Showing 21001 words to 24000 words out of 151781 words

Chapter 8 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2647

mata adalci ba kuma Ina jin tsoron Allah ya kamani "ya karasa maganar yana jan tsaki "kai wannan maryam din na saka mu cikin bala'in "kamar dole "! "amar nace banaso abarni mana akaiwa wani yayi magana a hargitse suna isa gidansa tamkar wani zararrre ya fito daga cikin motar? yana cewa "Allah ya tsinewa yayan mami gabad'aya domin duk abinda mami zatayi da shawararsu ne sune? sila koma ,hannuwansa duka ya kai ya rufe idanunsa dashi "ya Allah karkasa yarinyar nan ta amince da dawowarta gareni Allah ka min rai ka taimakeni kar ta dawo rayuwata dan wallahi bazan iya adakci a tsakaninsu da maryama ba ."





Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
MAR'ADAMS
=ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.



Page 5


Adamcy yayi shiru zaune bayan ya gama waya da umma,wani irin sanyi ke ratsa ilahirin jikinsa yanzu hankalinsa ya kanta sosai maryam bazata dawo rayuwarsa ba ga kuma maryamarsa zai mallaka tsadadden murmushin nan nasa? ya bayyana akan fuskarsa yana cewa "maryama kin kusa zama tawa ta har abada"cike da shaukinta ya kamo lip's dinsa na k'asa yana cizawa ahankali ahankali yana jin nishad'i mara misaltuwa yana shigarsa ,wayarsa dake ajiye a gefensa ta fara ringing ya d'an waigo a natse yana kallon screen din wayar sunan wanda ya gani yasa ya d'aga yana "cewa "hello baba !"daga can bangaren baba babban yace "adam ya kake "Alhamdulillah baba barka da dare?"barka d'an mamansa."
Adamcy yayi murmushi jin abind ya fad'a yana sosa keya "naji dadi kwarai da ka natsu ka shawo kan mahaifiyarka akan maganar aurenka ya kamata ka canza rayuwarka,rayuwar da zakayi yanzu ta samu canji kabi mahaifiyarka ahankali ku rabu lafiya domin daga lokacin dakayi rakiya aka binneta daga wannan lokacin rayuwarka ta da data yanzu ta samu canji na zahiri dana boye daga wannan lokacin zaka shiga cikin wata sabuwar rayuwar da zai zamo? baka da karfi komai ,kuma komai zai iya faruwa da Kai bare Kai da kake tsananin son? mahaifiyarka karka d'auka wasa duk wanda ya rasa mahaifiya kamar ya rasa duk wani jin dadin duniy ne domin kuwa ka rasa halittar da take son taga rayuwarka ta samu cigaba ,kuma ka rasa wacce zata dinga maka adduoin nasara a duk inda take a zaune ko kwance cikin sallah akoyaushe tana cikin adduar yadda saka samu nasara ne dan haka kabi? mahaifiyarka sosai kayi mata duk abinda kasan zatai farinciki "Ina maka fatan alkhairi ".


"na gode sosai in sha allahu zan cigaba akan yadda nake mata masha Allah daman Ina son naji a wani estate ko a wani guri zamu had'u da su iyayen yarinyar dan na Kira Zulai tace bata san a ina iyayen yarinyar suke ba, shine nace bari na kiraka naji dan in sha allahu gobe nake son mu? tsara yadda zuwan namu? zai? kasance "?adamcy yayi shiru yana tunanin yadda zai kwatatan masu unguwarsu maryama shiyasa yaso su tare a gidan daya basu bai yana kyankyamin gidansu bane a'a saboda irin haka ne yana son ko sun fahimci diyar talakawa ce amman suga girmasu shiyasa yake son yaje yaga umma a gobe duk dai yasan lokaci ya kure masu amman dai zai san abun yi "hello kana layi kuwa adamcy ya sauke wani naunauyen numfashi? sannan ya soma masa bayanin a unguwar da maryama take "yarinyar yar agage ce bayan ya gama masa bayani yace zai tura masa number wanda zasu kira idan sunje "baba babba yace "to shikenan Allah yasa albarka bari na kira babanka prof lawan shaaibu ayi tafiyar dashi ko hakan bai yi ba ?"yayi sosai na kuma gode sosai nima nayi tunanin haka Allah yasa yana k'asar "yana nan dan shekaranjiya mun had'u dashi a d'aurin auren diyar senater barau sukai sallam."


