Showing 144001 words to 147000 words out of 151781 words

Chapter 49 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2684

Allah yayiwa rayuwarka albarka? yace "ameen!  na gode daka mutuntani suna gama wayar ya kira commissioner? alokcin hankalin kowa ya kara tashi yan uwa kowa yayi curko curko adare aka sallamosu akace su rubuta undertaking akan bazasu sake shiga lamarinta ba aunty khadija tace bazata rubuta ba sai aunty shahida ce ta rubuta ."

maryama dai batasan iya awanni nawa ta kwashe? a hospital ba ita dai ta farka karfe d'aya na rana ta ganta kwance a gadon hospital ganinta kwance a dakin hospital yasa ta fashe da wani matsanancin kuka tana kiran sunan Allah cikin haka ta soma jiyo kamshin turarensa da motsin shigowarsa take tayi shiru? ta hadiye kukanta.tana ganinsa ta hau rawar jiki ta sunkuyar da kanta kasa tana son ta rokesa sannan ta bashi hakuri amman bakinta ya kasa furta hakan " jikin? bango d'akin ya k'arasa ya jingina jikinsa tare da zuba mata tsumammun idanunshi batare da yace komai ba sai dai zuciyarsa ban da tafasa babu abinda take "wato bazata ce masa komai ba ita kuwa duk hankalinta a tashe yake shirunsa ya sake d'aga mata hankali.kusan mintuna talatin yana tsaye yana kallonta sannna ya soma magana na gode sosai maryama ,shiga cikin abinda bai shafeki ba ya janyo min asara na rasa d'ana ko 'yata amman kisani zaki girbi abinda kika min "sai daya mai mata mata haka har sau uku sannan ya fice daga d'akin yana huci ".

"Inna lillahi wa inna lillahi rajiun kawai take furta wa tana maimaitawa a fili yayinda take Jin wani irin mugun zafi da ciwo "da gaske ta rasa cikinta? "mike wa tayi zaune ta had'e tafin hannu wanta duka waje d'aya tana kuka "dame zataji da cikinta data rasa ko kuma da fushin daya d'auka daita ?tana cikin wannan halin umma ta shigo d'akin da sauri ta karaso tana cewa "ke kuma daga tashinki sai kuka? "umma .." sai kuka yaci karfinta ta kasa cigaba da magana umma tace "kiyi hakuri Allah zai baki wasu masu albarka."ba rayayye bane shiyasa kuka rasa ta rungu mota tana shafa bayanta tana rarrashinta ."
Kullum adamcy zai zo ganinta akalla sau biyu amman babu wata magana dake shiga tsakaninsu kota gaishesa baya amsawa ita kam tarasa mene ne laifinta, ba wani abu tayiwa cikin ba daya d'auki fushi daita ,idan ma sanadi ne ai shine ya janyo ta? rasa cikinta , dan haka itama ta fita batunsa ta d'auki fushi dashi ko yazo bata ma kallonsa har? sai taga idanun umma ne take sakin fuska idan ta fita kuwa had'e fuska take har ya gaji ya wuce ."

adaidai wannan lokacin idan akwai abinda take? so be wuce ta samawa? kanta? mafitar da zata kubuta daga fushinsa ba sai dai babu fuskar da zata samu sausauci ,lumshe idanu tayi? da karfi lokaci guda ruwan hawaye dake kwance a tsakiyar idanunta suka fara zubowa cikin tsananin tausayin kaina.tambaya daya ce ke damunta da har yanzu ta kasa samun cikakkiyar amsar da zata gamsar da kanta? ,"shin ta ya zai d'aura mata laifi? har ya dinga? mata barazana da fushinsa ,wallahi sani ne bai yi ba amman fushinsa na raunana zuciyarta .wani kuka ta fashe dashi umma tace "dadina dake raki da son kuka? yanzu sabida Allah bazaki hakura da kukan nan haka ba? Ifyrki fa itace komai cikin kwana nawa zaki sak? samun wani indai ciki ne sai kin gaji dashi ".
Maryama ta share hawayenta tana shesheka ita fa umma duk tunaninta saboda tayi barin cikin ne batasan damuwarta ta mijinta bace? shiru tayi batare da tace? komai ba taci gaba da tsiyayar hawaye ahankali ta gyara kwanciyata tana tunanin had'uwarsu dashi gobe a gida tunanin take sosai most especially maganarsa ta karshe a ranar da abun ya faru "wallahi wallahi kikayi gigi wani abu ya samu cikin nan zan bala'i canza miki maryama zan miki abinda har ki mutu bazaki manta dani ba canzawa kam ta gani sauran abinda zai mata da har ta matu bazata manta ba Anya kuwa zata koma gidan ko dai tabi umma zuwa gida?to a gidan ma nashi ne!ta zabga tagumi tana sauke numfashi ."



Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

AYSHA A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Page 30

Sadam dake kwance akan doguwar kujera yaji an watsa masa hotunan a fuska,sama yayi da kwayar idanunshi yana duban nadia dake tsaye akan shi tana faman cika tana batsewa,ahankali ya mike zaune tare da dawo da idanunshi kasa yana kallon hotunan data yayyaga sosai gaban shi ya tsananta fad'uwa k'irjinshi na dokawa da wani irin k'arfi. hannunshi na rawa ya kai kan yagaggun hotunan yana dubawa a nutse hotunan daya sha wahala ya bari akayi masa print dinsu ne duk tama wulakancin haka ?"dan gabad'aya tayi masu kaca kaca idan ba wanda yayi wa maryama mugun sanin gaske ba ba zai ta'ba gane itace ba .cke da tarin damuwa ya sake d'agowa ya zuba mata kwayar idanunshi cikin 'bacin rai batare da yace mata komai ba "sadam !"ta kira sunansa tana jin fad'uwar gaba mai tsananin "still kallonta ya cigaba da yi "bafa zan juri wannan iskancin a gidana ba ,ko da yake idan ma ba hauka da toshewar basera irin naka ba banga ta inda matacce zai zauna yana 'batawa kanshi lokaci ba." kayi maza ka dawo tunaninka domin kuwa abinda kake hangowa kanka yayi maka nisa kuma har abada bazai dawo gareka ba gara ma tun wuri ka zauna ka shiga hankalinka sannan ka daina tunanin zaka dawo da abinda ka rasa sannan duk abinda ya faru recording video's din yadda kayi mutuwar karya yana nan a gurina kuma zan bayyanasu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso ,sannan ga babban albishiri a halin yanzu maryama matar aure ce "

sak? tsareta yayi da idanunshi kafin ahankali ya soma furta kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..! yana goge gumi d'aya rufesa alokci guda
hankali ya b'alle mab'allan gaban rigarshi saboda zafin da yaji yana ratsa har cikin b'argon shi lokaci d'aya kuma jikinsa ya kama rawa"ya rage naka ka cigaba da rayuwar a sabuwar duniyarka ka manta da abinda ya faru abaya ko kuma ka zauna kana tuna nin abinda ka rasa rashi kuma na har abada "shiru yayi yana sauraronta har ta dasa aya gabad'aya yama rasa abinyi ya rasa me zayyi."maryamarsa ce tayi aure ?"ya tambayi kansa cikin tsananin firgici da tashin hankali.
"yes tayi aure tana gidan mijinta idan ma da rabo watakilla zuwa yanzu ta samu, dan haka life goes on ka saki ranka kazo mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka tsara .bai san a fili yayiwa kan shi tambayr ba sai da yaji amsar data bashi "anya kuwa abinda nadia ta fad'a gaskiya ne?"aiko idan ya kasance gaskiya ne ba'a ta'ba fad'a masa abinda ya girgiza zuciyarsa ba sai yau .har ta juya tayi taku biyu ta tsaya tare da juyo da fuskarta kad'an tana masa murmushi wanda kana kallo kasan na mugunta ne ."

