Showing 63001 words to 66000 words out of 151781 words

Chapter 22 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2661

fad'a tana k'arasa wa inda zata ajiye tray maryama tai murmushi tace "sannu da kokari na fa gode !"da mamaki tabawa take kallonta domin a gidan babu wanda ya damu da aikinka bare yayi maka sannu cike da girmamawa tace" yauwa na gode zuwana na uku kenan Allah yasa ban takura miki ba ?"maryama ta girgiza mata kai tana murmushi tace "ko d'aya bacci nake lokaci" tabawa tai mata sallama ta fice maryama ta juya ta koma d'akin domin gabatar da sallar azahar ."

Bayan ta idar da sallah ta shafa mai ta sauya wasu Kayan ta fito ta bud'e kulat abinci ta farko white rice ce ta biyu kuma stew ne ta d'auki plet ta zuba taci kad'an ta soma tunanin raba d'aki da adamcy dan bazata yarda ya shammaceta ba ."
A natse ta mike ta bud'e d'akin dake gefen nashi ta shiga shima kamar nashi ne da gado da wardrobe da komai da sauri ta fito ta koma d'akinsa ta soma janyo akwatunanta d'aya bayan d'aya ta dawo dasu d'akin ta shirya kayanta bayan ta gama ta d'auki wayarta ta kira umma bayan sun gaisa take sake tambayarta bakunta ."tace "umma akwaita fa har da tsoro umma tai murmushi tana cewa "Allah dai ya yaye miki wannan tsoron kinje kin gaishe da mahaifintarsa kuwa ?"naje umma !"ta fad'a jikinta a sanyaye."
Umma tace " kiyi hakuri maryama da duk abinda zaki gani ki taya adamu biyayya ga mahaifiyarsa zuwa anjima kad'an ki sake zuwa ki gaisheta ki dinga zuwa safe da yamma duk mugun halin mutun Allah zai taimakeka akanshi kinji karki wani damu da duk abinda zata miki tunda Allah ya rigada ya had'a wata rana zatai hakuri ta rungumeki amatsayin suruka mafi soyuwa a zuciyarta ,ni adduata Allah yasa ki samu ciki da wuri "Kai umma daga aure sai wani ciki ?"

"to me ake jira maryama ai haihuwar ce zata sa ta sauko da wuri ta kauna ce ki sun jima suna hira kafin daga bisani sukai sallama ta kira layin aunty suka gaisa itama sun jima suna hira daita har hud'u saura sukai sallama ta mike ta gabatar da laasar dake akwai alwala ajikinta ."bayan ta idar ta fito a natse, tarba mai kyau ta samu daga hajiya zulfa'u cike da girmamawa ta gaishe da mami ta amsa fuska babu tabo babu fallasa ta zauna shiru yayinda suka cigaba da hirarsu ita dai zaune take bata fahimtar maganganunsu saboda hankalinta ya rabu gida biyu, wajensu mami da kuma wasu yara uku da bazasu wuce shera uku da shekara bakwai da kuma shekara biyar ba .masha Allah yaran kyawawa sunyi mata ga wayo hajiya zulfa'u ta juyo zata mata magana sai ta lura da hankalinta gabad'aya yana kan su Amir da mashkur ne ta zuba masu idanu tana murmushi ita dai yarinyar tana burgeta ta d'auke kanta alokcin da adamcy ya shigo hankalinsa a d'an tashe, shima shagala yay a kallon yaran sai faman zuba murmushi take ,da alamun yaran sun tafi da imaninta, naunauyen ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata irin wadatacciyar natsuwa dan lokacin daya hau sama bai ganta ba sannan bai ga kayanta ba ya shiga damuwa waje ya fita yana tambayr masu tsaron kofar shiga gidan mami suka tabbatar masa da tana ciki shima murmusawa yayi yana lasar lips dinsa na kasa kafin ya d'auke kansa ya maida ga mami da suke magana da hajiya zulfa'u."


