Showing 138001 words to 141000 words out of 151781 words

Chapter 47 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2658

koma parlour'n ki d'an zauna kad'an tun safe kike kwance tace"to !ta soma taku ahankali ta nufi hanyar parlour'n inda tafisu ta biyota da plet din abinci da roban ruwa ta ajiye mata akan k'aramin table ta jawo mata gabanta maryama tace "sannu da kokarin na gode inda ta soma yafitar abincin tana kai wa bakinta ."bayan ta gama cin iya wanda zata iya ta mike ta kwanta akan kujera tafisu ta mike daga zaunen da take ta d'auke plet ta fita dashi tana kwance ta soma jiyo hayaniya sama sama daga kasa tai shiru tana son ta saurara sai dai bata Jin komai sai hayaniya ."Daga can kasa ya'yan mami ne suke musayar yawu a tsakaninsu kuma duk akan maryama inda aunty khadija tace lallai sai an cire cikin jikin maryama anyi mata planning idan ma ta Kama acire mata mahaifar za'a yi amamn daga zuwanta bazata haihu ba . kuma duk sauran sun yarda kuma sun amince sai zabiba ce tace "la ku cirenei babu ni cikin wannan domin ni macece kuma Ina ji zafi da radadin abinda kuke wa yarinyar nan kuma ko mami bazata zuba maku ido ku aikata wannna aika aika a gidanta ba "

"ita mamin ce ta fad'a miki haka ko kuma kunyi haka daita "?zabiba tai shiru "to bari kiji itama mami zata goyin bayan acire mata wannan cikin ,to ma yanzu ke ina ruwanki tunda kince babu hannunki aje a haka daman mun dade da sanin kece munafukarmu duk abinda ke faruwa kece munafukar dake kwashe komai kina fad'a masa .""wai aunty khadija meye haka kukeyi ne say kace a zamanin jahiliya?zabiba ta fad'a afusace ta fito zuwa babban parlour'n mami inda aunty khadija da aunty shahida suka biyota nan fa abun ya jawo hayaniya a tsakaninsu suka fara misayar magana"wannan wani irin watsewa ne haka? zabiba ta fad'a cikin tsananin fushi "idan tausayin danuwnku bai sa Kun saurarawa yarinyar nan ba ya dace kuji kunyar cewar ku iyaye ne kuma ya kamata kuji tsoron Allah, sannan Ku tuna cewar yana sama yana kallonku,wani irin rudun duniya ne ya ke kwasarku haka?shin bakwa jin tsoron ranar da rayukanku zasu bar gangar jikin ku ne?yanzu idan mutuwa tazo ta daukeku acikin wannna halin fa me zaku fad'awa ubangiji ?ta Jera musu wannan ambayoyin tana sauke numfashi da kyar tamkar wadda ke dauke da ciwon Asthma ."wani kallon galala aunty khadija ke jifanta dashi wanda yafi kama da na rainin hankali sannan ta gyara tsayu warta tana zabga mata harara "ni dai wallahil azim babu ruwana kuma wallahi duk wacce tayi yun kurin cutar da yarinyar nan zan fad'a wa yaya ."tana gama fad'ar haka ta juya ta sak? komawa bangaren mami suka biyota da sauri "ai ko baki ce zaki fad'a masa mun san zaki fad'a amman wallahi muddin maganar ta fito zaki ga tsiya dan sai kinyi danasani domin bazaki fita ciki ba yadda muke yi komai dake haka ko kina cikin wannan ko bakya ciki kamar kina ciki ne inji cewar aunty shahida zabiba bata sake furta komai ba ta d'auki Jakarta ta fito fuuuuu ta bar gida ."ahankali tafisu ta shigo parlour'n bakinta d'auke da sallama maryama ta yunkura ta zauna still jikinta na rawa alamar tana jin sanyi sosai tace tafisu  meke faruwa ne a gidan nan yau naji hayaniya tayi yawa ?"tace yaran hajiya mami ne bansan abinda ya had'asu ba sai dai da alamun abu ne mai girma sai dai muce Allah ya kyauta maryama tace "ameen ta koma ta kwanta tana tunnain aranta ."