"Ka tuna yadda aka shirya komai akan mutuwa rka?"kika shirya komai dai!"ya bata amsa a zafafe yana huci yana jin kamar ya tashi ya rufeta da duka .tai murmushi"okay naji amman ka tuna ka amsa makudan kudad'e akan zaka saki mryama?"
yayi shiru yana kallonta jikinsa na rawa "nasan duk ka manta da hakan ?"ta cigaba da magana tana kallonsa abun na mata dadi "ka amshi maku dan kudi kuma kace saki mai sauki ne amman bayan mun dawo gida babu yadda banyi da kai ba kace na baka lokaci zaka saketa amman kaki sbd munafurci irin naka "saurin runtse idanunshi yayi da karfi yana jin bugun zuciyarsa na karuwa "ko kasan su waye wad'an da suka bada kud'aden nan ?"ya bud'e idanunshi da sauri ya zuba mata kawai yana kallonta yana jiran ta fad'a masa ko su waye sai dai yaga tayi dif tana cigaba da yi masa murmushi wanda yayi masa lakabi da harsashi dan jinsa yake tamkar harbinsa dashi take ."

"tunda yake ba'a ta'ba yaudararsa anyi wasa da hankalinshi da tunaninsa irin wannan ba a iya tsayin rayuwarshi, lallai nadia tayi wasa da rayuwarsa kuma muguwa ce ,mahainciya ce kuma makiyiyarsa ce sa'banin yadda take nuna masa duk duniya tafi kowa son shi ahankali ya mik'e tsaye ya nufi fridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi ya kafa a bakinsa. sakamakon makoshinsa daya ji ya bushe ,sai daya sha sosai sannan ya cire robar daga bakinshi tare sauke ajiyar zuciya da k'arfi yayi wurgi da roban yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa sannan ya nunata da d'an yatsansa "daga kaina kin gama rainawa kowa hankali nadia,in sha Allahu koda zan rasa raina ,koda zan rasa komai sai na dawo da maryama tunda dai har yanzu ban furta mata kalmar na saketa ba, sai na dawo daita rayuwarta idan zaki zauna daita fine idan bazaki zauna ba a shirye nake dana rabu dake nayi rayuwa daita ban san me ya faru dani ba da nayita biye miki amman nayi danasanin mara misaltuwa hatta had'uwa dake Ina danasaninsa a yanzu ".yana gama fad'ar haka ya ra'ba ta gefenta ya haye sama."

wani murmushin mugunta ta saki sannan ta biyo bayansa tana magana tana taka step "ai muddin maryama ta bar matsayin da take a yanzu ta dawo maka lallai ya tabbata talauci ajininta yake kuma ita da arziki har abada .sai abu na gaba sadam kana da yawon mantuwa anan fa mukayi aure da kai ba'a africa ba kayi singn nayi sign idan ka shirya rabuwa dani fine ni kuma na shirya makaka a kotu duk ta hanayr da kake son kabi dani zan bi da kai ko zaman lafiya ko akasa sinsa "bai tsaya ya cigaba da sauraronta ba ya cigaba taku yana jin yadda zuciyarsa ke sake d'aukar zafi ."ya shiga d'aki ya kasa zama sai zariya yake gumi na sake tsatsafo masa ta koina ajikjnsa .ta turo kofar ta shigo d'akin ta kallesa tana jin dadi acikin ranta ko babu komai a yanzu tana da makaman da zata yakesa ta hana rayuwarsa sukuni da samun kwanciyar hankali . maryama tayi aure idan ta tuna da haka wani farinciki ke mamaye zuciyarta sannan da hannunsa ya kar'ba kudin sakin maryama .wani sanyi taji ya sake ratsa ilahirin jikinta kuma duk tana da sheida a hannunta dan haka zata ga ta yadda zai mallaketa arayuwarsa tunda tasan bashi da wad'an makudan kud'ad'en dashi suka yi komai kuma dashi suka cigaba da gudanar da rayuwarsu kafin samuwar aikinsa kuma tayi imani maryama bazata rabu da mr ata ta dawo masa ba most especially ma idan taji abinda yayi ya waigo ahankali ya kalleta yana jin kamar yaje ya shake mata wuya ya kasheta ko ya huta da bakinci da tayi sanadin jefasa ciki amman kuma d'an cikinta fa?" ko bama haka ba bazai ta'ba iya kisa ba ."

