Showing 33001 words to 36000 words out of 151781 words

Chapter 12 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2642

auren ,auren wa kuma za'a d'aura "?umma tace bakiji nace kinyi goshi ba ai aurenki za'a d'aura nan da kwana goma masu zuwa, idanuta ta ware sosai akan umma tace "ni kuma umma da wa kuma za'a d'aura min aure ?"tayi mata tambayr ajere zuciyarta na bugawa da karfin gaske ".
"kwantar da hankalinki adamunki zaki aura tun shekaranjiya mukayi waya dashi cewar 'yan'uwansa zasu zo nema masa aurenki yau to Alhamdulillah sun zo har an gama magana"ta bata amsa cike da matsanancin farinciki maryama ta kasa furta komai dan zuciyarta ke wani irin bugawa? da mugun karfi babu abinda ke yawo acikin kwakwa luwarta kamar irin halaye da tsare tsaren mr ata yanzu daman duk ya shirya haka shine ya maidaita banza koma ya kirata ya fad'a mata cewar yan'uwansa zasu zo ?"
Umma ta riko hannunta cikin nata tasa takardar kudin "kinga kudin da suka kawo kawai na gaisuwar iyaye a zahirin gaskiya maryama adam yana matukar sonki kuma ina? fatan zai jiyar dake dadi da farinciki a gidansa "maryama tai shiru tana sauraron umma kawai dan ita kad'ai tasan halin tashin hankali da take tabbas tana tsananin son shi sai dai idan ta tuna tashin hankalin da zata tsinci kanta a gidansa sai taji gabad'aya son ya fita aranta kamar a yadda take ji yanzu dan ji tayi kamar kwanakin mutuwarta ne ya kusantota ahankali ta ajiye takadar kudin akan cinyar umma tana mai sunkuyar da kanta ta dafe ."


"Ya naga kamar baki farinciki da faruwar wannan abun alkhairin daya samemu ba ?"still shiru mryama tayi zuciyarta na wani irin tsinkewa tare da bugawa "maryama "!umma ta Kira sunannta "ta d'ago kanta ta kalleta cikin yanayi na damuwa "ki kwantar da hankalinki,ta gyad'a mata kai kawai batare da tace komai ba "yauwa ki saki jikinki,ya kika damu kamar baki son adam bayan nasan kina son shi sosai har ma fiyye da son da yake miki "umma ta karasa maganar cike da zolaya ".nan da nan maryama ta sake canza fuska "Allah umma ki daina cewa haka ni bana wani son shi .""wannan kuma wani zaki fad'a wa bani ba "maryama tai shiru dan umma ta bar zance dan tana mugun sakata jin kunya idan tace tana son mr ata "maryama!"umma ta sake kiran sunanta a karo na biyu." gabad'aya maryama ta tattara hankalinta da natsuwarta gareta dan ta fahimci tana son tayi magana mai mahimanci ne .
"ina neman wata alfarma a wajenki maryama "haba umma kiyi maganrki kawai ba sai kin tsaya neman wata alfarma ba umma ta sauke numfashi tace "na gode Allah yayi miki albarka"maryama tace "ameen!"adamu yazo min da wata magana jiya cewar idan an d'aura aurenku a gidansu zaki zauna tare da mahaifiyarsa sai dai na ara bakinki na bashi kwarin gwiwar babu wata matsala zaki zauna daita domin ke din mai biyayya ce agaresa "ai? nan take k'irjin maryama ya cigaba da bugawar da yake ta dinga kallon umma cike da matsanancin tsoro da tashin hankali ."