Bayan da adamcy ya gama magana tsayawa yayi cak dafe da goshinsa yana furzar huci amar ya matso ya tsaya kusa dashi yana dubansa cikin tsananin kad'uwa da tashin hankali dan gabad'aya yanayinsa ya sake canzawa ya dawo tamkar mutun mutumi a tsaye,zai iya cewa wannan shine karo na biyu daya gansa cikin tsananin tashin hankali irin haka kuma duk akan maryam ."cike da tausayawa amar ya dafa kafad'anshi sannan ya soma masa magana a natse"tabbas idan har da had'in bakin 'yan uwanka za'a sake dawo da maryam cikin rayuwarka basu kyauta maka ba amman ka daure adamcy komai zai wuce dan muddin baka daure ba wani sabon tashin hankalin da rikici zaka sake janyowa kanka ."
Adamcy ya sauke numfashi da karfin tare da cire hannunsa dake saman goshinsa yana girgiza ma amar kanshi sai dai bai iya cewa komai ba illa ya zuba masa rinannun idanunshi yana kallonsa yana sake jin wani sabon tashin hankali mara iyaka ,shima amar shiru yayi yana kallonsa acikin ransa yace"lallai kuwa za'a sake tafka wani sabon tashin hnkali da adamcy a karo na biyu muddin aka sake dawo masa da yarinyar nan shi kansa bai so mami ta sake saka kanta cikin wannan lamarin ba ,amman babu yadda suka iya daita duk hukuncin data yanke akansu daidai ne ,shi dai zai yi iyakar kokarinsa yaga ya bawa adamcy shawarar yayiwa mahaifiyarsa biyayya su rabu lafiya ,hakan yasa ya cigaba da magana cikin tsigar rarrashi "calm down adamcy ka share komai tunda har ka rigada ka amincewa mami zaka dawo da maryam."



Muryarsa a kasalance tamkar mai koyon magana yace "dole ce tasa na amince amar ."tunda ka amince kayi fatan ya zame maka alkhairi arayuwarka da addininka"amman laifin me nayi wa sweetheart haka ?"baka mata laifin komai ba kawai dai ra'ayinta ne haka sai kayi hakuri ka daure kayiwa mahaifiyarka biyayya ku rabu lafiya".ya sake dafe goshinsa zuciyarsa na wani irin tafarfasa "amar ban san me yasa nake Jin bazan iya rayuwa da yarinyar nan ba duk da kuwa akwai wani abu a tsakaninmu,bugu da k'ari Ina ji bazan iya mata adalci ba muddin zan kasance da maryama "ya kake yin abu haka adamcy kamar ba namiji ba ?" "nafa sanka kai din jaruma ne kuma cikakken nmj ne wanda zai iya handling din mata sama da biyar in da ana aurensu bare wasu mata biyu ".
shiru adamcy yayi zuciyarsa na wani irin zafi tare da barazanar tarwatsewa ."ahankali amar ya duba wayar hannunsa data fara ringin sunan madam dinsa yaga yana wayo a screen din wayar dan haka yace "adamcy ni zan wuce gida madam tayi kira amman dan Allah ka kwantar da hankalinka in sha allahu ma maryam bazata amince da hukuncin mami ba ."wannan yarinyar tasan kanta ne halan"?yayi maganar yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "mu bari muga mai gobe amman ni Ina ji ajikina bazata amince ba"Allah yasa"!ya fad'a yana ciza lip's dinsa
"ameen !"amar ya amsa yana kallonsa da kulawa yana jin kamar kar tafi ya barshi dan Allah yasani yana matukar jin adamcy aransa dan yayi masa komai arayuwarsa shiyasa shima yake tsaye a abayansa a duk halin da zai kasance .da haka sukai sallama da juna ya shiga mota aka jashi ya bar mr ata a wajen tsaye cikin tsananin tashin hankali."



