Showing 6001 words to 9000 words out of 151781 words

Chapter 3 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2651

lallai zan iya samunsa sai dai ina gudun wulakacin da cin mutunci domin matuqar ba namiji ne yace yana son auren mace ba bata ta ba samun kwanciyar hankali daga garesa .


Maryama tai shiru k wak waluwarta na budewa domin son gano wanda k awarta take mutuwar so haka a wajen aikinta to waye wanda take da yakinin muddin ta shiga ciki lallai zata iya samunsa ? me yasa subai a bazaki fad a min ko waye ba tunda kina ganin zaki iya samunsa ta hannuna? aa k awata bari dai naje nayi addua na dawo muga mai Allah zaiyi sun samu tsawon lokaci suna tautauna kafin daga bisa umma ta fito suka gaisa inda maryama ta sheida mata tafiyar subai a umma tayi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? farinciki tai mata addua sannna tace tai mika gaisuwarta ga maiaiki maryama sukai sallama da subai a har bakin sabon titi rakota sannan ta dawo .
umma tayita zuba idanun dawowar mr ata amamn taji shiru har karfe goma na dare ta kasa hakuri tace  maryama ba kince adamu zai dawo ba ? maryama tai tsam da ranta kafin tace  haka yace min amman Ina ganin ya canza raayi ne umma ta d an numfasa  nifa wallahi banason kuna nisa da juna ,daya zo bai ce miki ga ranar da wakilansa zasu zo bane ? maryama ta girgiza mata Kai alamun bai ce ba  ni kam ayi ayi auren nan ko zan samu natsuwa dan wallahi bani da wata cikikiyar natsuwa, umma dan girman Allah ki kwantar da hankalinki duk abinda kikaga bai zo hannun mutun ba to wallahi Allah ba rabonsa bane  haka ne Allah yasa muji alkhairi .



Tunda mr ata ya barta bai sake nemanta ko a waya ba haka itama bata nemesa ba har sukai sati d aya sai dai sakonin tunin da wannan yar uwarsa tasa take mata kullum shine abinda ke jefata cikin zullumi da rashin kwanciyar hankali sai dai kullum sukai chart da subai a tana maimaita mata tai mata addua ita kuma kullum tana cikin addua tana zaune shiru tana tunani kwanakin da suka rage mata acikin lokacin da suka bata, sosai tayi zurfi cikin tunanin har k arfe shida yamamcin ranar ta buga ahankali wayarta ta soma ringing ko data duba mr ata ne ta gani ai bata tsaya bata lokaci ba ta d aga had e da sallam  ya amsa mata yana cewa  princess yunwa nake ta lumshe idanunta sakamakon wani sanyi daya ziyara ilahirin jikinta  kina jina ?
tace  Ina ji me zaka ci  ? Ki dafa min wani abu mai sauki tun safe banci komai ba  me yasa zaka dinga barin kanka da yunwa ? bani da cikakkiyar natsuwa ne zuwa 7 :30 zan zo  okay sir ! ta fad a tana jiran ya katse kiran bayan ya katse jollof din kuskus tayi tunanin tayi masa dan shine abinci mafi saukin dafawa dan lokacin ya tafi bare tayi tunanin dafa masa wani Abu dabam .


ta shiga kitchen ta fara d auko abubuwan da zatayi amafani dasu cikin kankanin lokaci ta dafa masa kuskus wacce taji koren tattassai da kwakwamba albasa da hanta ta sauke ta zuba masa acikin wata yar madaidaiciyar kula sannan ta rufe sauran wanda umma zata ci dan ita kam murna son ganinsa ma yasa bata Jin zata iya cin komai ta fito ta duba fridge taga akwai sauran nah nahr da umma tayi ta maida fridge din ta rufe ta shiga d akin umma ta fad a mata zuwansa ai ko umma tayi farinciki yayinda maryama ta fito ta shiga wanka tare da dauro alwala ta fito .
Bayan ta fito ta goge jikinta turare kawai ta fesa a ilahirin jikinta ta shirya kanta da wata atamfa light blue mai zanen fulawa blue black kayan sun zauna ajikinta most especially Siket din dan ya fito mata da hips dinta ta gama shiri adaidai lokacin da aka kira sallah ta d auki hijab ta zira ta tada sallah bayan ta idar tai addua ta mike ta saka takalmi flat ta d auko mayafi blue black zata d aura sai kuma ta fasa dan bata son tana bayyana jikinta ta d auki hijab Wanda yabi kayanta ta saka .


