Showing 108001 words to 111000 words out of 151781 words

Chapter 37 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2694

shiga ko me ?"ka wani zauna wa mutane da towel d'aure tun d'azu sai neman magana kake tunda anki atanka sai kayi hakuri kayi abinda ke gabanka ya zagayo ya zauna kusa daita ya dan jawota jikinsa yana kallon kyakkyawar fuskarta "maryama .."tayi shiru shima yayi shiru yana nazarin ajiyar zuciya data sauke tayi kasa da idanunta domin kasa jurar kallon da yake mata dan wani kwar jininsa yake shigarta Kai tsaye ta kasa sarrafa kanta koda ta dage akan ta fuskancesa da kallo mai cike da muna tsantsar so sai wannan kwarnin nasa ya hanata ."ya d'an yi murmushi "ke kad'ai ce macen da zuciyata take yawan kawo min tunaninki ta d'ago ahankali ta kallesa da shayayyun idanunta "kaje kayi wanka ka raba kanka da wannan towel din ya kalli towel din jikinsa sannna ya kamo hannun ta cikin nashi yayi mata kiss "Ina ruwanki da towel dina ko tsirara naga damar zama a kusa da matata? zanyi ko ba haka ba ?"yayi mgnr yana d'age mata girarsa d'aya lumshe idanunta tayi tana girgiza kai ".

"maryama .."!
ya sake kiran sunanta a karo na biyu bata amsa ba illa ta zuba masa ido tana sauraronsa"kina da dadi !"ware masa idanunta tayi sosai? tana kallonsa cike da mamaki jin abinda ya fad'a ya d'age mata girarsa d'aya "yes Allah kina da .."tai saurin toshe masa baki da hannunta tana 'bata fuska "wai meye haka ne ?"ya kai hannunsa ya cire hannunta yana murmushin gefen baki "dan Allah ka daina fad'a min haka kana sani jin kunya ai kunyar ce nake son cireta a tsakninmu "ni dai a'a!"nima a'a!"ya fad'a yana wani shagwabe mata shiru tayi kawai tana kallonsa "kamar ba shine wannan miskilin da kowa yake jin tsoron tunkarar inda yake ba . daga inda? yake ya dawo gabanta ya zagaye kugunta da hannunsa yana shafa bombom dinta yana lumshe idanunshi."


Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
? ?? MAR'ADAMS
? ?? =ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


? ? ? ? ? Page 23

"My princess Ina son na karar da rayuwata data saura tare dake gashi wata rana dole mutuwa zata d'auki d'aya acikinmu,na kan gar gad'i zuciyata ta daina kawo min wannna mugun fatan domin kuwa duk lokacin data tunatar dani haka naka jin kasala ta baibayeni na rasa kwarin jikina na rasa amsar da zabawa wannna zuciyar wai idan kika mutu koni na mutu yaya d'ayanmu zai kasance ko ke yaya zaki kasance ?"shiyasa ina addua ko mutuwa ce ta d'auke mu tare dan bana son na mutu na barki wani ya aure min ke ko idan na mutun zaki iya aurar wani ?"shiru tayi kawai tana kallonsa tana nazarin maganarsa batare da tace masa uffan ba dan babu komai acikin maganarsa sai zallar kishi yayinda shi kuma jira yake yaji mai zata ce "yalla'ba!".ta kira sunansa ashagwa'be yana jinta yayi mata shiru yana cigaba da matsa bombom dinta yana cusa kanshi cikin rigarta".

