Showing 42001 words to 45000 words out of 151781 words

Chapter 15 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2664

kalleta sannan tace "wannan wace irin tambaya ce subai'a?"tace amsa kawai zaki bani ba tamabayata zakiyi ."tace "to Ina son shi shikenan "karki min karya maryama bakya son shi kalli yadda yanayin ki ya canza jikinki har rawa yake saboda tsananin tsoro wanda ya tabbatar da baki son shi kamar dole yayi miki kika auresa ".


karki zargi wani abu akanshi maganar bana son shi wannan ba gasky bace wallahi ina son shi kawai dai shi nashi son ne yayi yawa har yake rikitani "subai'a ta zuba mata ido kawai itama maryama ido ta zuba mata saboda a halin yanzu duk abinda zata fad'a ba fahimtarta zatayi ba shiyasa tayi shiru taki cigaba da cewa komai ba sai dai ahankali take Jin wata irin matsefaffiyar kaunarsa na bin jinin jikinta had'e da ratsa kowani part na jikinta damuwarta yan'uwansa."ahankali ta d'aga kanta sama tana kallon celling d'akin take ta soma tariyo abinda ya faru atsakaninsu a? mintuna data gabata" mskilili zakin maza,ya tafi ya bar zuciyarta da daddadan kamshin turarensa? tare da tsananin fargaba amman shi kallon yanayinsa kawai zaayi a fahimci yana cikin tsananin farinciki."


Amar dake zaune kusa da adamcy ya kallesa yace"ya jikin maryama din !"?taji sauki "dan Allah adamcy ka tausaya kabi yarinyar nan ahankali kaga bata da lafiya,babu fa wani rashin lafiya, tsabar tsoro ne yayi mata yauwa ."
ai dole yadda kake nuna mata ne yake tsoratata ".
"me nake mata !?yayi masa tambayar yana kallonsa da gefen ido yayinda ahankali yaji gamshin jikinta ya gilma cikin hancinsa ya kawata numfashinsa kamar tana kusa dashi
amar cigaba da kallonsa yayi yace "kafi ni sanin abinda kake mata "is like ka manta tarin abubuwan dake binne acikin zuciyata akanta?"nasani ban kuma manta ba , nasan irin k'awa zucin da kake dashi akanta, amman kasani? maryama na bukatar sausauci daga gareka domin har yanzu yarinya ce da bata wuce shekarun kuruciyarta ba dan da anyi maka aure a shekaru a shirin da uku zuwa da hud'u wallahi da ka isa ka haifa kamarta."


wani mugun kallo adamcy yayi masa wanda yasa take amar yayi shiru yana kunshe dariya adamcy? yace "a'a yanzu ma zaka iya cewa ni ne babanta "dariyar da amar ya kunshe ce ta samu nasarar su'buce masa ai kuwa yasa dariya? "kai me yasa baka son ace ka girma ne ?a ina girman yake ?"adamcy ya tambayesa yana had'e fuska ,"kai kake mata kallon yarinya amman yarinyar tasan abinda take sarai kuma tasan menene aure tunda ta ta'ba yi".duk da haka ni dai dan Allah na rokar mata alfarma ayi mata sausauci."Ka damu mutane da maganar sausauci sausauci as how ?"yarinyar nan fa ba wai bata ta'ba aure ba ta ta'ba yi har ma tasan dadinsa ,"duk da haka kafini sanin kanka Kai din cikakken namiji ne sosai ko a tafiyarka an sheida haka gaba d'aya ajikinka babu alamun ragwanta atattare da kai zaka had'a kanka da wancan lusarin mijin na.."shiru amar yayi ya kasa k'arasa maganarsa tare da lumshe idanunshi, yayi d'an gyaran murya kamar zai yi magana sai kuma yaja bakinsa yayi shiru ."


