai Allah ya had'ata da gamonta babu jimawa mami ta fito kafin yayi wani abu ta zame ta durkusa kasa tana gaisheta "ta d'an yi shiru tana dubansu dan ta ga yanayin da suke harara ta buga ma maryama tana nuna mata hanyar waje da hannunta ta d'an yi shiru tana dubanta duk da ta fahimci abinda take nufi .""Sweetheart kina nufi maryama ta fita?" ya tamabyeta yana had'e fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa "idan bata fita ba me zata min ?".

"haba sweetheart me yasa ?"idan bata fita ba yanzu zan bar maku d'akin d'an bazan kasance tare da makiyiyata ba domin duk mutumin da yayi silar rabaka da d'anka babban makiyinka ne bakinciki ya kama maryama zuciyarta kamar ta Kama da wuta "bana son gaisuwarta bana buka tar ganinta kai ma idan bazaka zo kai kad'ai ba na yafe amman karka k'ara shigo min da wannan abar tunda bayan asiri data maka yan uwanka ma ka bata damar ta rainasu wai har wannna yarinyar shahida zata gaya ma magana saboda ta samu d'aurin gindi a wajenka taci darajata jiya da jikinta ya gaya mata dan haka iskancita ya tsaya akanka kai da ka kawota amman ni da ya'yana kul .."cike da sanyin jiki maryama tabi ta gefensa ta bar d'akin zuciyarta na zafi bai ce ma mami komai ba shima ya fice ya biyo maryama yana k'ok'arin kamota ta goce tana buge masa hannu ta shige parlour'n ya shigo yana ya sake kai mata hannu ta sak? gocewa " gabad'aya ya cakumota yana cewa"ke menene haka ?"kuka ta fashe masa dashi mai tsuma zuciya tana cewa "kwanaki kawai nayi a gidan nan amman Ina Jinsa kamaar shekaru nayi acikin azaba, ni dai dan Allah ka rabani da gidan nan ko kuma ka sauwake min dan bazan iya cigaba da zama acikinsa ana ci min mutunci ana ciwa iyayena ba" ta k'arasa maganr tana kokarin kwace jikinta daga nashi amman ta kasa sakamakon rikon da yayi mata ba wanda zata iya kwacewa bane "ni me nayi wa mami ne data tsa .. ."bata kai ga k'arasa maganrta ba ya rufe mata baki da bakinsa ."


Mmn sudais


=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Page 24

Idanuwanta dake cike da ruwan hawaye ta zuba masa shima idanuwanshi ya zuba mata yana jin yadda soyayyarta ke sake ratsa shi yana tsananin sonta kuma bazai ta'ba son wata halitta sama daita ba,ya kusan minti goma yana tsotsar? lip's dinta da hakoranta sannan ya cire bakinsa ya damke yatsun hannunta cikin nashi ya tsurawa fuskarta ido yana cigaba da kallonta da yadda numfa shinta ke fita da sauri sauri "kiyi? hakuri in sha allahu zan d'auki mataki akai "d'ayan hannunta ta kai saman nashi ta zare hannunta tana cewa "karka wani d'auki mataki akan kowa dan bazan so na zama silar shiga tsakanin yan'uwa ba kawai dai mu nisanci juna kamar kowa zai fi samun kwanciyar hankali da salama ".had'e fuska taga yayi sosai yana jifanta da? mummunar kallo mai d'aga hankali wanda a duk sanda yayi irin haka to ransa yayi kololuwar 'baci,hakan yasa taji wani irin yanayi a gabad'aya ilahirin jikinta,k'irjinta ya dinga bugawa da karfin gaske kamar wacce ake bugawa guduma dan haka ta dinga sauke ajiyar zuciya tana wasa da yatsun hannunta bayan ya gama hukuntata da mugun kallo har na tsawon mintuna shabiyar sannan yace "to be your first and last da zaki sake furta min wannan kalmar idan ba haka ba zan canza miki canzawar da zai baki mamaki "sake tsura? masa shayayyun idanu wanta tayi wanda yaji kamar ya sume a zaunen da yake a gabanta ."tana kallonsa ya mike tsaye a natse? yana daidaita natsuwarsa da bugun zuciyar sa dake faman bugawa ,ya cire suit dinsa ya saura daga shi sai yar samanta da fara riga da dogon wondo ya cire shoe's? din kafafunsa ya sanya slippers ya fita ."


