Showing 132001 words to 135000 words out of 151781 words

Chapter 45 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2655

san lokacin daya d'auka ba sai dai farkawa tayi taga har ya cire mata robar drip din da'aka makala mata duk bata san karfe nawa bane? amman ta fahimci tsakar dare ne. ta gyra kwanciya tare da takure jikinta waje d'aya ganin haka ya rage
karfin ac d'akin, ya kwanto ya rungumeta ta baya bata? juyo ba dan bacci ne acikin idanunta tana jin yadda yake sake shigewa jikinta yana manne mata tare da shafo wasu wurare a sansar jikinta ".sannu princess "numfashi kawai ta sauke kusan mintuna talatin suna kwance yaji ta kira sunan shi "zumana ..!"ta furta cikin wani irin salo na marasa lafiya "na'am dadina!"ya amsa cikin wani irin? sautin murya hucin bakinsa da numfashinsa na dukan wuyanta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa"kayi bacci gobe fa akwai zuwa Office ".

"manta da aikin nan kina tunanin zan fita na barki ne ke kad'ai alhalin baki da lafiya ?"to mene ne ai zan iya kula da kaina wannan zuciyar tawa bazata? iya? samun natsuwa da kwanciyar hankali ba,a yanzu ma da nake tare dake na kasa samun natsuwar da zan runtsa bare na barki "juyo wa tayi gabad'aya ta shige jikinsa ta rungumesa tana kallon kyakkyawar fuskarsa ya matso da bakinsa zai yi kissing dinta ta kawar da bakinta tace "dan Allah ka dinga sausautawa kanka wasu abubuwa akaina ka daina zafafa son da kake min yayi yawa shiyasa kullum mami da yan'uwanka suke min kallon nayi maka wani abu ne ".wannan kuma damuwarsu ce ni babu ruwa na da duk abinda zasu ce "duk da haka ,ance idan zaka so abu kaso shi kad'an idan zaka kisa ka kisa kad'an dan Allah ka rage son nan domin Ina jin tsoron ranar da zaka ga wata ka juya min baya "kamo fuskarta yayi yana kallonta kamar ranar ya fara ganinta bazan ga wacce har zan juya miki baya akanta ba "to idan babu mutuwa fa akwai rabuwa ai tana gama fad'ar haka taji yaja dogon tsaki tare da zareta ajikinsa? ya juya mata baya ."

Shiru tayi tana kallon bayansa har kusan minti goma bai juyo gareta ba da alamun halin ne ya motsa kamar ta rabu dashi sai taji ta kasa ta matso jikinsa taji ya janye jikinsa daga nata? ya takure waje d'aya numfashi ta sauke ta sak? motsawa? ta rungumesa sosai, bai juyo ba amman yana jin yadda take sake shigewa jikinsa tana manne masa tare da shafo wasu wurare a sansar jikinsa kusan mintuna talatin suna kwance yaji ta soma magana"bazan iya runtsawa ba matukar ka cigaba da juya min ba a daren nan ta karasa maganar tana shafa qirjinsa zuwa nipples dinsa ahankali ya juyo gabad'aya wanda sauran kad'an su had'e ya tsura mata tsumammun idanunshi "daga na fad'a maka gasky shine kayi fushi dani ko ?numfashi kawai ya sauke yana cigaba da kallonta, matso shi ta sake yi tana shafa gefen fuskarsa muryarta a matukar sanyaye "ka fi kowa sanin cewar ni masoyiyarka ce kuma ina tsananin son na ganka cikin kwanciyar hankali da natsuwa bana son duk wani abinda zai zama damuwa a rayuwarka kayi hakuri zumana ..."

