Showing 147001 words to 150000 words out of 151781 words

Chapter 50 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2677

kina ganin wannan mufutace agareki sai kinbi matarsa kafin ki samu shiga a wajensa ?"kyak kwar zuciyarta ta jefeta da wannan tambayar "hakika wannan ba mafuta bace ki tsaya a ra'ayinki dana yan'uwanki kawai gur'batacciyar zuciyarta ta fad'a mata haka ."

Maryam bata Jima da dawowa d'akin ba sai ga adamcy ya shigo turus yayi alokcin da kwayar idanunshi ya sauka akanta cikin tsananin tashin hankali yace "what are you doing here ?jiya ma naga sunanki cikin list din wad'an da suka zo me kika zo yi ?menene had'in ki da matata ?ya jera mata wad'an nan tambayoyin ajere ita kuwa tunda ta ganshi ta birkice tasan ta shiga uku a hannunsa "tamabayarki nake "what are you doing here!"tayi shiru tana kallonsa jikinta na rawa wata razananniyar tsawa ya buga mata yana sake tambayarta bakinta na rawa tace "na kawo khaira ne bata jin dadi shine nace na shigo na.." "enough!"ya katseta ta hanyar fad'ar haka nan take ta ji wani irin mummunar fad'uwar gaba ta dirar mata "ki tsaya iya limit dinki bana son shishigi kuma bana son ganinki a kusa da matata domin idan wani abu ya samu matata bazan d'aga miki kafa ba dan banga dalilin da zai sa ki fara bibiyar matata ba tunda ke kanki kinsan cewa muguwa ce kuma macuciya ce"yana gama fad'ar haka yace "leave !"ya nuna mata kofa da yatsan hannunsa yana huci ."


Mmn Sudais

MAR'ADAMS
PAGE 31
"wani murmushi maryam ta sake saki? tare da share hawayenta ta d'ago ahankali ta kalli mami dake goge nata hawayen"Ina son d'anki mami ina matukar son shi Ina ma zai soni kamar yadda nake son shi da yaji dadi arayuwarsa domin kuwa zan sadaukar masa da rayuwarta ta hanayr masa biyayya tamkar baiwa sai dai ya nuna ya fi karfi na?"tayi maganar a kasan ranta idanunta na sak? cika da kwalla"na rokeki maryam karki sake shi ga harkar adamcy da wacan yarinyar ko babu komai adamcy makiyinki ne? kinga matarsa ma? makiyiyarki ce"ita dai ce makiyiyata mami sabda? mutun d'aya muke hari daita amman shi fa mami"?tai mata tambayr tana kallonta idanunta cike da kwalla "yaya ba makiyi bane a wajena bayan danganta akwai khaira a tsakaninmu duk abinda na aikata nayi saboda shi ne"karki sak? bana so dan yanzu baki ji yadda naji araina ba cike da sanyin murya tace "to mami kiyi hakuri in sha allahu bazan sak? ba ".tana gama fad'ar haka ta yunkura ta mike ahankali? ta d'auki wayarta ta bar d'akin inda mami tabi bayanta da kallo cike da tausayawa"Allah mai yadda yaso sai ya jarabe ka da son abu ya kuma hanaka shi,Allah ka kawo wa maryam mafuta? ka bata ikon cinye jarabawa.

"bedroom 'dinsu ta shiga tana zubar da hwaye ta haura gado ta tura wayarta a karkashin pillow ta kwanta kusa da khaira ta kamo yatsun hannunta tana kallo? tana k'ok'arin danne damuwarta sai dai hawayen dake cikin kwarnin idanunta yaki tsayawa dan haka ta bar gogewa ta bar shi yana tsiyaya akan pillow ."ahankali taji wayarta tana ringin da kamar bazata d'aga ba saboda halin da take ciki sai kuma ta tura hannunta ta lalu'bo wayar tana dubawa sunan aunty shahida ta gani numfashi ta sauke tana goge hawayenta sannan ta mike zaune ta d'aga kiran cikin raunanniyar murya tace "hello aunty Ina yini ?"hello maryam lfy? ya kike?"lafiya lau !ta fad'a tana kallon saman d'akin "mami tace ta sak? baki damar komawa gidan adamcy amman kin yanke hukuncin bazaki koma ba salim zaki auren?tace "eh aunty? !." Aunty shahida ta numafasa kana tace "maryam garaje ba naki bane ki tsaya? kiga yadda a sannu zamu tarwatsa rayuwar yarinyar nan , da duk wani munafukin dake zugata"gidan adamcy dake yafi da cewa ba da wann????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
an yar matsiyatan ba .