"love !"
ta kirasa da wannan sunan wanda yasa yaji gbdy tsigar jikinsa sun mike cike da shukin sonta yace "yes dadina!"ya amsa mata yana zare hannusa a kugunta ya riko hannuwanta duka cikin nashi yana murzawa ahankali "tashi ka shiga wanka ta fad'a tana rausayar masa da kwayar idanunta."
"sai kin bani amsata sannan zan tashi ."ta harare sa tana murmushi tace "ikon Allah kai da zuciyar ka take aiyana maka ai ita ya kamata ta baka amsa meye nawa aciki ?"ya murza hannuwanta da k'arfi yana tsareta da tsumammun idanun shi ."ahankali ta runtse shayayyun idanunta saboda jin zafin abinda yayi mata "ki bani amsa in har kina son na samu sukuni da kwanciyar hankali yau ."tayi shiru yayinda hawaye suka cika idanunta ta runtse idanuwanta kad'an sai ga hawaye shar sun gangaro daga cikin kwarnin idanunta,ba tare data bud'e idanuwanta ba tace "mai yasa zaka kawo abinda kasan zuciyarmu bazata jure ji ba ?"wannan sam ba abinda ya kamata ka dinga kawo shi acikin zamantakewar mu bane"koda ban kawo hakan ba ki tuna sai hakan ya faru damu wani lokaci"duk da haka banaso ace ka dinga sako mgnr acikin zukatanmu hakan na nufin rage mana walwalar zuciya da sukuni."

Ya saki hannuwanta ahankali ya mike tsaye jikinsa a sanyaye "in sha allahu bazanga mutu warki ba sai dai kiga tawa maryama ke kad'ai ce farincikina Ina sonki son da babu abinda ya isa ya kidaya yawansa acikin zuciyata duk gatan dana taso da kulawa irinta mahaifi da mahaifiya dana samu kasancewata namiji tilo tsakanin suke nuna min so da fifita sona akan komai ban ta'ba yin farinciki ba sai dana sameki na gode wa Allah da yayi min kyautar mace kamar ki maryama Ina sonki in sonki Ina sonki !!!har na kan rasa kofar da zan shigo miki da kyauta dan dinbin farinciki dana kasance adalilinki na rasa me zan baki duk kyautar dana miki ganin nake ban baki komai ba me zan miki wanda zaki kasance acikin farinciki har karshen rayuwarki?"tayi shiru kawai tana cgb da kallonsa, kalamansa sunyi matukar kashe mata sansar jiki sai dai mamakinsa take yadda wani lokaci yake iya kwnatar mata da kai ya tausa sa kalamansa agareta ya dawo mata tamkar wani bawa wanda hakan yasa soyayyarsa take sake bin jinin jikinta har take jin son da take masa ya zarta wanda yake ikirarin yana mata ita dai tana iya boye nata ne, yadda ya tsura mata idanunshi yasa take jin soyayyarsa na sake ratsata "burina a kullum na kyautata miki maryama."


Taso wa tayi da kyar ta tsaya a gabansa "bani da abinda nake bukata daga gareka da kyautatawa zuciyata face kaunarka mijina ka cigaba da sona kaine farincikina da samunka ne na samu yaye war damuwar komai arayuwarta kaine muradin Raina kaine farincikina bani da komai sai kai kana tattalina ka bani matsayi mai girma acikin zuciayarka ni da kai mutu ka raba zan dangwama cikin maka dagwamamkiyar biyayya bazan gaza ba in har hakan shine zai zama farincikinka Ina sonka mijina ta k'arasa maganar tana sunkuyar da kanta saboda tsananin jin kunyar maganrta .."
Ya matsota sosai ya rungumeta ajikinsa tsam suna shafa sansar jikin juna shauki da kaunar junansu na sak? mamaye zuciyarsu ji suke tamkar su had'e guri d'aya ."fad'a me kike son na mallaki?ya tambayeta yana kamo ha'barta yana kallon face dinta "ai na rigada na fad'a maka tunda ka soni a matsayin da nake ka gama min komai sukai shiru suna kallon kwayar idanun juna so take tai masa magana akan shan sigari duk da kwana biyu taga baya sha amman tana jin tsoron zai iya canzawa daga farinciki da yake ciki zuwa damuwa dan haka zata bari sai zuwa wani lokaci."

