Showing 84001 words to 87000 words out of 154870 words

Chapter 29 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1134

3?? 7??



*DUNIYA, ABAR TSORO CE, KANA TAFE KANA YIWA KANKA MAKIYA A LOKACIN DA KAI KANKA BAKA SANI BA, FATAN RABIH YA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIA=?O?




A wannan rana Sun wuni tare da Malan da Abdul, dan kuwa sallah kawai ke fitar da su, sun tatauna sosai, hankali malan ya kwonta ya kuma fada kan adu.ar Allah ya kubutar da ita,
A haka suka yi masa salama da yama suka kama hanyar garin Minna


Tun da ta ji motsin an shigo dakin ta yi tsai tana sauraro
kamar yanda aka saba aka so aka bude wajen da zata ci abinci aka saka mata mesa aka dudura mata abincin da sam babu dadin dandano sannan aka barta aka rufe mata bakin aka fita

Idannuwanta dake rufe cikin bakin kyale ta lunshe wasu irin hawaye suka bi tsuman suka jika, nan ta shiga buga hanci dan kuwa muguwar mura ke damunta na irin azabar da ake gana mata

Mamake take, irin yanda ba.a fita da ita a mota ba an fai ja ta an yi tafia mai nisa da ita a lokacin da aka rufe mata idannuwanta da bakinta aka kuma daureta aka durfafi wajen da ba zata ce ko ina ne ba aka kawota aka daureta saman kujera ake gana mata azaba kala daban daban dan kuwa namiji daya ne ke azabatar da ita sai ta fadi inda ta saka wayar da ta hada da computernta take sharing du wasu informations dan kuwa wannan dalikin kawai ya hana a kawar da ita aman mirsisi ta ki fadi, du ta fice a hayacinta ta zama wata iri sai karbar azaba take ko abinci sau daya ake bata wani irin damun da bata san ko meye ba a bata ba wani da yawa ba shikennan sai kuma gobe, ta yi ta yi ta kwonce daurin da sukai mata aman ta kasa san ba komai a jikinta wanda zai saka ta iya kwoncewar, so take a mayar da ita azabar tsoma kanta a cikin ruwan da aka yi ko zata samu ta damki wani abin da zai bata damar kubuta

Tarin tashin hankalinta shi ne
Bayan masu son ran Abdul ma tare da shi, tayi imanin kuma *A CIKIN GIDANSA NE AKA DAURETA* dan kuwa ta ina za.a bi a fita da ita a irin mugun tsaron da gidan ke samu? Idan sun jirge camera ai ba zasu jirge sojoji da su BS ba, ba zai yiwu duda dare ne a fita da ita a kafa a yi nisa da ita ba, in dai an fitan da ita to fah ana kusa!
Kai, irin girma da lungu lungu sako sakon gidan nan, ta fara tunanin ko dakin horon Abdul ne?

Motsin da ta ji an buda dakin da wani irin karfi ya saka gabanta yankewa ya fadi

Muryar da ta ji sama sama ana fadin magana kamar haka" *banzan sonta yake! Sonta yake, kuma ya iya fita da bada sau! Ka san irin yanda yake da mugun naci a kan abu, ina jin wannan yarinyar idan muka kasheta mun idasa tunzura shi! Damuwarta ya hana shi bin matan da wadincan sakarkarun suka hada shi da shi fa? Dan haka ka bude mani idonta idan har bata fada min a inda ta saka wayar nan na harbe banza a kai masa dakinsa a ajiye masa ya dawo daga inda ya je din ya tarar da gawarta mu ga abinda zai yi* !


Das das das das das shi ne abinda gaban Hafsat ke yi,

Wani irin mugun tausayin Abdul, da tata rayuwar ne suka kamata,
Shikenan,
Shi ne abinda ta iya fadawa zuciyarta

A hankali ta shiga neman taimakon Allah har ta ji an kama abin bakinta an vire shi da mugunta hakan ua sakata jin wani irin zafi

Bata gama jin zafin ba aka cire abin da ya rufe idannuwanta
Tar hasken wajen ya sakata saurin rufe idannuwanta dan wani irin dukanta abin ya yi a idannuwanta

A hankali ta ringa buda idannuwanta tana gannin dishi dishi da kumburariyar fuskarta har ta idasa buda idannuwanta saman fuskarsa