maryam tayi shiru tana sauraronta batare da tace komai ba har ta dasa aya sannan tace "Aunty kuyi hakuri? nasan kunyi iyakar kokarinku akaina kuma na gode maku sosai Allah ya bar zumunci amman Ina ganin ya dace zuwa yanzu kowa ya hakura ,ba kuma dan na daina sonshi ba wannan abu ne da bazan ta'ba dainawa ba har karshen numfashina da son shi zan mutu "shikenan zaki je gidan wani da son wani ?"ya zanyi aunty yaya adam yaki ni to the extended ya nuna wa duniya baya sona ba kuma zai soni ba kinga ko darajan khaira bana ci agurinsa kunga kona koma gidansa wahala kawai zan cigaba da sha zan auri salim kawai aunty. Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi arayuwata "ke dai karki yi gaugawa da saurin yanke hukunci tukun nan ki bamu lokaci dan wannan yarinyar sai ta bar gidansa dama aurensa gabad'aya.tana gama fad'ar haka ta katse kiran maryam tayi shiru rike da waya tana juya maganar aunty shahida ."

Bayan adamcy ya gama bawa maryama magani ya tashi zai bar d'akin "tai saurin riko hannunsa cikin nata tana murzawa tana kallon cikin kwayar idanunshi da nata idanun dake bukatar a tausaya masu dan tayi missing din jikinsa da komai nashi "menene kuma ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi yana karantar yanayinta dan kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin bukatarsa.ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana motsa bakinta ahankali "zumana na kasa gane kanka ." me yasa kake son rayuwar aurenka ya fita raina? ya kamata ka hakura ka manta komai mu cigaba da zamanmu kamar yadda muka faro ."zare hannunsa yayi cikin nata yace"baki san halina bane that's why maryama".
"nasani mana!.ta fad'a batare da ta d'ago ta kallesa ba sannan ta sauko daga kan gadon ta tsaya abayansa jikinta yana gugan nashi "kana da kirki sosai? amman baka da saurin yafiya amman kasani banyi laifin komai ba ".alright tunda baki yi laifi ba ki cigaba da tsayawa akan haka "tunda ka aureni na ta'ba maka abinda ya 'bata maka rai ne ?"no amman kin bari gangancinki yasa cikina ya zube" ya fad'a tare da juyowa ahankali ya zuba mata idanunshi "kin d'auka aure suna ne kawai ?ko kin d'auka aure sex ne kawai ?wai a gidan nan ake takaki ake wulakantaki har wacan yarinyar tasa hannunta ajikinki tana k'okarin miki illa amman kika min shiru saboda ko kasheki suka yi baki da asara ."

Ta sauke numfashi da ajiyar zuciya atare tana d'ago kanta ta zuba masa shayayyun idanunta
"Haka fa aka dinga shirya makirci akan kiyi auren wucin gadi dani ,wannan tsoron naki yasa kika amince kuma kika kasa fad'a min har sai da asiri ya tono ,ki sani acikin horon da zan miki ban miki komai ba domin sex ma da kika ga Ina yi dake all the time sa kaina nayi yanzu kuwa no sex no romance no fellings kinga I only love you understand "ya fad'a yana kara matsota tare da zura hannuwansa duka cikin aljihunsa yana kallonta da tsumammun idanunshi muryarta na rawa tace "na fahimta amman kayi hakuri dan Allah .."ai hakurin bashi da wani amfani a wajena yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi kofar fita ."tabi bayansa da kallo tana furta kalmar"inna lillahi har ya fice daga d'akin tana tsaye gabad'aya ta rasa me zata masa dan laifi kam yanzu tasan tayi laifi amman ita saboda gudun abinda zai faru ne yasa bata iya fad'a masa komai .amman shi gashi ya kasa fahimtarta ."

