Showing 81001 words to 84000 words out of 151781 words

Chapter 28 - Mar'adams Book 4 Complete Hausa Novel

Unknown   

29 Sep 2025

2680

gabanki dan zamu iya aikata komai domin babu abinda muke bukata daga gareki face ki fita arayuwar adamcy kuma acikin d'an lokacin nan kinji ko baki ji ba ?"ahankali ta gyad'a mata kai tace "naji ".

"Kin samawa kanki lafiya !"inji cewar aunty shahida ai bazata bar gidan? nan ba sai na wankewa shegiya mara dan kar bayan ta tafi abiyo mu da bakar yad'iya" good! inji cewar aunty khadija tun yanzu ki fara had'a kayanki ki ajiye abakin kofa dan nan yafi dacewa dake zagi kam babu wanda basu mata ba da gargadi da dunguri kafin kace me tunin yanayinta ya sauya idanunwanta sunyi tulu tulu sannan suka kama hanaya suka wuce ."ahankali ta zauna dafe da kuncinta hawaye na zubo mata tunanin take ta Ina zata fara"? bayan taci kukanta ta koshi ta zuba tagumi tana tunanin mafuta dan dole ta nemawa kanta mafuta kafin su illata mata rayuwa "jajurcewa zama dashi zatayi? ko kuma rabuwa dashi?tambayar data jefawa kyakkwan kwakwaluwarta kenan" tafiyar ki? itace mafi alkhairi arayuwarki kwakwaluwarta ta bata amsar tambayar data aika mata ."

Tana nan zaune har adamcy ya dawo? kallo d'aya yayi mata ya fahimci akwai abinda ke damunta ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sunbatarta yana tamabayarta, tace babu komai "yasan abinda zata fad'a kenan dan haka ya zareta ajikinsa? ya tsura wa fuskarta ido yana karewa fuskarta kallo gabad'aya ta canza har cikin kwayar idanunta kukan me kikayi ?" tayi shiru wani abu aka miki?"ya sake tambayarta still dai shiru tayi idanunta na cika da kwalla "shiru yayi kafin ahankali yace "su wa? suka shigo da bana nan ?shiru tayi tana tunanin abinda zata fad'a masa "su khadija sun zo ne? "kai tsaye ta? fashe masa da kuka tare da had'e hannuwanta duka rokonsa take son yi ya sauwake mata sai dai ta kasa sarrafa harshenta dan tana mutuwar son shi haka zalika tana son rayuwar iyayenta da ace matsalar a iya kanta zata tsaya da babu abinda zai hana bata sadaukar masa da rayuwarta ba tana kallonsa ya ciro wayarsa yana duba cameroring gidan daya saita a wayarsa."

Wani irin tsareta yayi da idanunshi yana kallon fuskarta ji yayi kamar alokcin khadija tai mata marin ,nan take kwayar idanunshi suka canza zuciyarsa ta dinga tuttukin bakinciki .yadda ya tsareta da idanunshi yayi matukar bata tsoro shi kuwa kallonta ya cigaba da yi yana jin zallar bakin ciki na ratsa shi ,bazai iya cigaba da danne? wannan matsalar ba gara ayita ta kare dan bazai d'auki cima iyalinsa zarafi ko barazana ba? wata irin zabura taga yayi ya mike tsaye tai saurin riko hannunsa jikinta na rawa "Ina kuma zaka ?wani kallo yayi mata mai firgitarwa wanda yasa ta sakar masa hannu da sauri ."fuuuuuu ya fice? daga d'akin ta yunkura da kyar ta biyo bayansa sai dai a parlour'n ta tsaya tana Kai kawo ."kai tsaye d'akin da hajiya zulfa'u take ya shiga yana wani irin huci ya isketa tana zuge zip din akwatinta yanayin yadda ta gansa yasa tace lafiya? ?"Ina son ki bar tafiyar nan a yau ?meke faruwa ka fa san tun jiya ya kamata na wuce ?ta? kallesa tana neman karin bayani "nasani akwai gagarumar matsalar dake faruwa? acikin gidan nan "subhanallah !"Allah ya rabamu da matsala "matsalar? akansu shahida da khadija kuma Ina son ayi maganar kina nan idan ba haka ba zanyi abinda ran kowa zai 'baci koma ya raba zumunci gabad'aya ba damuwata bace ,daman ni tuni na cire kaina acikinsu ".

