Showing 96001 words to 99000 words out of 151781 words

Chapter 33 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2689

"ahhh yau dai ga mommy and daughter an had'e hankali ya kwanta kuka ya kare ."suka kwashe da dariya cikin farin cikin ganin bilkisunsu ."

aunty ta kasa hakurin ta tashi taje ta riko hannun mahaifinta shima damke hannunta yayi sosai cikin nashi kafin ahankali ya rungumeta "nayi kewarka abba!"bai Kai wanda mukayi ba bilkisu kin tafi kin barmu da kewarki , kin tafi da ruhinmu da rayuwarmu ,kin bar zuciyarmu da ciwon rashinki "ya fad'a idanunshi na kawo ruwa kusan minti goma suka d'auka tsaye sannan suka zauna inda akan kawo masu drink's kala dabam dabam sai dai aunty bata iya sha ba kokarin neman gafara iyayenta take ta matso kusa da mahaifiyarta ta d'aura kanta akan cinyarta ta fara kame kame neman afuwa , "umm ummm? mummy abba kuyi hakuri ku yafe min laifina ."Shiru sukai suna kallonta kamar ba bilkisunsu ba gabad'aya ta canza kwata kwata babu wata alamun tana cikin jin dadi hasalima wahala ce atattare daita sai dai tana cikin farinciki.idanun hajiya rahma ya sake kawo kwalla "mumy Abba kuyi hakuri nasan ban kyauta maku ba amman a yanzu na gane kuskurena na bawa wani muhimmaci da rayuwata akanku amamn kuma qaddarata ce tazo min haka sai dai nayi nadaman hakan a yanzu ashirye nake dana faranta muku da kaunarku da maku biyayya ."

wani sanyin dad'i ne ya ziyarci zuciyar hajiya rahma dan ta dad'e tana mafarkin zuwan wanan ranan ,ta dad'e tana rokon Allah ya dawo mata da diyarta cikin koshin lafiya ,aunty ta kara gyara kanta akan cinyan hajiya raham" mumy ki ya femun dan Allah ku ya femun koh zansamu sassaucin abunda nake ji a raina kada zuciyata ta buga "tayi saurin saka hannu ta rufe mata bakinta dan bata son ma ta k'arasa kalamanta tana shafa kanta tana jin son diyarta har cikin bargon jikinta da zuciyarta , wanda a yanzu itace 'ya tilo daya da take jin babu kamarta ."bilkisu na dade da yafe miki? ban kuma tab'a rikeki a raina ba haka ma mahaifinki kullum addu'a muke? miki Allah ya baki ikon cinye jarabawarki "aunty ta d'ago kanta idanunta cike da ruwan hawaye ta kalli mahaifinta shima kamar yadda hjy rahma ta fad'a haka ya fad'a mata sun? dade da yafe mata ." "tabbas iyaye dabam suke yanzu duk tarin laifinta garesu sun? dade da yafe mata hannunta hajiya raham ta riko cikin? tace "ina kika baro min jikokina ?"shiru aunty? tayi ta kasa magana sakamakon hawayen dake zuba daga cikin kwarnin idanunta sai umma ce ta bata amsa tace"suna nan lafiya kuma sunce a gaishe ku ."su yaushe za'a kawo min su na gansu?" .

"in sha Allah very soon zamu kawo miki su ki gansu "umma ta k'arasa maganar tana murmushi itama hajiya rahama murmushin jin dadi take tana jin wani dadi da sanyi at the same time tana tunani a zuciyarta dama addu'an iyaye bata fad'uwa kasa banza Allah mai amsa addu'an iyaye ne akan y'ay'ansu ta godewa Allah daya amsa mata adduarta gata ga bilkisunta "ta sake riko hannun aunty tana cewa "yau kowa zai yi farin ciki idan yaji dawowar ki? yan'uwanki sunyi kewarki matuka duk inda akaje biki ko suna ko taron duk karshen shekara da mukeyi sai anyi jimamin rashinki,sai ance Allah sarki bilkisu mai son yan'uwanta? munyi kewarki sosai Allah yayi miki albarka shi hussein din fa me yasa baku zo dashi ba Allah yasa bai rikemu ba ?"nan take wani kuka yaci karfin aunty domin? an tab'o mata ciwon dake binne a zuciyarta wanda take jin bazai tab'a war kewa ba har karshen rayuwanta tunda ta rasa wani bangare na rayuwanta ."