washegari Karfe biyar daidai na yammacin ranar adamcy ya dawo sai dai tun kafin ya biyo jirgi yake kiranta bata daga ba aiko yaji hankalinsa ya tashi yana shiga d'akin ya isketa kwance akan gado tana sharar bacci yayinda tafisu take zaune a gefenta da girmamawa ta mike tsaye tana masa sannu da zuwa bai kalli inda take ba ya k'arasa ya hau gadon tafisu na ganin haka tayi waje da sauri ,ya janyota jikinsa gabadaya ya rungumeta tare da matseta ajikinsa ahankali ta bud'e idanunta tajita ajikinsa wani irin yanayi taji ajikinta."gabadaya tsigar jikinta suka mike numfashinta sai daya nemi ya dauke saboda rungumar da yayi mata, tasa hannu ta toshe hancinta da bakinta saboda sabon kamshin turaren daya kai wa hancinta ziyara "i really miss you dadina "kokarin zame jikinta take daga nashi yayinda shi kuma yaki sakinta ya sake mata wani kyakkyawan riko cikin dauke war numfashi tace "dan Allah kayi hakuri ka rabu dani haka kasan bani da lafiya fa tayi mgnr kmr zatayi kuka sake matseta yayi nan fa ta soma yunkurin amai ajikinsa kafin kace me ta fara kwara masa amai ajiki bai katseta ba har sai data gama ya Wauketa cak zuwa bayi ya taimaka mata ta wanke jikinta ya dawo daita daki yana kallonta ".
" wai har yanzu jikin ne?"kai kawai ta gyada masa alamun "eh !amman shine baki fada min ba bari na kira doctor ta duba min ke ta kalleshi a kaikace sannan tace "barni kawai zan ji sauki amman kamar ka canza turaren da kake amfani dashi ? "yayi shiru yana nazarinta yana tunani tabbas yayi amfani da wani turare dabam da wani abikinsa abraham yace masa yana da kyau "shine ya sakaki amai?ta gyad'a masa kai alamun "eh !"ya cigaba da kallonta tare da miko mata hannu nsa ta girgiza masa kai alamu bazatazo ba d'an bud'e idanunshi yayi tare da fixgo hannunta ta dawo jikinsa"kiyi hakuri ban san turaren zai cutar min dake ba da banyi amfani dashi ba bazan sake amfani da turaren ba hakan yayi miki shiru tayi bata ce masa komai ba ta cigaba da kwanciya ajikinsa tana sauke numfashi."


