Showing 27001 words to 30000 words out of 154870 words

Chapter 10 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1145

wani na nesa da na kusa, qminan arziki dama yan uwan yan uwa du sun tatara sun koma daga gaisuwar rasuwar mahaifiyarsa,

Kanwar mahaifiyarsa da Muhammad kawai suka rage, shima Muhammad ya yi zuwa uku kasarsa ya dawo ne,

Abdul Jabar ya zana wani silent man
Askin nan da yake yi kwalkwal ya aske kai, rabonsa da shi tun kafin rasuwar mahaifiyarsa hakan ya saka suma ta fito sosai kansa, suma mai yawa mai kuma tauri tauri hakan ya saka kan ya cika da gashi irin yanda samari ke tarawa ,
Sajensa da a da yake askewa baya barin ko kadan, yanzu ya fito sosai ko.ina ya zagaye fuskarsa,
Gemunsa ya kara cika, lebensa suna da dan girma, dan ba zaka taba kiransa da mai kananun lebe ba, aman kuma ba dambatsa dambatsa bane,
Idannuwansa sun fi komai girma a fuskar tasa idan ka cire karan hancinsa mai tsini, idannuwansa jajajir suke, rabonsu da su yi haske tun a lokacin da yake tataunawa da mahaifiyarsa yana mata murmushi itama haka,

Zaune suke su su uku,
Su biyun suna dan taba hira, ba ta komai ba sai ta zaman duniya da jimamin yau da gobe wanda bai bar talaka ko mai kudi ba,

Tunda suke magangannun shi dai kansa a kasa yana sauraron su, bai ce da su komai ba, haka kuma bai hana su maganarsu ba,

A hankali ya bude bakinsa, muryarsa da ta zama wata iri mai amon irin muryar nan ta kakarfan maza ko wa.inda giya ta kashe masu zakin murya ya ce" aure nake so.

Muhammad dake magana da aunty Firdausi ya juyo da sauri yana kallon Abduk Jabar,
Itama auntyn hankalinta ta maido kansa,

Dago da idannuwansa da a yanzu in dai ba dole ba , mutun ba zai so su kurewa juna kallo ba, ya sauke saman kansu,
Lebensa na kasa ya kamo da harshensa ya shiga dan tsotsa yana kallonsu bai ce da su komai ba,

Kai aunty ta kawar daga dubansa ta ce" Aure?

A hankali ya saki bakin nasa ya ce" eh, aunty na san kin san na yi rayuwar rashin jin magana,
To bana so na sake , dan ba zan so a tayar da mahaifiyata a nuna mata abinda nake daga kabarinta ba, kuma gashi ina son mace a kusa da ni, dan haka zan yi aure.....


Muhammad ya shiga jinjina kai yana mamakin jaraba irinta abokinsa,
Aman kuma ba laifi tunda yanzu ya nemi ya kara wani auren.....aman kuma wani abu ya tsaye masa a rai, ba irin maganar da ba.a fada masa kan ya daina harkar mata ko dan mahaifinsa idan baya tsoron sauran abubuwan, ya ji kunyar Allah, ya kuma kaucewa mahaifinsa shiga halaka ta dalilin sabon Allahn da yake,
Yakan ci gaba da shagalinsa , aman yanzu ya nuna zai fasa dan mahaifiyarsa? Me abansa ya yi masa haka? Ko dai da wata a kasa? Irin rayuwar rashin sannin ciwon kan da ya ringa tafkawa?

Dubanta ta kawo saman kansa bayan ta yi dogon nazarin maganarsa, a hankali, a nitse, da yannayi na rarashi, da neman cin galaba kan maganarta ta ce" aure ba laifi, za.a nema maka auren ko yar gidan wa kake so,
Sai dai da sharadi Abdul,....
Maganar *BODYGUARD* da mahaifiyarka har ta rasu tana fama yana nan daram bai canza ba,
Za.a je a dauko kwararun bodyguard biyar,
Daya zata baiwa matar da zaka aura tsaro.....
Hudu zasu kasance da kai idan maza kake so ko mata, a dukan motsinka,

Abdul kar ka yi min gardamar haka, dan na rantse maka da Allah sai dai ka ja na ja....idan kuwa nima so kake mu yi ta jayayar har a dauken kai da alburushin shikenan.............



Ku yi hakuri, i.m sick ne,=?
?, na gode da adu.o.inku, Allah ya saka da mafificin alkhairi
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 2??

