Showing 27001 words to 30000 words out of 151781 words

Chapter 10 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2646

kika sake fad'a min haka sai na tsine miki
"Dan ku fa nake wannna wahalar ko da yake ba laifinki ba aikin dake jikinki ne yake son lalacewa shine kike son ki dawo gidan jiya amman zanyi magani ki "karki sake d'aure min yara "inji cewar baba gali ,aunty salma ta d'auke idanunta akna sakina ta maida kanshi "eh haka na fad'a duk kin birkita min tunanin yara da shegen biye biyen malamanki na banza da wofi "aunty salma bata sake cewa komai ta shiga d'aki ta zari mayafi ta bar gidan ."


?? Adamcy dake? zaune a parlour'nsa bayan ya gama waya da umma shiru yayi ,wani irin sanyin dadi ke ratsa ilahirin jikinsa,yanzu hankalinsa ya kanta maryam ba zata dawo rayuwarsa ba ga maryamarsa zai mallaka ,tsadadden murmushin nan nasa? ya bayyana akan fuskarsa yana cewa "maryama kin kusa zama tawa ta har abada Allah yasa karki min rowar kanki dan ina tsananin bukatar ki "ya fad'a a fili yana kamo lip's dinsa na k'asa yana cizawa ahankali yana jin nishad'i mara misaltuwa wayarsa dake ajiye a gefensa ta fara ringing ya d'an waigo a natse yana kallon screen din wayar sunan wanda ya gani yasa ya d'aga yana "cewa "hello baba!".daga can bangaren baba babban yace "adam ya kake ?"Alhamdulillah baba barka da yamma ?"barka d'an mamansa ".
wani murmushi ya bayyana? akan fuskarsa sakamakon jin abinda baba babba ya fad'a "
Naji dadi kwarai daka natsu ka shawo hankalin mahaifiyarka akan maganar aurenka ,ya kamata zuwa yanzu ka canza rayuwar da kakeyi. rayuwar da zakayi yanzu ta samu canji kabi mahaifiyarka ku rabu lafiya domin daga lokacin dakayi rakiya aka binneta daga wannan lokacin rayuwarka ta baya? data yanzu ta samu canjin zahiri bazan? boye maka ba daga wannan lokacin zaka shiga sabuwar rayuwar? zaka zamo baka da karfi komai ."


"Kuma komai zai iya faruwa da Kai bare Kai da kake tsananin son mahaifiyarka karka d'auka wasa duk wanda ya rasa mahaifiya to fa ya zama abun tausayi ,domin kuwa ya rasa halittar da take son taga rayuwarsa ta samu cigaba kuma ya rasa wacce zata dinga masa adduoin nasara a duk inda take a zaune ko kwance cikin sallah akoda yaushe,dan haka ina shawartarka kabi? mahaifi yarka sosai kayi mata duk abinda kasan zatai farinciki Ina maka fatan alkhairi arayuwarka ".
"na gode sosai baba in sha allahu zan cigaba akan yadda nake mata ."masha Allah daman Ina son naji a wani estate ko wani guri zamu had'u da iyayen yarinyar dan na kira Zulai tace bata sani ba shine nace bari na kiraka naji dan mu san yadda zamu tsara tafiyar a jibi "?shiru yayi yana tunanin mai zai ce masa Allah yasani shiyasa yaso tuntuni su maryama sun tare a gidan daya basu ba dan komai sai dan samun wata daraja da kima a idanun yanuwansa amman dai zaije suyi magana da umma gobe "adam kana kan layi kuwa ?"numfashi ya sauke ahankali sannan ya soma masa magana a natse "ka bani zuwa gobe zanyi magana da iyayen yarinyar naji a ina zaku had'u baba babba yace "to shikenan Allah ya kai mu goben Allah kuma yasa albarka bari na kira babanka prof lawan ayi tafiyar dashi ko hakan bai yi ba ?"yayi sosai na gode Allah yasa yana k'asar dan gaskiya na kwana biyu rabona dashi ko a waya "ai kuwa yana nan dan mun had'u dashi a bikin diyar senater shehu mr ata yace "okay !"sannan sukai sallama ."