? ? ? ?? yana shiga d'akinsa ya sauke numfashi ya kai hannu jikin rigar jikinsa ya cire nan take murd'adden jikinsa ya bayyana ya ajiye rigar ya k'arasa ya bud'e bedside ya ciro kwalin sigari ya bud'e tare da ciro kara d'aya ya kai bakinsa ya kunna ya fara zuka ahankali yana fesar da hayaki cikin mintuna da basu wuce shabiyar ba ya tashi da kara uku ya kai na hud'u bakinsa ta shigo d'akin cikin sanyin jiki ta tsaya ajikin kofar d'akin ta tsura masa idanunta tana? kallonsa zuciyarta na wani irin tafasa kamar ta k'arasa garesa ta cire karan sigarin ta far fad'a masa mgn sai dai ta kasa k'arasa inda yake bare ma ta aiwatar da abinda yake ranta kallo d'aya yayi mata ya d'auke idanunshi akanta ya zuge zip din wondonsa ya soma cirewa yana tafiya yana zukar sigar har ya? shige bayi ."wani wahalallen numfa shi ta sauke da karfi tana dafe goshinta da hannu d'aya "ya rab ka kawo min mafuta wannan bawa naka so yake ya kasheni ."yana shiga ya kunna shawa ahankali ruwa ke sauka ajikjnsa ya kai hannu wansa duka saman fuskarsa yana wankewa kwata kwata bai ji motsin shigowarta ba sai jinta yayi ajikinsa ta rungumesa ta baya tare da kwantar da kanta a lafiyayyen bayansa jikinta d'aure da farin towel iya cinyarta .

juyowa yayi da sauri yana janye jikinsa daga nata yace "what are you doing here ?tai shiru zuciyarta cike da matsanancin tsoro da tashin hankali take kallonsa kamar ranar ta fara ganinsa ya matsota sosai ta mannu da bangon bayin hannuwanta duka ta kai daidai nipples dinsa at the same time tana kallon faffad'an k'irjinsa da ruwa ke sauka "i want you to give me a child again ta fad'a tana murza kan nipples dinsa zuwa gefen fuskarsa ."ahankali yabi yatsun hannunta da kallo jijiyarsa na mikewa ,zai kawar da fuskarsa gefe tai saurin tsaidaita suna kallon juna "I want to have your baby zumana wallahi a shirye nake dana sake samun wani ciki." ta fad'a tana kai bakinta ta had'e da nashi ta soma tsotsa bakinsa shiru yayi yana jin yadda take sarrfa bakinsa nan take komai na jikinsa ya fara sauyawa kamar zai bata had'in Kai sai kuma ya fixgeta daga jikinsa ya rike damtsen hannunta duka biyu wanda yasa hantar cikinta kadawa."bakiji abinda na fad'a miki bane bazan sak? kusantarki ba ,ko ance miki maye ne ni ?"ko dan kinga Ina yawon having sex dake kike tunanin saboda shi na aureki da kike son kija hankalina dahi ".

"amman ai ni matarka ce "so what ?"ya kamata ka dinga saka tausayi cikin zuciyarka "ai kin dade da sanin zuciyar dutse gareni "ya fad'a yana tamke fuska wato maganar data ta'ba fad'a masa abaya"amman ni Ina bukatar .."no sex I only love you. ya fad'a a tsawace "yasan yayi mata mugun horo mai tsananin wahala ,yayi mata horon da bazata iya hakura dashi ba haka zalika bazata iya yarda da kowa ba bayansa"wannan wace irin rayuwar zamuyi ?irin wacce kika zabar mana ita zamuyi.ya fad'a yana sakin hannunta ya tokare bangon bayin dashi fuskarsa na kallon nata Allah ya sani kawai daurewa yake amman gabad'aya ilahirin jikinsa suna bukatarta da mararinta ta tsura masa ido kamar yadda ya tsura mata sai daya gama kallonta ya d'auki towel ya fita ya barta tsaye rungume da hannuwanta a k'irji duk ruwa ya jikata da towel din jikinta "kayi hakuri nasan ka damu dani ne amman banason kana samun matsala da yan'uwanka ne yasa bana fad'a maka abubuwa ta fito cikin sanyin jiki taga har ya gama shirin bacci ya kwanta ya dafe goshinsa da mararsa ."

