Showing 141001 words to 144000 words out of 151781 words

Chapter 48 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2682

yana tura hannuwansa cikin aljihu yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa cikin tsananin tashin hankali auta suka fito tare da aunty shahida ta kallesa tsaye tare da polisawa sannan ta kalli mami dasu aunty khadija tace "meke faruwa !"ta tambaya ."officer's ga cikonsu nan ku tafi dasu" "what !"wallahi adamcy kayi hauka mu zakayi arresting?"bazaki san nayi hauka ba sai mun had'u a kotu cikin muryar kuka maryama ta mike tsaye ta riko hannunsa tana cigaba da rokonsa "kasan Allah muddin ka bari aka tafi dasu sai dai ka sakeni ".:

a matukar zuciye taga ya d'aga hannusa sama zai sauke mata mari tai saurin runtse idanunta ko ya tuna tana d'auke da cikinsa ne ya sauke hannunsa shiru bata ji saukar mari ba ta bud'e idanunta fess akan shi gabad'aya yanayinsa ya sauya ya dawo asalin mr ata din data sani yace "bar nan kafin nayi kwallo dake!"officers nace ku wuce dasu aiko suka tasa su gaba suna k'ok'arin fita dasu aunty khadija tace "zan Kira mijina kafin a wuce damu d'aya daga cikin jami'an tsaro yace "babu dama kin kirasa idan munje move"kasan kuwa ko ni din matar waye?  karku saurareta sai kunje headquarter ."adamcy ya fad'a yana jifanta da wani mugun kallo ."yana rufe bakinsa maryama ta kwasa da gudu ta hau sama biyu biyu take taka step jini yaga yana bin kafafunta da sauri ya dawo da kallonsa gefensa inda ta tsaya nan ma jini ya gani ahankali ya dinga bin jinin yana kallo cikin tsananin tashin hankali da kad'uwa ya biyo bayanta yana kiran sunanta."



Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

AYSHA A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Page 29

"Ahankali ya kutsa kai ya shiga parlour'n bai ganta ba ,sai dai idanuwanshi suna cigaba da kallon kasa ,sosai hankalinsa ya k'ara tashi sakamakon ganin yadda jinin d'anshi ko 'yarshi dake malale a kasa ,ji yayi kwalkwaluwarsa ta soma juyawa tmkr zata tarwatse tsabar tashin hankali,take launin idanunshi suka sake kad'awa ga wani irin zafi da kirjinsa ke masa tamkar zuciyarsa zata buga ."kai tsaye d'akinta ya shiga inda ya isketa? tsaye a gaban wardrobe tana fito da kayanta, cikin tsananin tashin hankali ya soma mata magana cikin d'aga murya "maryama jini ne fa ke zuba ajikinki ". ya fad'a yana huci tamkar wani zaki ,sai dai ko kallonsa bata yi ba duk da tasani ,dan tana jin dumin fitarsa ,sai dai ta cigaba da abinda take ,ta juyo ahankali ta ra'ba ta gefensa ta shigesa ta barshi nan tsaye cikin tsananin tashin hankali."ta isa inda ta ajiye karamar akwati akan gado ta zuba kayan data d'ibo tana jin wani sabon tashin hankali na shigarta ".

"maryama !"
ya sake kiran sunanta still bata amsa ba haka zalika bata d'ago ta kallesa ba "karki kuskura wani abu ya samu cikin jikinki ."me ye amfanin cikin da'aka tsine masa ai gara ma ya zube nima na huta,ya riko hannunta cikin nashi tayi hanzarin fixge hannunta tana cewa"bana so kaje ka cigaba da rashin mutun cinka tunda kai babu wanda ya isa yace ka bar abu ka barshi sai abinda zuciyarka ta kitsa maka amman kasani ni mryma a yau zan bar gidan nan kuma har abada na bar shi kenan bazan dawo cikinsa ba idan yaso hankalin kowa ya kwanta tunda daman nice matsalarku to zan barku ku cigaba da rayuwar ku .
ya had'e fuska sosai yana cewa "wai Ina ruwanki da hukuncin dana yanke ?ina ruwana fa kace ?ta tambayesa tana tsaida abinda take ta zuba masa idanu cikin tsananin damuwa ".