"ni masoyinki ne na gaskiya, ina da yak'inin nafi kowa sanki maryama bazan so nayi abinda zai cutar dake ba I m sorry "to ni me kaji nace da kake ta faman bani hakuri ko nace kayi min laifi ne ?" tai mgn kamar zata sakar masa kuka suna makale da juna sai can yamma ya riko tafin hannunta cikin nashi ya tsarke yace suje kasa ta d'an mike jikinta bata masa mutsu ba suka sauko zuwa kasa ya zaunar daita akan kujera yasa masu aiki suka kawo mata Kayan fruit iya wanda mai ciki zata iya ci da kanshi ya dinga bata cikin haka Maryam ta fito daga bangaren mami cak ta tsaya tare da zuba masu ido tana kallonsa duk ya wani dawo tamkar bawa agaban maryama ."nan take idanunta suka cika da ruwan hawaye wani dogon ajiyar zuciya ta dinga saki har ana iya ganin yadda jijiyon makogoronta suke mikewa saboda tsananin zafi da zuciyarta take hankalinta bai tashi ba sai data ga ya kwantar daita a saman cinyarsa yana shafa cikinta cikin tsananin kad'uwa jikinta ya Kama rawa shi kuwa adamcy da bai ma san da zamanta da rayuwarta acikin gidan ba."sak? kwantar da kai da murya yayi sosai luf luf dashi yana fad'a wa maryama kalamai masu sanyi da kwantar da hankalin" Ina sanki fiye da son da nake wa kaina ,kece burin zuciya ta ki kalli cikin idanuna babu abinda zaki gani face tarin soyayyarki dake neman illatani, yadda kika bani jan ragamar rayuwarki a tafin hannuna ni kuma nayi miki alk'awarin bazaki tab'a yin nadamar yin rayuwa dani ba, ya k'arasa maganar yana had'e tazarar datai saura atsakaninsu cikin salon d'aukar hankali ya lumshe idanunshi da goga kumatunshi a saman fuskarta muryarshi can k'asan makoshi wanda sai kayi da gaske sannna zaka iya fahimtar abinda yake fad'a"an halicci ruhina da soyayyar ki maryama a kullum burina mu mutu tare bana son na barki wani ya aureki kuma banason rabuwa dake ."hawayen dake gangarowa a saman kuncinta yasa harshenshi yana d'auke mata su,ahankali ta lumshe idanuwanta hawayen na sake gangaro wa, ta sallama mishi kanta tasan bata da zab'i bata da wani abunyi daya wuce ta mika masa rayuwarta gabad'a ya kuma ta rigada tayi haka amamn tana jin tausayinsa soyayyar da yake mata tayi yawa kuma ko tace ya rage haushinta yake ji tana jin yadda yake sake shigewa jikinta yana manne mata, cikin salo ya had'e bakinsu ya soma sucking din lips d'inta while yana tura mata harshenshi cikin bakinta ai da sauri maryam ta juya ta koma tana haki zuciyarta na wani irin mugun bugawa da karfin gaske "



wani irin deep kiss adamcy yake yi mata mai rikita kwakwalwa da hargitsa lissafi ya manta da inda suke dayake a hannu yake cikin k'ank'anin lokaci ya rikice ya birkice ya d'imauce,ya soma fitar da nisha akai-akai kamar wanda yayi gasar tseren gudu, tana jin yadda yake wasa da sassan jikinta amma babu yadda zatayi,jin zai zame rigar jikinta domin ya kai hannu saman boobs d'inta a fili ta fitar da wahalallan numfashi tace "ka bari mana ko ka manta inda muke ne ?"bai tsaya ya sake jin mai zata sake cewa ba ,cak ya d'auke ta yayi sama daita tun daga parlour'n ya soma rabata da kayan jikinta daga ita sai pant ya hau saman bed da ita, sosai yake romancing d'inta a gaggauce, saboda yadda ya k'agu bai tsaya yin long romance ba, ya jefa kwallosa a raga, sakaka ta sakar mishi jikinta aiko yayi yadda yake so daita sosai ta bashi had'in kai kusan a tare suka yi releasing, ya kwanta saman ruwan cikinta yana mayar da numfashi yana kissing sansar jikinta ita kam ta soma zuba masa raki bayanta ciwo mararta ciwo ya tsaya yana kallonta yana murmushi "okay bayan kin gama Jin dadin zaki fara complain?allah da gaske nake Jin abinda ta fad'a ya sauka akanta ya soma massaging din jikinta ."

