Showing 102001 words to 105000 words out of 151781 words

Chapter 35 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2659

da yake da amafani matukar ajikin d'an adam ko yanzu saurari yadda bugun zuciyarki yake sauka wanda alama ce ta kina tsanani sha.."da sauri ta juyo ta kai hannunta ta rufe masa baki batare data kalli fuskarsa ba,dan maganganunsa kunya suke sakata amman ya kasa gane hakan ".

tsareta yayi da idanunshi kawai batare da yace mata uffan ba ,bata cire hannunta dake rufe da bakinsa ba sai ji tayi ya kamo yatsun hannunta d'aya ya tsarke da nashi ya nufi hanyar fita daita suna fita taga ya wani had'e fuska kamar bashi ba sai wani aji yake ja cikin wata irin tafiya ahankali ta d'an ja baya dashi tana kallonsa "ya d'an tsaya tazo ta samesa "kiyi tafiya da kyau mana kallon jikinta tayi tana rausayar masa da idanu "tafiya mai kyau zakiyi ba rausayar min da idanu ba ta kallesa tana tunnain wace irin tafiya yake son tayi bayan wacce take yi ?taki d'auke idanunta akan shi ko zai mata Karin bayani "gani tayi ya kalli bangaren dama inda wasu mutane suke zaune akan kujera suna kallonsu da alamun shaukin ganinsa suke azahiri "kalli yadda idanun mutane suke kanki "sakin fuska tayi zata sakar masa mur mushi yace "karki sake murmushin nan ya bayyana akan fuskarki "yayi maganar tare da gargadi babu shiri ta had'e fuska ."ni dai bani suke kallo ba kai suke kallo"tayi maganar cike da shagwaba .ilai kuwa mutanen nan taso wa sukai suna k'ok'arin karasowa inda suke fahimtar haka yasa tayi gaba ta tsaya jiransa yayinda barinta wajen ke da wuya sai ga masu tsaronsa sun bayyana inda suka shiga tsakainsa da mutanen ."

Fuskar maryama ta cika da mamaki dan ita a tunaninta ya sallamesu tana kallonsa ya basu Umarni su kauce da hannunsa nan take suka ja baya suka tsaya zagaye dashi "cike da girmamawa mutanen suka fara gaishe sa ya amsa sai dai fuskar nan tasa a had'e take ."fuskar mutanen d'auke da murmushin farinciki suka bukaci suyi hoto d'an girgiza kanshi yayi yana sauke numfa shi kallo d'aya tayi masa ta fahimci ransa bai so ba amman haka taga ya gyara tsayuwarsa sun d'auka suna gama d'auka ya wuce ya barsu tsaye suna murna a ranta tace "Allah sarki rayuwa wanda kuke murnar gani ma shi ba mai damuwa da mutane bane ,dan a fahimtar datai masa kwata kwata bai son mutane ya isketa a inda take tsaye "muje !"ya tasa gaba suka cigaba da takawa har suka isa Ile inyo dake kallon radisin blue waje na mussaman aka kai su haushi yasa yaki kallon inda take wani gefe kawai yake kallo itama haushi ya kamata taji kamar ta tashi daga wajen sai dai ta danne zuciyarta tunda ta fahimci yana da tsananin kishi ,hannusa ta riko cikin nata tana murzawa ahankali ".

bai juyo ba ya kalleta ba ".muryarta a sanyaye tace "yalla 'bana ayi hakuri a yafe wa maryama duk da bata aikata laifin komai ba ".ahankali ya juyo ya zuba mata tsumammun idanunshi batare da yace mata uffan ba duk da magana yake son yi "kayi hakuri idan ba haka ba baza kaje second round ba "ta fad'a tana rufe fuskarta da hannunta d'aya sarai ya fahimci abinda take nufi damke hannunta yayi sosai cikin nashi yana cigaba da kallonta ganin ya saki ranshi tace "yalla'ba banji dadin irin tarbar da kayi wa mutanen can ba kamata yayi ka sakar masu fuska ko kad'an ne had'e fuskarka bashi zai sa raini ya shiga tsaka ninka da mutane ba amman fa ba dole nayi maka ba shawara ce idan kaji babu dadi kayi hakuri. yayi shiru kawai yana cigaba da kallonta kallon data fasaara da kallon Jan aji wani kallon kasan gira mai Kama da za'a lumshe ido "kace wani abu mana ka tsaya kana kallona?"me zan ce akan abinda ya shafi rayuwata "?jin abinda ya fad'a ta saki hannunsa ta mike zata tashi tana sakar masa harara yayi saurin riko hannunta ta fizge ya sake kamo yatsun hannunta,yayi masu riko mai kyau ya zagayo daita gefensa ya zaunar
Daita yana cewa "ki natsu mana ko kin manta inda kike ne ."?