Muryarta na rawa tace "umma gidansu kuma ?umma ta gyda mata kai alamun "eh !"haka? yace maryama "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "umma mai yasa kika amince masa ?allah bazan iya zama tare da mahaifiyarsa ba wallahi tsoronta nake ji Ina tunanin wahalata ta rag? a she wahala basu ragu agareni ba ? ashe akwai wasu sabbin shafukan a gabana ?sai yaushe ne zan daina shan wahala mai dan karen wuya da azabtar da zuciya da gangar jiki "?yaushe ne ruhina zai samu salama ?kiyi hakuri ki yafe min maryama nayi karambani gashi har na bashi kwarin gwaiwa zaki iya zama da mahaifiyarsa ashe ban sani ba cewar bazaki iya ba kiyi hakuri wallahi da nasan bazaki iya ba da ban amince ba nan take umma ta rikice ta soma kuka itama tana? bata hakuri ."Allah sarki maryama ganin hawayen umma ya sake rikirkita mata lissafi? ta zube gabanta tana kuka tana bata hakuri "dan girman Allah umma kiyi hakuri ki daina kuka ki daina bani haquri naji duk abinda kika fad'a zanyi kece komai nawa, duk yadda kikayi dani daidai ne na na amince na mika wuya zan zauna daita lafiya rokon da nake dashi agareki kiyi min addu'a,ki sani cikin kowacce addu'aki Allah ya bani hakurin zama daita , ya hanani gazawa bare na watsa miki kasa a ido sannna na samu juriya mai yawa" tana kaiwa nan ta kasa cigaba da magana ta fashe da wani irin da kuka mai ta'ba zuciya tana tuna mugun halin yan'uwansa a kullum suke addabarta dashi ,tana son fadawa umma sune silar saceta amman kuma tsananin kaunar data ga umma take ma mr ata yake hanata fad'a mata dan tasan dole kaunar zata juye izuwa mummunar kiyayya mai zafi dan umma bata wasa da duk wani abinda ya shafeta ."



"kiyi hakuri da rayuwa maryama? in sha allahu babu abinda zai faru sai alkhari "ita dai ta barwa Allah komai duk hukuncin daya yanke akanta mai kyau ne idan zama dashi na har abada idan rabuwa dashi umma ta mikar? daita ta zaunar daita a kusa daita ta rungumeta tana rarrshinta kuka take sosai kamar wacce zaayiwa? auren dole "maryama ko akwai wani abu ne bayan wannna ki fad'a min dan hankalina ya tashi da kukanki "me zata ce ?"wanda ya wuce babu komai ai kuwa shi din tace mata babu komai ayanzu babu abinda nake bukata sai adduarki? ."to ki bar kuka nan haka in sha allahu zamanku alkhairi ne babu abinda zai faru kuma nayi miki alkawarin zan dinga zuwa akai akai ina duba lafiyarki? "ni wallahi daman zamu tafi tare gabad'aya umma ."
Umma tai murmushi tace"maryama kenan ai gidan miji ba'a bin mutun ,mutun shi kad'ai yake shan gwagwamarya a gidan aurensa duk wanda kika gansa a gidan mijinsa to fa daga shi sai halinsa ne ina miki kyakkywan fatan nasan halinki a duk inda aka kai ki bani da haufi zaki zauna lafiya da kowa sai dai kiyi kokari ki cire tsoron mahaifiyarsa idan adam ya gane kina jin tsoronta bazai ji dadi ba ki tayasa yiwa mahaifiyarsa biyayya kinji diyar albarka "jiki a sanyaye maryama ta gyada mata kai"alamun taji ."
"ki s? mahaifiyarsa ki kuma so yan'uwansa ki ja kowa nashi ajikinki ki kuma kyautata masu domin zuciya tana son mai kyautata mata ahankali umma ta dinga mata nasiha tana fad'a hanyoyi da zata bi wanda zai kawo mata kwanciyar hankali a gidan mijinta ."