Ido cikin ido suke kallon junna, a hankali ta buda baki ta ce" *WHY? WHY? Kai ne wanda ya fi kowa kusanci da shi, kai ne wanda ya fi kowa sannin sirrin sa, kai ne wanda ke yi masa fada kan ya bar desir na vengeance ku juya gida, kai ne wanda a duk lokacin da aka kawo masa hari ka fi kowa rikicewa da shiga tashin hankali, aman ka san kai ne ka shaka masa abu da kanka a wajen auren yar gidan aminin mahaifinsa? Bashi da baban abokin shawara sama da kai, ka kasance mai yi masa fada a kan banzan burin daukan fansa da nacin zama a wajen da ake son gannin bayansa! ME YA AIKATA DA GIRMA DA KUMA ZAFI HAKA DA HAR KA ZABI ZAMA MAKUSANCINSA MAFI KUSANCI SANNAN MAKIYINSA MAFI GIRMA A DORON KASA? KA MIN ALFARMAR SANAR DA NI WANNAN DALILI NAKA KAFIN KA KASHE NI=?O?

Gashin kansa ya shafa cike da dumbin mamakin yanda aka yi a kankanin lokaci, kwanakin da basu fi wata uku ba yarinyar karama ta shigo ta gane abubuwan da sauran mutanen basu gane ba, wato cewar banda bin bayan Abdul na son kashe shi da yake shi ne ya kashe mahaifiyarsa da hannunsa, ya kuma saka aka kashe kanwarsa? Kai wannan yarinyar dole a yau a yanzu ya kasheta dan kuwa yana gannin take takensa da dukan jama.ar dake tare da shi, a kowani lokaci suna iya gane wanda ke saka su a rudun rayuwa su kashe shi kafin shi ya kashe shi!


Kafarsa ya dora daya saman abin kujerar yana kallonta ya ce" dalilinsa hukuncin sare kai ya hau budurwata wace tun da aka haifeta nake son ta tamkar raina, ina ji ina gani ta afka soyayarsa a lokacin da muka tasa dan ya fito a matsayin zakaran da ya zarce kowa ya ci aikin baban bodyguard na kasar *SAUDIYA*

Mun kasance mun fi karfin a kiraye mu aminai , sai dai yan uwa
Ni ke zuwa gidansu hutu a lokacin da ya je aikin da take takamar shi rikeken dan bincike da kuma gane mai laifi ne,

Tabas na san dukan abubuwan dake faruwa tsakanin mahaifinsa da yar da ya haifa, na kuma san du wani shirye shiryen uban ,

Mahaifinsa ya dauke ni kamar yanda ya dauke shi, dan kuwa har shi kansa bai san ainahin waye ni ba , bai kuma san na yi alkawarin karar da danginsa ba!

*Hasina* ta kasance mai son bakin namiji jarumi dan kuwa muguwar harija ce a tana kananun shekarunta ma na san da haka dan wani lokacin sai na taimaka mata nake samun lafiarta,
Tun da ta yada ido ta ga Abdul, ta shiga tarda shi ni tana kewaye ni,

Abin ya zama jaraba ta tsane ni tamkar ranta, shi kuwa ya tsane ta tamkar mutuwarsa!

Takan tarda shi du inda ta san zai je, ya wulakanta ta ko a gaban waye ya taketa ya yi tafiarsa,
Gana da kanai ciki akoy wace sak irin halayanta ne da ita dan kuwa itama nunawa ta yi tana son sa,

A lokacin shi harkar mata bata gabansa, ni kuwa ina bibiyar kanwarsa jira kawai nake ya yarda ya so Hasina ni kuwa na bi kanwarsa dan kuwa cikin ma.aikatan gidan na samu mai bin mani du wani motsinta

Ke bara na takaice maki, dan ya kori Hasina sai ya fara kula kanwarta a lokacin ya dawo ya zama cikeken sojan boye, yana shirye shiryen zuwa gida wajen iyayensa wani lokaci aka wayi gari Hasina ta Kashe kanwarta da hannunta , binciken da ya yi ya gano ita ce ya fakasata aka kawot tsakiyar gari aka gile kan Hasina ina tsaye ina kuka ina magiya ina kallo ya gurgura gangar jikinta ta fadi gefe

Daga wannan ranar na zama makiyin Abdallah, ke ko raina zai shiga sai na ga Abdallah na kukan jini yana magiyar a yi hakuri a kashe shi dalilin bakin cikin rayuwar da yake gani kala daban daban kafin na kashe shi da hanuna

Hafsat kyam shi take kallo, kafin ta ce" *tabas, mutuwarsa zata fi zuwan masa da sauki da jin mumunan labarin cewa kai MUHAMMAD kai ne bakin kumurcin dake bibiyar rayuwarsa cikin innuwa yana kasara shi, na baka albishir din a lokacin da zai san da hak, abinda zai hana zuciyarsa bugawa to fa lale baban abu ne mai girman sauran kwanakinsa a duniya, kuma tabas na yarda da maganar cewA......makashinka yana tare da kai, ko ba komai na gane cewa duniya sai Allah*