Narke masa fuska tayi kamar zatayi kuka yayi murmushi yace "shikenan zan canza ai yanzu sai abinda kikace tunda kujerar mulki tana hannunki idan kina son na had'a miki da takobi sai ayi miki yalla'biya bata san lokacin data sakar masa murmushi ba ,ya ciza lip's dinsa "haka kake cewa akoda yaushe kujerar mulki tana hanuna amman daidai da second d'aya ban ta'ba jin dadin mulkina ba"karkiyi karya mana "!ya fad'a yana mata kallon kasan ido ahankali ya dinga fad'a mata kalamai masu sanyi da narkar da zuciya basu suka dawo ba sai cikin dare suka dawo bayan sunje sun d'an ciye ciyen su a restaurant din dake cikin hotel din suna komawa tare sukayi wanka dan idan da sabo yanzu ta saba da wankansu tare dan ko yayi nashi idan yaga zata shiga sai ya biyota ranar ma kwana yayi romancing dinta." kwannsu biyu a raddisi blue suna more wa rayuwa maryama taji kamar kar su koma gidan mami ,a kwana biyu din da basu gida yasa akayi capturing dinta wa international passport, ya'yan mami aranar suka zo gidan bata hakuri da kyar mami ta sauraresu ranta a 'bace tace "ai kun cuceni wata killa da wani zata aura bashi ba,gashi yau kwana biyu kenan tunda suka saka kafa suka bar gidan nan banga dawowarsu ba,babu kira babu komai Allah ya gani banason adamcy da yarinyar nan dan jikina yana bani iyayenta basu barshi haka ba duk da zulfa'u tace na daina fad'ar haka amman na kasa daina wa kana kallon adamcy kasan baya cikin haiyacinsa nifa nafi tunaninta yarinyar nan completely ba mutun bace ."

Aunty khadija tace" mutun ce kmaar kowa tsabar dai biye biye ne da rashin imani irin na ya'yan talakawa nifa shawarar da nayi zan sa ayi edit din pictures dinsu da adamcy a buga a jaridu duniya ta gani ta haka ne kawai zan huce takaicin marin da yayi min"girgiza kai mami tayi fuskarta a d'aure tace "khadija bazan yarda da wannan shawarar ba kuma gara da kika fad'a naji domin kuwa da kin zartar da hukunci nan dana yi mugun sa'ba miki dan bazan ta'ba yarda ba duk abinda adamcy zai min bazan bari mutuncinsa ya zube a idanun duniya ba domin zubewar mutuncinsa kamar ta'ba kimar zuriar tariq ne zan dai tashi tsaye da addua da sadaka idan ma dauresa akayi Allah ya fidda shi. gabad'a yansu numfashi suka sauke kafin ahankali aunty shahida tace "ai kuwa zata ci uwrta a gidan nan karki sake barin ya fita koina daita ta shiga cikin sawun masu aikin gidan nan wata killa idan taga an maidaita baiwa zata bawa kafarta iska ."ita dai mami shiru tayi dan ba wannan bane damuwarta damuwarta yadda take hango rayuwar d'anta dan hatta soyayyarta gani take ya rag? acikin zuciyarsa ."