shima mr ata shiru yayi zaune yana tunanin maganarsa da kuma dalilin da yasa ya kasa cigaba da maganar yace "ma marigayi tsohon mijinta lusari ne? ta yaya zai ce masa lusari ko maryama ta ta'ba fad'a masa wani abu ne akan shi ?"kai she can't do that !"nasan halinta bazata ta'ba fad'a masa komai akan rayuwar aurenta? ba ."sai dai haka nan? yaji babu dadi aransa kwata kwata bai ji dadin? kalmar lusari da amar ya kirasa dashi ba ,duk da ya fahimci yana tayasa kishi ne ,amman koma menene? a yanzu baya duniyar ya rigada ya zama mamaci ko shima wani lokaci da yake jin kishinsa idan ya fahimci maryama na cikin alhininsa ne duk sai yaji babu dadi acikin ransa,har suka k'arasa gida babu wanda ya sake cewa d'anuwansa kala ."


bayan motocin sunyi parking suka firfito daga cikin motocin kai tsaye inda zasu gabatar da walimarsu sauran abokansu suka nufa inda aka bar amar ,hisham ,mb tare da adamcy tsaye mb yace "yanzu ya zaayi da wad'an nan kulolin abincin ?"adamcy yayi shiru dan shima bai san yadda zaayi dasu ba "ko akai wa mami ne ?"iniicewar amar "kana ganin babu matsala idan an Kai mata "?mb ya fad'a yana dubansu d'aya bayan d'aya "bana ce ba amman a gwada kai wa adamcy ya fad'a nan take yasa aka shiga da kulolin guda biyu d'aya na tuwon shimkafa d'aya kuma na miya ."ahankali ya dubi abokansa yace "bari na shiga naje naga sweetheart na fito "okay "! suka fad'a a natse yabi bayan wad'an da suka shiga da kulolin alokcin da wasu tsirarun mutane ke zaune a parlour'n mami dan bata gayyaci mutane ba sai wad'an da baza'a rasa ba suma kuma na gidan ne sai yaranta da hajiya zulfa'u wacce tun jiya ta sauka tana faman bawa mami baki akan ta saki ranta amman furrrr? mami taki sanki ranta ."


Byn wasu yan mintina sai ga mr ata ya shigo da sallamarsa,mutane dake zaune a parlour'n suka amsa suna masa Allah ya sanya alkhairi bai ga mami ba ,haka zalika bai ga yaranta ba dan haka yayi tunanin suna tare daita a d'akinta? kai tsaye ya zarce zuwa d'akinta? ilai kuwa anan ya iskesu gabad'aya suna tautaunawa? wani mugun kallo ya d'aukesu dashi wanda yasa suka sha jinin jikinsu gabadayansu suka mike suka nufi kofar fita dan basu waje .ahankali ya karaso cikin d'akin sosai ya durkusa a gaban mami? yayi zaman dirshan har da tankwashe kafafunsa sakamakon ganin yanayinta sai dai zuciyarsa da gangar jikinsa cike suke da rauni ba dan namijin kokarin da yake? ba da tune zuciyarsa ta buga tsabar halin da sweetheart dinsa take son jefa kanta akan aurensa wanda shi sam bai yi tsamanin zata masa haka ba, a tunaninsa ko dabba ya kawo mata yace ita yake son ya rayu daita zata hakura ta bar shi bare kuma mutun mutun din ma mai nagarta da cikar kamala wacce samun irinta sai mai sa'a .



Yadda yayi shiru yana kallonta haka itama? tayi shr tare da zuba masa? idanunta da suka gama canza kala saboda kukan da tayi numfashi ya sauke ya sunkuyar da kanshi tsawon lokaci suna zaune mami ta tasa shi? gaba tana kallonsa yayi kyau sosai cikin shigar d'aurin aure ba kamar lokacin auren maryam ba daya zare masu ya hana su kwanciyar hankali ya dawo tamkar mahaukaci a natse ta soma magana cikin sanyi muryata ta Kira sunansa "adam tariq abdullah .." ahankali adamcy ya d'ago idanunshi yana duban sweet heart dinsa dasu batare daya amsa ba sai dai a yadda ta kira sunanshi din ya girgiza zuciyarsa sosai domin kuwa ya manta when last da yaji ta kira complete name dinshi haka a koda yaushe bakinta adamcy yake? furtawa dan haka ya tattara dukkan hankalinsa da natsuwarsa gareta cikin sanyi murya da ta sha kuka tace "adam yau dai burinka ya cika ka auro matar da ni mahaifiyarka banaso ,kuma har zuciyarka kana tsananin jin dadi zakayi rayuwa da matar da ni zulai banaso amman shikenan babu komai gaka ga ta nan na barka da matarka."