"Kullum kuka ake yi dani gashi yau akaina ka zartar wa yan'uwanka hukunci mai tsauri ga.." "babu ruwanki da hukuncin dana yankewa 'yanuwana yayi saurin katseta ta hanyar fad'ar haka "yanuwana ne ba naki ba dan haka babu ruwanki "okay kaga gara na bar gidan gabad'aya kuma gara cikin ya zube ba sai na koma gidanmu dashi ba dan bazan cigaba da zama da mutumin da? baya d'aukar shawara yana jin haka ya zaro mata tsumammun idanunshi cikin kar karwa"wallahi wallahi kikayi gigi wani abu ya samu cikin nan zan bala'i canza miki maryama zan miki abinda har ki mutu bazaki manta dani ba ."ya k'ar????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? asa maganr yana mata gargadi da yatsan hannunsa daga haka bai sak? cewa komai ba ya juya fuuuuu ya bar d'akin kunnensa manne da waya."jikinta ne ya d'auki rawa sai dai bata fasa had'a kayanta ba .parlour'n ya koma yana cigaba da kiran number likita mutun d'aya daga cikin polisawan yace"yalla'ba zamu wuce.  ku wuce dasu ."ya fad'a atakaice yana cigaba da neman doctor aiko suka tasasu gaba suna basu umarni ".

aunty shahida tace"ita mryam shayarwa take a barta a gida? mu zamu biku .adamcy najin haka ya d'ago da sauri yace"karku saurarawa kowa acikinsu ku wuce har daita"wai adamcy ko dai kaje kayi shaye shayen ka da kasa ba?ba shaye shaye nayi ba wuta na sha na rantse da Allah? tunda kuka gwada min rashin imani nima zanyi daku zaku sha mamakina aiko polisawa suka soma kokarin fita dasu khaira na ganin mamar ta zata fita tasa kuka tare da rarrafawa ta biyosu aiko kukan maryam ya k'aru tana tafiya tana waigenta adamcy yasa hannu ya d'auki? khaira? ya rungumeta a kafadansa."mami? dake zaune tana kallon sarautar Allah an tattara mata ya'ya gabad'aya an? wuce dasu? "ta mike tsaye tana zaro idanu waje tare da? fasa ihu muryarta a tsarke tace "meye haka zan gani yau ni zulai ?"yanzu adamcy abinda zaka min kenan?"ta fad'a tana kallon inda yake tsaye yana huci gashi gabadaya jikinsa rawa yake itama mami jikinta? ya d'auki rawa da sauri takarasa kusa dashi tana kallon sa? da idanuwanta cike da ruwan hawaye.
"yanzu sakayar dazaka min kenan adamcy ?ka rasa hukuncin da zaka d'auka sai wannan?"Sweetheart kiyi hakuri hukuncin da yakamacesu kenan kuma na d'auka kina zaune acikin gidan fa? suke wulakanta min mata, baiwarsu ce ko kashe min ita zasuyi ?ya k'arasa maganr adaidai lokacin da likita ta d'aga kiransa cikin gaugauwa ya bata umarnin tazo yanzu yanzu yana katse kiran mami tace wai ma me aka mata daka damu mutane ?"kuma ko me aka mata a ganinka ya kamata kayi masu irin wannan tozarcin da auren su fa ?"ko rikonsu nake a tunanina bazaka masu haka ba bare ya'yan cikina."

Adamcy dake tsaye? sai faman huci yake yana fidda numfashi sai dai ya kasa cewa maminsa? komai? ya barta tana fad'ar duk abinda taga dama dan wallahi yasan yana bud'e bakinsa bakar mgn zai furta mata a yadda zuciya take? cinsa kuma bazai so faruwar haka ba ,dan zata sak? d'aukar wutar tsanar maryama ne? ta k'arawa zuciyarta ta kuma ce ya zageta saboda matarsa .dan haka ya kiyin magana, hakan yasa mami ta sake Jin haushi ta d'aukesa da mari? tana kwace khaira a hannunsa tace "maza maza kasa a dawo min dasu kuma a yanzu idan ba haka ba sai dai nima ka sameni a police station din ".ya zuba mata tsumammun idanunshi da suka rigada suka rine sai dai bai ce mata uffan ba kuma baya ji zai ce din kma bazai sa a dawo dasu ba sai ya nuna masu iyakarsu cikin tsananin fushi mami ta shige bangarenta rike da khaira?tana shiga d'akinta ta soma neman layin baba babba ta fad'a masa abinda ya faru kai tsaye yace babu ruwansa ."