Tsura mata ido ya yi, yana gannin mugun kamanin mahaifiyarsa a tatare da ita,
Tunda aka yi rasuwar suke nan ita da yarta kwal da ta malaka a duniya mai sunna Ni.ima wace ta bi ta makalkalewa du wani motsinsa,
Tabas shi ba zai ce ga halayen matar ba, aman ta kasance mai fatan alkhairi a gare shi,
Bai wani yi zama na sosai da ita ba, tunda du yawancin zamansa a saudiya ne, sai idan mahaifinsa ya tada balin maza ya zo yake zuwa ya dan yi kwanaki ya juya,

Idannuwansa ya lumshe , ba tare da yace komai ba ya mike ya fice a wajen,
Dubanta ta maida kan Muhammad kafin ta dafe goshinta ta ce" ni bana gane yarensa,

Muhammad ya yi murmushi ya ce" ai ya amince kennan, da bai amince ba, zai fada ne kwaro kwaro ....

Kanta take gyadawa sannan ta mike ta shiga ainahin dakin da suke kwana,

Kwonce ta tarar da ita tana hawaye,
Ni.ima, yarinya ce nutsatsiya, domin bata da hayaniya,
Tana da kamun kai daidai gwargwado,
Kudin mahaifinta bai saka ta zama sangartaciyar yarinya ba,
Tana da baci a gaban mahaifanta, baci irin tsaftatacen nan,
Bata da hayewa,....sannan ta iya zama inda ake da muradinta.

Tsayuwa mahaifiyarta ta yi a kanta tana dubanta,
A hankali ta ce" lamarin har ya girmama haka??

Mikewa ta yi da sauri dan bata san tana kanta ba, da kallon tambaya ta bi maman nata, kafin ta ce" wami lamari Mama?

Kanta ta girgiza ta zauna tana dubanta ta ce" bari ki ji Ni.ima, ba zan iya tirsasa yaron nan kan komai ba, ke ni inada fargabar hakanma na fada maki gaskiya, dan ko mahaifiyarsa nada rai ba zata yarda da haka da gagawa ba dan kuwa akoy kuli, mugun kulin dake tare da shi, hatsari baba,
Bayana haka, namiji ne mai zaune da ra.ayin kansa,
Ni bana tunanin Abdul zai iya yin soyaya, sai dai ya yi aure dan wata manufar....., yau da ace zai so ki, bani da damuwa a hakan, da ace zai iya rayuwar soyaya da ke , da zan fi kowa farin cikin ganninku tare,
Ki sani, Abdul rayuwar Saudiya ya yi,
Mata na bibiyarsa, sun saka shi daukan kansa tamkar wani sarki,
Baya iya bautawa mace da zuciyarsa idan dai ba kamuwa ya yi da sonta ba, yana iya rayuwa da mace dan kawai ta zama abin marmarinsa, Abdul, atajirin saudiya ne, dan jin dadinsa yana iya kashe ko nawa ne, aman kuma zuciyarsa daban...

Gaba daya ta tsure, duda ta sha mamakin irin yanda mamanta ta gane halin da zuciyarta ke ciki, sai dai tashin hankalin abinda ta fada ya hana mamakin yin wani tasiri a tare da ita,

Kanta ta dago ta saukewa maman nata kallo tamkar marainiya,
A hankali ta sauko kafafuwanta ta dora kanta saman kafar maman nata cikin shashekar kuka ta ce " mama, ni ban ce sai ya so ni ba, ni ina son sa, ba damuwana bane dan ana kashe matansa, lokacinau ne ya yi, mama , in dai zai bani gurbi a rayuwarsa, zan zauna da shi....

Sai da gabanta ya tsinke dan tarin tausayin yar tata, sai dai ba zata taba kaiwa dan yar uwar tata tayin auren Ni.ima ba, koda kuwa zata mutu ne!

Ranar ba zata

Suna tsaka da cin abincin dare, bayan kwana uku da maganarsa da kanwar mahaifiyarsa, mijinta ya yi kiranta cewa yanzu jirgi ya sauke shi garin, gashinan zuwa gidan,

Kallonta ta kai wajen Abdul, ta ce" Abdul, aban Ni.ima ne ke tafe wai yanzun, ko lafia?

Abdul da tunda ya zauna a dinning din bisa tursasawar auntyn tasa, yake dan surbar jus din kankana da aka yi ya gyada kansa ba tare da yace komai ba,

Kanta ta girgiza kawai, ta ci gaba da cin abincin tana aikawa Ni.ima hararar irin yanda take kure shi da kallo bama ta tsoron ya ankara da ita ya yaba mata maganar da zata kwana tana kuka!