Karfe bakwai da rabi saura ta fito parlour n ta zauna tana tunanin mr ata dake manne acikin zuciyarta bata wani jima da zama ba sai ga kiransa ta daga a natse tana gaishesa  ya amsa yana shafa sumar kanshi tare da yin shiru  zaka iya shigowa ina parlour n . Ina kan titin unguwarku  na fito ne ?amman ahankali dan nasan kinyi missing dina sosai  ta harare ta cikin waya tana cewa  inji wa yace maka nayi missing sonka  na gode da harara akayi min Ina jiranki . numfashi ta sauke sannan ta mike ta shiga d akin umma ta sanar mata da zuwansa amamn yana bakin titi  ki gaishesa !tace to ta juya ta d auki jakar data had a masa abinci ta fito tana tafiya kamar mai tausayin kasa. natse ta karaso bakin titi inda ta hangosa tsaye a jikin motarsa sai kwayar idanunshi na kan hanyar fitowa daga lungunsu ahankali ta cigaba d aga kafafunta ta karaso ta tsaya a gabansa tana cewa  yallabai bai dace ka tsaya anan ba  inji wa ? ya fad a yana bud e gaban mota ya zauna a mazaunin direba yace bissimillah shigo .


Take ta fahimci abinda yake nufi maimakon hakan daya bukata sai ta bud e bayan mota ta ajiye jakar hannunta sannna ta zagaya ta shiga ta zauna ta rufe kofar tana cewa Ina yini ! madadin ya amasa mata da lafiya sai kawai taji ya kamo hannunta ya sumbata  ina son muyi wata magana dake mai mahimmanci  bissimillah Ina sauraron ka ta fad a tana kokarin zare hannunta maganar tana bukatar natsuwa wanda ya nuna bai dace ayita anan ba idan baayita anan ba mu karasa gida sai muyi acan ko  gidanku ne kawai ya dacewa ayi magana mai mahimmanci ta lumshe masa idanunta alamun ce  gidana zamu ! bangene gidanka zamu ba yallabai gasky ni dai a a idan har maganr ta wuce ayita anan ko a gidanmu sai dai a hakura daita .


 Baki isa ba nace ga abinda zaayi kice aa  yana gama fad ar haka yaja mota kai tsaye gidansa ya nufa daita suna isa ya zare mata hijab din jikinta  cire ki huta ! tana masa magana ko kallonta bai yi ba shigewa yayi ya barta tsaye a babban parlour nsa kam kema da jikinta tana kallon komai dake ajiye a parlour n har da kwalin sigarin da yake sha kusan minti goma sha biyar sai ga shi ya fito da doguwar rigar hutawa ta maza hannunsa rike da cup wanda ke d auke da lemu ya karaso ya zauna kusa daita yana cewa  kinyi kyau fa ta dan yi musmushin dole bata ce masa komai ba ta gefen idonsa ya kalleta  bani wayarki. me zakayi da wayata  banason tamabya cikin tamabaya kuma nasan kinsan da haka Allah ya huci zuciyarka  bani waayrki kafin komai ya biyo baya .ya fad a yana mika mata tafin hannunsa  kyawawan yatsun hannunsa tabi da kallo k irjinta na bugawa da matsanancin k arfin gaske .