Gida ya cika da murna umma aunty banda bangaren baba gali ,habib ma daya dawo gida ya samu labari bakaramin murna yayi ba da gudunsa ya shigo parlour'n umma yana wani irin ihu yana ganinta bai tsaya wata wata ba ya d'agata sama aiko maryama ta fara ihun ya sauketa kar yarda daita amman yaki sai faman juyi yake daita a parlour'n kasancewarsa karfafa dan idan ba sani kayi ba zaka d'auka shine yayanta "wallahi after dad ka saukeni umma kice ya saukeni wallahi juwa nake gani shi kuwa dariya kawai yake yana furta congratulations heartbeat ."
Umma tayi murmushi tace "kai ban son iskanci sauke min yarinya tace juwa take gani ahankali ya zaunar daita akan kujera sannan ya zauna gefenta alokacin ta dafe goshinta yace "sorry sorry wallahi na rasa me zanyi ne" ya kai hannu zai ta'bata ta kwace hannunta zata kai masa duka yayi saurin rike mata hannuwanta yana murmushi "umma tace "kinga illar rashin cin abinci ko kalli yadda habib yayi sama dake kamar wata yar kaza "ai gabad'aya suka sa dariya maryama tace "allah umma ko ina cin abinci bazan iya da after dad ba baki ga yanzu karfe yake ci ba "yiwa mutane shiru ko baya cin karfe bazaki iya ba da wannan jikin naki "habib yayi shiru yana kallonsu bayan umma tayi shiru habib yace "yanzu hearbert gabad'aya ATA zaki aura gaskiy am so happy da wannan hadin daman irin wannan kan ya dace dake Allah ni me yasa ba'a d'aura auren ba ?umma tai murmushi tace da yau da kwanakin da suka saura ai duk daya ne a wajen Allah Allah dai ya kai mu yasa muna da rai da lafiya yace "ameen !"


tun daga wannna lokacin gidansu ya samu bakunta mutane masu zuwa taya umma da aunty murna ta bangaren yan'uwa da abokan arziki duk da dangin mahaifinta basa sonta amman a wannnan karon jin wanda zata aura yasa taga sauyi akan fuskokinsu dan ."masu yara kanana har kamo hannunta suke ta dafa kan yaransu ko Allah yasa su dace irin nata ita kam abun shirme ta d'aukesa dan ta kanta take dan acikin tsananin damuwa da firgici take duk yadda take son ta cire tsoron mahaifiyar mr ata da yan
uwansa aranta abun ya cutura kullum tsoronsu karuwa yake acikin zuciyarta wanda sanadiyar haka ta kamu da ciwon mummunar fad'uwar gaba second second gabata ke fad'uwa da karfi ,idan gabanta ya fad'i sai jikinta da hantar cikinta sun d'auki rawa karin damuwarta a yanzu yadda mr ata yayi mata banza kusan sati biyu kenan bai kiranta a waya ba dan tun kafin iyayensa suzo rabon ya kirata gashi har yau kwana biyar kenan babu shi babu labarinsa bare wayarsa.tashin hankali data shiga yasa ta kasa sheidawa kawayenta an kawo kudin aurenta da lokacin auren sai umma ce ta kira subai'a da yusura ta sheida masu dukkanin su babu wanda bai yi mamakin cewar mr ata zata aura ba ,ai ko kuwa da yamman ranar sai ga subai'a ta jawo motarta tazo tayata murna ".


ta iske umma a parlour tare dasu aunty fatima da aunty hasana umma tace "subai'a har kin karaso?tace "ba dole ba umma ai kina fad'a min lokacin tashi ma bai yi ba na nemi excuse a wajen E D amar kinsan da yake dan'uwan mr ata ne jin uzurina ya barni " Allah sarki ashe har yanzu kuna aiki tare ?"eh umma! " ayya to Allah yasa albarka Allah kuma ya nuna mana naki haka subai'a tai murmushi ta gaishe dasu aunty fatima tana tamabayi umma maryama fa "?tana d'akinta kai tsaye ta shiga dakin inda ta iske maryama kwance tamkar mara lafiya tace "Ke shegiya tashi ki mike Allah yasamu a danshi ki domin kuwa kawata kinyi babban kamu mr ata fa ?inna lillahi ya rab Allah yasa albarka maryama ta yunkura ta zauna tana dubanta da fuskar babu yabo babu fallasa dan ita duk masu taya murna ganinta da kuka suka tayata da zai fiyye mata dadi dan ita kad'ai tasan abinda ke gabanta ,subai'a ta janyo kujerar da maryama Ke aiki daita ta zauna tana fuskartata tace "kawata daman soyayya kuke dashi amamn ko da wasa baki ta'ba labarta min ba gsky maryama Allah yayi miki zurfin ciki ?kema fa kinsan halin da nake ciki da zarar ance aure sai matsaloli su kunno kai ".haka ne kuma allah yasa albarka congratulations my friend maryama tai murmushi kawai yanayinta bai nunawa subai'a cewar akwai wata matsala ba dan tasan haka take normal."
Subai'a tace "to yanzu ya ake ciki ?"meye shirye shiryen biki da za'a gabatar dan ga biki yazo wannan satin ne fa ?"