Ya kai hannunsa ya riko hannunta "dan Allah sweetheart ki daina damuwa wallahi maryama? yarinya ce karama mai tsananin? hakuri zaki ji dadin zama daita duk wani abinda kike so shi zata miki kuma bazan d'auki wani raini daga gareta ba akanki duk abinda tayi wallahi ni mai hukuntata ne sannan na fahimtar daita ta hanyar da zata gane bare nayi imani bazata miki wani laifi ba "ni fa babu ruwana da wata maryama da wani kirkinta dan ita din ba damuwata bace kuma bata gabana damuwata maryam tun jiya maryam har zuwa wannan lokacin kuka take ta rufe kanta a d'akin kuma nayi imani tayi haka ne akan aurenka ,adamcy nasan maryam tana sonka ta dai ki amaicewa ta sake dawo maka ne saboda mugun halinka Ina matukar tsausaya mata ."mami ta k'arasa maganar tana hawaye ."


adamcy ya rude? yasa hannushi yana share mata hawayen cikin tsananin tashin hankali yace "dan Allah sweetheart ki daina zubda hawayenki haka kinyi girma da kuka yanzu,kiyi hakuri da kadda rata, zubda hawayenki bakaramin maseefa bane atattare dani " kince na maida ita na amince miki matsalar ba daga gareni bace daga ita ne? idan har yanzu kina bukatar? a maida aurenmu da maryam wallahi a shirye nake zan amince sai dai fa wannan son da kaunar da gabadayanku kuke bukatar na yi mata na maryama ne kad'ai domin maryama? kad'ai zuciya da gangar jikina suke so."

Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 10


"Sweetheart ina son ki fahimci wani abu shi so wani yanayi ne na halitta da'ake jin shi acikin zuciya wanda yake sa tsawon rayuwa sannan yake sa mutun cikin nishad'i da farinciki wallahi sweetheart Ina matukar son maryama da dukkan nin zuciyata da raina,ina son tafiyar da rayuwata da maryama ne kawai mu rayu tare daita har abada saboda Ina matukar sonta irin son da bazan iya rabashi da kowacce irin mace ba a duniya ,shiyasa ma tun farko kika ga na kasa gabatar miki da kowace mace amatsayin matar aurena. da kin barni tun farko to da yanzu zukatanku suna cikin natsuwa da kwanciyar hankali domin da ba'ayi auren danasani ba dan wallahi da ban had'u da maryama ba to kuwa zan karar da rayuwata ne ni kad'ai batare da kowace mace ba saboda Itace farincikina itace halittar da zuciya da ruhina da gangar jikina suke marukar so."

runtse idanu mami tayi k'irjinta yana wani irin bugawa saboda d'acin maganarsa dan jin maganar tayi tamkar fad'ar mutuwar wani daga cikin ahlinta,sai dai tai shiru tana saurronsa har kusan minti goma ta kasa furta masa komai dan bakinciki da kalamansa suka jefata ciki zata iya cewa tunda take ba'a ta'ba fad'a mata magana mai d'acin wannan ba ,cikin yanayi na kuka mami take kallonsa ".bil hakki abinda yake fad'a mata a yanzu haka maganar take dan yanayinsa kad'ai ya tabbatar mata maganar daga k'asan zuciyarsa ta fito. kenan idan yafi son yarinyar akan kowace mace a duniya kenan har daita kenan tunda har zai iya kallonta ya fad'a mata cewar yana sonta da zuciya da ranshi. "inna lillahi!" hakan yasa mami ta cigaba da kukan bakinciki da take ita kam wannan son bai mata rana ba .gabad'aya sai taji abun ya had'e mata ga matsalar maryam ga kuma wannan zazzafar son da yake wa wannan maryama ."