*******

Bayan wata uku da sati d'aya wanda cikin maryama yake da daidai wannan kwanaki dan zuwa watan gaba za'a fara mata awo duk wani gata da Kuluwa adamcy yana bata kuma babu ruwansa ko a gaban waye haka zai makaleta yana bata kulawa wanda kusan ita take janye jikinta idan taga idanun mami amman idan a gaban maryam ne ko yan'uwansa sakar masa jiki take yayi yadda yake so daita babu abinda zata ce wa Allah sai godiya daya mata arziki da samun miji kamarsa mutumin daya kasance miskili amman yanzu akanta bakinsa ya d'an bud'e kullum kalmarsa dadina Ina sonki maryama Ina sonki me kike son nayi miki shiyasa kyautatawarta bazata gushe ba agaresa daga shi har mahaifiyarsa haka ma yan' uwansa a yanzu tana barinsu dan sbd darajarsa sai dai kullum tunaninta yaushe ne zasu bar gidan saboda kalu balin da take fuskanta daga yan'uwansa dan a yanzu ma zaune take tana shafa kuncinta inda tasha mari daga aunty khadija kan abinda bai kai ya kawo ba kawai dan ta d'auki khaira ."tana zaune shiru dafe da kuncinta ya karaso ya tsaya kusa daita sai dai bata san da dawowarsa ba bare shigowarsa d'akin ahankali ya zauna kusa daita ya janyota jikinsa wanda yayi sanadiyyar data dawo haiyacinta ta sauke wani wahalallen numfashi tana dubansa "sannu da zuwa yaushe ka dawo ?"kayi hakuri ban san ka shigo ba bari naje na kawo mata lemu ko ruwa ka sha ta fad'a zata mike ya dawo daita jikinsa ya tsura mata idanunshi yana kallonta kafin ahankali ya motsa bakinsa "menene yake damunki ne na dade tsaye acikin d'akin nan kina tunani tai shiru tana sak? zurfafa tunaninta tana Shafa kuncinta "fad'a min me ya faru ne "uhm babu komai ta fad'a tana karyar da kai kallon natsuwa yayi mata ."Amman ya naga kamar kuncinki yayi ja ?" nace maka babu komai d'azu ne na zame a bayi na buge kaina bayan shi babu wani abu da yake damuna bugewar dai da nayi ce ta k'arasa maganr tana yatsuna fuska "akwai alamu bakya fad'ar gasky ya d'auki wayarsa yana daddanawa ita kuma ta had'e hannuwanta waje d'aya ta dafe ha'barta dashi jin shirunsa yayi yawa ta cire hannunta ta d'an leko cikin wayarsa "sarkin bincike bincike me kake binciko wa?.

yace "nothing !ya fad'a yana d'auke fuskar wayar tace da gaske yace "uhm yana cigaba da ganin duk abinda ya faru a gidan bacin ransa ya niku sai dai bai nuna a fuskarsa ba yayi kokarin ya danne damuwarsa yace mata suje kasa da kyar ta yunkura suka fita inda suka iske gabad'aya yaran mami zaune ban da mutun d'aya zabiba wacce kusan ta rage zuwa gidan yanzu tare suka zauna akan kujera d'aya maryama na kokarin gaishe da mami amman kiri kiri ta d'auke kanta"can kasan makoshinsa yace tashi ki d'auko min khaira ".a d'an rikice ta kallesa gabanta na fad'a uwa da matsanancin karfin gaske "ko baki ji abinda na sakaki bane?"tace uhm amm sai kuma tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta ya d'ago fuskar nan tashi a had'e tamkar an aiko masa da sakon mutuwa da sauri ta mike ta fara taku ahankali tamkar kazar da Kwai ya fashewa aciki cike da sanyi jiki ta k'arasa inda khaira take rarrafenta ta duka ahankali zata d'auketa taji sautin murya biyu ajere "karki sake ki d'aukar min ya !"aiko cak maryama ta tsaya tare da zuba masa idanu tana kallonsa jikinta na rawa shima suna gama rufe baki ya zabura ya mike tsaye yana nuna su da yatsansa."yarki ko tawa!"ya fuskanci maryam yana zaro mata ido dan bashi da lokacin aunty khadija nan take abu biyu ya had'e wa maryam waje d'aya tashin hankalin ganin yanayinsa da kuma farinciki ya furta kalmar 'ya ga khaira daga mami har aunty khadija da maryam da nana hauwa'u zuba masa idanu sukai suna kallonsa irin mugun kallon da yake ma maryam ta fahimci amsarta yake bukata dan har lokacin idanunsa na kanta."