Bayan sunyi sallama da baba babba mikewa tsaye?? yayi? ya shige? bedroom Winshi yana mai manna wayarsa a kunnensa da wani kira ya sake shigowa? ? daga yanda yake magana a wayar zaka fahimci yana cikin farinciki inda yake fad'a ma mb batun aurensa, mb yaji dadi sosai har yace zai zo a tsara yadda bikin zai kasance "."aa mb abar batun biki nan tukun? tunda kaga sweetheart ba wai tana son auren nan bane akan bikin nan komai zai iya faruwa ni dai babban burina maryama ta shigo lafiya."hakan ma yayi amman gasky zamuyi biki daga baya "babban biki a wajena mb maryama ta shigo hannuna ,mallakarta da zanyi amatsayin matar aurena wallahi ya fiyye min duk wani biki da zaayi kasan ni ba wai Ina son hayani bane ".
mb ya kwashe da wata dariya yana cewa? "gsky abokina ka mugun kamuwa da son yarinyar nan "yarinya duk ta susuta maka lissafi haka? Allah yasa ta canza mana kai gabad'aya mu sarara da iskancinka " yayi shiru kawai yana sauraronsa yana tunanin tare da lumshe idanunshi "?anya kuwa maryama zata iya canzasa gabad'aya?"


"yauwa abokina daman Ina son na maka wata magana dan nasan kai kad'ai ne zaka fad'a aji kuma ayi aiki dashi "mb yayi maganar yana sauke naunauyen numfashi "Ina jinka!"mr ata
ya fad'a ba tare daya bud'e idanunshi ba "daman akan maryam ne ."wani dogon tsaki yaja yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa "ka tsaya kaji me zance ."? "ban san me yasa wani lokacin kake kasa gane bana son ko jin sunanta "amman kuma ai gashi zaka auri mai sunanta ?" "ina daf da canza mata suna bari dai ta shigo hannuna mb yayi murmushi kana ya cigaba da magana "adamcy rigimar duniya "ita sukuwa ce da zata bari ka canza mata suna bayan sunanta mai ma'ana ne ?"kai ma kasani babu macen da zan ajiye a karkashina taki bin dokata da abinda nake so ."let me go to my point ,maryam ke d'aura khaira a shafukan sada zumunta na TikTok da instagram ,a gasky abun bai min dadi ba dan saboda komai ba ,sai saboda bakin mutune ,azahirin gsky banso na fad'a maka ba duk da nasan babu abinda fad'a maka din zai yi saboda rashin damuwar da kake nunawa akan yarinyar ,amman dai at least ya kamata ka duba lamarin khaira ko a yaya aka sameta diyarka wacce bayan ranka zata gajeka kuma baka sani ba ko ita kad'ai ce diyarka a duniya ."


adamcy ya ta'be bakinsa yana jin wani iri ajikinsa kafin ahankali ya bud'e tsumammun idanunshi yana kallon saitin shigowa bedroom dinsa yace "wannan ai maganarku ce zaka iya mata mgana ba sai kun sakoni ciki ba " "ai nayi mata magana taki ji ne dana ce ma zan fad'a maka babu kunya maryam tace na fad'a maka ita yanzu ta rigada ta? kuna ta zama guguwa babu mai tsaidaita tayi matukar bani mamaki dan sam banyi tunanin haka daga gareta ba "dan Allah adamcy kayi hakuri kasa baki cikin al'amarin yarinyar za'a duba tayi kamara kuma abinda zai baka haushi da takaici wakar da take d'aurawa da yarinayr wai ga yar da ba'a so ta girma ,ga yar da ba'a so tai karfi,yo su barta ko dan Allah. har mb ya kai karshe maganarsa? adamcy na zaune yana sauraronsa sai daya dasa aya sannan yace "okay haka ta fad'a?"ai daman ku kuke d'aure mata gindi har kuke mata kallon macen kirki amman ni tun tin tin nasan bata da mutunci amman tunda tace ita guguwa ce ni zan nuna mata ni teku ne kuma mai wanke duk wata kurar guguwar data taso dan ubanta zan nuna mata bata isa ba,yar ma idan naga dama sai na kwace? gabad'aya naga ta karyar iskanci ".