jikin hajiya rahma yayi mungun? sanyi,dan ji tayi kukan wahalar da take ciki take yi wannan Karon ma umma ce tayi mata bayani" ai zaman nasu bai yi tsawo ba ya dade da rasuwa ."Allah sarki rayuwa kenan Allah ya jikinsa Allah kuma ya jikan muslim gabad'aya "inji cewar alhaji rafi'u giwa ."anan? suka wuni sun ci abinci kala dabam dabam anyi hira yaushe gamo sai dai aunty bata fad'a masu irin tsananin rayuwar da tayi ba ,da kuma matsayin da diyarta ta taka ba dan karsu d'auka ta dawo garesu ne saboda ta samu sauyin rayuwa ,da zasu wuce gida? hajiya Aysha? na cikin wad'an da suka? masu rakiya har gida suka kawosu da? mototarta GAC 2023 wanda kimanin kudinta ta kai 85 million duk da tasan gidan amman sai data zubar ma yar'uwarta hawayen tausayi kuma ta d'auki damaran taimaka mata da inganta rayuwarta ta dawo cikin gatanta kamar da ."zuciyar aunty fes ta kasa boye murnarta acikinsu babu wacce ta shiga banga renta sai da suka leka ko aunty salma ta dawo sai dai suka iske bata dawo ba jaje suka sake yiwa baba gali da Allah ya kyauta? sannan suka fita ."

********

?? tsawon sati? uku kenan? adamcy bai neme maryama ba tsakaninsa daita sai dai yayi wasa da jikinta tare da? tatalinta domin yana son ta fahimci zallar ita din yake so ba wani abu nata ba sai dai? a sati? ukun nan ? matukar matse yake fellings kamar yaci babu tunda kullum ne sai yayi romancing dinta kafin suyi bacci duk wani nau'in wasa na auratayya? kusan adamcy ya sabawar maryama dashi ,duk kuma abinda yayi? mata? zatayi kokarin ta mayar masa a yanzu ma makale suke da juna kowanensu babu kaya kamar zasu yiwa juna numfashi ta bala'i kafeshi da kwayar idanuwanta cike da natsuwa ta kai tafin hannun ta saman fadadden kirinsa tana shafawa har zuwa kan nipples dinsa bai yi mamakin abinda take ba dan yasan ya rigada ya gama d'aurata akan network ta kai limit din bukatuwa dashi."
ahankali ya dinga jin hannuta a tsantsar ajikinshi tana yawo dashi tana cigaba da shafa laulausan gashin dake kwance ,wani irin sha'awa yaji ya tsarga masa bai san sanda ya sake manneta a? jikinsa ba ya rungumeta tsam tsam yana sakin numfashi tare da daura hannushi kan sumar kanta yana shafa gashin kanta zuwa bayanta ."

kusan mintuna dayawa? tana rungume a k'irjinsa suna jin dumin juna yayi imani da zai yi wani abu daita bazata hanashi ba ?cikin sati na hud'u ne adamcy ya fara tunanin fara fita kuma yace ta shirya tare zasu ,kamar tace masa a'a yayi tafiyarsa shi kad'ai sai dai tai shiru ,ya shirya cikin wani hadadden suit? riga da wondo ash colour sun matsifar masa kyau da tsumammun idanunshi yake binta da kallo dole ta fara? shirya kanta cikin wani hadadden doguwar rigar abaya? mai yar ciki rigar? black ce wacce aka yi mata kwaliya da zare gold masha Allah tayi matukar kyau,? simple make up? tayi ,tasa takalma masu dan saukin tafiya, tana kokarin feshe jikinta da turare ne ya karaso ya tsaya bayanta yana kallonta ta cikin mirrow "nasan kin san abinda kike aikata wa a yanzu haram ne ko ?"ya tambayeta? yana had'e fuska sannan ya kar'bi kwalbar turaren hannunta ya ajiye ya cigaba da magana ".

