Showing 3001 words to 6000 words out of 151781 words

Chapter 2 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2652

tura masa sako akan yadda sukai da mami bangaren mami kuwa bayan fitar amar madam some ta kira bayan ta d aga kiran da girmamawa tace  ki turo min da address din yarinyar nan maryama da number wayarta madam some tace  okay ma ko kuna tare daita ne ? no ma ta kwana biyu bata zuwa aiki kamar ta ajiye aikin ne dai bamu sani ba duk dai bata rubuto mana latter ajiye aiki ba shikenan ki turo min yanzu yanzu  okay ma ! mami ta katse kiran ta zauna tana jiran madam some tare da d aga kanta sama tana tunanin da jin zafin kaurace mata da adamcy yayi akan mace bayan second biyar taji shigowar sako wayarta ta duba taga sakon some ne dan haka ta soma Neman number maryama wacce ke duke abayan d akinta jikinta sanye da wata yar riga baka mai gajeren hannu da zani tana wanke kayan umma taji wayarta tana ringing da sauri ta cire hannun ta acikin ruwan wanki ta d auki d aya daga cikin rigunan umma mai dotti ta goge hannunta sannan ta d auki wayar tana dubawa dan a tunaninta mr ata ne sai dai taga sa banin haka domin kuwa wata bakuwar number ta gani tana yawo a screen din wayar .



shiru tayi tana tunanin d aga kiran,bata d aga kiran ba har kiran ya katse wani kiran ya sake shigowa yana daf da katsewa ne tayi kundunbala ta d aga tare da yin sallama cikin sanyayyiyar muryarta mai cike da natsuwa sannan tayi shiru. madadin a amsa mata sallamarta sai taji murya wacce babu tantama ta ta ba jin muryar
arayuwarta  .
 ke Ina adamcy yace miki yake ? gyara tsayuwa maryama tayi cikin tsananin tashin hankali da matsanancin firgici da tsoro  dan take ta fahimci muryar sweetheart din mr ata ce akan layi muryata na rawa cike da ladabi tace  Ina yini ma ! ?  lafiya ! ta amsa mata atakaice tana sake tamabayrta  wallahi mumy ban sani ba bai fad a min inda yake ba .karya kike kin sani dan kunyi waya dashi a yau din nan zaki ce bai fad a miki inda yake ba ? maryama tayi shiru zuciyarta na karkarwa da sake shiga mummunar tashin hankalin yadda tasan sunyi waya  kece mutun ta qarshe da kukayi waya dashi idan wani abu ya samu yarona bazan barki ba  ta fad a cike da tsawa nan take fad uwar da gaban maryama yake ya qaru ta fara zazzare idanu kuma take ta fahimci hanayr data bi tasan sunyi waya .


jikinta na karkarwa inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta shiga furtawa yau kwanaki biyar kenan ban saka shi acikin kwayar idanuna ba sannan bai kirani ba abinda bai ta ba faruwa ba kenan duk yadda zai yi fushi tabbass zai nemi inda nake ,ki sani duk wannan abun ya faru ne saboda ke km ya bar gida ne saboda ke dan haka kiyi duk abinda zakiyi d ana ya dawo gida kuma a yau din nan . cikin qarfin hali maryama tace  to mumy in sha allahu kiyi hakuri numbobinsa basa zuwa nima nayi kwana biyar bamu yi waya ba dashi sai d azu ya kirani  ta fad a cikin tsananin firgici da sake shiga tashin hankalin  dan Allah kiyi hakuri mumy ? nace kin min laifi ne ?! maryama ta girgiza mata Kai da sauri kamar tana gabanta tace  Im sorry ma!  d ana ya dawo gida kuma a yau din nan shine abinda nake da bukata nan take maryama ta d aura hannunwanta duka bisa kanta tare da juyowa bayanta cak ta tsaya cikin wani irin sabuwar gigita sakamakon ganin mr ata tsaye datayi a bayanta rungume da hannunwansa duka a k irji yana kallonta hannunta ta kai da sauri ta murza idanuwanta tana son ta sharewa kanta tamtamar shi ne tsye agabanta ko kuwa gizo ne? sai dai koda ta cire hannuwanta a idanuwanta shi din ne tsaye idanunshi kyam a kanta yana kallonta from head to toe .