"no karka rabata da 'yarta ka dai yi magana nasan za'aji maganarka zaka iya kiran mahaifinta yayi mata magana ".kenan ma kana nufin a lalla'bata ?mb yayi shiru dan ya rasa me zai ce "idan dai haka ne ..."kaga bari kawai ma zan kira babanta muyi magana dashi "mb ya katse mr ata ta hanyar fad'ar haka "wannan kuma ya rage naku idan na tashi nawa kai kasan me zan iya yi."yana gama maganarsa yayi hanging call din yana shafa goshinsa karo na farko da yaji wani abu mai kama da damuwa akan khaira,lallai jini ba karya ba ahankali ya dinga juya maganar mb acikin kwakwaluwarsa ita yanzu ta rigada ta kuna ta zama guguwa babu mai tsaidaita ya jima zaune yana tunanin abunyi ba wai bazai iya taka mata burki ba ko d'aukar mataki akanta ba aa zatayi tunanin ko ya fara damuwa da khaira ne idan hakan ta faru kuwa zatayi tunanin wani abu akanshi wanda shi?? bazai so? faruwar hakan? ba ?"ai dole adamcy wata rana zaka damu da khaira dan ko yanzu kaji damuwa aranka har aka kira sallar magrib yana zaune yana tunanin khaira ,ahankali ya ajiye wayar a gefan gado ya mike ya shiga bathroom ya d'auro alwala ya fito ya sauya kaya zuwa Jallabiya fara sol ya feshe ilahirin jikinsa da turare sannan ya nufi kofar fita zuwa kasa inda ya iske mami tsaye da alamun itama shirin shiga sallah take? yayi mata? sallama zashi massalaci ,fuskarta babu yabo babu fallasa tace "a dawo lafiya!".


yasa kai ya nufi kofar fita yana takun nan nasa mai matuqar d'aukar hankali kamar baya son taka kasa bayansa tabi da kallo gabad'aya sai taga yanayinsa ya canza daga adamcyn data sani zuwa wani dabam ,bai dawo gidan ba sai da yayi sallah isha'i lokacin daya dawo bai isketa a parlour'n ba tana d'akinta a can ya isketa? yace mata ya dawo tace "sannu da dawowa" taja bakinta tayi shiru kusan minti shabiyar yana zaune ba tayi magana ba bare ma ta kalli inda yake ganin tayi masa shiru ya mike ya fito ya nufi samansa har kusan karfe goma adamcy bai ga alamun za'a kawo masa abinci ba ,dan ya tabbatar da za'a bashi ko baza'a bashi ba ya kirata tana d'aga kiran tace "uhm !"yayi shiru yana juya kalmar uhm din da tace "uhm ina jinka?"ta sake maimaitawa runtse idanunshi yayi sannan yace "sweetheart abinci ?"muryarta a dake tace "babu!"shi abincin ne babu !?ya furta ahankali sai dai direct kalmar ta shiga cikin? kunneta kafin ya sake cewa wani abu ta katse kiran ,shiru yayi zaune rike da waya yana juya wayar yana mamakin canji daya kara samu daga mahaifiyar dake tsananin son shi yasan duk ya samu sauyin ne akan maryama yasan da zai ce mata ya fasa auren maryama zata ji dadi sosai har ma ta sauko daga dokin fushin data hau sai dai ina bazai iya ba dan ba abu ne mai sauki agaresa ya iya hakura daita ba? yana mutuwar son maryama soyayyarta kullum sake karuwa take acikin zuciyarsa ."