Mmn Sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
? ?? MAR'ADAMS
? ?? =ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan? 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


? ? ? ? ? Page 2


"Ajiye cup din hannunsa yayi a gefensa ya matso da fuskarsa daf da nata har suna iya shakar numfashin juna ,wani irin tsalle zukatansu yayi ."lokacin d'aya zuciyar kowannensu ya fara lugud'en bugu ,ahankali ya lumshe mata tsuma mmun idanunshi yana cewa "bani mana wani abu zan duba" ya k'arasa maganar tare da bud'e idanunshi fes akanta ."shiru maryama tayi? tana kallonsa cikin wani irin yanayi yayinda k'irjinta ke cigaba da bugawar da take "give me the phone.! ya sake bata umarni,bata san lokacin data hararashi tana mai kawar da fuskarta gefe acikin ranata tace "wannan mutumin ya cika damuwa? banda? neman magana me zai yi da wayata ."
ya kai hannunsa ya juyo da fuskarta suka sake fuskantar juna"tsorona kike ji da bazaki maganar a fili ba ?"wata harara tai masa tare da tsuke bakinta matsota yayi sosai "irin wannan baiwar da Allah yayi miki kina saurin nuna min ita a arha kamata yayi sai na dinga biya kafin a nuna min ita saboda wannan irin kallo haka mai k'arawa mai kallonki ganin kyaun fuskarki, har ma yaji sonki ya kara shiga zuciyar wanda ya kamu da ciwon sonki ."Idan kuwa daman neman shiga yake idan kika yi masa irin wannan kallon lallai sai yayi tsammanin ya samu kar'buwa ne acikin zuciyarki ."



?? Shiru tayi kamar yadda shima ayi shiru yana dubanta yana shafa sajen fuskarsa had'e da ciza lip's dinsa na k'asa yana jiran ta miko masa wayar ,baya son ya takura mata ne yasa ya bata dama ta bashi da kanta? if not da tuni ya fara lalubarta, dan ko da bai ga wayar a hannunta ba yasan tana soke a jikinta" maryama ya kamata ace a yadda kike haka babu abinda Allah ya rageki dashi kamata yayi a samu hikima da wayo da iya jan hankali tare da tattali da? biyayya ta hanyar aikata abu aloakcin da'aka umarceki batare da 'bata lokaci ko jayayya ba amman kashi da alamun banyi sa'a ba ta wannan bangaren ."
"ina ganin ya kamata ki koma makarantar da'ake koyar da wad'an nan gaba saboda ni namiji ne mai son mace mai irin wad'an nan halayen kinga idan kina son ki juya ni na zamo sakarai a gareki dole sai kin zamo mai irin wad'an nan halayen dana lissafa." yana gama magana ta sake kawar da fuskarta dan ta fara shiga wani yanayi sakamakon numfashinsa da take shaka ."


"Maryama!"
Ya sake kiran sunanta a karo na biyu sai data ji duk wani gashi dake kwance a jikinta sun mike tsaye saboda sanyayyiyar muryar da yayi amfani daita sai dai batayi gangancin kallon inda yake ba dan tasan abinda zataji sai ya nikan wanda take a yanzu ."maryama ni namiji ne mai tsananin son ayi min biyayya sannan mai son idan ya bada umarni abi umarninsa, sannan a kula dashi kamar k'aramin yaron goye dan nifa shagwa babbe ne na bugawa ajarida sai kin gaji dani wajen son jiki koda yake zuwa yanzu kinsan
wasu abubuwana ".ta d'an waigo ta kallesa ."
"yes dole ne na fad'a miki dan kiyi biyayya dan kin samu dami akala ne dan samuna ba abu ne mai sauki ba"zaune kawai maryama take a wajen tana dubansa tana tunanin abinda ya d'auke ta?.
"sakariya ya d'auketa ko me "?"eh mana ita ya d'auke ki "zuciyarta ta bata amsa da haka,bata san abinda ya kamata tayi ba dan tunda ya bukaci wayarta ta shiga cikin mummunar? tashin hankali."