"Da wannan shawarar suka kawo karshen tau taunawwrsu washegari maryama suka koma gida zuciyarta cike da matsanancin fargaba suna shiga parlour'n mami idanunsu daita suka soma cin karo tana tsaye tana magana da wani mutun dake k'ok'arin kafa makeken hoton maryam ajikin bango shiru maryama tayi tana kallon hoton tana ma matar kallon sani bama kallon sani take mata ba ta ta'ba ganinta kuma acikin gidan a rana ta biyu data fara zuwa gidan matar zaune akan kujera na alfarma yayinda babynta ke zauen akan cinyarta tana bulbura murmushin maryama ta d'an waigo gefenta inda adamcy yake tsaye sai dai taga baya wajen can ta hangosa zaune yana kallon sama da alamun hoton bai d'auki hankalinsa ba kamar yadda ya d'auki nata ta d'auke idanunta akanshi ta k'arasa gaban mami ta durkusa har kasa sai dai ta rasa me zata tace mata "sannu da gida zata mata ko kuwa gaisheta".?shiru tayi durkushe har second goma tayi tana tunanin abun cewa can dai tayi tunanin gaisheta dan haka cikin kwantar da muryar tace "mami ina yini ?"shiru ne ya biyo bayan gaisuwar har ta cire rai da zata amsa sai taji tace mata "lafiya !"

wani naunauyen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mike tsaye tana wasa da yatsun hannunta tamkar kazar da kwai ya fashe wa aciki haka ta dawo a gaban mami wacce ko kallo bata isheta ba cike da sanyin jiki ta nufi hanyar step har tayi taku biyu taji adamcy yayi gyaran murya ta tsaya tare da juyowa tana kallonsa da hannunsa yayi mata alamar tazo tai saurin girgiza masa kai tana kallon inda mami take tsaye alokacin har an gama kafa hotun nan take taga adamcy ya had'e fuska har kaminsa sai daya canza bata san lokacin data juyo gabad'aya ta soma taku zuwa inda yake cike da matsanancin fad'uwar gaba ba ta d'an zauna nesa kad'an dashi tana cewa "me zan maka ?!"shiru yayi yana ciza gefen lip's dinsa "dan Allah ka barni naje!"still share ta yayi tare da ware kafafunsa .zata sake magana mami ta k'arasa inda ya maida hankalinsa kanta yana gaisheta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa sannna ta samu guri ta zauna a kujerar dake kallon nashi tana kallon maryama dake zaune cike da tsoro "tashi ki bani guri zan yi magana da "d'a..."

ai maryama bata gama jin karshen maganr ba ta mike da sauri ta nufi hanyar step adamcy yabi bayanta da kallo har sai daya daina ganinta sannna ya dawo da kallonsa ga mami tace "baka ga yadda khaira ta k'ara girma ba ?"yace na gani tayi fine !yayi maganar batare daya sake kallon hoton ba tai shiru na second biyu tana nazarinsa sannan ta cigaba da magana "yanzu saboda manzon sallahu alaihi wa salam adamcy ka d'auki yarinyar nan tun sheka ranjiya sai yanzu ?"Menene illar haka sweetheart? "ya tamabya batare jin komai ba sai dai ganin irin kallon da take masa yace "am sorry "ta sauke numfashi ta cigaba da magana "na tura maka wasu addu'o i kajisu da kyau kuma kayi kokarin kayi duk wanda aka yiwa sihiri idan yana karan tasu safe da yamma Allah ubangiji zai maidawa mai shi kayansa dan na fahimci wannna yarinyar bata barka haka ba dan yanzu rashin jin barinka yayi maka yawa kana abubuwa baka san kanayi ba gabad'aya baka cikin hankalinka dan yadda kake bare bare akan yarinyar nan ba a banza ba dan dai Kai din nan ba adamcyn da ni na haifa bane ."

tunda mami ta soma magana yanayinsa ya canza zuwa mummunar 'bacin rai sai dai yayita kokarin danne wa yace "sweetheart duk naji bayaninki kuma in sha allahu zan duba adduoin sai dai abinda kike tunani akan yarinyar nan ba haka bane dan ko qurni aka bani zan iya rantsuwa akan bata shirka dan Allah ki kwantar da hankalinki ki bari zuciyarki ta samu natsuwa daita kallonsa kawai tayi tana kwabe baki daman tayi expecting kareta zai yi "ni dai babu ruwana da ita dani wallahi har yanzu bana sonta da zaka rabu daita ka auro wata da zan fi jin natsuwa da kwanciyar hankali"ai kuwa mami sai dai kiyi hakuri ki cire wannan tunanin a ranki dan bazan ta'ba iya rabuwa daita ba, maryama ko aljanace ni ita zuciyata ta gani take so."