"wallahil azim da zai iya rabuwa da maryama da zai hanzarta barinta kodan sweetheart dinsa ta samu sukuni da natsuwa amman son maryama ajininsa yake ya zame masa jarabawa arayuwar sa, idan ma yayi ganganci barinta yasan yayi gan ganci da rayuwarsa ne ,bare a yanzu da kullum abun karuwa yake har ma ya had'e masa da tsananin sha'awarta ."waje ya samu akan dogu war kujera ya mike tare da d'aura hannunsa d'aya a saman ruwan cikinsa d'ayan hannun kuwa ya dafe goshinsa dashi ya runtse idanunshi ahankali fuskar maryama ta soma masa gezo wai gata tsaye a gabansa bai tsaya wata wata ba ya kai hannunsa ya fixgota ta fad'o? jikinsa ya rungu meta tsam tsam yana sauke ajiyar zuciya duk da ba a zahiri yake jinta ajikinsa ba sai daya ji jijiyarsa ta harba da sauri, a natse yayi kasa da hannunsa ya dafe daidai inda? jijiyarsa ke kwance tana? wani irin harbawa da sauri sauri ji yayi wai ta sake lafewa ajikinsa ,ya sake rikota sosai yana shinshin wuyanta yana kokarin kamo bakinta da wannan imagination din bacci yayi awon gaba dashi a parlour'n."

******

Washegari tunda ya tashi yayi sallar asuba ya koma bacci bai tashi ba sai around to 12:00 Kai tsaye bayi ya fad'a ya jima yana cud'a? jikinsa da sabulu sannan yayi alwala dan har an fara kiran sallar azahar ya fito d'aure da dogon farin towel a ?ugunsa,ruwan dake Wigowa ta cikin sumar kansa ya fara gogewa bayan ya gama ya shafa lotion ajikinsa ya shirya cikin wani had'a den yadi dark blue mai matukar kyau da taushi a gaban rigar an rubuta "TAT"kamar sauran manyan kayansa ."
kayan ya matseefar kar'bar jikinsa ya d'aura hula a kansa hular daya saka ma ta matukar taimaka wa wajen fito da aihinin kyawunsa ya Wau tsadadden links ya saka a bakin hannun rigar sanyayyen turarensa red me sanyin ?amshi ya feshe jikinsa dashi? ya sanya? takalmi? sannan ya kwashi wayoyinsa ya fito bai iske mami a parlour kasa ba dan haka ya nufi d'akinta inda anan ya isketa zaune akan daddumar sallah tana jan casbaha da alamun sallah ta idar ya k'arasa har inda take zaune ya durkusa a gabanta ya kamo hannunta cikin nashi ya sumbata kamar yadda ya saba sannan ya gaisheta "sweetheart kin tashi lafiya ?"ya tambayeta yana kallonta cike da tsananin kulawa."


muryarta a sanyaye tace "Alhamdulillah na tashi lafiya ya kai ma ka? tashi ?"ya karyar da kanshi gefe alamun lafiya sannan yayi shiru yana kallon yanayinta kwata kwata yanayinta ya nuna masa? bata cikin farinciki da walwala ahankali yace "ina mai k'ara neman afuwarki sweetheart kiyi hakuri ki yafe min ki manta komai "numfashi ta sauke da kyar tace "komai ya wuce". yayi kissing din saman hannunta yana mai sake karewa yanayinta kallon sannan yace "na gode sosai sweetheart thank you for suppointing my marriage Allah ya kara miki lafiya da tsawon rai mai albarka ." "kallonsa tayi na second biyu kafin Ahankali? tace "ameen "!yace zanje nayi sallah daga nan zan fita sai dai? zan d'an jima kafin na dawo "a dawo lafiya !" ta fad'a ataikaice fuskarta a d'aure babu annuri bare ta tambayesa inda zashi da kuma abincin da zai bukata idan ya dawo da alamun ma yau haka zata barshi ya kwana da yunwa numfashi ya sauke sannan ya fito zuwa haraban gidansu ya soma taku zuwa massalaci dake cikin estate dinsu bayan ya idar da sallah kai tsaye ATA company direbansa da masu tsaronsa suka? nufa dashi bisa umarninsa ."