da kyar ya shigar da kansa parlour'nsa yana jin wani irin damuwa mara misaltuwa kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya kwanata rigingine akan gado ya d'aga kansa sama yana kallon saman d'akin yana tunanin yadda rayuwarsa ke gudana mai tattare da qalubali iri iri shi ba maraya ba amman bashi da maraba da wanda bashi da uwa sannan cikin yan'uwansa babu wanda zai nuna a yanzu yace wannan d'anuwa ne mai son shi da son farincikinsa domin da yan'uwansa da rashinsu gara babu a wajensa gara ace bashi da su zai fiyye masa samun kwanciyar hankali ."
ji yayi komai ya sake dagule masa yaja numfashi ya fesar da kyar yana cewa"maryam a kullum kina cin darajan mami ne a wajena dan saboda ita kad'ai zan iya d'aga miki k'afa har ki sake dawowa kiyi rayuwa dani domin ita ce halitta mafi soyuwa a cikin zuciya ba kuma zan so nayi abinda zatayi Allah wadai dani ba duk runtse zan daure sai dai tabbas an rage min wani jin dadi ne daga cikin jin dadin da zanyi a duniya "ya dade a ringingine yana jin ciwo aransa kafin ahankali ya zame ya kwanta ya cigaba da tunanin a halin da yake ciki babu abinda yake da muradi ji kamar sautin muryar maryama sai dai sanin cewar zai iya kiranta itama ta k'ara masa damuwa akan wanda yake ciki yasa ya share ya d'aura hannu wansa duka a sama cikinsa yana sake zurfafa tunani duk abinda suka tautauna da mami babu abinda bai samu kyakkwan mazauni acikin zuciya da kwakwaluwarsa ba,duka hukuncinta biyu sun yi shock dinsa kuma sun fi tsaya masa arai zaman maryama tare daita da kuma dawowar maryam cikin rayuwarsa a karo na biyu a haka ma har gara zaman maryama akan dawo war maryam ,shi tunda mami ta sako zaman maryma tare daita yasan shirin ya'yanta ne sai dai emran bai fad'a masa akwai wannan shirin ba "to ai kuma ba komai emran zai kwashe ya fad'a maka ba "zuciyarsa ta bashi amsa da haka da kyar ya samu bacci barawo yayi awon gaba dashi a can kusan k'arshen dare."



kusan tsawon kwanaki uku kenan mr ata bai fita zuwa koina ba haka zalika bai saka marayma a Idanunshi ba kuma bai nemeta ba sakamakon fushi da yayi daita sosai na rashin nemansa da batayi ba taji dalilin da yasa bai je gurinta ba kamar yadda yace mata zai koma a washegari ".
Ita kuwa maryama ko ajikinta sai dai ta cigaba da zuba ido ta ga har zuwa karshen satin idan har bai zo ba tasan mahaifiyrsa taki yarda da batun aurensu ne hakan kuwa zai mata dadi domin zata cigaba da rayuwarta cikin kwanciyar hankali batare da barazana ba."
bangaren ya'yan kuwa gabad'aya conference call suka had'a da maryam bayan sun gaisa sukai mata bayanin abinda mami take da bukata "shiru tayi kafin ahankali ta soma magana cike da rauni "gasky aunty shahida bana jin hakan zai yuwu dan bazan so na koma garesa naje na cigaba da zaman bauta ba ,nayi zaman rashin yanci nayi zaman da kullum za'a tashi a fad'a min bakaken maganganu ba ,Allah yasani har zuciyata yanzu bazan iya wannan zaman ba ina bukatar zaman 'yanci kamar kowace mace sai dai Ina masa fatan alkhairi a aurensa da zai yi ,ni da khaira kuma Allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi amman bazan zan sake wanan gangancin ba".