Ta sauke numfashi ta fita ta koma d'akinta tayi shirin bacci ta dawo ta kwanta kusa dashi yana ganinta? ya juya mata baya taja bargo ta rufesu tana ji ya cire bargon ajikinsa bata damu ba tayi kwanciyarta sai dai babu wanda ya runtsa a tsakaninsu tsakar dare tasa masa kuka dan hukuncin da ya yanke yayi mata tsauri da yawa!yana jinta ya shareta so yake yayi mata hukuncin da gobe idan aka mata abu ko bata samu karfin zuciyar ramawa ba zata fad'a masa sannan idan taga yana d'aukar mataki ido ne nata ."
washegari! haka ya shirya ya bar gidan batare daya sallameta ba sai shiga d'akinsa tayi taga wayam kamshin turarensa ne yasa ta gane ya fita sauyarsa gabad'aya ya dameta dame yake son taji ?"da rasa cikinta da tayi ko da wulakancinsa?tunda abun nan ya faru take kuka! al'amarin dai yana nema ya zama tashin hankali tana ganin abun kamar wasa a she tashin hankali na gaba domin gabad'aya ya canza canzawa ta ban mamaki a inda take d'an samun sukuni idan tana kasa kuma a gabansu mami nan zai zage ya nuna mata kulawa da tarairaya kamar babu komai acikin ranshi amman da zarar sun kasance su kad'ai ko kallonta baya yi ."

tun karfe biyar ta shirya cikin atamfa riga da siket? ta sauko parlour'n kasa inda ta iske mami zaune ita kad'ai."tai mata sallama sai dai tayi mata tsuru da idanu kamar yadda ta saba ta gaisheta koda wasa batayi tunanin zata amsa ba kuma yadda tayi zato hakan ce takasance bata amsa mata ba ta kawar da kanta gefe a yanzu kam ma kiyayyar tayi yawa kuma tasan duk fushin abinda mijinta yayi ma yaranta ne,kuma da alamun sun shiga hankalinsu dan tunda ta fito daga hospital sati biyu kenan bata gansu a gidan ba ."mami ta d'an saci kallonta tayi kyau sosai cikin atamfa yellow mai zanen fulawa ga lalle ta sha a yatsun hannunta ta kashe d'aurin manya mata sai kamshi jikinta yake fitarwa .sai dai duk da haka ganin take bata kai marym dinta ba dan maryam farinta ma abun kalla ce ita kuma Allah daya halicceta tana son farar mace koda data so adamcy ya auri? maryama kafin yayi abinda yayi mata ta amince ne saboda tana son taga yayi auri ba dan kalarta tayi mata ba .jikin maryam ya bata mami ita take kallo dan haka ta waigo ahankali sai dai mami tai saurin? d'auke idanunta ta maida wani bangare tana tunanin yadda zata fito da maganar dake cin ranta ba wai bazata iya bane sai dai amatsayinta na uwa tana jinjina maganar a bakinta ,ta kalleta tace mata bata son ta sak? d'aukar ciki d'anta? ko karta sak? barin wani abu ya shiga tsakaninsu da adamcy gasky maganar tayi mata nauyin da bazata iya furtawa ba zan dai tasan matakin da zata d'auka amman bazata yarda ta sak? d'aukar wani cikin ba ."