fixgota yayi gabad'aya ajikinsa cikin wani irin salo ya had'e bakinsu ya soma sucking lips dinta yana tura harshensa cikin bakinta wani iri kissing yake mata wanda ta kasa jurewa da kyar ta samu ya sakar mata baki gabad'ayansu numfashi suke saukewa ,ya kamata kayi bacci saboda fita gobe "wai wa ya fad'a miki zan fita zuwa wani guri baki da lfy babu inda zani muna tare sai naga yadda? jikinki yayi ya fad'a tare da rungumota ya lullubesu .wani bacci ne yayi awon gaba dasu suna rungume da juna basu suka farka ba sai daf da ana tada sallah? asuba ,maryama ta kasa ta mikewa sakamakon nauyin da jikinta? yayi ."
kusa daita ya matso yana mata sannu tare da riko hannuwanta "ka taimaka min bazan iya tashi ba cak ya d'auketa ya nufi bayi daita ya zaunar daita akan setbath ahankali ta fara fitsari tana runtse ido ya dawo gabanta ya durkusa yana kallonta "wani guri na miki ciwo ne ?"kai ta girgiza masa tana rausayar masa da kwayar idanunta "babu komai kawai dai jikina ne naji yayi min nauyi shi ya taimaka mata ta mike byn tayi tsarki tai alwala shima yayi suka fito atare ."


bayan sun idar da sallah komawa sukai? sai wajen karfe goma ya farka yana kallonta kwance tana sauke numfashi ko bacci take a natse take? bai jima? da farkawa ba itama ta farka tana mika da salati ya kamota jikinsa wani irin zafi yaji ya ratsa shi muryarta cike da shagwaba tace "ni ka barni bani da lafiya tayi mag kamar zatayi kuka kissing din k'irjinta yayi yace "sarkin raki "dole kace haka tunda baka san yadda nake ji ba ta k'arasa fad'a tana zare jikinta da k'ok'arin saukowa yayi saurin taimaka mata ya manneta da k'irjinsa yana cigaba da kissing dinta saurin lumshe idanunta tayi tana sauke numfashi "yanzu bazaka bar mutu yaji da kanshi ba ?"bai ce mata uffan ba ya cigaba da kissing dinta har suka shiga bayi tare sukai wanka suka fito ya zaunar daita yana goge mata jiki bayan ya gama yaje ya d'auko mata doguwar riga puppy colour ya? dawo inda take zaune ya sanya mata kaya yana ta'ba wasu wurare a sansar jikinta yana gamawa ta zube akan katifa tana sauke numfashi sama sama dan da zai sanya mata kayan sai da yayi amfani da kwarewarsa ya murza kan nipples dinta duka biyu ."

biyota yayi ya kwanto jikinta yana kallon yadda take sauke numfashi kamar wacce tayi gudun tsare ta kai hannuwanta duka? ta kamo fuskarsa ahankali ahankali ya dinga motso da fuskarsa har ya had'e bakinsu waje d'aya ahankali ta lumshe ido tana sauke numfashi ,Ahankali ya zagayeta da hannunsa ya d'agota sama da sauri ta ware idanunta suna kallon juna cikin tsananin shaukin juna fuskarta daf da tashi suke? shakar numfa shin juna ,a haka ya sauko daita daga kan gadon tana hannunsa yana tafiya daita yana kallonta itama? tana kallonsa tana jin wani irin sanyi na ratsa ilahirin jikinta ,bai ajiyeta akoina ba sai akan kujerar dinner a parlour'n kasa ya zauna kusa daita ya had'a mata tea ya fara bata abaki itam shiru tayi kawai tana kallonsa bata ankara ba har shima ya had'a tea ya sha sai da taji bakinsa kusa da nata ya kamo kumatunta da hannuwansa yana kallonta da wad'an nan tsuma mmun idanun nashi masu narkar da zuciya da gangar jiki ,gabad'aya ya gama dabai baye rayuwarta ya hana zuciyarta sakat bata da wani aiki sai na soyayyarsa narke fuska tayi kamar zatayi kuka still suna kallon juna yaja hannunta suka nufi step ".