An min haihu in sha allahu sai bayan suna zaku cigaba d jina =?O?=?O?=?O?

Mmn sudais
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Page 22

Hankalin? mami a matukar tashe ta kafeshi da idanuwanta tana dubansa tana nazarin mgnrsa
at the same time kuma tana maimaitawa kanta abinda ya fad'a "ai kuwa mami? sai dai kiyi hakuri ki cire wannan tunanin a ranki dan bazan ta'ba iya rabuwa daita ba, maryama ko? aljanace ni ita zuciyata ta? gani? take so."sama da minti goma tana filla filla da maganar kafin daga bisani ta furta "mami !a fili wato? sunan daya kirata dashi yanzu "yaushe rabon ya kirata? da wannan sunan bama zata iya tuna when last ba.nan take mami ta nemi natsuwarta ta rasa? kuma alokci d'aya ta soma jin zuciyarta kamar zata buga sakamakon fad'uwar gaban data risketa tana kallonsa ya runtse idanunshi tare da kai hannunsa zuwa goshinsa ya dafe? yana furzar da iska mai zafi bayan kamar second goma ya cire hannunsa a goshinsa yana dubanta a tsanake yana tunanin abinda zai fad'a mata ."muryasa a tsarke yace "dan Allah sweetheart kiyi hakuri amman karki k'ara cewa? na rabu da maryama na auro wata ."

"shikenan adamcy? naji na kuma gode sosai? daka nuna min cewar bani da mahimmanci agurinka matarka ta fini dan haka gaka nan gata nan na bar mata kai kaje ku k'arata, kayi duk abinda kaga dama ai duk abinda ido ya gani shi ya jawa kanshi adduar ma idan kaga dama karka yi rayuwarka ce ba tawa ba "tana gama fad'ar haka taja bakinta tai shiru tana kallon wani gefe sai dai idanunwanta sun canza sosai alamun tana cikin tsananin damuwa ."sak? runtse idanunshi yayi a karo na biyu yana sak? dafe goshinsa "har sai zuwa yaushe zata gane mahimmanci mryama a rayuwarsa,matsayinta dabam haka zalika na maryamarsa dabam bama zai ta'ba had'a matsayinta dana maryama ba haka zalika yafi sonta akan maryama sai dai akan ya rabu da maryama ya auro wata ne a'a!dan duk wacce zai auro bazata? ta'ba kai masa kamar maryama ba ."ya cire hannunsa a goshinsa ya dawo kusa daita ya zauna yana kiran sunanta in a low voice sweet heart."! "dakata.."!tai saurin katse masa hanzari ta hanyar fad'ar haka tana waigo da fuskarta ."

"shiru yayi yana kallonta kamar yadda itama tai shiru tana dubansa up and down "zai fi kyau ka kirani da mamin daka kirani yanzu ko kuma zulai! "ya salam!"ya furta a saman lip's dinsa yana sauke ajiyar zuciya"sweetheart dan Allah ki fahimceni wallahi maryama dabam ce she's? different daga sauran mata,maryama tana sonki kuma zaki ji dadin zama daita akan duk wata macen da zan kawo miki a matsayin matata zata ji mganrki, zata miki biyayya, za kuma ta guji duk wani abinda zai 'bata miki rai yarinya ce mai natsuwa da hankali da sanin ya kamata sannan bata san komai akan abinda kuke tunani akanta ba,totally ma bata san menene rayuwa ba.a yanzu babu abinda tasani sama dani kema kuma kinsan da haka "Idon't know and don't care? about all that ni cutarwar da za'a maka kawai nake hango maka amman naga alamar baka cikin haiyacinka an rigada an gama da kai sai yadda akayi da kai."