muryarta cike da matsanancin tashin hankali tace"adamcy har zaka iya bud'e baki ka fad'a min cewar kana sonta da zuciya da ranka ?"kenan ma kafi sonta dani mahaifiyrka ?"tun da har ka iya bud'e baki ka fad'a min haka nasan da gaske ne".
ta fad'a tana janye jikinta daga garesa byn ta d'auke hawayen idanunta ."runtse idanunshi yayi yana mai sake kamo hannuwanta cikin nashi yana jin rashin dad'in jin maganar mami ta yaya ma zata had'a kanta da maryama !"ai ita bata cikin misalinsa dan soyayyarta dabam ce."
ahankali sautin muryarsa ta fito tamkar mai koyon magana "dan girman Allah sweetheart karki min haka ta yaya ma kike irin wannan tunanin ,kina ganin akwai macen da zan so sama dake ne ?"kefa mahaifiya ce Ina magana ne akan wata mace dabam "naji amman ita din wacece da har ta cancaci irin wannan son daga gareka ?"


Shiru yayi tare da bud'e idanun shi akanta bai san yaushe ne sweetheart dinsa ta dawo haka ba ita din macece da bata fiyye shiga abinda babu ruwanta ba koda kuwa akan ya'yanta ne bata matsa masu akan ra'ayinsu most especially shi amman me yasa a yanzu take son canzawa asalin halinta zuwa wani hali dabam?"kuma ma idan zata canza sai da abu yazo kanshi !"shi fa sai dai tayi hakuri idan dai akan maryama ne ba zai ki bin umarninta ba sannan bazai ki son farincikin sa ba, ko yanzu tace a maida aurensa da wancan yarinyar a shirye yake da ya sake cika mata burinta amman fa batun na son ne babu zai yarda yayi rayuwa daita amatsayin matar kaddara."
"ai ni kam nasan bakincikika ne zai yi sanadin mutuwata adamcy dan gabad'aya ka haukace akan soyayya,ka canza daga d'abiarka kamar wanda aka yiwa wani abu".tayi maganar tana dubansa sai dai wannan karon cike da tausayawa ne."


numfashi ya sauke yana dubanta zuciyarsa na wani irin bugawa da karfi shi ba abinda yayi tsamanin kenan daga gareta ba, abinda yayi tsam mani dabam abinda ya iske dabam har yanzu ko fatan alkhairi bata masa ba a auren nan da yayi abinda ya kamata shine farkon abinda yayi expecting daga gareta dasu shahida da khadija amman gabad'ayansu babu wanda yayi masa fatan alkhairi sai ma saka shi damuwa da take son yi ."tun sanda ya fara magana har zuwa sanda yayi shiru yana kallonta kuka mami take yayi duk yadda zai yi ya tsaida kukan abun ya fassaka dan bai son kukanta jin kukan yake har tsakiyar kanshi ."cikin tausasa muryar da sigar rarrashi yace "sweetheart kiyi shiru haka wannan kukan da kike yana ta'ba min zuciyata Ina jin kamar nima nayi kuka ne." hannu tasa ta goge hawayenta "kiyi hakuri sweetheart ban san yaya zanyi da soyayyar maryama bane amamn wallahi kinsan Ina sonki fiyye da son da nake mata ."


a sanyaye tace "baka sona adamcy tunda ka kasa son farincikina ".murmushi takaici yayi kafin yace "wannan rana ta yau din nan ta kasance ranar farinciki ce agareni bayan tsawon lokacin dana d'auka Ina gurzuwa da tarin damuwa iri iri murna tare da taya farinciki ya kamata kowa ya tayani acikinku ,nayi expecting komai ya wuce a zuciyarki tunda mun rigada mun gama da mgnr wannan yarinyar, sweetheart ya dace ki sauke wannan nauyin akanki a yanzu tayani murna da wannan auren ya kamata kiyi ,mami ta kwa'be baki tana kawar da fuskarta ."a wasu lukutan bana gane miki sweetheart ni ne bakya so ko kuwa farincikina na ne bakya so ?".