? ? maryama ta gyda mata kai alamun "eh!"tace "wannan satin ne za'a d'aura aure batun biki ne dai babu "ban gane babu ba ?"da gaske babu "haba haba karki mana haka mana ?"subai'a ta fad'a tana gyra zama gasky zan yiwa E D amar magana naji me ake ciki amman taya zaki ce babu biki tayi maganar cike da damuwa "maryama ta riko hannuwanta cikin nata "subai'a fad'a min wanda kike so Z&A shiru subai'a tayi tana jin mummunar fad'uwar gaba ".
"me yasa bazaki fad'a min ba ?"maryama tayi maganar cike da marairaicewa tana duban fuskar subai'a "kinga ki bar wannnan maganr muyita daga baya yanzu maganar biki ne gabanmu dan zaki wani shigo da wata magana kenan dan ki shashatar da wacce muka fara ni dai kinji n? fad'a miki zan yiwa ED amar magana numfashi kawai ta sauke tai shiru tana kallonta sun dan jima sannan subai'a tai mata sallama ta wuce tana zuwa gida tayi test din Amar yadda sukai da maryama bayan kamar awa biyu har ta fitar da rai zai reply dinta taga reply dinsa inda yace zai nemi adamcy yanzu duk abinda yace zai bari tasani ."bayan ta gama karanta sakonsa tayi shiru kawai rungume da pillow a kirjinta tana tunani nata damuwar ,akwai matukar ciwo ka kamu da son wanda bai ma san kana son shi ba ta kai hannunta tana shafa idanunta da suka cika da kwalla? bata kai ga maidasu ba suka zubo akan kuncinta tana nan zaune ta sake jin shigowar sakonsa "he doesn't need a party"iya shi kawai ya rubuto sai dai ta karanta yafi sau babu adadi ."


******

Washegari? ranar talata da yamma mami?? na zaune? a babban parlour'nta sai ga wasu daga cikin ma'aikata mr ata suna neman izinin shigowa ta bassu izini inda tagansu ,su biyar? suna shigowa da akwatunan?? shiru tayi zaune tana kallon guda biyar din da suka fara shigowa dashi ahankali suka dinga fita suna shigowa da akwatuna tun tana kirgawa? har ta dawo ta daina akwatuna ne tsadaddu da matukar kyau da d'aukar hankali bugun england set set sukayi har sai da sukai goma shabiyar sannan suka suruna mata suka fice suka barta zaune tana kallon akwatuna? wanda take ta fahimta akwanan auren 'yar gwal dinsa ne yasa akawo mata ."
tana tsaka da kallon? akwatinan? ya shigo sanye da bakaken? kaya? da facin cap baki hatta takalmin ?afarsa baki ne? kasancewarsa? fari sai kayan suka amshesa fiyye da duk kayan daya saba sakawa? sai kamshi yake zubawa fuskarsa ta sake fitowa sosai? saboda gyaran fuskar da? yayi? ya karaso har gaban mami?? ya durkusa yana cire facing cap dinsa cike da girmamawa ya? gaisheta"sweetheart kin yini lafya ?"
"lafiya lau !" tayi maganar atakaice sannna fuskarta a daure tana daura hannunta? akan cinyarta murmu shi yayi yana kallonta tace "wadan nan kayan? fa ?
kai tsaye yace mata "kayan maryama ? ne " ya fada yana mikewa tare da zama? akan kujera idanu ta tsura masa?? for two second tana masa kallo mai cike da tsantsar mamaki"ikon Allah ashe yasan yadda akeyi komai amman alokacin maryam yayi buris ya share yakiyi dan kawai ya tozartata ita da diyarta ?"