Tun daga haraban ma'aikata yake samun? gaisuwar? mutane, wasu ya amsa wasu kuma ya d'aga hannu ,wasu kuma ya share a haka har ya kusan karasowa? inda sagir pA dinsa? yake? zaune yana ganinsa ya? mike tsaye da sauri yana cewa? "good morning sir !?morning !"ya amsa atakaice ya shige? office dinsa ya zauna yana kallon makeken table din gabansa kusan minti goma yana zaune sannan sagir yayi knocking tare da Neman izini shigo "may I coming sir ?"bayan kamar minti biyar? yace "coming !"ya bashi izini ya shigo ,a natse sagir ya shiga? ya tsaya a gabansa cike da girmamawa yana sake gaishesa mr ata bai d'ago ba ,bayan kamar minti goma sagir yace " sir "!mr ata ya d'ago ya kallesa? a d'age? alokcin da yake kokarin ajiye wani file a gabansa "sir ana bukatar saka hannuka anan."
ya fad'a yana nuna masa inda zai saka hannu "mr? ata bai ce komai ba ya d'auki biro yayi masa singn da zanen fuskarsa cike da girmamawa ya d'auki file din yana cewa"sir akwai wasu mutane da suke son ganawa da kai kusan kwana uku kenan suna zuwa basa samun ganinka "me yasa baka bari nasan da zaman haka ba tun kafin yau ?"im sorry sir naga kwanakin nan ne baka samun zama amman dai yanzu haka suna kasa? ".
shiru yayi na wasu mintuna har sagir ya fidda rai da zai yi magana dan har yana kokarin juyawa yaji sautin muryarsa a kasan makoshi "kace masu su dawo gobe dan yau banzo da shirin ganinsu ba akwai wanda zan gani ."okay sir ya juya da sauri ya fita kmr zai tuntsura."


? Karfe biyar na yammacin ranar a gidansu maryama tayi masa yana zaune a parlour tare da umma wacce farincikinta ya kasa boyuwa Allah ya sani tana tsananin kaunarsa ko d'an cikinta sai haka bata sani ba ko dan ta fahimci maryamarta na son shi ne? bayan sun gaisa daita ya soma da tambayar maryama umma tace bata nan yayi shiru sai dai acikin ransa ya fara fad'a yau ma kamar jiya fita tayi to Ina take zuwa haka ?"wato ma zata iya fita yawonta zuwa Office ne bazata yi? ba bare ya samu ya dinga ganinta akan time ?"kamar umma tasan abinda yake cin ransa tace "bata dade da fita ba taje nan bayan layinmu ne akwai wata yar makarantar islamiyarsu da zatai aure acikin? satin nan dake tana cikin kawaye ai naso tun jiya na hanata kanwance duk da dai? ba wai tana ra'ayin yi? bane? ita firdausi ce ta matsa mata da magiya amman bazata wani? jima ba zata dawo ko a kirata ne ? ."a natse yace "a'a ki barta kawai ya fad'a tare da yin shiru umma ta mike domin kawo masa abun sha bata wani jima ba ta dawo? hannunta rike da karamin tray dake d'auke da? cincin da drinks, ta aje mashi akan table din gabansa tace "adamu ga cincin kaci ni nayi da kaina yayi d'an yi murmushi kana yace "na gode umma !"bayan second biyu yayi gyaran murya sannan ya soma magana "umma naso ace kun tare a gidanku kafin zuwan wannan lokacin dasu baba zasu zo amman ban sani? ko kuna da? dalilin ku na rashin son tarewa? ba ko kuma maryama ce ke? hanaku ?".


umma tayi murmushi irin nasu na manya tace "sam ba maryama bace munyi magana da auntynta itace dai tace abari har ayi auren tukun shiyasa kaji mun yi maka shiru amman ba wani abu bane. numfashi ya sauke da kyar shi dai gasky ya so ace sun tare amman bashi da yadda zai yi dasu kar ya matsa su d'auka ko yana kyamkyaminsu ne ko kuma ya raina muhallinsu ne ,muryarsa a sanyaye yace "shikenan umma Allah ya nuna mana lokacin sai magana ta gaba wacce kusan itace musababin zuwana "umma tace ina sauraronka ya d'an ciza lip's dinsa na kasa yace "mahifiyata tace maryama a gidanta zata zauna amman nasan zaman na wani lokaci ne in sha allahu"
umma tayi shiru tana sauraronsa domin gasky abun bai mata dadi ba zaman maryama tare da mahaifiyarsa kasancewar bata sonta amman babu yadda suka iya shi shaani aure sai anyi hakuri kuma ahankali komai zai wuce bare tasan hali maryama bada mutun ba ko? da aljanu ne zata iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login