ahankali ta zare jikinta tana duba agogo "yalla'ba ya kamata ka shiga wanka ka fito lokacin na tafiya kuma nasan taru takardu na can na jiranka shima agogo ya kalla sannna ya nufi hanyar bathroom yasa hannu ya bud'e sannna ya juyo tana tsaye tana kallonshi "bana tsamanin zamu wuce wata biyu a kasar nan dole idan zanje england dake zani kiyi renon ciki acan". yana k'arasa magana ya fad'a bathroom har ta bud'e baki zata masa tuni da adduar shiga ban d'akin sai taji mgnr daya sakar mata shi kuma har ya rufo kofar abun shi ta girgiza kai kawai tana kallon kanta "wani irin ciki kuma ana zaman kalau duka yaushe akayi auren ?."sak? girgiza Kai tayi tace "yalla'ba kenan Allah ya bar min kai Allah ya kara maka lafiya yasa kayi tsawon rai mai albarka tana zaune tana tunnain irin soyayyar dake wakana a tsakaninsu dashi a kullum .a dan lokacin da sukai tare jinsa take kamar sun d'auki tsawon shekaru tare dan ya iya soyayya ."

bata ankara ba sai ganinsa tayi akanta ya fito daga wanka lallai tayi nitso cikin tsananin tunaninsa mai tarin yawa, ahankali ta d'ago ta kallesa domin tasan yana nan ya tsareta da wad'an nan tsumammun idanun nan shi masu karyar mata da zuciya, gabanta ne ya shiga fad'uwa ganin launin yanayin su ya sauya kamar ba daga wanka ya fito ba gabad'aya hankalinta a tashe yake kar yace zai yi wani abu daita gani tayi yanayin fusakrsa ta gauraye da murmushi wanda bai bayyana akan fuskashi sosai ba amman ita ta fahimci murmushi ne." tafiya yayi da baya da baya yana kokarin sakin towel din dake d'aure a kugunsa tai saurin sunkuyar da kanta kasa tana jin fad'uwar gaba mai tsanani ."har ya gama shirinsa bata d'ago ta kallesa ba kamshin turarensa ne da ya doki hancinta yasa ta d'an d'ago kanta taga ya shirya cikin wasu hadaddun kananan kaya yana tsaye ya zuba mata idanunshi yana kallonta kamar wani maye kafin ahankali ya tako ya zauna kusa daita batare daya d'auke idanunshi akanta ba ita kam tuni kanta yayi kasa tana kallon kasan kafet ".

"har ka gama shiri ?"ta fad'a tana cigaba da kallon kasa bai amsa mata ba yace "ki taso ki shirya mijinki shima ya zama abun kunya a wajenki ?ta d'ago a natse ta kallesa da shayayyun idanunta "yaushe nace abun kunya ne ?"ta fad'a tana masa wasa da idanunta ya d'an yi murmu shin gefen baki "idan ba haka bane mai zasa da zan shirya kikayi saurin yin kasa da kanki?"Tayi shiru kawai domin ganin ya ranfota bata da ta cewa dan gaskiya tana jin kunyarsa sosai "me zai sa ki dinga jin kunya ta haka nifa mijinki ne bai kamata ki dinga jin kunya ta haka ba komai kikayi min daidai ne haka nima komai na miki ke din tawa ce bata kowa ba still dai bata ce masa komai ba sai dai ta aro murmushi tace "nifa ba kunyar ka nake ji ba kawai abun nan ne nake jin..."sai tayi shiru ta kasa k'arasa maganrta tana jin wani irin fad'uwar gaba "wani Abu kenan ?".
tai shiru tana kawar da fuskarta gefe aranta tace "wannan maganar tafi karfin bakina "Ina jinki!"allah ya gani bazan iya fad'a ba"ya jinjina kai yana dubanta "look at me !ya fad'a cikin wata irin murya mai kashe sansar jiki da kyar ta waigo ta zuba masa idanunta kamar yadda shima yake kallonta "Ina bukatar acire kunyar nan a dinga kula dani yadda ya kamata ."