Zuwa can fad'a ya kaure tsakanin yaran d'an shekara biyar din ya fixge jirgin wasan daga hannun mashkur yazo wajen maryama ganin tun d'azu hankalinta na kansu yana tambayarta "aunty see mashkur remove the flight board shima mashkur ya karaso yana huci ya nuna mata game dinsa da amir ya buga da kasa duk da maganar yaron farko bata fito sosai ba amman maryama sarai ta fahimcesa dan haka sai tayi murmushi ta kamosu gabad'aya ta zaunar dasu akan cinyarta tana sake murmusawa, duk abinda ke faruwa akan idanun adamcy da turanci maryama tace " kai gsky mashkur baka kyauta ba amman kayi hakuri kaji murmushi ya mata shima, yace "aunty mashkur mugu ne kullum sai ya bata min kayan wasa "yi hakuri ka daina ce masa mugu ba yayanka bane ?"da sauri ya girgiza mata Kai alamun a'a tace "da gaske?"maryama ta fad'a tana dafa kafad'arsa kansa ya d'aga mata kai mahukr yace "nima ya buga game dina da kasa bazan yarda ba! shima hakuri ta bashi Aunty na koya miki game ?"ta gyad'a masa Kai Amir yayi sauri yace "aa ni ne zan koya miki yadda ake wasa da jingina ko ?" maryama ta d'aga masa kai alamun "eh !tana jin wani farinciki yana shigarta duk suka d'aura mata akan cinyarta alokcin iyayensu dake cikin d'aki suka fito suna kallonsu gabad'aya yaran sun zagayeta tana tambayr sunan mace Amir tace ."rayhana "

Murya aunty khadija ce ta dawo daita haiyacinta ta tuna da inda take "mashkur oya gida Ina takalminka ?"hannuwansa ya ware mata alamun bai sani ba "ba tun d'azun nace kaje ka dubo ba ai kuwa anan zan barka "da gudu amir yaje bayan kujera ya d'auko ya mika wa mashukur yace "ungo tunda tafiya zakuyi "ai gbdy sukayi dariya wato Kai ne ka boye masa takalmin kenan ?"amir ya d'aga mata Kai , a yadda ta fahimta Amir da rayhana yaran aunty zabiba ne yayinda mashkur kuma d'an aunty khadija ne zasu wuce sai da suka matsa kusada maryama suna bata hannu alamar sallama . itama ta mik'a musu gabad'aya kumatunsu ta sumbata tana sama rayuwar su albarka daga nan sukai gaba, maryam ta binsu da kallo tana murmushi, yaran ma sai waigenta suke suna d'aga mata hannu."sai bayan da suka wuce ta maida kallonta gasu hajiya zulfa'u anan taga gogan nata zaune yana aikin latse latsen a waya tamkar ba shi ba ,mikewa tayi ahankali tayi masu sallama tana fita ta sauke ajiyar zuciya bata Kai minti biyu da fita ba shima ya mike ya biyo bayanta".

mami ta tabe baki tace "kina ganin adamcy kuwa yana haiyacinsa ?"dan girman Allah ki d'auke idanunki akan yaron nan da matarsa "amman baki ga ya dawo wani bita zai zai ba yaro kamar an shaye sa "kiyi masa addua da fatan alkhairi yaran zamanin nan fa ba sai anyi masu wani abu suke abubuwa ba ,yanzu shi adamcy yaron zamani ne ?"hajiya zulfa'u ta kwashe da dariya tace "to shi ai wannan ya wuce da duk tunanin yaran zamanin nan dana zamanin su ke dai kawai kibisu da addua dan wallahi da alamun yarinyar nan bata da matsala kuma daman dan kin fahimci yanayinta yasa kika ce su zauna anan ahankali zaki gane ko wacece ita ,"mami zata sake magana tace "dan girman Allah ki barsu su hutu ni wallahi sha'awa suke bani ,kema dad'i da farinciki ya kama kiji yaron nan zai samu natsuwa bayan wasu shekara nasiha tayi ta mata mami har da kwalla, wanda ita kad'ai tasan fasaarar kayanta, alamarin ta yanzu yana bawa hajiya zulfa'u mamaki suna mata wani kallo ne saboda ya'yanta duk mata ne a yanzu zasu gane asalin halinta gashi kuma suna gani ."