"ki tashi kije ki? canza wasu kaya dan baza ki fita kina wannan kamshi ba "!.ya fad'a cikin low voice?? dinsa mai matukar kashe jiki yana sak? had'e fuska,ta cikin mirrow ta d'ago kanta ta kallesa shima ita yake kallo ko kiftawa bayayi ."tana son tayi magana sai dai? tasan halinsa kaifi d'aya ne idan ya fad'a abu kawai gara ka aikata abinda yake so ka huta ,murmushi ta sakar masa tace '"shikenan yalla'bai an gama ta yunkura zata mike ya dafa kafad'anta alamun tayi? zamanta shi da kanshi yaje ya d'auko mata wasu kayan riga da siket ya dawo ya mika mata ya koma ya tsaya rungume da hannunsa a k'irji yana kallonta numfashi ta sauke sannan ta zuge zip din rigar ta tura hannunta duka alokcin d'aya tana kokarin cire na jikinta,? ta saka rigar batare data zuge zip ba sannan ta soma kokarin saka siket alokcin aka kira waya dan haka ya fita amsar kiran."

Bayan ta gama saka siket ne ta soma k'ok'arin zuge zip din rigarta sai dai ta kasa tai ta gwada zuge wa amman ta kasa dan hannunta yaki kai wa kasancewar wuyar riga a sama akayisa tunda take ta kokarin zuge din yana tsaye a bakin kofa? ya harde hannunwansa a k'irji yana kallon yadda take ta faman yin sama da hannunta amman ta kasa har ta fara had'a gumi taja tsaki tana cewa? "da yanzu ya barta da doguwar rigarta da bazata sha wahala haka ba ."ahankali ya taka zuwa inda remut din ac yake ya d'auka ya kunna tare da kure karfinsa ji tayi sanyi ya wadatu a d'akin ta d'ago ahankali ta kallesa ta mirrow fuskarta a d'an had'e ,kallo d'aya tayi masa ta d'auke idanun ta akanshi ,bata jiyo takunsa ba kawai sai ganin? mutun abayanta tayi ta? sake d'agowa suka had'a ido ta cikin mirrow fuskarsa a had'e kamar yadda nata yake babu walwala muryata a sanyaye tace "yanzu abinda kayi daidai ne ?"ya d'age mata girarsa d'aya alamun "eh!"d'auke idanunta tayi akanshi tana cewa "ni dai gasky banga abinda ya samu wad'an can kayan da kace na cire? ba abd turaren da nayi amfani dashi babu yadda zai ji yasan nayi amafani dashi "haka kike gani amman ni ba sakarai bane tunda har na iya jin kamshinsa kowa ma zai iya ji ."ya fad'a yana juyo daita suka fuskanci juna ya kai hannunsa bayanta batare daya kalleta ba ko sake mata magana ba ."

ahankali ta dinga jin tafiyar hannusa a gadon bayanta kamar yana mata tafiyar tsutsa kafin ahankali taji yayi kasa da zip din gabad'aya riga ta rabu? gida biyu saurin rike rigar tayi ya d'ago tsumammun idanunshi yana mata alamar ta saki bata iya mutsa masa ba ta sakar masa taga abinda zai yi sai gani tayi ya juya da alamun suma wad'an kayan canzasu zai yi mamakinsa ya kamata dan a tunaninta kawai taimakawa zai yi ya zuge mata ,da mamaki riga da zani ya d'auko ya mika mata "da riga da zani zan fita "?su din ba kaya bane ?"ya bata amsa atakaice yana had'e fuska "saurin runtse idanunta tayi "inna lillahi wannan wani irin bahagon mutun ne ganin tana rike da kayan bata da niyyar cire siket din jikinta ya kara taku ya tsaya gabanta ya janyota ya had'e ta da jikinsa ya soma k'ok'arin zuge zip din siket din. da zai zuge sai daya makaleta ajikinsa cikin wani irin salo daya sakata shigewa jikinsa har wata zabura tayi saboda sakonsa ya kai mata har cikin kwakwaluwar kanta ,ya d'an kalleta yana wani sakar mata miskilallen murmushinsa tare da d'age mata gira alamar tambaya? numfashi ta sauke kawai tana lumshe idanunta? har ya gama cire mata siket din ya d'aura mata zani ya saka mata? riga ya zuge mata zip din rigar bata bud'e idanunta ba ."