 wannan wace iri magana ce haka adamcy "?ka dinga hakuri da yan'uwanka batare da bata lokaci ba? ya karanto mata duk abinda ke faru wa tun daga farko har zuwa yau din nan " karka? zargi yanu wanka adamcy "aunty ba zargi bane gaskiyar da nake ta k'ok'arin boye? ce akansu , Ina ruwansu da rayuwata ?"maryama zabina ce kuma duk duniya babu wanda ya isa yasa na rabu daita Allah ne kawai zai rabamu na hakura amman ba mutun ba" kalli kiga irin mummunar wulakanci da khadija sukai mata"ya fad'a jikinsa na kyarma ya fito da wayarsa ya nuna mata marin da khadija ta zabgawa maryama hajiya zulfa'u tace "Kai gaskiya basu kyauta ba". baiwarsu ce ko dan sun ga bata da hayaniya ?na rantse da Allah bazan yarda ba ".kayi hakuri lallai basu kyauta ba amman ka bari abi komai ahankali ai kamar ma basu wuce ba jirani bari naje na dubosu ayiwa tufka hanci "ta fita har da saurinta kasa cigaba da jiranta yayi ya biyota aiko suna nan zaune tare da mami suna zantawa suka ga sun shigo kamar an jehosu ."

wani irin mummunar kallo yake binsu dashi wanda yasa suka ji mummunar fad'uwar gaba mami ta kalli hajiya zulfa'u a tsanake sannan ta kalli adamcy dake tsaye yana huci kamar wani zaki ,hajiya zulfa'u tace "aunty ko zaki d'an bamu guri zanyi magana dasu shahida, mami ta mike tsaye ta shige bedroom dinta sai dai ta kasa kunnenta taji tautaunawar akan me ye inda hajiya zulfa'u ta zauna tana dubansu d'aya bayan d'aya kafin ahankali ta soma magana "khadija shahida me yasa zakuyiwa d'anuwanku haka ?" "me yasa zaku dinga cutar dashi a boye har kullum Ina fad'a maku matsayinsa da martabansa ya zarta na maryam a wajenku uwa d'aya uba d'aya fa ya wuce wasa "yanzu wani irin cutarwa yace anyi masa "?hajiya zulfa'u ta soma bayani kamar yadda adamcy ya koro mata "tana dasa aya aunty khadija tace "tabbas babu karya akan haka aka kulla aure kuma shi bai isa yasa mu janye kudirinmu ba ,mari kuma ta dinga shansa kenan muddin tana cikin gidan nan "Acikinku duk wanda ya sake? marinta zan d'auki mataki kuma banga uban daya isa ya hana ba ta yunkura ta mike tsaye tana dubansa "yanzu ma ka d'auki mataki akan wanda nayi ma"...ai bata gama rufe bakinta ba ya sauke mata mari biyu ajere ."

Mmn sudais

=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?
? ?? MAR'ADAMS
? ?? =ؖ?=ؖ?=ؖ?=ؖ?
=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?=ؗ?

BOOK 4

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


? ? ? ? ?? Page 18

"Wani razanannen kara aunty khadija ta saki tare da kurma ihu ta dafe kuncinta da hannu biyu saka makon kara data saki ne yasa jikin mami ya kama rawa, hakan yasa ta sake matsowa jikin kofar da sauri ta tsaya gabanta na wani irin fad'uwa,tana son fitowa amman tana jin tsoron abinda zai biyo baya dan tasan tabbas akwai abinda yake faruwa a parlour'n, cigaba da tsayu wa tayi agurin cikin tsananin tashin hankali sosai? ta kasa kunnuwanta dan so take? taji abinda ke faruwa. hajiya zulfa'u kam d'aya bayan d'aya take kallon fuskar kowannensu cike da tsananin tashin hankali. yadda aunty khadija ta dafe kuncinta tana kallon adamcy haka aunty shahida ta dafe nata kuncin tana dubansa amatukar
firgice,hajiya zulfa'u ta kai hannunta goshinta ta dafe tana mai runtse idanunta cike da matsanancin bakin ciki abinda adamcy ya aikata."shi kuwa gogan ko d'ar bai ji komai ajikjnsa ba sai faman huci yake yana k'arawa yana kallon fuskokinsu ."