bayan maryama ta gama had'a kayanta ne fa ta fara jin ciwo na ratsa mararta sosai dan haka ta shiga bayi nan fa hankalinta yayi mugun mugun tashi ganin yadda jini ke? fita daga jikinta har da guda guda wani rikitaccen kuka ta fashe dashi tana d'aura hannuwanta duka a saman kanta "shi kenan na rasa cikina gashi kuma tasan tunda ya furta sai ya mata rashin mutunci tabbas bazai barta ba sai ya ci kani yarta,wani irin murd'awa mararta tayi da sauri ta kai hannuwanta duka ta dafe cikinta tana murkususun ciwon mara,rarrafe ta fara acikin bayin tana tunanin yadda zatayi ta gudu ta bar gidan kafin ya dawo ya sameta ."da kyar ta mike ta dafe bangon bayin ta dinga jan jiki ga jinin na tsiyaya ajikinta hankalinta ya sake tashi gabad'aya ta kasa amfani da komai domin tare jinin sai dai hannuta na dafe da mararta dake mata wani irin azababen ciwo .da kyar ta samu? ta fito daga bayin,ta zube kasan d'akin? tana sakin numfashin wahala,har lokacin jinin dake zuba a jikinta bai tsaya ba tana kuka tana kiran wayyohhl Allah cikina zan mutu muryarta da gangar jikinta duk rawa suke cikin haka ya shigo d'akin ya isketa kwance cikin jini dafe da cikinta da kyar ya iya furta sunanta da karfi.
"maryama "!
"meyasa kika min haka?" nace me yasa kika min haka? me yasa kika sa bakinki ?ita kuwa kuka take sosai tana jujjuya kai, yayinda hannuta duka ke? kan cikinta tana murkususu ciwo kmr ranta zai fita jini kuwa sai malala yake? ta kasanta bai san sanda ya buga mata tsawa? yana sake? furta me yasa zaki min haka maryama ?tamkar zaki ya' karaso gareta ya d'agata tsaye zai kai mata gigitaccen mari".

tace  dan Allah karka mareni ka barni da azabar da nake ji wani iri yaji a gabad'a ya ilahirin jikinsa wanda yasa yaji? ya kasa marinta .yayinda rashin kwarin da babu ajikinta yasa tayi kasa ta zube cikin matsanancin ciwon mara da sauri ya durkusa a gabanta ya kai hannunwansa duka ya tarairayota ya manneta ajikinsa ya zuba mata idanunshi kamar zai yi kuka dishi dishi take kallonsa da idanunta da suka gama canzawa tsabar azaba."a haka? doctor ta shigo ta samesu. Ahankali ta karasa gabansu tana kallonsu a fusace yace"kin ja kin tsaya,I think abd ya kawoki kenan ki duba min ita ?tace "sorry sir dama nake jira abani, a zafafe? yace" ki duba min ita nasan halin da take ciki ta d'an tsugunna tare da daga hannuta tana jin yanayin numfashnta sannan ta fito da kayan aiki cikin kwarewa da iyawa gurin aikinta.ahankali tasoma hada allurar da zata mata da kyar doctor ta somu jinin dake siyaya ajikin ya? tsaya ."idanun maryama a rufe suke? sai dai tana jin duk taimakon da doctor take mata da maganar da adamcy yake furtawa " meyasa zaki bari damuwarki ta? zubar min da ciki na ? yayinda ita kuma take furta "wayyo Allah cikina mutuwa zanyi ka tamakamin " ji yayi kamar ya zuba mata lafiyayyun marukan?ko zai samu sau sauci luuuf idanunta suka rufe tana sakin numfashin sama sama ga azabar ciwon dake nukurkusanta ga azabar tashin hankalin da kalaman adamcy ke sak?? jefata ciki tunda take? bata ta'ba ganinsa?cikin yanayi makamancin na yau ba.idanunshi sun kada sunyi jawur gabadaya jikinsa babu inda baya kirma tsabar tashin hankali da yake ciki muryarsa na rawa yace" doctor cikin ya fita ko "?ya fad'a yana kai tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa."

