Showing 3001 words to 6000 words out of 154870 words

Chapter 2 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1111

bata taba barin ta kwana ba, koda yan uwanta ciki guda bale na waje, idan ta fita a ajiye take sai an kawo kararta , an dasa mata mujiya a anguwa da irin girman idannuwanta da tsagerancinta,
A haka ta kai shekara goma sha shida,
Gidansu ba.a fita sai ta kama, aman ita ko ta katanga ne sai ta haura ta fece abinta, walahi ko yan anguwa dadaya suka san asalin sunnanta domin fatiyar masalaci ya yi, sai karfe goma ya yo taron aminnan arziki da yan kasuwa da yan siyasa,
*UWATA* du yawanci haka ake kiranta, domin Uwar Malan, Uwar kowa ce, sunnan uwar malan din kuwa ba kowa ya sani ba sai na jikin malan, wa.inda ko bayan ran malan ba zasu yi garajen kama sunnan ba,

Tana tafka tsiyarta, tana shagalinta , du irin tsaron mahaifinta a haka ta fara soyaya da yaro nan cikin anguwar mai suna Abdul Karim, ,
Abdul Karim kam dan baba da rai ne, motarsa biyu, yaro karami da shi aman idan ka ga abubuwan da yake yi sai hankalinka ya tashi kai mai hankalin fa nake nufi, domin marar hangen nesa lamarin birge shi zai yi,
Yarinya yar dagwas, tunda ya ganta sai da ya koya mata son sa, suke soyayrsu a haka har ya koya mata zuwa gidan rawa, a hankali ya kara fetsarar da ita, yar maganar mahaifiyar tata da take ji ta fasa ji, ya koya mata fada tamkar karya, bata ji bata gani, ga kirtawa samari rashin mutunci, ko kai dan waye zata zabga maka rashin mutunci ta yi gaba, haka idan aka ce yau ana marche ( fitowar da dalibai ke yi su yi ta kone kone a gari, ko mutanen gari dan nunawa gwamnati wani abinda ta yi bai yi masu ba) zaka ganta tsamo tsamo a ciki, an sha a kwashe su harda ita a kai a rufe sai dai bata taba kwana ba za.a dake su a sake su,

Mahaifinta ya yi dukan tamkar gangan dan gannin ya tsoratar da ita, aman ina, hakan ya sa ya ci gaba da adu.a da nema mata miji, dan kuwa har sadaka ya gwada badata aman sai a silibe masa,

A haka wani lokaci suna gidan su saurayin nata suna hira kanwar mahaifiyarsa ta zagi mahaifiyarta, ita kuwa du tsakaninka da ita du abinda take yiwa iyayenta bata lamunci wani ya taba mata su, dan haka ta tsinkawa matar mari, da yayanta da girmanta da komai, inda shima ya nuna ai ita ta jata suka kusan karyata a gidan da kyar ya kwaceta ya yi fushi yace sai an je an aura masa ita zai dawo gidan,

Kwonci tashi, kara shekaru take, aman kara baudewa take,
Gaba dayanta ta zama wata iri, haka idan suna magana da mamanta tanai mata nasiha kan ta kimtsu, ta nutsu, ta daina abinda take yi ko zara samu mai aurenta, sai ta ce" mama, ni fa ba.a yi namijin da zai iya da ni kamar Abdul karim ba, zai zo neman aurena da kansa idan iyayensa basu zo ba, mu yi auren mu mu fi tafiarmu mu huta,

Takan fashewa malan da kuka kan halayar yar, sai malan ya rarasheta ya ce da ita" tabas ana cewa idan kyau ya yi yawa yana jan fitintunun rayuwa, ban san ba ko soyaya na nunawa uwata mai yawa? Abinda dai na sani wannan ikon Alllah ne, muguwar kuruciya ne da uwata, fatana Allah ya tsare min ita, ya shirye ta, ya bata miji na gari,

Haka suka ci gaba da yi mata adu.a,
Wani lokaci ya je taro garin adarawa dan amininsa ya nemi iri a wajensa,.

Bai boye masa komai ba ya sanar masa dukan halayen ta, nan ya nunawa abokin mahaifinsa da ya ji ya gani, a aura masa,
Kai na takaice maku bai bar garin Dogon dutsi ba sai da suka tsayar da magana ya karbi sadaki dan daidai kaya kuwa yace idan ta je gidanta zai yi mata idan yana da halin hakan,

Yana zuwa ya shiga shirye shirye, ya fada masu aurenta sati guda kawai ya tsaida,

Kowa murna yake, da masu murnar zata tafi su huta , da masu taya mahaifiyarta murnar ta samu miji duda basu ganshi ba, basu san ko waye shi ba,

A ranar da ta ji, ta kyarta rashin mutunci, domin wuka ta dauka ta yi tsaye ta kyarta saman tiles din dankareren gidansu dari kal ta yi masa katuwar shaida ta kawo rantsuwa ta ratsa ta ce" in dai kuka ga an daura min aure da wannan mutumin to sai na yanka shi na kawo kansa har gidan nan!

Ba wanda ya kulata, kowa ya yi ta kansa , suka yo gum, domin ko yayunta basa haye mata, mahaifiyarta kuwa ta girgiza kai ta ci gaba da sha.anin gabanta,

Ita du a wai take dauka, hakan ya sa ta ci gaba da wadakarta a gari da anguwa, tare da Abdul Karim dinta,
Ana jibi aurenta suna zaune a restaurant suna cin abinci ya dubeta da kyau ya ce" bab, dan Allah ki fada min sunanki na gaskiya mana?