Maryama na k'ok'arin cire hijab dinta ya shigo ya nufo inda take zama yay a kujerar dake kusa da ita yana fad'in "sorry my princess kina bacci na d'an fita zuwa wajen baba babba tace "babu komai tare da sunkuyar da kanta kasa dan tasan tayi laifi ,yayi shiru yana kallonta kafin ahankali ya kamo hannunta "dama haka kike da son yara?ta d'ago ahankali ta kallesa tare da gyad'a masa Kai "yallabai kenan, waye zaice bai son yaro a duniya babu abinda ya kai k'uruciya dad'i"whl
yara abun so ne Ina matukar son yara ".da gaske kina so tace "sosai ma kuma na tabbatar wannan amsar kowa ma zai baka idan ka tambayesa "kamar nawa zaki iya haifa ?"dayawa nake so gsky dan na tarawa mahaifina zuria kaga bamu da yawa ".tai mgnr fuskarta na bayyanar da murmushi "okay kina matukar son ya'ya dayawa amman mai yasa bakya son ayi abinda zaki samu naki ?", take murmushin fuskarta ta d'auke ta sake tsura masa ido fuskar a tamke tamkar ba shine yay maganar ba "kinga da kin barni jiya da wata killa na cila kwalona a raga ya mike daita tsaye suka fara tafiya acikin d'akin tace "idan aka ganka haka kamar baka magana nan kuwa manya manya magana ne acikin wannan bakin naka yace "really?".a tsakiyar d'akin ya tsaidaita suna fuskanta juna itama shiru tayi tana kallonsa sai dai bata ce uffan ba".

ya ruk'o hannunta yana had'e fuska a zuwan baya son raini "kince manya manya magana ne a bakina? tai shiru tare da yin kasa da kanta "
Matsota yayi sosai ya d'ago ha'barta ya sanya kwayar idanunshi cikin nata "my princess yunwa nake ji muryarta a sanyaye tace "muje ga abinci can a parlour'n"sake matsota yayi "ke nake son ci!"yayi mgnr a can kasan makoshi sosai kalmar ta sata jin wani iri ajikinta kamar ya jona mata wutar lantarki k'ok'arin janye idanunta daga cikin nasa take amma sai ya hana hakan faruwa tace "dan Allah ka daina irin wannan maganar ba girmanka bane "kin fa san ba mara lafiya kika aura ba cikakken namiji kika auraba" ai ko baka fad'a ba na sani "to d'an bari na shige ki yau ko ba yawa "zaro idanunta tayi a she a fili tai mgn"
" kema nasan lafiyayya ce kuma kina bukata dan ga yanayinki a hannu kike"no karya haramun banji komai, lips d'insa ya d'an ciza da hak'ora yana matso da fuskarsa dab da nata , gashi ya sarke kwayar idanunshi cikin idanunta ta kasa matsa wa, d'an yatsansa ya d'ora saitin zuciyarta muryarsa k'asa can kasan makoshi tamkar mai koyon magana yace, "zuciyoyin masoya juna ta kan kar'bi sak'oninin juna a lokacin d'aya sannan aikashi ga gabad'aya ilahirin jiki yadda nake bukatar ki haka kike bukatata yana gama fad'ar haka ya juyo daita ya manne bayanta da faffad'an k'irjinsa ,ya d'ora kansa a dokin wuyanta, cikin kunnenta yace karki zurfafa tunani domin yana kawo ciwon kai da hana hutu ke dai ki shirya kar'bata "ya fad'a yana zare ajikinsa yana kallonta tare da d'age mata gira yajata zuwa kan gado ya rungumeta tsam yana cewa yau dai sai na cire tsoron nan ."