Irin yanda take hawaye yake kallo kafin ya yi wata yar karamar dariya yana kallonta ya ce" na kasa gane shin son ki ne ya saka shi a wannan halin ko shakuwar ce da yake fada? Dan kuwa a yanzu ina cikin tsakiyar abu biyu, ban taba gannin ya yi rikicewar da ya yi sai da na dauke ki! Shi kashe ki zai idasa haukata shi ko kuwa cire maki kayan jikinki nake, na mayar da ke matata na tsayin wata guda, gefe guda shi kuwa ina kara tunzura shi, sai na maki ciki , cikin ya fara fitowa sannan na cire maki kai na dora masa a kofar dakinsa a lokacin da zai fito ya yi tozali da ke? Kin ga an yi dai dai,
Taya ni gannin shawarar da ta fi dacewa?

Ido Hafsat ta rintse tana adu.a a cikin zuciyar, ba wata adu.a take ba sai rokon Allah kan kar Allah ya bashi damar taba jikinta da mugun nufinsa,

A firgice ta buda idannuwanta sanadiyar jin ya.......





Comment comment commetn=?-?=?-?=?-?=?-?=?-?=?-?=?-?=?-?
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 8??




Wani irin shake gashin kanta dake baje ne ya yi, hakan ya sakata buda idannuwanta ba shiri sai kuma ta mayar ta rintse,
Walahi da za.a tona zuciyarta da an ga rubutacen abu cewa taba fatar jikinta da ya yi a yanzu ya fi mata ciwo fiye da azabar dukan da yake gana mata,

Murya na shake mata ta ce" Ta yaya zaka yi tunanin muna soyaya da shi bayan ba wani abu makamancin haka da ya taba hada ni da shi?

Kara matsa fuskarsa kusa da tata ya yi sosai sannan ya ce" irin alwashin da ya ci a kan du wanda ya dauke ki na shi ne ajalinsa da hannunsa kadai ya isa ya shaida cewa kina zuciyarsa,

A kan ya ci alwashin kake son halakani?

Yana shirin bata amsa wayarsa ta dauki ruri,

Da sauri ya rarumo abin rufe bakin ya rufe bakinta sannan ya saita kansa ya daga wayar

Yana dagawa ya ce" Abdul, ina ka je kuma? Ina ka je? Kana ina ne? Shin yaushe zaka daina tayar min da hankali idan kana fita? Yaushe zaka san ciwon abubuwan dake faruwa ka daina fitar nan da kake har sai wani abu ya same ka? Sai da na tashi na neme ka ban same ka ba shin yaya kake so hankalina ya kwonta?

Abdul ya yi murmushi ya ce" Muhammad, gani fa na dawo kai ne nake nema ban gani ba, ka yi hakuri nima kana raina, na je wani uzuri ne

Muhammad ya yi gagawar kashe wayar ya koma wajen Hafsat dake binsa da kallo , da yatsarsa ya yi mata nuni da zasu sake haduwa ne, sannan ya juya da sauri ya fice ya bar mata dakin, wanda yana fita mai tsaron nata ya dawo ya rufe mata idon ya ci gaba da gadinta

A lokacin da Muhammad ya koma ya tarar da Abdul zaune a falonsa,

Sai da ya kimtsa yannayinsa sannan ya karasa wajen Abdul fuskarsa na nuna tsantsar damuwar halin da yake ciki,

Yana zama ya kura masa ido kafin ya ce" yaushe zaka cire damuwar yarinyar nan a ranka ne? Kana abu cikin yannayin da kai kanka baka sani ba, nace da kai kaunarta kake ka kamu da son macen dake baka tsaro, wace aka bata horo irin na gardawa aman ka musa min?

Abdul ya girgiza kansa ya mika masa hannu ya ce" kai kuwa yaushe zaka daina dirowa wajen mutun ka rufe shi da fada da accusation ne? Asalamu alaika

Muhammad ya mika masa hannun da ya shaki gashin kan Hafsat sukai musabaha kafin su ci gaba da tataunawa suna musun da suka saba a haka har ya mike ya ce da shi zai je ya watsa ruwa

Da ido Muhammad ya raka shi har ya shige kafin ya bi masu bashi tsaro sai shawagi suke a wajen,

Murmushi ya yi kasa kasa sannan ya mike shima ya nufi dakinsa

A lokacin da Abdul ya shiga dakinsa tubewa ya yi ya dauki tawul ya nufi bayi da niyar yin wanka
Tsayuwa ya yi kasan shower rufa na sauka jikinsa ba tare da ya goga sabulu a jikin nasa ba,