tsurawa juna idanu sukayi yana tsaye har lokacin rungume da hannuwansa a k irji yayi kyau sosai cikin kanana kaya riga da wondo duk bakeke rigar mai gajeren hannu ce idanunshi na manne da farin glass dinsa na kaida sai dai ya d an rame wanda ke nuna alamun yana cikin damuwa bata san tayi kewarsa na tsawon kwanakin ba sai da ta ganshi tsaye a gabanta ,gabad aya ma mantawa tayi da halin damuwar da mami ta sakata ciki taji Ina ma zata iya data k arasa ta rungumeshi abinda ke cikin ranta shine acikin aranshi dan shi tuni ya ware mata hannunwa nsa alamun tazo garesa,ahankali ta soma girgiza masa kai alamun bazata iya aikata hakan ba dan da zata iya wallahi da babu abinda zai hana bata isa garesa ta rungume sa tayi kuka a kirjinsa ba dan ahalin da take ciki yanzu hawaye ne cike a idanunta .
ahankali ya karaso inda take tsaye tamkar an dasata ya fixgota zuwa jikinsa ya rungumeta tsam a faffadan k irjinsa yana sauke wani bayanannen ajiyar zuciya  ga abinda ya kamata kiyi nan ba kuka ba ya fad a yana sake matseta gam ajikinsa ta d an saki kara mara sauti  washhh! karka  ballani mana,kema kin san bazan ta ba ballaki ba ,idan na ballaki wa zan runguma? .


mami ta runtse idanunta da sauri zufa na karyo mata ta koina ajikinta dan da furucin adamcy da na maryama babu bambamci dan hakan ya nuna mata alamun suna rungume da juna ne . inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yaushe adamcy ya dawo haka ? daman adamcy zai iya rayuwa ko babu ita ? a she zai iya fifita mace akanta? a she zai iya d aukar kwanaki bai ganta ba ya zauna lafiya alhalin ba wata kasar yaje ba  ? gashi ita ta rasa kwanciyarta hankali akanshi amman shi babu abinda ya damesa rayuwarsa ma yake da abinda tace bata so, kenan idan ma mutuwa zatayi sai dai ta mutu bazai bi umarninta ba ?
mami na can cikin matsanancin tashin hankali yayinda adamcy nta ya kamo face din maryama yana kallo  I miss you badly! tare da kai mata kiss sannna ya d an zareta ajikinsa yana kallonta sanye da rigar jikinta wacce ta nuna tsayuwar brest dinta dan har kan nipples dinta yana gani .
da sauri ta kai damtsen hannunta ta kare inda yake kallo ,yana kokarin sake maidata jikinsa tace  dan malam sakar min jiki haka babu damar kaga mutun shikenan  me kike son nayi ?da zarar na ganki nake mance komai ban ta ba jin Ina Allah Allah na mallaki wani abu ba kamar yadda nake son na mallakeki laifi ne dan na kalleki? .



 Dan Allah mu ajiye wannan maganar ba girmanka bane yanzu dai ka fad a min ina kaje  ?me ma yasa zaka bar gida kai ba yaro ba ? tayi masa tambayr tana harararsa tare da kai hannu zata d auki mayafin umma dake ajiye a kasa ta rufe jikinta dan ta lura da yadda ya tsurawa qirjinta idanu kamar wani tsohon maye yayi saurin riko hannunta cikin nashi yana cewa  no ! I don t understand no sir ? dan Allah ka bari na rufe jikina mana  no !! maryama karki rufe ki bar shi haka babu abinda zan masu  I m not comfortable  an so cinyeki zanyi !ya fad a yana canza face  bance zaka cinyeni ba amman muddin kana son na cigaba da tsayuwa anan sai na rufe jikina .tana gama fad ar haka ya miko mata mayafin tare da yi mata kallon nan nashi na gefen ido mai rikita mata lissafi yana cewa  banga abun wani boye wa ba. taji abinda yace sarai amman ta share ta cigaba da magana cikin sanyayyiyar muryarta me yasa zaka bar gida  ?bai yi mamaki jin tambayarta ba dan yaga sakon ammar shine ma dalilin zuwansa dan yasa lallai sweetheart zata nemeta  sweetheart dinka ta kira ni yanzu, dan Allah ka koma gida ko dan kwanci yar hankalin mahaifiyrka  .