Duk wannn abun akan idanun mami da maryam
Ne tsaki mami taja tana girgiza kai"Maryam ki dinga d'auke hankalinki akansa kin dai san halinsa idan ya gano har yanzu kina son shi wani tashin hankali ne "ni mami ya zanyi da rayuwata Ina ganin zan zo na wuce abuja cikin satin nan" "akan me zaki wuce wai ma jiya me salim yazo yi ne wajenki ?numfashi ta sauke tana lumshe idanu"wai sona yake saboda bashi da mutunci "ta fad'a tana jan tsaki dan yace yana sonki shine rashin mutunci?"Maryam ta kalli mami"ni kuwa da zaki d'auki shawarata da kin auresa duk da ni har yanzu adamcy nake son ku k'arasa rayuwarku dashi.nan take? idanunta suka ciko da ruwan hawaye muryarta a sanyaye tace "wallahi mami duk sanda na kalli khaira sai na zubar da hawaye n tausayinta yarinya kamar marainiya wallahi mami banason nayi? aure biyu arayuwata shiyasa nake kuka da umma domin duk ita ta rusa min rayuwar gidana"ki daina kuka haka daman can ko batayi komai ba adamcy baya sonki kuma baya son zama dake ,amman me yasa dana bashi umarni ya maidake kuma ya amince kika ki dawo wa?ko na dawo mami gidansa gidan jiya? za'a koma amman nasan da wannna matsefar zan mutu "kiyi hakuri idan da rabon sak? rayuwa dashi zaki koma hannunsa Amman?Kiyi tunani akan salim din ."

A parlour'nsa suka tsaya ya? zaunar daita? a kan doguwar kujera? ya kunna ac parlour'n da tv sannan ya zauna ya kwantar da kanta a saman cinyarsa ya sunkuyo da kanshi daidai fuskarta yana shakar numfashinta shiru tayi kawai tana kallonsa dan duk abinda zai yi yanzu ya daina bata mamaki dan tasan zai iya aikata fiyye da haka ahankali taji yana yawo da hannunsa a saman k'irjinta nan da nan k'irjinta ya soma bugawa yayi shiru yana kallon k'irjinta so take ta bud'e baki tayi masa magana amman gabad'aya ta kasa bud'e bakinta saboda fellings dinsa dake kashe mata sansar jiki dole ta runtse idanunta tana jinsa yana cigaba da abinda yake mata sai daya gaji dan kashi kuma yaga alamun bacci ya d'auketa ya maida kanta akan pillow ya sauko ya nufi bangaren mami ."Inda ya isketa zaune cikin tsananin tashin hankali da jin haushinsa mrym tana ganin shigowarsa ta sa'ba diyarta a kafad'anta ta fice daga d'akin batare data ce masa uffan ba ."

ya gaishe da mami ta amsa sai dai daga wannan amsar gaisuwar da tai masa bata sake kulashi ba
Duk maganar da yake mata bata tanka masa ba haka zalika bata d'ago ta sak? masa cikakken kallo? ba yadda ya lura ma data kallesa zatai saurin kawar da fuska gefe hakan ya d'aga hankalinsa shi dai yanzu maminsa ta tsanesa kullum cikin laifi yake? ?"ya dan matso kusa daita ya riko hannunta "sweetheart wani abu ya faru ne ?"tace mai ka gani shima still bata kallesa ba "gani nayi kamar Baki son kallona? Kai tsaye tace haka ne da zaka daina zuwa inda nake da naji sanyi da kuma rabuwa da bakinciki dake daskare da zuciyata . yayi shiru yana kallonta yana nazarin maganarta bayan mintuna talatin yana zaune ya mike yace Allah ya huci zuciyarki ya koma sama sai dai zuciyarsa tana can wajen mami duk da bai san takaimamai laifinsa a yanzu ba amman zai sake zuwa anjima ya bata hakuri bai jima da dawowa ba jikin maryama ya rikice dole ya sake kiran likita tazo karin uku tayi mata tace a dinga bata ruwa mai dumi jinya da lalla'ba maryama yayi tayi ."

ita kuwa sai kuka take tana cewa ka? kira min umma mutuwa zanyi "umma kike son gani ta gyad'a masa kai bai sake cewa koma ya kira umma ya fad'a mata ta shirya za'a zo a taho daita maryama bata da lafiya cikin awa d'aya sai ga umma inda? mami tana zaune a parlour'n aka shigo da umma a natse ta gaisheta sarai mami ta ganeta shiyasa ma da kyar ta amsa mata kai tsaye Wanda ya shigo da umma ya juya yana kiran adamcy batare da bata lokaci ba mami taga?? ya sauka? da girmamawa yana mata sannu da zuwa kamar itace ta kawosa duniya tana kallonsu suka nufi sama aiko ta sak? kulewa da bai tsaya ya gabatar mata da umma ba ."maryama na gani umma ta sake narke wa umma ta zauna kusa daita tana mata sannu ahankali ta dawo jikinta ta kwanta tana cewa "wayyo umma mutuwa zanyi? "maryama daWina dake rakin ciwo wllh idan baki da lafiya yanzu sabida Allah dan kawai bakida lfy shikenan seki hau kuka azo dani?ni umma ki tafi dani gida dan Allah ."