A hankali ya kawo hannun da sukai musabaha da Muhammad da shi ya saka wajen fuskarsa yana share ruwan dake rubar masa a fuskar

Tsai ya yi da hannun, inda gabansa ya wani irin bugawa,
A hankali ya maida hannun wajen hancinsa da kyau dan kara shakar kanshin turaran gashin matan da ya shaka wanda ya tabata da turaran gashin mata ne dan kuwa a da mamansa ke anfani da shi sai kuma da ya ji shi wajen Hafsat dan kuwa irin yanda ake zama na matsewa junna waje dole a ji iskar kamshi ko warin da jikin mutun ke iya fitarwa, dan shinema ya saka GN basu kulawa dan kiyaye fitar da warin jiki

Tsai ya kurawa pampon ido kafin ya mika hannunsa ya dauko sabulu ya shiga gogawa,

Wankan ya yi ya gama ya dauro tawul ya fito ya tsaya gaban gadonsa yana kallo,
A fili ya furta" aa, Ni.ima da na shiga dakinta bata kanshinnan, hasalima ban taba jin kanta na kanshi ba sai dai abin ruwa ko kanshi kanshin man gashi hade da warin ruwa,

Tawul din ya yar ya mika hannunsa ya dauko jalabiyarsa zai saka ya kuma juyowa ya ce" aman, malan kawai na yi musabaha da shi a fitan da na yi, me zai hada hannun malan da kanshin turaran ruwa na gashin mata?

Yarfe hannunsa ya yi kafin ya kara kai hannun wajen hancinsa ya sinsina, wankan da ya yi da sabulu ya saka babu kanshin,

Dan tsaki ya ja ya shinfida salaya ya tsaftace tunaninsa ya gabatar da sallah

Yana gamawa ya shiga jan carbi yana mai kallon waje daya, ya jima yana adu.a kafin ya shafa ya mike ya cire rigar daga shi sai wandon cikin ya kwonta saman bed dinsa

Shiru ya yi yana mai jin tunanin turaran nan na dawo masa,

Mikewa ya yi ya zauna, a ransa yake ayanna bayan malan sai Muhammad da muka yi musabaha da shi,

Muhammad? Ya Salam, me ya hada Muhammad da turaran gashin mace wanda hakan na nunin ya taba gashin ne? Shin Muhammad ya saka kansa a harkar bin mata ko meye?

Saurin rintse idannuwansa ya yi, dan ba zai yarda yana ji yana gani ya kyale Muhammad ya saka kansa a muguwa kuma lalataciyar rayuwa irin ta bin mata ba, rayuwar da idan kana yi baka da mutunci a idannun al.uma? Ita kanta abokiyar watsewar naka ba mutuncinka take gani ba, a wajen Allah baka da rabo, haka a duniyar du abinda ka taba sai dai ya ringa yin baya? Ina ba zai bari amininsa ya saka kansa a wulakantaciyar rayuwa irin wannan ba

Waje ya samu ya kwonta aman fir baci ya ki zo masa, haka ya yi ta juyi yana tunane tunane ga tarin gajiya, karshe dai ya mike ya kara dangana kansa da darduma dan kara fadawa Allah ya kare mutuniyarsa a samu yar mutane lafia ya shige gaba kan matsalarta na kaso a wanketa tsaf ya mayar da ita wajen iyayenta lafia idan ya so ya daga ya yi tafiarsa shima saudiya tare da amininsa!


A lokacin da ya gama shafa fatiya wayarsa message ya shigo,

Hannunsa ya saka ya shiga message din dan kuwa yanzu baya sake da du wani abinda zai shigo masa dan gudun ya taka kaya ya bar abinda zai kai shi ga Hafsat

Yana dubawa message ne kamar haka" *Ba.a gane mahinmancin abu sai yana nesa da kai, yanda kake ji, haka nake ji ba dare ba rana tun daga bakin lokacin da na shiga jirgi da niyar yiwa yarona daya kwal da matata karyar na mutu, Abdallah damuwa ta hana ka baci ne? Rabona da baci tun lokacin da aka kashe min yarinya,.........BA NI BANE*

Tsaki ya ja ya jefa wayar saman bed dinsa ya mike ya fice a dakin a lokacin karfe hudu ne na dare dan kuwa ko kiran sallar farko ba.a yi ba

Ky din wajen sa ya saka ya buda dakin ya shiga, yana shiga ya zarce inda yake kwonce ya saka hannunsa ya dada masa wani duka mai karfi wanda ya saka shi mikewa tsaye a firgice yana kallon Abdul

Abdul ya kura masa ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login