Sake miko mata hannunsa yayi yana mata wannan d'an iskan kallon? nasa mai matukar firgitarwa da jefe mutun cikin tsananin fargaba da tashin hankali,batare da 'bata lokaci ba ta ciro wayar dake soke a gefen siket dinta ta mika masa tana fesar da iska , ya amsa yana shan iska tare da ciza lip's dinsa na k'asa ."shiru tayi tana kallonsa tare da jin matsanancin tashin hankali da tsoron kar sakon yan'uwansa ya shigo adaidai lokacin gani tayi yana kokarin d'aura kanshi a saman cinyarta kamar ta janye k'afafunta sai dai tunawa? da tayi a gidansa take da kuma sanin halinsa da tayi yasa ta hakura tayi zamanta a yadda take kar ta jawa kanta wata? matsalar sai dai bakinta da zuciyarta basu yi shiru akan furta kalmar "la ila a illa anta subuhanaka inni kuntu minal zalimi ba ."tana kallonsa kai tsaye what's app dinta ya shiga ya fara duba sakonnin mutane cike da fargaba ta cigaba da kallonsa dan dai ta san anan bazai ga komai ba haka ma message bazai ga komai ba dan bata barin sako a wayarta? da zarar sako ya shigo ta karanta take gogewa tashin hankalinta a yanzu shine kar sakon 'yanuwasa ya shigo ."



bata san lokacin daya d'auka yana duba wayarta ba sai dai taji yana girgizata sannan tayi saurin dawowa haiyacinta cikin tsoro taga yadda yake kallonta yace "maryama me kike tunani haka ?."
Nan fa ta soma in ina jikinta har karkarwa yayi wajen cewa "babu komai ."sake matsota yayi sosai? fuskarsa a d'aure sosai sai dai ita tunin ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta duk da tasan babu abinda ya gani a wayarta amman zuciyarta cike take fal da fargaban abinda zai biyo baya,har tsawon minti goma yana kallon face dinta sannan ya sake kira sunanta "maryama d'ago ki kalleni ido cikin ido saboda maganar da zan miki babu wasa acikinta "jin abinda ya fad'a yasa ta d'ago kanta ahankali ta tsura masa shayayyun idanunta kamar zatayi kuka dan sosai zuciyarta ke bugawa da matsanancin sauri "a'a ya naga kamar kina son kiyi kuka ?"ta sake narke fuska "karki sake kiyi min kuka anan "ya k'arasa maganar cike da gargadi ,take ta soma kokarin maida hawayen dake kwance acikin kwarnin? idanunta? ".


"Maryama waye ni agareki "?kai mai gidana ne a wajen aiki "ta bashi amsa tana sake jin fad'a uwar gaba? mai tsananin ".ban dashi fa ?kai mai sona ne ."da kyau da kika gane haka ya kamo hannu
wanta duka cikin nashi "ki saurareni sosai zanyi magana dake, ba zance wasa ko raha ko kuma tsorotaki zanyi ba amman ina son ki yarda? a zuciyarki komai ya fito daga bakina to gasky ne ."ya d'an yi shiru kad'an yana kallonta ita kuma ta kawar da fuskarta gefe dan kallonsa ba k'aramin haddasa mata jin mummunar fad'uwar gaba yake ba "amatsayina na wanda zan aureki da zuciyata d'aya ba zan ta'ba yarda na cutar dake ba saboda haka kema banason ki aureni dan cutar dani sannan karki d'auki maganata a matsayin cutar wa ko takurawa domin magana ce ta amfanin ni dake amman fa idan kina sona dan Allah ".