Jin abinda ta fad'a yasa ya? mike tsam bai tsaya wani k'arin dogon surutu ba ya nemi hanyar step har ya kure matattakala mami na zaune a inda ya barta tana kallonsa cikin tsananin firgici sai dai shi? ko juyowa bai yi ba ya cigaba da taku a natse har ya sauka ya bud'e kofa yana k'ok'arin shiga parlour'nsa yana girgiza kai dan yasan babu abd ke damun mami? sai rikicin tsufa da kuma zugan ya'yanta wanda shi kuma bazai ta'ba barin tayi amfanin da zugan ya'yanta ta raba shi da matarsa ba ."a tsaye ya iske maryama tana zariya a cikin parlour'n tana ganinsa ta karaso gurinsa da sauri ta tsaya gabanta na wani irin matsanancin fad'u wa tare da? kafesa da shayayyun idanunta masu d'auke da tarin tambayoyi kallo d'aya yayi mata ya d'auke idanunshi yana k'ok'arin? wuceta ya shiga bedroom dinsa? tayi saurin? sha gabansa? tana dubansa cikin tsananin tashin hankali dan yadda ya had'e fuska babu sauki? ta jima bata ga yayi irin haka ba wanda hakan yasa taji wani irin yanayi a gabad'aya ilahirin jikinta da zuciyarta dan? jin zuciyarta take tamkar ana buga mata guduma ."

loakci d'aya ta dinga jin zuciyarta na karkarwa saboda? tsananin tashin hankalin da fargaban dake bin jikinta,da kyar take iya janyo numfashi saboda wahalallen yanayin data shiga runtse idanunta tayi da karfi alokacin data ji zuciyarta tana tattarewa waje d'aya acikin ranta take hango girman tashin hankalin dake shirin tun karota cikin wata irin kasalalliyar murya wanda ke fallasa asirin zuciya da gangar jiki take furta kallamar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kafin ahankali ta bud'e idanunta tace "mami tayi fad'a ko !?"ta'be bakinsa yayi yana girgiza mata kai alamun a'a! sannna ya ra'ba ta gefenta ya shige d'akinsa ."bayansa tabi da kallo tana sak? jin tashin hankali from know where yana shigarta ahankali ta had'e hannuwanta waje d'aya tana cigaba da kallon kofar d'akinsa hannuwanta ta sauke? tana ciza gefen lip's dinta da d'an karfi "yace mami batayi fad'a ba amman mai yasa yanayinsa ya sauya haka ?" tayi wa kanta tmbayr da bata da mai bata amsarta sai shi? ."

"lallai wani abu ya faru ko kuma mami ta fad'a masa maganar data 'bata masa rai ya dai boye mata ne "ya Allah ka bani mafuta akan wannan iftila'in dake shirin zama barazana acikin rayuwa r aurena ya Allah ka bani hakuri acikin rayuwar aurena ,ya Allah bazan iya wannan tashin hanka lin ba ka kawo min saukinsa haka tayita tsayuwa a wajen kafin daga baya? jiki a sanyaye ta biyosa ta tsaya nesa kad'an dashi tana kallonsa tsaye rike da kugunsa taku uku tayi ta k'araso garesa ta tsaya tana sauke numfashi da karfi tare da kai hannunta tana k'ok'arin kamo hannunsa cikin nata ."ya zame yana furzar da iska mai zafi shiru tayi tana cigaba da dubansa tare da nazarinsa gabad'aya ya sake ba kamar sanda suka shigo gidan ba sai dai tayi tunanin ta barshi tukun nan zuwa wani lokaci amman kuma ta kasa fita daga d'akin ta samu waje ta zauna a bakin gado tana kallonsa? ya soma kokarin? duba camarorin gidan."

a natse yayi komai ya gama tare da yin shr? yana kallon saman d'akin batare daya kalli inda take zaune ba ".jikita a sanyaye ta tashi daga inda take ta dawo inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login