"kayi hakuri wata rana zan daina "ya gyara zamansa ya matso sosai kusa daita hakan yasa ta sak? sunkuyar da kanta hannunta ya kamo ya rike ya had'e da nashi "idan ina kallonki bana iya rike kaina Ina son naga kin cire kunyar nan ya fad'a yana k'ok'arin had'e fuskokin su kafin tayi wani abu har lip's dinsa sun sauka akan nata tana kallonsa ya fara tsotsan lip's dinta lumshe idanun ta tayi tana kallon cikin kwayar idanunshi sai daya tsostsa son ranshi sannna ya tashi makale daita a parlour'n ta zame hannunta cikin nashi tana masa fatan alkhairi da dawowa lafiya "ban gane nufinki ba !"sarai ta fahimcesa dan haka tace "kayi hakuri anan zan tsaya ". yace saboda me !?
"Ka fahimta mana"! tayi maganr cike da shagwa 'ba ya dawo kad'an ya janyota jikinsa "ban gane ba ki ganar dani na fahimta ,fuskarta ta manna a k'irjinsa tana boye fuskarta ."ya fahimceta sarai saboda yanayin tafiyar ne "idan saboda tafiyrki ce zuwa anjima zaki dawo normal ta d'ago ta kallesa tana hura masa hanci batare da tace masa uffan ba ," muje kici wani abu "ta girgiza masa kai" for now bana jin cin komai idan ina bukatar wani abu zan sauka "duk yadda yaso tabisa taki binsa anan sukai sallama ya kamo bakinta yana tsotsa da kyar ta samu ta cire bakinta acikin nashi ya tsaya yana dubanta tare da kai hannunsa ya kamo kuncinta yana kashe mata idonsa d'aya kamar wata sokuwa haka ta tsaya tana kallonsa ya kai bakinsa daidai kunnenta ya sakar mata zazzafan kiss, saurin d'auke numfashi tayi tana lumshe idanunta bata san tsawon minti nawa ya d'auka kafin ya cire bakinsa ba sai ji tayi ya fice ."


Tunda ya fita suna makale a waya ko kiransa akayi zai ce ta rike wayar da zai shiga metting ne yace ta shiga d'akinsa ta duba durowa da system dinsa take kai zata ga wani book ta d'auka ta karanta kafin ya fito tace "okay tare da mikewa ta shige d'akinsa ta d'auko ta fito zuwa parlour tana zaune tayi zurfi sosai cikin karatun book din soyayya ne sai ga tabawa tana nemi izinin shigowa. bayan ta shigo ta gaidaita cike da girmama wa tace "hajiya tace kizo !" tai tsam da ranta tana tunanin kafin ahankali tace mata "okqy ganin nan zuwa "tabawa ta juya ta fice bayan fitar tabawa ta mike ahankali tana jin fad'uwar gaba dan bata san dalilin kiran ba kuma jikinta tuni ya bata kiran bana alkhairi bane ".ahankali ta koma d'akinta ta d'auko hijab ta sanya ta fito tana taku a natse har ta sauko babban parlour'n gidan sai dai bata ganta a parlour'n ba ta tsaya shiru tana tunanin shiga parlour'nta na biyu dan haka ta samu waje ta zauna akan kujera tare da had'e hannuwanta tana wasa dasu bata jima da zama ba sai ga tabawa ta fito daga hanyar parlour'n mami ,d'an murmushi tayi tace "ranki ya dade ai hajiya tana wan can parlour'n ki k'arasa can ."tana gama fad'ar haka ta shige kitchen."

jikin maryama da muryarta a sayayye ta nufi hanyar parlour'n gabanta na matsanancin fad'uwa da karfin gaske ,aiko tana gama shiga parlour'n tayi mugun gani domin kuwa aunty khadija,aunty shahida zabiba da auta ne zaune sai mami dake zaune a tsakiyarsu suna tautauna wa ,nan take jikinta yayi sanyi haka gabanta ya cigaba da fad'uwa da yake bata san lokacin data soma karanto adduar da zata kare mutun daga duk wani abinda ya tunkarosa( allahumma inna na'uzubika min jadil bala'i wadarki shaka'i wasu 'il kad'a'i wa shamatatil ahda'i ) da kyar ta dinga d'aga kafafunta tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki ta cigaba taku inda gabad'aya suka zuba mata idanu suna mata kallo mai d'auke da tsana da kaskanci ,bata tsaya akoina ba sai a gaban mami ta durkusa har kasa ta gaisheta a tsorace "mami ina yini "!?da kyar mami ta bud'e baki ta amsa mata da "lafiya !"atakaice sannan ta juya ta gaishe da yayyen mijinta da zabiba batare data gaishe da nana hauwa'u ba zabiba ce kawai ta amsa mata gaisuwarta itama babu wani sakin fuska ,ta maida hankalinta ga mami tace "mami gani !"