Tai shiru zuciyarta na wani irin bugawa da sauri sauri "kina son ki aureni dan kiyi rayuwar aure dani ta har abada ne ko kuma kina son ki aureni ne dan cima wani buri naki ?"yayi mata tambayr da batayi tsamaninta ba ,kwayar idanunshi na kanta kyam ko kiftasu bayayi yana nazarinta muryarta a sanyaye tace "bangane abinda kake nufi da maga ..."yayi mata wani kallon da yasa tayi shiru dan dole ba dan ta shirya yin hakan ba "idan har aurena zakiyi dan Allah to ina da sharid'd'ina guda uku? da zan fad'a miki aciki zaki zabi biyu wanda yayi miki "ya sake had'e fuska "ina son idan kina da wani muradi ne aurena ki janye haka ki aure ni dan Allah ko kuma ki fasa aurena gabad'aya ."zance na fasa aurenka ma bai taso ba haka ma? zance? janye muradin aurenka bai taso ba ."tayi maganar acikin ranta ."


"Na baki minti talatin kiyi tunani kafin na fad'a miki sauran duk maganar da yake fuskarsa a d'aure take "ni dai dan Allah ka cigaba da magana kawai dan hankalina ya fara tashi tayi maganar tana jin wani sabon tashin hankali na shigart "dole hankalinki ya tashi yayi maganar a cikin ranshi amman a zahiri cewa yayi "tunda na rigada na fad'a sai bayan minti talatin zan cigaba da magana sai kiyi hakuri har lokacin yayi ni yanzu yunwa nake ji abinci zanci ."ya mike tsaye ya barta nan zaune cikin jimami da zullumi mai tattare da tashin hankali da haushi? da takaici duk sun taru sun rufeta alokci d'aya taji kamar ta shakesa ko ta rufesa da duka haka kawai tana zaman zamanta zai sake jefata cikin wani tashin hankali ."su kam wasu irin family's ne haka masu mugun hali ?"to kodai an halicci zuriarsu ne dan su jefa mutun cikin damuwa ?"daga shi har 'yan'uwansa da mahaifiyarsa duk halinsu d'aya mugaye ne masu muguwar zuciya."



har ya zauna akan tebirin cin abinci ya juyo ya kalleta bayan ya zauna "Kayan abincin da kika sa a bayan mota nawa ne ko kuwa ?"ta d'auke kanta gefe batare data bashi amsa ba ai yasan nashi ne sarai da zai mata wata irin tambaya ,sosai? kwalla ta cika idanunta" ita kam gara duk su taru su kasheta ta huta da? wannan duniyar dan sam ba Jin dadin zama acikin duniyr take ba bata an kara ba sai dai kawai ta ganshi a gabanta lokacin har kwallar idanunta sun zubo "yanzu me ye abun kuka "?shiru tayi kawai tana shesheka ya kai hannunsa zai? share mata hawaye ta kawar da fuskarta gefe alamun bata so "ki fahimceni ban kawo ki gidan nan dan na sakaki kuka ba ".
"Amman me ya kawo wad'an nan maganganun?"
"ai kasan? dole maganar tasani kuka , ban San dalili da yasa baka son ganina cikin farinciki ".
"ni din ?!ta gyad'a masa kai alamun "eh!"tana harararsa "okay zamuyi mgana amamn kiyi min lamani inci abinci tun asuba dana yi training na sha ruwan zafi ban ci komai ba har yanzu kiyi min hakuri in samu na saka wani abu acikina sai mu cigaba da magana."


Bata ce masa? komai ba illa? ta juyo ta? kalli agaogon bangon parlour'n karfe tara saura minti shadaya "karki damu zamu gama komai zuwa karfe goma kilama ba zamu Kai ba,still dai shiru tayi masa dan ita tsoronsa ma take ji "me yasa zai bincika mata wayarta?" sannan me ya kawo batun? idan tasan dan wani muradi ne zata auresa ta janye, ta aure sa? dan Allah ko kuma ta fasa aurensa gabad'aya duk me ya kawo wad'an nan maganganun ?"idan dai abincin da kika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login