muryarta a tsarke tace"yarka ce "!okay tunda har an yarda cewar 'yata ce good ya kalli maryama dake tsaye jikinta na cigaba da bari yace "kina son khaira zaki riketa !"bata da zabin daya wuce ta amincewa hakan , dan haka ta gyda masa kai alamun zata rike "good daga yau ta bar hannun wannan har abada ta dawo hannunki dan haka ki d'auketa na baki ita kyauta kiyi duk yadda kike so daita "ai Maryam na gama Jin haka ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali "ma..mami ki taimakeni ya kyautar min da yarinya bayan duk wahalar dana sha tun kafin haihuwarta har zuwa ranar dana haifeta mami karki bari ya kyautar min da khaira "wannna maganr tasa jikin maryama yayi sanyi dan tayi imani rainon ciki kawai akwai wahala bare haihuwa tana kallonta tana kuka tana rokon mami tasa baki cikin maganar aunty khadija tace "dan Allah kiyi shiru hauka yake a ina ya ta'ba ganin an kyautar da mutun khaira yarki ce idan kuma har ya tabbatar haka walalhi sai munyi sharia dashi mara mutunci kawai da bai san ciwon Kansa ba "kece mara mutunci da bata san ciwon kanta ba ya fad'a yana kallon inda mami take zaune cike da mamakinsa yace "sweetheart kiyi hakuri dan matakin da zan d'auka yau bazai miki dadi ba ke mahaifiyatace duk abinda kika min da maryama kin ci lafiya kuma kinci banza saboda kece kika kawoni duniya ."amman kinga wad'an nan ya'yan naki wallahi bazan sak? d'aga masu kafa ba ko duba wata halaka dake tsananimu ,tsakanina dasu back to back ne ya d'auke idanunshi daga kallon mami ya zuba masu "ku kuma muatanen banza zaku gane kurenku a yau ne zaku gane bani da mutunci ya ciro waya ya soma kiran commissione of police yace "police din sun karaso okay shikenan bari nasa a shigo dasu yana gama rufe bakinsa ya juya ya fita cikin tsananin tashin hankali duk suke kallon bayansa maryama kam hannunwanta ta d'ora duka saman kanta ta koma ta jingina bayanta da bango tana karanta" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun mami ta kalleta "idan nace aurenki ya zame min alkhairi nayi wa Allah karya kin shigo rayuwarmu kin ruguza komai tsakanina dake Allah ya isa ban yafe miki ba,ai dai ciki gareki ba zaki haifa kuma za ki san me nake ji akan d'ana Ina addua Allah yasa ayi miki irin abinda kika min "maryama ta dukurshe kasa tana jan gwiwowinta tare da had'e hannunta duka tana rokonta "dan girman Allah mami kiyi hakuri ki yafe min wallahi ban rabaki da d'anki ba Allah shine sheidata ."



Tana kuka tana rokon mami har ma da aunty khadija tana bata hakuri adamcy ya shigo da polisawa yana nuna masu aunty khadija da nana hauwa'u da maryam,ya kalli auta afusace yana cewa "ina shahida!?bakinta na rawa tace tana d'akin mami tana sallah maza ki shiga ki kirata zan nuna maku tsantsar rashin tausayi ta nufi hanyar da sauri inda take jikin mami ya Kama rawa tana kallon adamcy wanda yaki kallonta dan kallonta zai sa ya kasa aiwatar da komai ."maryama ta ja gwiwowinta zuwa gabansa "ke kuma menene haka please get up? " ya fad'a a tsawace yana jifanta da mugun kallo da sauri ta girgiza masa kai "dan Allah ka duba halin da mami zata shiga akan matakin daka d'auka "kuma menene amfanin wannna matakin ?dan Allah ka janye kudirinka idan dai akaina ne wallahi na yafe masu duk abinda suka min "idan ke baki da hankali ni inda hankalina kuma nasan ciwonki "wai har ita wannna take yunkurin kasheki baki fad'a min ba "ya fad'a yana nuna maryam da d'an yatsansa "well da man kisan kai ba sabon abu bane a gurinta amamn idan ta gwada yi akanki ne zata sheka lahira dan da hannuna zan kasheki."Ya dawo da idanunshi ga maryama data had'a gumi tana rokonsa "ya d'an yi kasa da muryarsa "kima daina wahalar da kanki dan kema baki tsira ba bari na gama dasu zan dawo kanki ne .""Naji ka had'a duka hukuncin kayi min wallahi na yarda kuma na amince mutuncin mami da darajanta zaka duba pls d'auke kanshi yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login