"Kana kallona!ya d'auke kanshi yana jan tsaki ".
"A kallon da kake min kana tunanin kasheni domin ka biyawa kanka bukatar ka ko ?"da zan iya aikata hakan zanyi amman bazan iya ba amman nadia me yasa kika yi wasa da hankalina da tunanin ?"me yasa kika yaudareni me yasa kika bari na kar'ba kud'ad'an nan ?"ya jera mata wad'an nan tambayoyin yana cizan lip's dinsa da karfi dan wani irin rad'ad'i azaba yake ji acikin zuciya dama gangar jiki "duk saboda Ina sonka ne sadam kasan zan iya rayuwa da kai ko baka da kowa baka da komai tunda kasan a baka da komai na fara sonka to kai mai yasa zaka canza raayinka bayan nasan ni kad'ai zuciyarka take so ."tsura mata idanunshi yayi yana kallonta yana nazarinta "tabbas yasan tana matsanancin son shi kuma zata iya aikata komai akanshi shima kuma yana sonta daga baya ne ya fara jin son maryama da tunanin komawa ga mahaifiyarsa wanda yasan hakin ummansa ne yayi saurin Kama shi.to shi yanzu menene mafuta agaresa ?"
Yayi shiru yana tunanin yana son nemawa kanshi mafuta tun lokaci bai sake Kure masa ba ".

"Ka zaunar daita ka tsarata kawai ka nuna mata ka hakura da maryama wajen ummanka zaka tasan kana raye .kana ganin zata amince da haka ?"zaka iya gwada sa'arka mata kuma da karamin kwakwaluwa tsab zata amince idan ta kama ka sakin maryama sai kayi alabashi bayan ka furta sakin sai ka dawo daita tunda yasan shi Allah da zuciya yake amfani .wannan itace mafutar da zuciyarsa ta tsayu akai dan haka ya sake kallonta adaidai lokacin data mike tsaye ta haura kan gado ta kwanta tare da juya masa baya ."ya sauke numfashi ya karaso ya kwanta abayanta yana kokarin kai hannunsa jikinta tayi saurin mikewa zaune tana cewa "bana son muna furci menene haka kuma ?"I'm really sorry nadia kin san Ina sonki son maryama hakinta dana mahaifiyata ne Allah ya jarabeni amamn nayi tunanin hakura daita tunda har tayi aure ."
numfashi kawai ta sauke ba tace masa uhm ba bare uhm ta sauko ta d'auko takarda da biro ta mika masa rubuta mata sakin anan tare da sa hannunka kana min haka magana ta kare zaka iya tafiya ."

"Yayi shiru yana kallonta daman yasa karshe abinda zata bukata Kenan daga garesa nan da nan kwakwaluwarsa ta shiga kai kawo "in dai har acikin zuciyarsa yasan da gaske ba sakinta zai yi ba koya furta bata saku ba sai dai idan yasan da gaske ya saketa to wannan fa ta saku dan shi saki koda wasa akayisa ya saku kuma ko batasani ba ta saku kuma duk randa labari yaje mata a sak? take daga ranar zata kama gabanta amman shi yasan a zuciyarsa ba sakinta zai yi ba neman mafuta yake kuma zai iya mata saki d'aya kuma ya dawo daita a take. ya sauke numfashi yace anything for you ya kar'bi takada da biro tace "saki uku zaka mata ya tsaya yana dubanta yace "ai kinsan a muslimci ba'a saki uku a take ko anyi amatsayin d'aya ne dan haka zan mata d'aya ."
tai shiru tana tunanin can tace bari na tambaya ta mike tare da wayarta ta fita ta barshi cikin tsana nin tashin hankali bayan kamar minti goma ta dawo d'akin tace "ka rubuta d'ayan yayi kmaar yadda ta bukata ya mika mata ta nad'e takardar ta tura karkashin pillow ta rungunesa ajikinsa "ban ta'ba jin natsuwa da kwanciyar hankali irin na yau ba." ka faranta min sosai ka yafe min duk abinda nayita maka nayi saboda sonka da kishin ka ne" nasani nadia nima ki yafe min ai kai mutumin kirki ne, matsalarka wannan maryama din kuma tunda an rabu shikenan kowa ya zauna lafiya "yayi murmushi yana sak? had'eta da jikinsa ."a ransa kuwa yace idan kinsan wata baki san wata ba ko waye ya aurar min mata wallahi sai ya dawo min daita tunda addini ya bada zabi idan an nemi miji an rasa duk ranar daya dawo za'a bawa matar zabi ."