"ni d'agani bani zaki wa wannan? sangarci ba tayi magana tana kokarin dagata daga jikinta duk kin narke min ajiki"adamcy yayi murmushi yace "sai kace mage "eh wallahi ai gara mage da wannan ai zaka sha? fama ga rakin ciwo ga rashin son sha magani" dan Allah umma idan zaki wuce gida ki wuce dani ,gidanku dake da gida.kusan anan umma ta yini suna jinyar maryama tare da adamcy duk da bai fad'a mata abinda yake damunta ba ta fahimta dan haka bilkisu take da laulauyin ciki da zarar ka ganta a kwance to ciki gareta ,sai bayan datayi sallar laasar ta mike tace "to ni zan wuce gida shima adamcy ya mike tsaye ya biyota maryama tace yanzu? umma bazaki tafi Dani ba ?umma tai murmushi tace Allah dai ya baki lafiya "shikenan ki gaida gida Allah ya tsare har bakin mota adamcy ya rakata sai daya ga tashin motar da take ciki data masu tsaronta sannan ya juyo a parlour'n mami ta tsaida shi cikin isa da izza ".

"amman dai kasan gidan nan muna da doka ko?"
Shiru yayi yana kallonta "ba'a zuwa gidan nan batare da an sanar min ba zuwan ma kuma har na yini guda "me ma tazo yi ?"tai masa tambayar batare data kalli inda yake ba tsananin mamaki yasa harshensa? ya kasa furta mata komai"wannan ya zama karo na farko daza'a dinga kawo mana kwashe kwashe gida "wannan fa ba kwashe kwashe bace tamkar mahaifiya ce? ga maryama kuma zuwan nata yana da dalili "wannan kuma ku ta shafa ni magana nake akan dokar gidan nan tana gama fad'ar haka taja bakinta tayi shiru tana cigaba da kallon wani gefe bai ce mata komai ba ya nufi step zuciyarsa na masa zugi da tuttukin bakinciki."akwance ya iske maryama ta tsura masa idanu tana kallonsa ganin yanayinsa ya d'an sauya ,a natse ta yunkura ta mike still kwayar idanunta na kashi har ya zauna kusa daita ya tsiyayya lemu acikin glass cup ya miko mata bata amsa ba ta cigaba da kallonsa tana nazarinsa."

ya Kai cup din bakinta "ungu sha !me ya same ka?"lumshe mata tsuma mmun idanunshi yayi alamun babu komai tai shiru dan tasan ba haka ya fita raka umma ba duk yadda akayi akwai abinda ya faru"sha lemu !"makale kafad'a tayi kamar yadda yara suke tace "uhm uhm ni bana sha "yi hakuri ki d'an sha ko kad'an kinji dadina ayi laulayin ciki ace baza'a sha komai ba "to amai nake ai !ta maganar kamar zatayi kuka "nasani but at least ki sha wani abu zai tsaya acikinki "cike da shagwaba ta kai hannunta d'aya jikin cup din atare suka kai bakinta ta sha kad'an tana yatsuna fuska ta kawar bakinta"ya kamar kin sha mad'aci?bata ce komai ba ta kamkame jikina tana cigaba da yatsuna fuska "wannan cikin fa Kamar zai takura miki ko za'a cire ne ki huta zuwa wani lokaci"nan take ta had'e rai bangane nufinka ba "naga tun baaje koina ba kina shan wahala ni kuma gashi bana son duk wani abu da zai wahalar min dake dan nafi sonki akan abinda ke cikinki "tai murmushi kawai tana kallonsa ya janyota ya kwnatar daita akan cinyarsa yana shafa k'irjinta "nasan ke yanzu kin fi son cikinki akaina ?no no !!nafi sonka akan cikin "wannna ba gasky? kika fad a ba , dukkanin alamun sun nuna min kina haihuwa sunana sorry ".murmushi tayi tana rufe fuskarta ya duku da fuskarsa daidai nata yana mata magana cikin rad'a wani murmushi kad'an ya sake bayana akan fuskarta? ya kai hannunsa kan nata yana shafawa yana k'ok'ari kamo lip's dinta haka suka kasance makale cikin tsananin son juna ."