mami dake tsaye acikin d'akinta duk ta damu tace "meke faruwa ne?"me yasa khadija tai kara haka ?" tai wa kanta tambayr da bata da mai bata amsa sai su gashi so take ta fito taji ba'asi sai dai zuciyarta ta gargad'eta akan haka dan haka ta cigaba da tsayuwa sai dai ta k'ara kasa kunnu wanta sosai domin ta jiyo abinda zasu cigaba da tautaunawa dan tana jiyo wasu hirarsu wasu kuma bata jiyo wa ."aunty shahida ta kalli idanun aunty khadija jini ta gani akwance acikisu ."cikin tsananin tashin hankali ta matso kusa da aunty khadija ta sauke hannuwanta tana duba cikin kwayar idanunta "yanzu adamcy akan waccan banzar yarinya ka mari khadija haka ?"
"karki sake ce mata banza dan ba banza bace."
a d'an rikice mami tace "Khadijar ya mara kuma akan waccan yarinyar"? ta furta cikin tsananin tashin hankali ".

"akan wannan tsinanniyar yarinyar fa ka mari khadija ,khadija fa ka mara ? "wacece ita da ba zan mareta ba !"? "wallahi adamcy ka haukace ka zama rago ka zama wawa , ace akan wannan matsiyaciyar yarinyar tsinanniya zaka mari yar'uwarka lallai adamcy an gama da kai wayyo Allah ka cire adamcy a inda yake"babu ruwanki da inda nike kuma idan an gama dani meye damuwarki "?ya fad'a yana zabga mata harara kasan Allah sai nayi mata dukan mutu wa kuma a yau din nan zata bar gidan nan dan kar shen aurenku yazo."tana gama maganar aunty khadija wacce gigita tasa ta dawo tamkar mutun mutumi a tsaye ta zube jagwab akan kujerar data tashi tare da sunkuyar da kanta kasa ta dafe cikin tsananin jimami.yayinda aunty shahida ta juya da sauri zata nufi hanyar fita da zumar zuwa ta samu maryama taci uwarta ,adamcy yayi saurin riko tsintsiyar hannunta cikin zafin rai yana cewa"kul shahida"!tsayawa tayi shiru tana kallonsa tana tunanin abinda kalmar" kul!din daya fad'a mata yake nufi "cikin zare idanu tace "adamcy kana hauka ne ni ka rike wa hannu tare da min gargadi ?". shima cikin zare idanu yace "ba iya rike hannun kad'ai zanyi ba in dai zai ta'ba lafiyar matata to zan iya ciresa gabad'aya in yi wurgi dashi ".ya k'arasa maganar da karfi tare da sakin hannunta yana huci kamar zaki ."wani irin asirtaccen murmushi aunty shahida tayi tare da kallonsa "ai ko zaka ga abinda zai biyo bayan wannan rashin mutunci da kayi mana"karki sake ki aikata abinda zakiyi dana sani sannan kina maganar maryama zata bar gidan nan akan wani dalili kenan zata bar gidan nan"?.ya fad'a yana kafeta da tsumammun idanunshi da suka gama canza kala tsabar 'bacin ran da yake ciki "."

"Kasan Allah bazaka cigaba da zama da yarinyar nan ba ko zaka mutu sai ka saketa"ke kanki kinsa ko sweetheart bata isa ta hanani son abinda zuciyata take so ba bare ku, ban aurin maryama dan na rabu daita ba, kuma bana tunanin akwai abinda zai sa na saketa sai dai mutuwa ta rabani daita amman muddin Ina numfashi a doron duniya Ina tare daita ."ware idanunta tayi sosai akanshi tana cigaba da kallonsa alokcin da mami ta gaji da tsayuwa ta samu guri ta zauna dafe da kuncinta dan Allah ya sani tana son fita tasan halin da ya'yanta suke ciki sai dai hakan nan zuciyarta ke gargadinta dan gabad'aya maganganunsu akwai rud'ani da tashin hankali aciki""Wallahi wallahi!!kinji na rantse shahida bazan canza maganata ba duk wanda ya sake ta'ba min lafiyar matata acikinku sai na masa rashin mutuncin da har ya mutu bazai manta dani ba zaman laf???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?iyar mutun? ya tsaya iyakarsa ".