*****
Maryama tana kwance akan gadon hospital kawai sai ganin maryam tayi ta shigo sanye cikin doguwar riga baka wacce aka yiwa stone work da pink stone a gaban rigar da hannun rigar tayi rolling kanta da mayafin abayar tayi kyau sosai ga wani kamshi da tunda ta shigo d'akin ya sauya yayinda khaira ke rungume a kafad'anta sosai tayi mamaki ganinta adaidai lokacin ."wani tsoro da matsanancin firgici maryam taga ya bayyana a kan fuskar maryama yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da karfi numfashinta ya soma barazanar d'aukewa cikin sanyin jiki ta yunkura ta zauna tana cigaba da kallonta still fuskarta d'auke da mamakin ganinta ."ta kara taku biyu ta tsaya nesa kad'ai da inda take tana shafa bayan khaira sannan ta motsa bakinta ahankali "maryama sannu ya jikin ?"wani sanyayyen ajiyar zuciya maryama ta sauke a fili sannan tace "Alhamdu lillah da sauki tana k'ara mamaki acikin zuciyarta.

"D'akin ya d'auki shiru tamkar babu wasu halitta aciki kowanesu da abinda zuciyarsa take kissa masa bayan kamar minti goma maryam tace "kiyi hakuri da duk abinda ya faru duk da nasan akwai matukar wahala ki iya hakura amman dai kiyi hakuri komai ya wuce na ari bakin gabad'aya 'yan uwana " maryama tace "babu komai dan ni a wajena komai ya wuce ."maryam ta had'iye wani tuttukin bakinciki da zazzafan kishin maryama dake makale cikin ranta ta cigaba da kallonta da kananun idanunta "ance kin rasa cikinki ko ?"maryama tai shiru tana kallonta tana tunanin abinda zata fad'a mata wanda ya jawo suka sak? d'aukar wasu minti goma sannan ta bud'e baki zatai magana sai ga likitoci sun shigo su uku suna cewa "good afternoon mrs adam ?!maryam ta d'an matsa kad'an domin basu dama suyi aikinsu dan taga suna kallon maryama wacce ta amsa da "afternoon! excuse us suka fad'a tare da duban inda maryam take tsaye."

fita tayi daga d'akin ta tsaya a bakin kofar d'akin tana zance zuci .""we have checked all your scan and checkups is all fine I hope your husband can be here in few minutes ?"ahankali ta gyd'a masu kai alamun "eh!"suka dubata sannan suka fita maryam ta sake shigowa d'akin "ki zauna mana !maryama ta nuna mata kujerar dake ajiye wanda an ajiyesa ne saboda mai kula da mara lafiya "
ta girgiza mata kai alamun bata bukata sai dai tayi shiru tana kallonta tana tunani acikin ranta bata ga abinda ta fita wanda yasa yaya adam yake mutuwar sonta ,har ma ya iya rufe idanunshi ya kai yan'uwansa ga hukuma ba.wallahi ita dai a ganinta bata ga shararren kyawau da take dashi ba gashi ita din bakowa ba ,sannna ba diyar kowa ba ,wannan son da yake nuna mata itace tafi cancanta ya nuna wa ba ita ba amman tasan ita kam har abada sai dai ta hangesa daga nesa shiyasa ma tayi tunanin gara ta zubar da maka manta ta rungumi maryama din koda bata so ko hakan zai sa ya tausaya mata ."anya maryam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login