"bazan tabbatar da haka a yanzu ba sai mun dangana daita hospital zamu tabbatar da komai? ta hanayr duba mahaifarta duk da ita a tunaninta a yanayin yadda ta zubar da jinin cikin ya fita sai dai wani ikon Allah,da kyar ya iya cire tafin hannushi yana kallon fuskarta? hawaye ne kwance acikin kwayar idanunshi ya d'agata ya rungumeta ajikinsa muryasa na rawa yace" maryama me yasa zaki min haka ? yana tafiya yana kallon face dinta ya nufi kofar fita daita ."
Suna isa? hospital likita ta soma aikinta sai dai cikin kankanin lokaci ta gano cikin jikinta ya fita ta dawo d'akin da take kwance bata ga adamcy ba ta tsaya akanta tana kallonta? kwance? tana sauke numfashi ahankali "wasu matan dai suna da sa'a a rayuwarsu. karamar yarinyar daita amman kuga? yadda tayi saa shahararren d'an kasuwar nan ke ji daita kallo d'aya zaka masa ka fahimci zallar son da yake mata tsagwaron so ne wanda babu cutarwa acikinsa ."
tana k'okarin fita? daga d'akin shi kuma yana k'ok'arin shigowa tayi saurin dawowa cikin? d'akin inda ya zubawa maryama idanunshi batare da yace komai ba ,ahankali doctor ta soma masa bayani cikin sanyi murya"cikin ya fita ko?"ya fad'a yana ciza lip's dinsa da karfi tace "kayi hakuri yalla'bai ya fita sai dai fatan Allah ya bada wani rayayye mai albar.."tun kafin ta k'arasa maganarta ya runtse idanunshi da karfi yana sak? ciza lip's dinsa ."ahankali ta juya ta fice daga d'akin da kyar ya soma neman? number umma bayan ta d'aga da kyar ya? iya bud'e bakinsa yayi mata bayani halin da maryama take ciki aiko ta rikice yace ta shirya zai turo azo a d'auketa yana gama fad'ar haka ya jawo kujera gabanta ya zauna tare da riko hannunta cikin nashi ba'a d'auki lokaci ba umma tazo dan haka ta maye gurbin sa shi kuma ya wuce police station dan tun awanni uku da suka gabata yake samun kira ta bangaren dabam dabam acikin yan'uwansa koda ya isa station ya cika makil da yan uwa duk wanda ya bud'e bakinsa acikin yan uwa cewa yake ban da halin adamcy wannan case din ai na gida ne a gida ya dace ayisa ."

Har sanda adamcy yazo alhji kabir bai sak? d'aga kiran aunty khadija ba dan tana fad'a masa abinda ya faru yace babu ruwansa" nan fa hanka linta ya soma tashi? sai dai ta dake taki nuna damu warta. gabad'aya zaune suke a Office din commissione yayinda adamcy ya bala'i had'e rai aka bukaci ya fara magana a natse yayi bayani komai da yayita faruwa yace "gasu nan babu wacce ban kira mijinta acikinsu ba amman suka d'auki maganata? banza gashi a yau sun zama sanadin dana rasa gudan jinina "me nayi maku da yasa kuka zabi ku? min haka ?kun zubar min da cikina "aunty khadija ta sauke sanyayyen ajiyar zuciya tace "ka dai zubar da abunka "ni yanzu banason Jin komai commissione take us to court" aunty khadija tace "sai me muje mana wake jin tsoron shari'a  amar? yace " aa aunty khadi kiyi shiru? karki sake cewa komai? saboda sulhu ake nema. cikin haka alhaji bashir ya shigo customer controller ne na jahar lagos kuma miji ga aunty shahida."