******

zaune sadam yake a office d'in jakadanci ta kasar amerca Kusan awa d'aya kenan daya kifa kanshi asaman table ya tsunduma duniyar tunanin duk yadda yaso ya manta da rayuwarsa ta baya, ya sake shinfid'a ma kanshi wata sabuwar rayuwar.abun ya cutura da zarar ya runtsa idanunshi ummansa da maryama yake gani "hakika bai kyautawa mahai fiyarsa ba kuma bai kyautawa maryama ba me ma yasa zai yi haka ?"ahankali ya d'ago kan shi tare da mik'ewa tsaye ya rungume hannuwanshi duka a baya yana sauke numfashi cike da jimami cikin ranshi yake fad'in"kasan yarinyar nan mareniya ce bata da kowa sai mahaifiyarta haka zalika ummanka duk duniya bata da kowa sai Kai iyayenta duk sun mutu lallai idan baka koma zuwa ga mahaifiyarka ka nemi yafiyarta ba hakika zuciyarka baza ta'ba samun sukuni ba haka ma hakin maryama bazai barka? kasamu kwanciyar hankali ba ,kuma hakan zai sa ka kamu da cutar depression har abun ya fara zame maka menta problem a yanzu tausayin kanshi yake ji dan wallahi yasan zuciyarsa ta kamu da matsananciyar soyayyar maryama a gaske a she dausarar kanshi yayi tayi kamar ma kar ya auri nadia shikenan yaji komai ya sauya agaresa dan haka ma yake son ya soma kar'bar allurar mantau ta yadda zai manta da son da yake ma maryama? yayi tunanin ta yadda ya fuskancinci ummansa?? lallai ya kamata ya ajiye komai ya koma gida ga mahaifiyarsa ."kana ganin a soyayyar da kake wa maryama yanzu akwai wata allura ko maganin da za kai amfani dashi yasa ka manta daita ?"kwakwaluwarsa ta aiko masa da wannan tambayar ."bango ya kai wa naushi batare daya san ya aikata hakan ba radadin azabar da yaji ne yasa har ya fahimci abinda yayi ya yarfar da hannunsa yana runtse ido "ina sonta wallahi ina sonta wannna shine kawai abinda yake maimaitawa."



Mmn Sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

MAR'ADAMS

=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?



BOOK 4



AYSHA A BAGUDO



WATTPAD @HAUESH

AREWABOOKS USERNAME

AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Page 28

kwance sadam yake akan doguwar kujera mai zaman mutun uku a parlour'n gidansa sanye cikin doguwar rigar jallabiya maron colour yana kallon hotunan maryama yana zurfafa tunanin abubuwan da suka faru a tsakaninsu daita,irin soyayyar data fara nuna masa kafin yayi mata butulci ,hawaye ne ya dinga zuba daga cikin kwarnin idanunsa saka makon ummansa da zuciyarsa ta hasko masa ,mace jaruma mai hkr da tsananin tausayinsa da kaunarsa ya gujeta saboda gudun rayuwa da maryama yau gashi mrayama tana tare da iyayenta shi kuma yana tare da wata ,yayi imani idan itace bazata ta'ba gudu ta bar ahlinta saboda an bata mijin da bata so ba tunda ya gani a zahiri tun bata son shi ta hakura ta dawo tana son shi."to ai shima yana ji aransa bada son ran shi komai ya faru ba shima tsintar kanshi yayi acikin rayuwar da yake, yanzu ne yake nadamar abinda ya aikata sosai yayi zurfi cikin tunanin bai kula ba sai jiyo sautin muryar nadia yayi daga saman step"ashe kana nan ?."wata irin zabura yayi ya mike tsaye har wayarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login