A lokacin da ya zo sai da Muhammad ya fita sannan ya samu shigowa, duda kuwa powernsa na kasancewa baban sojan da ake ji da shi, aman yana zuwa wajen sai suka hane ahi shiga,
Da yake bakin aikinsu suke, shima sai bai wani ja ba, ya tabo mai gidansu ya zo ya saka shi,

Yana zuwa matarsa da yarsa suka mike suka rungume ahi cike da farin ciki,

Aa haka ya lakaci hancin Ni.ima ya ce" auta, wato ke kin zo kennan ko? Shikennan daga nan ma ai bama zamu koma da ke ba,

Da mamaki suke masa kallon tambaya kan abinda ya ce,
Bai yi kasa da gwuiwa ba , ya basu labarin da ya basu matukar mamaki,

Da sauri mahaifiyar ni.imar ta kai dubanta wajensa, hankalinsa na kansu shima, so yake su gama gaisawar ya gaishe da mutumen aman sun kasa sakinsa,
Kaunar dake tsakannin famillyn ya tsaya kallo cike da tuno abubuwan da suka faru a da,
Shi bai san kauna irin wannan tsakaninsa da mahaifinsa ba, aman mahaifiyarsa da girmansa da komai kulun cikin kula da lamarinsa da bibiyar lamarinsa take, har hakan ya siyo rayuwarta,

Aman Elhaj, yaushe aka yi haka? Ni nan bai fada min maganar nan ba, aman ta yaya haka zai faru?

A hankali ya mike ya karasa inda suke tsaye su duka,
Hannunsa ya baiwa Elhajin suka gaisa domin shi ya fara bashi,
Cikin nutsuwa ya ce" to yanzu dai bani da mama bale baba,
Ke ce kika rage min, shi kuwa mijinki ne , kin ga shi ne babana,
Na yi kiransa na fada masa muradina dan na san mata basa zuwa neman aure, a zagaya a zagayo dai shi zai nema min auren koma wacece, idan ita ta nuna bata iya zama da ni .....fine, sai a nemo min na wata,

Yana gama fadar haka ya juya ya nufi dakinsa,
Daga elhaj, da aunty, da Ni.ima, da Muhammad gaba daya binsa suka yi da kallo,

Aunty ta juya ta koma wajen table din cin abincin ta zauna,

Jiki sabule suka bi bayanta, ciki kuwa harda Muhammad dake son tausar su,

Yannayinta na nuna tsantsar damuwa ta dube su gaba dayansu ta ce" ba zan yarda da irin wannan rayuwar rashin incin da take son saka kanta a ciki ba,

Wannan wani irin bahagumen rayuwa ce?

So fa ba hauka bane,
Ke yaushema aka haife ki? Baki tafasa bama bale ki kone, ki rufawa kanki asiri da Abdul, kin ga irinta ko? Har ya fahimci kina sonsa, gashi tun ba.a je ko.ina ba yace idan mahaifinki ya taso ya zo, kuma ya ce idan za.a bashi fine idan ba za.a bashi ba kuma ba laifi yana da kudi ya tara ya san ko dan yan canjinsa ba za.a hana shi auren ko yar gidan waye ba, tabas ina cike da tausayin rayuwar dan yar uwata uwa daya uba daya, aman baya bani damar na fuskanci waye shi bale har a nema masa sanyin rayuwa,

Elhaj dake kallonta ya zauna da kyau saman kujera,
Tabas shima irin yanda ya nuna a bashi ko kar a bashi ba damuwarsa bane ya taba ransa, aman yana yi masa uzuri da yannayin kadaicin da ya tsinci kansa , duba da irin shakuwar da ya yi da mahaifiyarsa,

Murya tausashe ya ce" uzuri ya dace mu yi masa,
Wannan rashi na lokaci daya na iya taba wasu lamuran da suka danganci dangantakarsa da mu.amalarsa da mutane,
Ki yi hakuri Fannata,

Elhaj, ba maganar rashi bane, halayen abdul ne, tunda har ya nuna idan ba.a bashi Ni.ima ba wata damuwa ba a barshi kawai, ya nemo watan ya aura,

Wato kin nuna son kanki? Ke ki kilace taki ki shige gaba a kawo yar wani ko me kike nufi? Elhaj ya fada yana mai dan nuna jayayar ta ishe shi haka,
Kafin ya kara tausasa muryarsa, du dan kar a kauce hanya ko a bata zumunci ya ce" ba tashi zamu bi ba,
Zamu yi masa uzuri, kuma ni da ya kiraye ni ya nunan na zo a yi maganar aurensa da Ni.ima, koda baya sonta, shi ya nemi aurenta, koda ya lura da tana sonsa kamar yanda kika fada , shi ya nemi aurenta ba tirsasa shi aka yi ba,

Dubansa ya maida wajen Ni.ima dake zaune hankalinta tashe sai bin iyayen nata da kallo take ya ce" ke auta, kina son sa ko bakya son sa?