Take takensa yasa yau din ma kamar jiya tana ganin ya fita tai k'ok'arin kulle d'akin sai dai taga ya zare key'n d'akin data wa kanta masauki kai tsaye ta nufi d'akin jiya abun mamaki shima ya zare key ta sake fita ta koma d'aki tayi shiri mai kyau tayi kwanciyarta akan kujera ta runtse ido kamshin turarensa yasa ta fahimci ya shigo d'akin tana bud'e idanunta ta ganshi a gabanta ya durkusa,kawar da kanta tayi tare da yin shiru taki motsawa bare ta sak? kallonsa tashi muje d'akina tana jinsa taki tashi ya kai hannu ya ta'ba ta bud'e baki zata sakar masa kuka ".
"Wasa nake bazan miki komai ba ?"girgiza masa Kai tayi alamun a'a "yace oh my god nace wasa nake bazan miki ba" ta sake girgiza masa kai alamun bata yarda shi ba "to naji me kike son ayi yanzu "ka barni anan zanfi yi bacci cikin kwan ciyar hankali da natsuwa sake matsowa yayi gabanta yasa hannuwansa ya tayarda ita zaune "yace bazan iya barinki ki kwana anan ke kad'ai ba muje d'akina mu kwana" ,tayi masa shiru tana kallonsa "na rantse idan nayi niyyar wani abu dake a daren nan wallahi wannan tsoron naki bazai hanani ba zan yi komai dake koda kuwa zai zamo silar rashin kwanciyar hankalinki." shiru tai tana tunani wannan ikon nashi kuma tasan zai aikata abinda ya fad'a."sai dai zuciyarta cike da rauni tace "nifa bazan kwanta d'aki d'aya da kai ba yau" tayi maganar tana masa wani irin kallo na rashin yarda ". "tashi muje !"ya sake fad'a yana mikar daita tsaye tare da riko tsintsiyar hannunta da wani irin sauri ta fixge tace "bazan kwana d'aki daya da kai ba kiri kiri kake nuna jikina kake so dan haka nifa bazan ta'ba yarda wani abu ya shiga tsakaninmu ba tunda auren ma..??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????" ai kafin ta k'arasa sai saukar wani gigitaccen mari taji akan kuncinta ."





Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Page 15


Dishi dishi take gani? acikin idanunta saboda wani irin hasken daya? gilma a cikin kwayar idanunta cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa ta ware idanunta da kyar tare da? kai hannu ta dafe daidai inda marin ya sauka tana kallonsa, wani irin tsoro ne yaga ya bayyana akan fuskarta yayinda zuciyarta ta dinga? bugawa da karfi, kallonsa kawai take tana mamakinsa akan d'an wannan maganr zai zabga mata mari haka ?"mari d'aya yayi mata amman ji tayi kamar goma yayi mata saboda zafinsa .shima kallonta yake? ranshi amatukar 'bace, sai dai sam sam bai ji dadin marin da yayi mata ba alhalin ita din? duniyarsa ce wanda idan babu ita komai zai iya faruwa dashi .nan take ya fara bleming din kansa? "me yasa na mareta?"why !!! i slap her ?abinda yayita fad'a kenan acikin zuciyarsa yana maimai tawa ,hawaye yaga ya zubo akan kuncinta cikin sanyi jiki ta sauke hannunta daga kuncinta tana mai k'ok'arin share hawayenta ."

bayan ta share hawaye ta sake d'agowa ta kallesa ido cikin ido suke kallon juna kowannensu fuska cike da matsanancin tashin hankali muryarta cike da rauni tace "yalla'bai akan na fad'a abinda yake gaskiya shine ka mare ni ?"naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi? tare da sak? tsura mata tsumammun idanunshi cikin kaukausar murya
yace"har? sau nawa zan fad'a miki ba jikinki nake so ba?"yanzu har wannan ya zama dalilin da zaka? min irin wannan zazzafan marin mai barazana da lafiyata?"shiru yayi yana kallonta zuciyarsa na wani irin bugawa da sauri sauri ,dan kallo d'aya zaka masa ka fahimci a matukar fusace yake." cikin tsananin fushi ya shiga nunata da yatsan hannusa yana huci tamkar numfashinsa zai bar gangar jikinsa sannan yace "look at me maryama babu wasa a fuskarta ki bud'e zuciyarki da kunnu wanki da kyau ki saurareni wannan shine karo na farko kuma ya zamo na karshe da zaki sake furta min haka,"yana gama rufe bakinsa tace "kai ma ka sani wannan shine karo na farko kuma na karshe da zaka sake kai hanunka fuskata dan wallahi ka sake marina a bakacin aurenka dan bazan zauna da mutumin da zai dinga ta'ba lafiyar jikina ba, kana ganganci sake marina wallahi aurenka ka ma..."baki isa ki kafa min wannan dokar ba ."