Ahankali ya maidaita ta zauna ya gyara mata gashi kanta ya tufkesa da kyar yasa reborn ya Kama sai lokacin ta bud'e idanunta ya wani tsareta da tsumammun idanunshi sai dai ta kasa jure wa kallonsa ta maida idanunta tayi ta? rufe tana mamakinsa daman ya iya abinda mata suka iya ko da yake baza'a yi mamakin iya warsa ba tunda cikin mata ya tashi "bai barta ba sai da yayi yadda yake so daita bayan ya gama shiryata ya d'auko? abaya ya d'ora mata a saman kayan jikinta shiru tayi ta kasa bud'e idanunta ta kallesa bare taga wainar da yake to yawa."ahankali taji yana sauke mata? iskar bakinsa a wuyanta dole ta bud'e idanunta ahankali alokcin da yake sake matsota suka zubawa juna ido ko kiftawa basayi bugun zuciyoyinsu yasa ta maida idanunta ta lumshe tana sauke karamar ajiyar zuciya shima naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi yayi baya ya fita daga? d'akin? jin ya bar d'akin ta bud'e idanunta duk jikinta ya saki wani ajiyar zuciya ta sak? saukewa tana jinjina masa tana sak? jin soyayyarsa na ninkuwa acikin zuciya da ma gangar jikinta ,tayi imani da Allah akwana d'aya kawai aka bar adamcy da mutun sai ya canza masa lissafi sannan ya dasa kaunarsa mara iya ka ."

Tana roling din mayafi ya sake dawowa ya tsaya abayanta ya manneta da jikinsa yana zagayo da hannunsa duk biyu cikin miskilalliyar muryarsa yake magana "anya bazamu canza wasu kayan ba dan naga wad'an sunyi miki kyau over fiyye da wad'an da kika cire kuma suma? kamar kamshi suke ?"nan take ta had'e fuska dan kyau ita kanta tasan tayi kyau most especially abayar d'aya d'aura mata dan sai ta dawo tamkar? bakar balarabiya? tayi kyau sosai,kasa d'auke idanunshi yayi akanta yana nazarin yanayin data shiga "okay dan nace ko za'a canza kayan ne kika wani had'e fuska haka kmr na fad'a mugun abu ?"ya fad'a yana sak? matseta shiru tayi taki cewa komai "ki saki fuska ko kuma wallahi sai an canza wasu "a ranta tace" to a canza mana sai me amman a zahiri murmushin dole tayi tana kallonsa ta cikin mirrow har lokacin hannusa na mararta yana faman aikin shafawa yana lumshe mata tsumammun idanunshi ."

ta kai hannunta ta shafo gefen fuskarsa tace "yalla'ba kai ma ka saki fuskarka "batare daya daina shafa kasan mararta ba yace "barta a yadda take ,kema kuma karki sak? naga kin sakarwa kowa fuska a office "ya fad'a yana cigaba da shafa kasan mararta, yadda yake mata a wuyanta da yadda hannunsa ke canza salo ajikinta yasa tayi k'ok'arin juyowa ko hakan zai sa ya d'auke hannunsa a mararta wanda ta rasa dalili sai dai idan basa tare duk yadda zai yi hannunsa ya kai ga mararta sai yayi ,idan suna bacci kuwa wayyo Allah ai ko fitsari idan zata tashi tayi da kyar take bambare hannunsa ."Juyowarta a she sak? kunnosa tayi gabad'aya adamcy ya rikice hannnuwansa ya zagayo dashi kugunta yana sak? matso daita jikinsa sosai ya d'aura lip's dinsa akan nata, kasa jure wa tayi ta dinga tayasa sha tana sauke numfashi tana lumshe masa idanunta idan da sabo ya sabar mata tun tana kuka akan shi yanzu ta zama yar hannu." ya d'auki lokaci yana shan bakinta sannan ya zare bakinsa yana kallonta "numfashi ta sauke tana lumshe idanunta muryarta can kasa tace "ko dai mun fasa fitar ne ?"me kika gani ?!ya tambayeta yana sak? had'e bakinsu saurin zare bakinta tayi gabanta na fad'uwa tana kallonsa yaja hanunta suka fara tafiya tace a haka zaka fita ?!