"idan kuma ba'a tsaya iyakar ba fa me zai faru ?"tayi maganar cikin d'aga murya da zare masa ido" "ni duk zare idanunki da ihunki ba d'aga min hankali zai yi ba illa ku sakarwa matata kuruwa"okay kuruwarta ma muka Kama "?"sosai kuwa dan kun hanata natsuwa da samun kwanciyar hankali, kuma wallahi bazan d'auka ba duk abinda zaku yi ku tsaya iya kaina "ya k'arasa maganar yana nunata da d'an yatsansa "to ko nima zaka mareni kamar yadda ka mari khadija? cikin zare idanu da matsifa yace "ba zaki gane hakan ba sai kin ta'ba lafiyar maryama zaki ga yadda zanyi daku "."enough adamcy !"ya jiyo sautin sanyayyiyar muryar hajiya zulfa'u"ya isa haka!"ta sake fad'a tana dubansu d'aya bayan d'aya ".ke shahida samu waje ki zauna ,kai ma adamcy zauna tai maganar tana nuna masa wajen zama jiki a matukar sanyaye aunty shahida ta zauna kusa da yar'uwarta tana huci,haka shima adamcy cike da jin kai da kasaita ya matso ya zauna akan kujerar da hjy zulfa'u ta nuna masa ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya, haka ma hajiya zulfa'u zama tayi tana fuskantansu kafin ahankali tai gyaran murya ."

Ahankali damcy ya kau da kanshi gefe yana cika yana batsewa cikin tsananin fushi dan baya ma son ko kallon fuskokinsu ."ahankali hajiya zulfa ta fara masu nasiha tana basu hakuri tare da bawa su aunty khadija rashin gaskiyar akan abinda suka aikata, shima kuma adamcy tace yayi gaugauwar d'aukar mataki ai khadija yayarka ce duk abinda zata wa matarka bai dace ka zabga mata mari ba,amman duk ku taru kuyi hakuri ku yafewa juna komai ya wuce ." sai dai rufe bakinta ke da wuya cikin zafin rai aunty khadija ta d'ago idanunta da sukai jajur ta soma magana cikin zafin rai "aunty banki duk abinda kika fad'a ba amman kinsan Allah zaman lafiya a gidan nan ya kare bare wani sulhu a tsakaninmu kuma sakamakon marin da yayi min shine sakin yar iskar yarinyar nan ."da sauri adamcy ya juyo cikin tsananin tashin hankali "wannan kuma karya kike yi dan babu wanda ya isa ya rabani da matata ."

"a she kuwa zaka had'u da tashin hankali kala dabam dabam dan zan nuna maka karfin ikona yadda kake kare matarka kasan nawa mijin zai iya min fiyye da haka,idan kasan wata bakasan wata ba ka jira sabuwar jaridar da zata fito cikin satin nan na rantse sai na tozartaka "ahankali ya tashi ya mike tsaye yana kallonta a wulakance bazan hanaku yin duk abinda zaku yi ba bissimillah ga fili ga mai doki "har yayi taku biyu yaji ance "adamcy dawo nan ! "muryar wacce yaji ne yasa wani irin azababben zufa ya fara tsatsafo masa a ilahirin jikinsa, ahankali jikinsa ya Kama rawa mami dake tsaye gabad'aya idanunta ta zuba masa cikin tsananin 'bacin rai ." ahankali ya juyo gabad'aya ya sauke idanunshi akanta yana kallonta da fuskarsa dake had'e dan ya rantse da Allah komai zai faru sai dai ya faru amman bazai d'auki cin zarafi ga maryamarsa ba "meke faruwa ne duk da naji wasu maganganu wasu kuma banji ba ?".