Shiru tayi tana sauraronsa "karki manta akan mafarkin yarinyar nan babu kalar damuwar da ban shiga ba, babu irin wahalar da ban shiga ba sam ban d'auka bayyanarta har zuwa mallakarta zai zama damuwa a zuciyarki ba amman babu komai, na gode sosai ba dai kuna son maidani marayan karfi da yaji ba?" gabad'aya duk kun juya min baya akan yarinyar nan maryam ?"
"Idan bazaku tayani murna ba ni zan taya kaina zan kuma godewa Allah daya nuna min wannan ranar mai cike da tarin farinciki mara misaltuwa congratulations to me."ya k'arasa maganar cike da rauni yana k'ok'arin kikewa tsaye ."ai nan take mami taji ilahirin jikinta yayi sanyi taji tausayin d'anta ya mamayeta, taji hukuncin data d'auka akanshi yayi tsauri sai dai bata jin zata sausauta masa yayi rayuwar cikin farinciki yayinda d'iyar d'anuwanta take rayuwar kunci ."


tayi biris dashi taki cewa komai har sanda ya mike tsaye ya nufi kofar fita tana zaune tana kallon bayansa cike matsanancin tausayawa tasan bancin abinda yake tsakaninsa da maryam da babu shakka zata nunawa wannan auren gata babu wanda zai kaita murna da farinciki dashi duk da tasan har abada ba zata ta'ba dawo da burbishin soyayyar maryama data fara samun kar'buwa acikin zuciyarta ba sakamakon tozarcin da yayi mata a gaban d'anuwanta ."Jiki a sanyaye adamcy ya fito zuwa parlour'n idanunshi ya sauka akan yan'uwansa suna kallonsa kowace fuskarta a had'e banda zabiba wacce alamunta ya muna tana son masa magana sai dai yanayinta ya nuna masa tana jin tsoro.kallonsu ya cigaba da yi gabad'aya ya kasa samun taya murna daga garesu atakaice dai sun had'e masa kai lallai kuwa zai yi dasu ."


"yadda suka nuna masa shima haka zai masu zai ciresu acikin rayuwarsa zai yi rayuwarsa babu su zai yi rayuwarsa daga sweetheart dinsa sai mrym da ya'yan da zata haifa masa daman ba tun yau ya saba da rayuwar rashin d'an uwa namiji ba domin yasan da ace yana da yaya ko kani namiji da bazai ta'ba juya masa baya akan wannan matsalar ba ." shi a yanzu har gara su sultan akan su, domin duk tswon lokacin da'aka d'auka suna nuna masa kiyayya da rashin jituwar dake tsakaninsa da baba karamin yau dasu aka d'aura masa aure ."inda hajiya zulf'au ta kallesa tsanake sannan tace "Adam har ka fito ?"kan shi kawai ya gyad'a mata alamun "eh!" tare da kai hannu yayi baya da hular kanshi ya shafa goshinsa hajiya zulfa'u ta kalli su aunty shahida taga duk sun yi masa dip sunyi wani iri kuma tasan duk wanan shirun bai wuce na auren yayi bane tunda mahai fiyarsu bata so dole suma bazasu so auren ba amman duk da haka bai dace su zare kansu cikin lamarin auren ba ."


magana take son tayi dasu gabad'ayansu sai dai taga yanayin adamcy din kamar yana cikin tsananin damuwa tana kallonsa ya fara taku a natse ya nufi kofar fita ta yunkura ta biyosa tare da kiran sunansa ,adaidai bakin kofa yaja ya tsaya batare daya juyo ba yana jin zallar damuwa acikin ranshi ta tsaya a kusa dashi tana cewa "ka natsu ka kwnatar da hankalinka komai mai wuce wa ne ,"bana son ka tsani 'yanuwnaka duk da sunyi maka ba daidai ba, lamarin mahaifiyarka zaka duba su ya'ya mata ne wad'an da a kasani da Taya iyayensu kishi amman da sannu komai zai wuce barin ma idan yarinyar tana da kwantar da kai ".numfashi kawai ya sauke batare da yace uffan ba duk da maganar yake son yi sai dai ya tsinci kanshi da kasa yi ."


"zuwa karfe nawa ne zaaje d'auko surukartawa dan ina son na d'an kwanta kad'an kafin lokacin "my aunty ki kwanta abunki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login