Kafin mami tayi yunkyrin yin magana aunty shahida tace "ita nana hauwa'u sa'arki ce da ba zaki gaishe daita ba ko kuwa rashin mutuncin da kike wa shi wancan shayayyen sokon mijin naki zaki kawo ma mutane ?"maryama tai shiru tana dukar da kanta kasa azahirin gasky taso ta gaishe daita amman ganin yanayin yadda take jifanta da mummunar kallo yasa taki gaisheta"idan shi kin shanyesa kin gama dashi mu baki isa ki gama damu ba, idan ma ba shi ba me ne ne abun so a wajenki ?"wallahi idan na kalleki kullum dariya nake fashe wa dashi saboda ba inda ya kamata soyayyarsa ta kare ba kenan amman munyi masa uzuri tunda ba haka aka barshi ba an rigada an dabaibayesa da mugayen asiri wallahi rayuwarsa is so pity kin d'auki kaya kin d'aurawa kanki kiji tsoron Allah abinda kikayi kika rufe wa d'an uwamu ido dashi ki kwancensa"ke da iyayenki kunyi shirka kun mallake sa idan ba haka ba ina shi ina ke bare wannna tsinanniyar unguwar taku da ko masu aiki a karkashinaa bazasu zauna acikinta ba bare macen da yake aure ."ahankali maryama ta d'ago kanta tana kallon aunty shahida dake magana cikin nuna isa da mata kaskanci ."

"Wallahi ina namiji bazan ta'ba had'a iri dake ba ko ba dan komai ko dan zuriar da zan had'a dake na kaicewa aurenki wai fa ashe ubanta d'an giya ne kuma acikin giyar ya mutu uwarta kuma sai da suka gama hole warsu da ubanta akayi auren wallahi tur da aurenki "aunty shahida ta k'arasa maganar tana zabga mata harara"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryama ta dinga furtawa tana runtse idanunta tana danne damuwarta da hawa yen daya cika idanunta dan karsu ga raunita bayan aunty shahida tayi shiru itama aunty khadija ta Kama hakan yasa mami ta mike ta shige d'akinta tana goge hawayen bakinciki abinda adamcy yayi mata uba dan gida uwa karuwa wani irin zuriar zata hanfo masa tashin mami ya bawa maryama kwarin gwaiwar yin magana ".tace kuyi hakuri duk abinda zakuyi ya tsaya iya kaina amman karku ta'ba min mutuncin iyayena sai maganar asiri da kuke ta faman mgan akai kusani ni ba jahila bace inada ilimi bazan yiwa namiji asiri dan ya soni ba dan banga ribar me zan samu akan haka ba"yanzu ku amatsayin ku na iyaye iyaye wad'an da suke da ya'ya mata ..""ke dan ubanki waye sa'anki anan nana hauwa'u ta fad'a tana katse maryama ta hanyar fad'ar haka ."

wani kallo maryama ta d'auketa dashi wanda hakan yasa nana hauwa'u ta mike tsaye tana k'okarin rufeta da duka maryama tayi sauri ta mike ta nufi kofar fita da sauri nana hauwa'u tana biye daita tana zaginta sauran taku uku tsakaninsu ta cafko maryama ta shige ta banko kofar da karfi kofar ta rufe kanta aiko tayi tayi ta bud'e kofar ta kasa dan haka tsaya a bakin kofar tana buga kofar da karfi "wato ke gaki yar iska yau sai dai karki fito yunwar cikinki ma kad'ai ta isheki amman muddin kika fito sai kin ci ubanki "maryama dake tsaye a tsakiyar parlour hawaye take zubar wa jikina na rawa " wai ke har kin isa aunty shahida tana fad'a kina fad'a wai gaki shegiya zaki fito ne yar gidan matsiyata matsefa" can sai ga aunty khadija tace "auta kofar a rufe take ne ?"shegiya matsiyaciyar yarinya ta rufe kofar amman zata ci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login