kai tsaye aunty shahida tace "khadija ya mara akan waccan yar iska kwartuwar yarinyar daya aura "wani irin wulakantaccen kallo yayi mata sai da hantar cikinta ta kad'a cikin rashin Jin tsoro yace "shahida ki saisaita kalamanki akan matata idan ba so kike na miki rashin mutunci ba "ka min shiru ana mara mutunci kawai "mami ta fad'a a fusace tana masa kallon banza " yayayyen naka kake fad'awa haka akan wata macen banza macen da a gobe ma zaka samu wacce ta fita komai ,bari kaji kullum haihu war sababbi kyankyasa ake da zaka wani damu mutane akanta ,menene ka tsinta ajikinta da babu shi ajikin sauran mata "?sarai ya fahimci inda maganar mami ta dosa kuma dan ita uwa ce kawai zai barta ta fad'a son ranta akan maryama amman acikinsu duk wanda yayi gigi zai ga rashin mutunci "nayi amai na zuba a fuskarta ko Karen gidana ka mara akanta bare ka marar min 'ya saboda baka san ciwon kanka ba,wallahi kasa na sake tsanarta akan yadda na tsaneta dan karen gidana ya fiyye min ita albarka kai adamcy am so sorry I'm so sorry for you."ta fad'a tana dafe goshinta."

"Haba aunty hakan fa ba daidai bane "kenan daidai ne shi ya d'aga hannu ya mari khadija?"Ta fad'a tana cire hannunta a goshinta ta zubawa hajiya zulfa'u idanunta "khadija ko kwanwarsa ce kinga ya dace ya mareta da aurenta bare yayarsa ce kusan shekara uku zuwa hud'u ta bashi." gasky bai kyuata ba amman kiyi hakuri dan Allah? ki koma d'aki karki saka bakinki ciki al'amarin nan kiyi shiru abunki kawai ni zanji da komai "babu inda zani sai naji dalilin da yasa ya mari khadija har yake ikirarin ita ma shahida zai mata rashin mutunci saboda shi bashi da mutunci. "ke dai nace ki wuce zan miki bayani abinda suka aikata masa "babu inda zani sannan ba zan ji bayanin komai ba har sai khadija ta tashi ta rama marin da yayi mata tukuna "to ai sune basu da gaskiya dan sun aikata masa ba daidai ba akan matarsa,kuma idan su aka yiwa haka a gidan aurensu mazajensu bazasu yarda ba ,ki koma d'aki abunki kawai dan idan kikaji abinda suka masa sai kinyi Allah wadai dasu ."

"komai ya faru kinga ya kamata ya mareta kuma akan matarsa "?khadija ta shi ki rama marinki ."
tai magnar tana bata umarni aiko take aunty khadija ta mike tsaye "hajiya zulfa'u tace a'a gaskiya bazata rama ba ta dai yi hakuri su yafi juna komai ya wuce" ta fad'a tana tsayawa a gaban adamcy wanda yake kallon mami cikin matsanancin 'bacin rai yana jiran aunty khadija ta maresa yayi mata dukan mutuwa sai dai suyi sharia da mijinta " cikin tsananin fushi mami tace "lallai zata rama marinta ko ba yau ba idan kuwa bata rama ba ni zan rama mata "naji jeki zan shigo yanzu na fad'a miki komai mami ta juya ranta a 'bace ta shige d'akinta ".haba khadija wai me yasa kuke yin haka ne ?"
"kuyi hakuri mana!"shiru sukai mata har ta gama maganarta tace adamcy ya basu hakuri "Aunty kiyi hakuri bazan iya basu hakuri ba dan bana son wani sulhu a tsakanina dasu kowa yayi rayuwarsa,suyi rayuwarsu kamar basu sani ba Nima nayi tawa da matata that's all "ko baka fad'a ba muma hakan take agaremu ko da Kai ko babu kai zamu cigaba da rayuwarmu ,sai dai ka sani bazaka ta'ba jin dadin auren yarinyar ba da kanta zata bukaci saki dan uwarta inji cewar aunty shahida,"

wani takaici da bak'in ciki tattare da b'acin rai ne suka taru suka dabaibaye zuciyarsa, alokacin da yake kallon aunty shahida ya dinga Jin wata irin tsanarsu a ransa kamar yasa hannu ya bugeta.daya ga hakan bazai samu ba ya dinga zuba mata harara tare da gintse fuskarsa har girarsa tana alamar tattarewa gefe guda yana ciza leb'ensa al'amari ne da yake nuna ya kai k'ololuwa wajen b'acin rai yace "karku fasa ni kuma zan nuna maku rashin imani "yana gama fad'ar haka ya fice daga parlour'n aunty khadija kam jinjina kai ta dinga yi dan ita kad'ai tasan abinda zata masa dan bazata fasa abinda tayi niyya ba."kai tsaye hajiya zulfa'u d'akin mami ta shiga inda ta isketa tsaye a gaban wardrobe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login