ya d'an tsaya yana kallon jikinsa a tsanake shi bai ga abinda ya samesa ba ,magana yake son yi amman? harshensa ya kasa furta mata komai "duk fa yanayinka ya canza ka tsaya ka daidaita bugun zuciyarka da natsuwar ka dan za'a iya ga.."wata uwar harara ya buga mata hakan yasa tayi kasa da kanta tana jin wani irin? yrrrr ajikinta, kyakkwan riko ya sake yiwa hannunta suka cigaba da tafiya cikin nishadi,sai dai fuskar nan tashi a had'e take tamkar hadari hanuwansu sarke da juna suka karasa fita,suka nufi bangaren mami duk yadda taso ta dojewa shiga yaki aiko sunga abinda suke bukata daga gareta kallon banza da ko in kula tayi masu duk sukai shiru tamkar babu wasu halittu? masu? numfashi acikin d'akin ,daga mami har adamcy kowannensu shi kad'ai yasan mai yake sakawa acikin zuciyarsa ."karar wayarsa yasa ya mike muryarsa a sanyayye? yace "sweetheart mu zamu? fita zuwa Office sai mun dawo "da mamakinsa yaga ko d'agowa ta kallesa batayi ba bare? ma ta amsa masa sai dai sai dai ita mami sai faman maimaita kalmar da ya fad'a take acikin zuciyarta ."da hannu yayi wa maryama umarnin ta tashi su wuce aiko ta mike da sauri suka nufi kofar fita inda mami tabi bayansu da kallo cike da matsana ncin namaki ."Kamar wanda aka asirce yabi ya makalewa yarinya kamar wata yar gwal."

Cike da soyayya suka k'arasa ma'aikatansa abin gwanin sha'awa, ana? yaga ma'aikatansa suna kalar masa mata ya fara zazzare ido? yana harehare yana cika yana batsewa? ba karya matarsa? tana da kyau sosai na bugu da karin mamakin wasu suke yi wai shi ne ya aureta."most especially wad'an da ya mata wulakanci ? gaban su, sunfi mamaki kwarai gashi da alamun yana ji da ita sanan yana matukar son ta ."
sosai yayi d'aya sanin zuwa daita kuma yayi? haka ne saboda ya bata kariya daga sharrinsu khadija duk da ya kara tsaro sosai a gidan? ta hanyar dasa camerori akoina a gidan har kitchen."dariya ya dinga bata a duk lokacin da suka had'a ido sai ta sakar masa murmushi shi kuwa ya had'e fuska tace "yalla'ba ina neman izinin magana da yusura da madam some "ba dai anan ba !ya fad'a atakaice yana hura mata hancinsa ."

adadafe suka kai azahar yace su wuce? sai dai basu koma gida ba kai tsaye sabon gidansu umma suka nufa maryama ta sha mamaki daman sun tare abunsu shine ko su fad'a mata aiko ta dinga cika tana batsewa ta kasa hakuri tace "umma ni menene laifina da baza'a fad'a min tariyar ba .?"umma da aunty suka yi murmushin umma tace "duka yaushe ne muka tare shekaran jiya ne fa kuma mijiki ne yace kar a fad'a miki? kinga ban san dalilinsa ba shiyasa mukai miki shiru amman ai gashi ya kawoki."sake had'e rai tayi tana kallonsa had'e da zabga masa wata uwar harara ya kalleta kawai yana d'an ciza lip's dinsa na kasa bayan sun gama gaisawa aunty ta koma bangarenta inda hira ta barke tsakanin umma da adamcy ,adamcyn na matukar kaunar umma kamar yadda itama take matukar ji dashi kuma yafi sakewa daita akan aunty? yayinda maryama tayi masu dip taki cewa komai daga baya ma mikewa tayi tare d'an jan gutun tsaki ta shiga bangaren da aunty take ,inda ta soma da? tamaba yar aunty lafiyar mahaifiyarta sannan ta k'ara da cewa "aunty wai yaushe ne zamu je muga granny itama ta ganmu ?"Allah na matsu naje naga yan gidanku aunty tai murmushi tace "suma? kullum maganarsu kenan suna son su ganki wai? so nake ki tare tukunan a gidanki sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login