tana ganin fitarsa ta janyo numfashi? da kyar ta sauke tana fashewa da wani kuka mai cin zuciya ita kad'ai tasan yanayin data shiga alokcin da suka kira mahaifinta da d'an giwa tare da ai banta mata mahaifiya wacce duk duniya bata da kamarta ,ta sak? runtse idanwunta da karfi alokcin taji tsokar zuciyarta tana tattarewa waje d'aya acikin ranta take hango girman tashin hankalin dake sak? shirin tunkarota"da kikace ku rabu ke zaki iya rabuwa dashi ne?"nan take wani bangare na zuciyarta ta jefa mata wannan tmbayr? "zan iya rabuwa dashi mana tunda ba tare muka zo duniya ba na rasa mahaifina ma na cigaba da rayuwata bare wani miji akan dai a dinga ciwa iyayena mutunci gara na hakura dashi. shiru tayi zaune kafin ahankali ta zame ta? kwanta tana sauke numfashi da tunanin inda ya nufa dan tasan ba ma'akata zashi ba tunda ya rage kayan jikinsa "kai tsaye adamcy bangaren mami ya nufa inda ya isketa zaune? tana waya wanda ke nuna masa alamun da d'aya daga cikin ya'yanta ne bai tsaya ta gama wayar ba?? ya soma magana cikin zafin rai "a gaskiya sweetheart abinda kike yi kwata kwata ba girmanki bane ki dinga biye ma wad'an nan ya'yan naki ana? ciwa yarinyar mutane mutunci a gidan nan ana zalintarta ke daya kamata ki tsawata masu amman kece kike karfafa masu gwiwa kina biye masu mussaman ma wannan 'yar iskar khadija din to gaskiya Ina ganin lokacin zamanmu a gidan nan ya kare gaskiya zan d'auki matata mu kara gaba muje inda zamu samu zaman lafiya da kwanciyar hankali tunda kema tsamgwamarta kike? yi ."

tunda ya soma magana take kallonsa hankalinta bai tashi ba sai data ji batun zai d'auki matarsa su bar mata gidan muryarta cike da matsanancin tashin hankali tace"adamcy ni sa,arka ce da kake fad'a min magna da min gargadi ?"idan ka manta ko ni wacece bari na tunatar da kai ni magaifiya ce agurinka ba rikonka nake yi ba da kazo? kayi tsaye akaina kana fad'a min magana son ranka tunda yar gwal ta fad'a maka magana? akaina bayan ma nice? na taka masu burki da yanzu ba wannan maganar akeyi ba dan da baka dawo gidan nan ka isketa da lafiyar jikjnta ba ai dana san wannan iskancin zaka min dana barin sun d'auki mataki akanta ko shahida sa'arta ce da zata fad'a mata magana?" to ko? auta? ba sa'arta bace bare khadija saboda ka rasa hankalinka da tunaninka yarinya ta fad'a maka karya da gaskiya kabi ka hau batun tsam gwama kuma daman ni nace maka Ina sonta ne ?".Ai bance Ina sonta ba kuma baka isa kasani na sota ba kamar yadda ban isa nasa kaso abinda nake so ba dan haka zaka iya d'aukarta ka bar gidan nan daita saboda baka san ciwon kanka ba sannan ka cigaba da bata kofar da zata raina maka yan'uwanka kuma na sak? jin ka Kira khadija da yar iska sai 'bata maka rai sha shashan banza sha shashan wofi kawai ."ta k'arasa maganar tana goge hawaye Wanda yasa yaji hankalinsa yayi mugu mugun tashi domin kuwa zubar hawayenta na cikin abinda yake saurin d'aga masa hankali da dagula masa lissafi."


Muryarsa a sanyaye yace "kiyi hakuri? sweetheart ba wai na fad'a miki magana bane gani nayi abinda suke yi kece ya kamata ki taka mutsu burki sai kuma naga ..."saurin d'aga masa hannu tayi ta hanyar cewa "karka bani hakuri kaje can ka bawa ita yar gwal din taka? hakuri tunda kana gudun 'bacin ranta amman kasani idan ka bar gidan nan da yarinya nan batare da izinina ba wallahi har abada karka dawo min daita cikin ahlina ."tana gama fad'ar haka ta juya masa baya tana cigaba da zubar da hawaye "inna lillahi ...!"ya furta a fili yana jin wani sabon tashin hankali ya shigarsa? yayinda zuciyarsa ta dinga? tafasa tana tuttukin bakinciki da sauri ya fito daga d'akin yana neman layin baba babba cikin sa'a
ya d'aga sun d'auki lokaci yana koro masa halin da'ake ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login