saurin matsota yayi sosai yana kokarin kamo hannunta taja baya da sauri tana cewa  no sir karka ta bani , na rasa me yasa ka kasa gane banason kana ta bani  karya ne maryama kina so mana  ya fad a yana lasar lip s dinsa na kasa  Allah banaso tayi maganar cike da shagwaba kamar zatayi kuka .mami dake rike da waya tace yau ga karuwanci anya kuwa yarinyar nan ta bar adamcy haka ?  muga wayar ya fad a yana miko mata tafin hannunsa ta mike masa wayar tana sake ja baya dan tasan halinsa bakaramin aikinsa bane ya sake fixgota ya rungumeta  kallon screen din wayar yayi sannnan ya d ago a natse ya kalleta sakamakon ganin har lokacin mami tana kan layi wanda alamun ya nuna tana sauraronsu ne yasa ta bar wayar batare data katse ba,ya nuna ma maryama fuskar wayar ai ko da sauri ta zaro idanu waje tana d aura hannuwanta duka a saman kanta .  ya kashe wayar yana cewa  matsalarki kenan maryama saurin rikicewa ,ganina da kikayi ne yasa kika mance tana kan layi ? ta gyad a masa kai da sauri tana cewa  na shiga uku nah ni maryama shikenan taji maganga nunmu ,da me zanji daga wannan tashin hankalin sai wannan  .tayi maganar cikin siririyar muryarta tana k ok arin durkushewa kasa yayi saurin rikota zuwa jikinsa .


kuka ta fashe dashi ji tayi kunyar duk duniya ta kamata wani irin fassara mahaifiyarsa zata mata .? gabad aya ta rasa natsuwarta ji take kamar zaciyarta zata buga kokarin zare jikinta take ajikinsa ya sake matseta yana cewa  ki natsu mana bai zama lallai taji abinda muka fad a ba ? ya fad a domin ya kwantar mata da hankali dan ji kam yasan sweetheart taji wasu daga cikin maganarsu.hawaye take zubar sosai  da wahala bataji ba shikenan ka sake ja min wata tsana a wajen mahaifiyrka daman bata son ka aureni yanzu ga hujjar da zata sake tsanar auren 
Ya d an lashi lip s dinsa na kasa kad an yace  ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru sannna babu abinda zai hana aurenmu muddin Ina raye baki da wani miji bayan ni .
wani sassanyan numfashi ta sauke ta gyara tsayuwarta ajikinsa dan k afafuwanta sun fara gaza d aukarta,shima numfashi ya sauke tare da kai tafin hannunsa ya share mata hawaye ya sake maida kacokan hankalinsa gareta, ita kam ta shiga uku taga ta kanta yanzu haka rayuwa zatai ta zuwa mata da kalu bali ? bata fita acikin wani kalu balin ba ta sake shiga wani .



 wai meye haka ne ? yayi mgnr cikin muryarsa mai tsananin kashe sansar jiki ,shiru tayi taki yin magana sai kwalla take zubarwa a natse ya cigaba da magana cikin kasalalliyar murya  idan baki daina kukan nan ba zan tafi na barki kuma bazaki sake ganina acikin sauki ba  wai ya kake son nayi da rayuwata ? .dole fa na damu tayi maganar wasu hawaye na zubo mata  okay shikenan ki cigaba da kukan idan zai miki maganin matsalarki ni zan wuce  .yana gama fad ar haka taga ya zareta ajikinsa ya zaro wasu document abayan aljihunsa ya kamo hannunta ya damkasu ciki  takardun gidansu umma ne zan so su tare acikinsa kafin qarshen satin nan amamn bazan masu dole ba duk lokacin da suka shirya ki min magana zan turo a d aukesu ya k arasa maganar tare da juyawa yana taku cikin isa da nuna rashin damuwa da abinda ya faru . bayansa tabi da kallo tana jin kamar tace masa ya dawo kar ya tafi dan tasan halinsa tunda ya furta idan ya wuce bazata sake ganinsa cikin sauki ba tasan haka ne zai faru ,mutumin daya kauracewa mahaifiyarsa ai kowa ma zai iya kauracewa ba damuwa zai yi ba ,tana tsaye cikin tsananin damuwa da fad uwar gaba har sai data daina ganinsa  .



bata iya cigaba da aikinta ba ta dafe goshinta da document din daya damk amata tana adduar Allah yasa mahaifiyarsa bataji hirarsu ba domin ita shine damuwarta ba kauracewarsa ba . ahankali ta koma ta jigina jikinta da bango wajen tana rike da kugunta da hannu d aya still rike da takardar yayinda d ayan hannun ta jefa shi acikin bakinta tana ciza wa alamun tunani ,a nan umma tazo ta sameta duk ta firgice  Ina adamun yake ko ya wuce ne ?da sauri maryama ta dawo haiyacinta tana d auke hawayenta tare da d an tsotsa kanta tace eh umma ya wuce amman yace zai dawo zuwa anjima . ta tsinci kanta da girbawa umma karya  kai Alhamdulillah wallahi ba kiji irin farinciki da naji ba dana gansa, Allah ya sani bana son mu rasa shi Ina son kema kiyi aurenki ki zauna a gidan mijinki lafiya kamar kowace mace da dadi da babu dadi kiyi hakuri bare khairan in sha allahu adamcy na matukar sonki .