cikin haka alhji kabir ya Kira commissioner yace yasa wayar a handsfree ya soma bawa adamcy hakuri yana kuma tabbatar masa shi dai zai d'auki mataki akan matarsa "takama take da matsayinka ni kuma zan nuna mata kafafuna suna da tsawon daya fi na mijinta "ba sai anyi haka ba amar ma ya saka baki yana bashi hakuri sai dai fur adamcy yaki"kun sa fa matsalarsa taurin kai awa mutanen farko? inji cewar salim ya waigo inda yake ya watsa masa kallon banza. juyin d'uniya akayi dashi yace wallahi sai anje kotu idan kuwa har sai anje kotu ai babu makawa anan zasu kwana.nan fa hankalin maryam yafi na kowa tashi dan ma salim ya kawo mata khaira ta sha? nono ."aka kira baba babba shima yace ai hjy zulai ta kirashi? bazai? zo bane? kuma bazai?? kira adam ba ai sai daya fad'a masu sukai kunnen uwar shegu da maganarsa? suna taimaka da mazajensu to sai suyi amfani da karfin ikon su su fito dasu ".

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun hisham ya furta adaidai lokacin da adamcy ya mike ya fice abunsa? yana waya "Aunty khadija ta kalli aunty shahida tai mata rada a kunne"kin wani daga hankalinki ki kwantar da hankalinki bafa zamu kwana anan ba, ni wallahi ko kwana nayi bazan yi takaici ba tunda cikin shegiyar yarinyar nan ya zube? ."Kus kus haka sukai ta magana hisham yace "bari na kira momy ko idan tasa baki zai ji aiko itama tace babu ruwanta har karfe goma? na dare mami sai faman Kira waya take taji halin da'ake ciki amman babu wani bayani sai ce mata sukai magana ake zuwa anjima za'a sallamesu? zabiba kam ta sha kuka har ta gaji? idanunta sun kunbura "bakincikin ta wai yau danuwansu wanda yafi kowa so da kaunar su shine ya zama silar kawo yan'uwanta hukuma wannan wacce irin rayuwa ce."?

Abu fa kamar wasa dare ya fara hankalin kowa na sak? tashi alhji kabir ya sake kiran commissioner sun jima suna waya yace shifa gaskiya kar ya bari matarsa ta kwana a gurin.ya d'aga kafa ne saboda adam danuwan matarsa ne if not shima yasan zai iya amfani da matsayinsa na commissioner wannan haka yake amman dake case din na gida ne dole ayi hakuri ai saboda kai nima na tsaya da yanzu na Kama gabana suna gama waya alhji kabir ya kira adamcy bai wani tsaya bashi hakuri ba yace "kaga kaje ka janye case din"adamcy? yace akan wani dalili ne kenan zan janye case ?" "saboda bazan d'auki wulakancin ga matata ba wannan ma ai tozarci ne "aikin banza kawai ni kuma abubuwan da sukai matata ance maka zan d'auka ne ?bari kaji idan zaka zama cikakken namiji a gidanka ka zama idan kuma zaka cigaba da zama lusari ne fine amman ni ba a haifi matar da zan fad'awa magana taki bi ba ko na kafa mata doka taki ba, babu wannan matar matsayi kake takama dashi to bissimillah kayi amfanin dashi ni kuma zan biyo maka ta sama adamcy yana fad'a shima alhj kabir? yana fad'a."

cikin haka direban mami ya kawota itama tayi kuka kamar me hisham ya sake kiran mumy "dan girman Allah kisa baki mumy a halin yanzu nayi imani ke kad'ai ce zaki masa magana yaji dan girman Allah mumy kinsan halinsa sai ya bari su kwana anan kinga kuma hakan ba daidai bane da kyar aka shawo kanta ta kirasa tana bashi hakuri yayi shiru yana sauroronta har ta dasa aya yace "shikenan mumy sunci darajanki wallahi if not da sai dai mu had'u a kotu tace "aa baza'a yi haka ba yaron kirki allah yayi maka albarka kayi hakuri da yanuwanka Allah kuma ya sake bamu wasu baby's rayayyu masu albarka ka gaishe min da maryama zan kirata zuwa gobe in sha allahu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login