"shikenan maryam munji kuma in sha allahu zamuyi mami wannan bayanin "kuyi hakuri idan har na bata maku rai ."to ya zamuyi maryam za dai mu so ki koma din tunda har mami tayi masa magana kuma ya amince da komawarki "inji cewar aunty khadija "aunty khadija ya amince ne saboda bashi da yadda zai yi dan anfi karfinsa ba wai dan son ranshi ba .."tai maganr tana jin kmr suna son dawo mata da abinda take ta kokarin binnewa ne daga cikin shafukan arayuwarta aunty shahida tace "maryam kiyi tunanin akai rayuwar khaira zaki duba a yanzu."
shiru maryam tayi taki ce komai ba tabbas rayuwar khaira abar dubawa ce amman baza tayi sakacin da zata koma gurin mutumin da bai sonta bai kaunar ganin ko abinda ta haifa masa ba ,dama yana son khaira ne da sai tace zata ci darajan khaira a wajensa amman sam bata ga alamun haka ba "sister kiyi hakuri ki dawo mana dan akwai shirin da muka shirya akan yaya wannan auren nasa ba dangwamamme bane domin na wuncin gadi ne zasu rabu abinda yarinyar zata masa zai sa yaji ta fita ransa kuma kinga alokacin dole hankalinsa zai dawo gareki da khaira ."


Duk sukai shiru suna jiran suji mai maryam din zata ce akan maganr da auta tayi sai dai har kusan minti goma bata ce komai ba akarshe dai zabiba ta tsoma baki dan kar suji haushin bata ce komai ba ta soma mgn wacce ba lallai ne yayi wa yan'uwan dadi ba"ni dai a wata shawarar da ku barta tunda ta nuna bata son komawa gidansa domin kuwa mai daki shi yasan inda yake masa yoyo idan dadi ta ji a gidan yaya tasani idan wahala ta sha ta sani "ni dai har kullum maryam zan baki shawara karki rayu a auren da ba'a san kima da darajarki ba, nmj idan bashi yace yana sonka ba idan duk duniyr zasu taru suna son zamanka dashi na banza ne saboda ba da mutane zakayi rayuwa ba dashi zaka rayu amman dai kiyi tunani kamar yadda suka fad'a Allah ya zaba miki abinda yafi zama alkhairi ".sun dade suna tautaunawa sannna sukai sallama daita aunty shahida tayi kokarin d'auko mami wacce take zaune a parlour'nta tayi tagumi tana tunanin adamcy tunda ya bar gidan bai sake waiwayota ba ,yayinda gefenta mai aikinta tabawa ce zaune tana mata magana cike da girmamawa sai dai zurfin da mami tai cikin tsananin tunani bai sa taji sallmar datai ba bare taji ringing din wayarta sai da tabawa ta d'an ta'bata tare da mika mata wayar ta waigo inda take da hanzari tana kallonta "me ya sameki mami kin dade zaune kina tunani "?ta tambayeta duk dai tasan tunnain ba zai wuce akan tilon d'anta ba dan duk abinda yake faruwa acikin gidan sun sani ."



tabawa ta mika ma mami wayarta dake faman ringing numfashi ta sauke tana cewa" babu komai tabawa sannan ta kar'bi wayar ita kuma ta tashi ta bata waje ta amsa wayar idan ta gama ta dawo taji me zasu d'aura ahankali aunty shahida ta soma korowa mami bayanin yadda suaki da maryam "haba mai yasa maryam zatayi min haka ?ko da yake daman zuciyata ta tabbatar min da wahala ta amince, ai naji dadi shine gari a irin wahalar data sha a hannunsa ai bazata so ta sake koma wa gidansa ba ,amman babu komai dani daku bamu isa mu tsara komai ba sai abinda ubangiji ya tsara zamu jira mu bata lokaci ku kirata ku fad'a mata injina nace tayi tunani sosai akai duk abinda ta yanke ta gaugauta sanar maku ."
Maryam kam bayan gama wayrta da yan'uwanta d'akinta ta shiga duk ranta babu dadi ta kwanta a kusa da khaira dake bacci ,ta zuba mata ido tana kallon yarinyarta wacce hankalinta ke kwance bata san me ake kira da damuwa ba tunani ne ya rufe zuciyarta"maryam ki duba karancin shekarun diyarki zakiyita zama haka ne har girmanta sannan kiyi aure?" ki yarda kawai ki koma ko babu komai yarinyar ki zata taso tare da mahaifinta sannan zaki zame ma adamcy karfen kafa ,ki koma ki zame masa baraza arayuwarsa yadda bai barki kinji dadin rayuwa ba kema karki bari yayi rayuwa mai dadi tare da matarsa ".wannan ganganci ne maryam karki sake kiyi wannan kuskuren life goes on ki tsira da rayuwarki datayi saura domin ki duba diyarki mikewa tayi ta fad'a bandaki."