 maryama ta kalli umma bata san yadda umma zataji ba a ranar da zataji cewar auren contract tayi dashi dan dole dai sai tasani idan lokacin mutuwar auren yazo  maza ki karasa aikinki kafin ya dawo ko kuma ki barshi na karasa  a a umma bari na karasa ai nama kusan gamawa yazo, maryama ta mikawa umma takardun hannunta  takardun gidan daya baku ne yace  duk lokacin da kuka shirya tarewa ayi masa magana zai turo azo a d auke ku umma ta kar ba tana washe baki ita kuma maryama ta duka domin cigaba da aikinta umma tace  kai masha Allah Allah mun gode maka da wannna niimar da kayi mana umma tayita kallon takardun tana santin gidan da bata gani ba kafin daga baya ta ajiye a gefe tasa hannu cikin d ayan bucket din tana d auraye kaya tana shanya tana wa mryama hirar adamcy abinda ta lura dashi tun da batun auren nan ya taso umma bada da wata hira sai tashi bini bini tace adamcy kaza ko ranar auren kaza zatayi atare suka k arasa aikin maryama ta d auraye bucket din da tai amafani dasu suka shige ciki sai dai ita kam duk arikice take bata da wani kuzuri .



Maryama tana zaune cikin zullumi sai ga subai a ta kawo mata ziyara  cike da murna ta tarbeta suka rungume juna maryama tace  subai a kinga yadda kika dawo kuwa ?ya na dawo  kin yi kiba kinyi kyau ,ke baki ga yadda kikayi fresh ba ? maryama ta harareta tana nuna mata wajen zama  ana kai ina ke ta kaya Allah dai ya rufa asiri kawai  inji cewar maryama ,ki zauna bari naje na kawo miki ruwa subai a ta samu waje ta zauna tana tambayr maryama umma daga inda take tsaye gaban fridge tace  tana cikin d akinta tana lazimi ,ta dawo hannunta rike da ruwa da lemu ta ajiye mata kana ta zauna suka fara hira k awata kisan abinda ya kawoni? maryama ta girgiza mata Kai  tun bayan da aka ganki nayita son nazo muyi magana akan batun aurenki da alhji mansor sai dai ban samu time ba saboda yanayin aikinmu to jiya na d auki hutu saboda Ina son zan biya kudin zuwa umara cikin wannnn sati  tun kafin ta gama magana maryama ta fad a da fuskarta da murmushin farinciki tana riko hannun subai a cikin nata  Kai masa Allah subai a na tayaki murna Allah yasa ayi ibada kar babbiya tace ameen k awata na gode shine nace nazo naji ya ake ciki idan har zan iya zuwa naje na dawo na sani duk dai sati biyu ne kawai zanyi  .



 kiyi tafiyar ki subai a dan tuni an fasa wannan auren subai a ta zaro ido waje tana cewa  me yasa aka fasa kuma matsalar daga Ina ce ?to wannan Karon dai matsalar daga wajena ce Allah dai ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi arayuwarmu . Ikon Allah amamn mai yasa zaki fasa aurensa maryama a inda yanzu maza suke wuyar samu ko dan kinga kina da saurin samu ne yasa kika fasa ? Sam ba haka bane subai a wata matsala ce ta taso  wace matsala ce ki fad a min ko akwai shawarar da zan baki?wannnan matsalar bazata fad u ba subai a domin fad ar sa kamar sake jefa kaina cikin damuwa ne ni dai idan kinje umara kiyi min addua sosai dan Ina bukace da addua wallahi  ai shikenan daman sai da nayi tunanin bazaki fada min ba kina nan dai da wannna zurfin cikin naki addua kuma in sha allahu zan miki  maryama tai murmushi  tace na gode .


 K awata nima fa Ina da damuwa kusan ma abinda yasa zanje umara kenan akwai wanda na kamu da son shi a wajen aiki sai dai wallahi bazan iya fad a masa cewar Ina son shi ba amman wallahi ina mutuwar son shi zanje na roki Allah idan har alkhairi ne agareni Allah ya bani shi cikin sauki idan babu alkhairi Allah ya musanyamun da wanda yafi shi .
 kai subai a mutun bai ce yana sonki ba kawai sai ki kamu da son shi ? wallahi maryama jarabawar data same ni kenan mutumin ya had u sosai sai dai ayi min nisa da yawa dan ko gaisuwata ma da kyar yake amsawa  fad a min waye shi a wajen aikin ? bazan fad a miki ba domin nasan muddin kikasani zaki shigar da kanki wajen nemo min abinda nake mutuwar so dan nasan muddin kika shiga ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login