"ina mai? tabbatar miki da baki isa ba."ko kinga nayi miki kama da wanda za'a kafawa sharadi ko doka ?"ki sani komai zai faru dole ki cigaba da zama akarkashina,"ko kin ta'ba ganin inda aka raba hanta da jini "?yadda ba za'ata'ba raba hanta da jini ba hk baza mu ta'ba rayuwa babu juna? ba ,zaki? rayu dani koda kuwa hakan zai zama? silar? rasa komai na rayuwaki? "fuskarta a had'e take kallonsa kafin ahankali ta motsa lab'banta "zaka iya fad'ar komai amman kasani ba zanye magana ta ba "maryama ko kin shiga? d'imuwa ne ko kuma? nace ko kin? haukace da har? zaki amincewa kanki da rudin zuciyarki ?"kina ganin zaki iya kafa min sharadi akanki ne ?"ko dai har kin? manta ko ni wane ne? da matsayina agurinki?" idan kin? manta ko ni wanene da matsayina agurinki bari na tuna miki ,ni mijinki ne ke kuma matar? aurena? ce me d'auke? da igiyoyin aurena uku ras akanta?? dan haka idan hauka kike yi kiyi maza ki dawo cikin hankalinki?
"idan kuwa dimuwa ce tasameki? kike tunanin jikinki nake so ko kafa min wani sharadi kiyi hanzarin ki dawo? cikin haiyacinki dan adam bazai? ta'ba d'aukar wannan rashin mutunci ba."

"babu ruwana da duk wani abinda zaka fad'a ni dai kaji abinda na fad'a karka sak? marina kayi d'aya kayi biyu amman idan kana ganin wasa ne dan Allah ka sake? mareni? kaga abinda zai biyo baya? tana gama fad'ar haka ta juya zata ra'ba ta gefensa tamkar wani zautauce ya fixgota ya rungumeta tsam tsam a faffad'an k'irjinsa gabansa na wani irin? dokawa da sauri tamkar wanda yayi gudun tsare? nadamar marin da yayi mata yake "me yasa na mari cikar burina?" why? na mari zuciyata?."irin matsar da yayi mata yasa? nan nake jikinta ya fara kyarma amman ta kasa kwacewa hular kanta ta zame kitson kanta da ya sauka a kan kafad'anta ya bayyana tamkar an jonata da wutar lantarki haka taji ,cikin sanyi murya yake magana" Allah ya sani princess Ina sonki ba dan jikinki ba dan Allah ki fahimci ke din nake so ba wani abu naki ba ."

wani takaici ya kamata bayan ya gama wanketa da mari zai wani rungumeta yana mata maganar banza ?"fahimtat me zata masa ?"nan take ta soma kicin kicin kwance jikinta daga nashi sak? matseta yayi gam yana cewa "da alamun hakuri kike son na baki sai dai ki sani adam bai yi laifin da zai? iya bada hakuri ba saboda yasan bayan? wannna tsoro kina da shiri akainsa, iya sanin shekaru dayawa nayi miki Ina jin da kinsan da haka da baki yarda anyi amfanin dake dan aga karshena ba "ya k'arasa maganar yana fesa mata hucin numfashinsa,tafiya ya soma yi daita zuwa bakin gado ya zaunar daita? ya janyo karamar stood? gabanta ya zauna tare da tsura? mata idanu yana kallonta ."

runtse idanunta tayi tana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba sakamakon kai kawon da maganarsa ta karshe ta shiga yi acikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login