Maryama na zaune tana duban mami ya shigo yana lumlumshe ido, tai masa sannu da zuwa ya amsa yana cewa "ya gida ?!sannan ya gaishe da mami yana cewa wasshi Allah alamun gajiya a tattare dashi ,mami ta amsa fuskarta babu tabo babu fallasa ya samu waje ya zauna kusa da maryama tana ganin haka ta mike taje ta kawo masa kunnu aya mai sanyi wanda itace tayi ya sha kad'an ya mika mata cup, in da? tasan har yanzu fushi yake daita ko yace mata ya gode kamar yadda ya saba a duk sanda tayi masa wani abu zai ce mata" thank you!ta zauna nesa dashi sai dai taga ya motsota sosai kamar zai mata magana mami ta numfasa tace "wai adamcy yaushe zaka bar gidan nan ne"?sai ranar da'aka had'a Kayan khaira "ya bata amsa da haka "kaga bana son iskancinka daka saba duk wulakancin da kayi karka d'auka bai dameni bane kawai dai na barka da duniya ne ,amman batun khaira kar na sak? jin shi a bakinka dan komai zai faru baza ta dawo hannunka ba kuma kwanaki bakwai kawai na baka ka tattara ka bar min gidana "haba sweetheart me yasa duk kika damu kika d'auki zafi haka ne ?tace ban sani ba ni dai kaji abinda nace ."ya riko hannun maryama cikin nashi yana kallon yatsun hannunta daya sha lalle yana murzawa ahankali wanda nan take taji duk jikinta ya mutu,godiya ta dinga yi acikin ranta sakamakon jin mami ta sallamesu."

? ? wayarsa ce ta soma ringing ya ciro yana dubawa sunan maryam abdulra'uf ya gani wanda trucualler ya nuna masa tun last week yake ganin kiranta sai dai baya d'auka yanzu ma bai d'aga ba kuma baya tunanin d'agawa ya kashe wani kiran ya sake shigowa a kalla sai da tayi masa kira kusan biyar duk baya d'agawa daya duba yaga numberta ce zai katse ta fito daga cikin d'aki tana sake nemansa sai dai tana kallonsa ya katse ."
Waje ta samu ta tsaya nesa kad'an dashi tace "abban khaira!yana jinta har sai data maimaita kiransa da wannan sunan .amman yayi mata banza maryama tayi kmar zatayi masa magana ta tuna itama a tsaka mai wuya take a wajensa dan haka ta d'auke idanunta da hankalinta akansu tana k'okarin zare hannunta cikin nashi taji ya cafko da sauri? ya cilla cikin bakinsa yana tsotsa yana kallonta tayi masa kyau sosai inda mami tai kamr bata gansu ba ta zuba wa maryam ido tana tmbyrta da kwayar idanunta ta girgiza mata kai zuciyarta na wani irin dokawa sakamakon abinda taga adamcy yake wa maryama ."

ta sanyawa jikinta jarumta ta sak? kiran sunasa a zafafe yace "what!?ina son nayi magana da kai ne fuskarsa a had'e yace "bani da lokaci 'batawa ."
"maganar tana da mahimmanci idan kuma zaka bani dama sai nayiwa matarka bayani"not now ?"
Ya fad'a atakaice yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa .duk ma yana sauraranta ne saboda ganin idanun mami tayi shiru tana runtse idanu nta tare da sauke ajiyar zuciya maryama na son tambayarta menene amman tana jin tsoron abinda zai biyo baya? daman ita mai laifi ce karta k'arawa kanta gara ita tana da mami "mami tace ke me kike bukata da zaki tsallakeni ki zo gurinsa dan kawai ki bashi damar fad'awa mutane magana ?"mami khaira ce kinsan tunda ya fara batun mgnr zai kar'beta yarinyar nan take rashin lafiya jiya kinga ko bacci bamuyi ba har safe shine nake son na rokesa ko zai kar'beta ba yanzu ba ya ma bar mganar gabad'aya zuwa wani lokacin idan ma da hali ni abar min diyata na rike".

wani kallon kasan ido yayi mata yana jan tsaki ,numfashi mami ta sauke da karfi tace "kima je ki kwantar da hankalinki idan dai akan wannan ne babu mai rabaki da diyarki sai dai idan bana numfashi amman muddin Ina raye khaira tana hannuki ko aure kikayi da abarki zaki tafi "adamcy ya kalli mami ta kasan idonsa tace d'ago ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login