Da sauri ta kai dubanta wajen mahaifiyarta,
Da sada kanta inda gabanta ke dokawa ta kasa magana sai jikinta da ya kwashi rawa,

Muhammad ya kara matsawa a hankali ya ce" mama, Baba...., dan Allah, ina mai rokar masa yafiya,
Tabas yana da murdadan hali, sai dai wannan lamari da ya riske shi ya kara taurara abubuwa da dama a tare da shi,
Ko ba komai dai Ni.ima yar uwarsa ce, ba zai wulakanta ta ba,
Dan Allah, ku yi hakuri idan da dama a yin...

Ajiyar zuciya kawai Aunty ke saukewa, bata da ta cewa, domin Ni.ima bata nuna bata son Abdul ba, saima wani kallon munafurci da take na tsoro, ba laifi, ba ita tace zata iya ba? Ta iya!

Mikewa ta yi ta nufi dakinta ranta na suya,

Elhaj kuwa hakan da ta yi ya bashi kunya, domin koda Muhammad na yaro a shekaru, baban mutun ne mai daraja, idanma abinta zata yi , ta yi iya su mana? Ya zata nuna hali irin haka?
Dan haka ya sakarwa Muhammad murmushi ya ce" ka yi hakuri, ka san wani lokacin cikin jinsin maza da mata , idan rai ya tabu, muna kawar da mahinmanci abu, mu dauki abinda zuciya ta yanke, in sha Allah za.a daura aurennan a gobe sannan ku shirya daga wajen daurin auren zamu dawo mu dauke su mu je dauko *BODYGUARDS* din, domin kuwa komai matsayina sai na taka da kaina zan iya daukan su.

tana shiga dakin nata ta zauna bakin gado tana mai jin haushin wannan abu, ta kai ruwa , ta kai mari, ta rasa yaya zata yi, dan haka ta budewa mijinta daki da ya hauro inda take, nan yake shaida mata ya bada kudin sadakinsa za.a daura aurensa da safe!

Wannan shi ne tabatuwar Ni.ima a matsayin Matar Abdul Jabar ta shida............
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 3??



Yannayin shigarsa , ba zai tabatar maka da shi din ko wanene ba koda kuwa ka saba gannin jalabiyoyi masu tsada,
A yau , ranar da aka daura aurensa, suka dauki hanyar zuwa dauko mutanen da zasu kasance masu basu tsaro, cikin tawagarsu, da mutanen Muhammad amininsa, da mutanen Elhaj, da auntynsa da amaryar tasa kanta wace ta sha abaya sai walwali take goshin amare na kara haskata, sai shi,
Jalabiya mai shigen milk ce ya saka,
Bai wani gyara kasumbar da ya ajiye ba, tana nan yanda take, saima kara cajeta da ya yi ya dora hirami saman kansa,
Sai takalmi da ya zura mai shige da silifas inda Muhammad ya sha farar shada ta karbe shi sai annuri yake bazawa tamkar shi ne angon,
Dubansa ya yi a lokacin da ya gama shirin ya ce da shi" daurin aurenka ne zamu je fa Abdul?

Abdul ya dage girarsa guda yana dubansa sannan ya ce" na *Shida* ba, ina cike da zumudin ku gama jana a kasa ku bani macen ta sakar min mara!

Kansa kawai ya girgiza, domin kuwa lamarij na abdul tamkar wanda akaiwa asirin da mace? Baya iya boye bukatuwarsa da harkar mace ko a gaban waye, wannan abin ba da shi aka haife shi ba, domin ya san shi ba yau ba, sun yi karatu tare sun yi yawo tar, wannan lamari ya same shi ne daga baya, yana mai binsa da kyakyawar adu.a......yana mai cike da tausayin Ni.ima da ya fahimci irin yanda take rawar kai da murnar samunsa a matsayin miji, bai san yaya zata iya da tashin hankalin jarabar mijin nata ba bale idan suka daga baki daya suka kara yin nesa da iyayenta, wato suka juya saudiya


GN ne da kansa ya laya Bodyguard din da yake ji da su maza da matan biyu rak dake iya tafia, domin kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login