A kalla sai da mr ata ya d'auki sati guda bai je inda maryama take ba haka ita ma koda wasa bata nemansa ba wannan abu yayi masa ciwo matuka Allah yasani zuciyarsa ta fara jin tsoron kardai marayma ba son shi take ba da gaske dan zatayi auren wuncin gadi ne dashi yasa ta kawo masa kanta, shiru yayi zaune tare da tunani mai zurfi dan yau gabad'aya ko d'an sigarin da yake sha ya ragewa kanshi damuwa bai iya sha ba muryarta kawai yake son ji idan da hali ma ya sanyaya acikin kwayar idanunsa ."
Maryama tana zaune suna cin abinci da umma wayarta dake gefen karfata ya fara ringing ganin karshen number ta fahimci mai kiranta wani sanyi taji ya lullubeta dan duk yadda take son ta ciresa aranta ta kasa dauriya kawai take ta d'auki wayar tare da mikewa tsaye umma wacce gabad'a ya hankalinta ke kanta ta d'an tsaida cin abincin dake gabanta tana kallonta ta nufi hanyar d'akinta domin amsa call ."a ranta tace Allah yasa adamu ne ya kira dan ta kula kwana biyu basa waya kuma bai zo ba, kullum addua take akan lamarin su ,idan akwai alkhairi a tsakaninsu Allah ya tabbatar da auren dan bata son mryama tayi biyu babu ba alhji mansor babu adam sai makiya suyi masu dariya daman auren tasan bazai masu dadi ba , kuma da za'a fasa tabbas zasu fi kowa murna ."



Maryama tayi shiru bata ce masa komai ba tana sauraron yadda yake sauke numfashi ahankali natsuwa tayi sosai dan tasan tunda yayi shiru haka tabbas akwai mgn a bakinsa dan haka cikin tsigar Jan hankali tace"a koda yaushe idan naji mr ata yayi shiru koda a waya ne nasan akwai wani babban al'amari dake nuna cewar yana cikin damuwa me zai hana ka sanar dani damuwa rka "numfashi ya sauke da kyar sannan ya motsa lip's dinsa yace"maryama kenan a wasu lokutan kina bani mamaki ".shiru tayi bata sake cewa komai ba sai faman juya maganarsa take acikin ranta "tana bashi mamaki kuma ?"to wani mamki take bashi ?"jin shirun yayi yawa ne ya katse shirun ta hanyar cewa "hello kina jina kuwa ?"
"Ina jinka yallabai wani mamaki nake baka "kinsan me kikayi ai ?"gasky ban sani ba dan ban san nayi maka wani abu ba"tayi maganr cikin sanyin murya tana jin tashin hankali ."shiru yayi yaki cewa komai domin dai ya fahimci raina masa hankali take son yi taya zata ce masa batasan laifin da tai masa ba "? please let me know ,"yayi shiru kawai yana ciza lip's dinsa ahankali "what did I do to you sir dan gsky ban san nayi maka wani laifi ba kuma bazan ta'ba samun natsuwa ba muddin banji laifina ba ?"".maryama tayi maganar cikin sanyi murya tana mai nuna damuwarta a fili numfashi ya sake saukewa cikin rashin bawa maganrta mahim manci yace "karki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login