Yadda mami take kallonsa shima ita yake kallo? hawaye ne suka fara turereniyar zubowa? akan fuskarta, yayi saurin mikewa ya dawo gabanta ya?? kamo hannuwanta duk biyu yana cewa "no no sweetheart"?dan girman karki min haka idan na bata miki rai ne Kiyi hakuri "yanzu? adamcy farinciki kake son nayi da wadan nan kayan ?"idan bai sakaki farinciki ba sweetheart sai amayar dan wallahi bana son ganin hawayenki yana daga min hankali? ya kai hannu yana goge mata hawayen yana bata hakuri yana? kallonta? cike da tsananin kulawa Kiyi hakuri sweetheart bani da wata uwar da zan kaiwa kayan
Bayan ke,ke din dai kece dole bari nasa a bud'e miki kiga kayan adamcynki ya fad'a yana goge mata fuskarta yana rarrashinta ,jinsa kawai take tana mamakin karfin halinsa yanzu ya gama cewa bai son damuwarta amman kuma yake maganar a bude mata kayan ta gani wanda yasan ganin kayan yana cikin damuwarta ,ita kan wani irin d'a ta haifawa kanta ?."har sanda ya kai hannu ya danna bell din dake kai sako bangaren ma'aikatan gidan tana cike da mamakinsa? sannan fuskarta? bayyane? da tsananin bakinciki ."
cikin kankani lokaci sai ga mutun uku sun fito cike da girmamawa suka gaishesa ya basu umarnin su bud'e akwatina da sauri suka fara aiwatar wa daya bayan daya suka dinga bud'e wa mami tace "wai ma? a yaushe ka soma hada kayan lefe ban sani ba? ?"
"jiya? zuwa yau ne fa? sweetheart ."ya karasa mganar yana murmushin gefen baki haka masu aiki suka dinga bud'e mata? akwatin daya bayan daya shiru mami? tayi tana jinjina kai tana sake mamakinsa? a lokacin daaka bude mata akwatin? kayan? bacci ganin duk ya zabo hadaddun kayan zamani masu matukar kyau da daukar hankali tace "da kanka ka zabo wadan nan kayan bacci ?"


Kai tsaye yace mata "yes "ta kalleshi tace "yes !"da saurin ya gyada mata kai alamun "eh "? batare da yace mata komai ba"amman me yasa lokacin maryam bakayi mata ba ?ko abinda baka so baka bayar a auren ba "dan me yasa zan bayar wacan auren aurenki ne wannan kuma aurena ne" yayi maganar a kasan ranshi" yanzu duka kayan nan zaka bazawara har da ziniri fa naga ya kai goma anya kuwa baka haukace ba adamcy ?"ya fuskanceta sosai sai dai kafin ya soma magana sai daya sallame masu aiki bayan sun bar wajen yace "sweetheart babu abinda ya same ni wallahi ina cikin haiyacina fiyye da auren farko "okay to baza'a kai kayan nan ba ka ajiyesu tazo ta iskesu "dan Allah sweetheart karki yi haka na rigada na fad'a a gidansu za'a zo ranar alkhamis akawo idan kikayi haka kin zubar min da mutunci duk da nasan wadan nan kayan ba damu warsu bane ko dashi ko babu zasu bani auren maryama amman dan Allah kiyi hakuri nifa a yanzu a shirye nake da nayi miki komai idan akwai abinda kike so ki fad'a wallahi zan miki zare hannunta tayi tana jijiga kai "please sweetheart tace "naji banason magiya "thank you".mami yayanta kawai ta kira suzo suga kayan lefe? su kansu sunyi mamaki irin kayan daya zuba sai dai suka ce iya rabonta kenan kwanaki kad'ai? ya rage ungulu zata koma gidanta na tsamaiyya ."


Koda mami tace suzo washegari akai kaya dasu suka ce a nemi wasu su kai amman su kam suna bayan maryam muddin sukaje kome yaya zataji babu dadi mami tace "to shikenan ta? kira wasu daga cikin manyan gidan saboda babu isasshen? lokaci mutane sukayita? sawa kayan da auren albarka "Allah yasa auren yafi kayan albarka ranar alkhamis mr ata ya bada motocin da za'a kai lafe"tun safe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login