Murmuahi ta yi ta ce" to wai menene a sunan nawa? Ba na fada maka ka kirani da du wanda ya yi maka ba? Ka tambayi babanka mana idan har ya samu chance din zuwa fatiyar haihuwana,

Kansa ya girgiza yana tabe baki, kai yana son yarinyar nan dan walahi ba daren banza da baya mafarkinta, du irin yanda ya so rudarta dan ya cin mata aman ta kiya, kai ko gidan rawa da take zuwa fa bata shigar banza, sai dai ta saka doguwat riga har kasa kuma ta daure kanta cikin hula yar das das,
Kansa ya juyar ya ce" ina son ma ci jarabawar nan da zamu yi bab, ko.na yi karatu baya zama,

Murmushi ta yi kafin ta zabga masa harara ta ce" a ina kake yin karatun? Ka yi karatu Aladji, sannan ka lazumci Nasurun minalaho wa fatahun kariba,

Kallonta yake, shi a kulun yana mamakinta, ko abu ta saka gaba zata lashe shi ba wani dar, ga karatu, ga adu.o.i, kai ko irin rubutun alo idan ta zauna sai ta rubuce walahaula dubu ta wanke ta shanye, takan yi dariya idan ta gama sha ta dubi kishiyoyin mamanta ta ce" Walahaula dubu tsakaninka da mugu, ah to wa ya san zuciyar wani? Ana maka allah ya isa da mugun fata a gaban ido a zuciya wa ya san me ake maka fata? To li.ilafi kuraish!

Haka suka wuni tare, sai da yama ta nufo gida ta je dakinta ta sha barcinta domin fashin sallah take,

Baya bikon bidi.a, yakan yi walima hakama iyalansa, dan haka ne ba wani kakatsamniya sai shiri a adinance da kuma gayance,

Ana gobe daurin aurentama wuni ta yi tana barci, daga ita sai sket dinta na atamfa da pant dinta mai dauke da audugarta, sai farar rigarta kalkalkal,

Tana tsaka da baci ta ringa jin hayaniya, ana kafin a hankali warin barkonon tsohuwa ya farkar da ita a gigice,

Ohun mutane da dirufkiya ya shaida mata ana tashin hankali a gari ana dauki ba dadi da iko da mutanen gari kennan, ya yi tsamarin da har ya shigo cikin gari,
Dan haka aka bata dauki komai ba ta dirko daga saman lafiyayan gadonta ta fito da sanda, gannin ba kowa tsakar gidan ya sakata dariya ta fece domin du sun labe kowa na neman lumfashin kirki dan shakar barkonon taohuwa ba dadi,

A haka ta fice a gidan, bata san wace irin rigima ake yi ba, bata san da wa da wa ta hado ba, ta kirmu ta shiga cikin kartin da ake bi da gudu suna jefa dutsi suna ihun haukan kwatar yanci,
A haka aka radada su aka matse su aka sakar masu barkonon tsohuwa mai yawa, wanda du aka kwashe su a sume aka yi police station da su.......



*Menene sanadiyar karasawarta prison? Ya maganar aurenta? Iyayenta basu da labarin halin da take ciki ne ko me?*


Naira dari biyu ne, ko dara dari ta orange money
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3??


*Free page*









Koda suka dawo hayacinsu, du sun jigata, domin duka kai sun sha shi, haka suka zuba idon a sake su? Aman shiru,

Wasa wasa suka kwana a gidan nan, nan fa hanali ya fara tashi, cikin gari iyaye na cigiya, cikin police station yaya na zuba ido,

Ba.a wani dauki lokaci ba aka shiga kwasarsu zuwa kotu da su,
Tabas sun ga ikon Allah, ashe sojawa sun biyo wasu yan fashi ne suka fantsama gari, au kuwa yan gari masu zaman banza da neman fitina suka fara jifansu, hakan ya hadasa fada da tashin hankalin da ya si kuwa du suka kwaso su suka zuba gidan kason,

Hankali bai gama tashi ba sai da ta ganta sanye da ancor, an tiso keyarta an sakata a mota,
An gabatar da ita gaban alkali a matsayin daya daga cikin yan fashin,
Bata gama tsurewa da mamaki ba sai da ta ji lauyan nan ya mike ya lauyo karyar wai itace budurwar shugaban yan fashin, dan haka kotu mai adalci ta yanke mata hukunci daidai da laifinta na zama yar fashi a kasa, sanann ta fito da saurayinta,
Gabanta bai buga ba sai da ta yi ido hudu da alkalin da ya dage yana zazago hujojin karya, da nadidiya karyayaki kan ita din muguwa ce ta ga ai mijin kanwar maman Abdul karim ne, innalihi wa ina ilaihi raj.une, mutumen da ta dudurawa ashar dan ya tareta ya tambayeta dan me ta mari matarsa ita da take sarakuwarta? Mutumen da ta yiwa ihun kwarto dan zai wanka mata mari hakan ya saka shi guduwa bai shirya ba, sam ya ki jinnin ganninta ko jin labarinta, yau shi ne tsaye a matsayin wanda zai dulmiyar da ita,

(Bincikena ya nunan cewa tabas kana iya samun kanka a irin wannan prison da ba.a kai kowa sai manyan yan fashi, wa.inda suka kashe mutane, ko wa.inda suke kaso suna karawa cikin babar prison mai cike da rashin tausayi, rashin imani, tsaro na gangariya, rayuwar kunci, irinta ba sai idan mutun ya aikata laifin nan mai muni, ko kuwa wajen sharia *LAUYAN DA ZAI YI JA SHARI.AR YA KASANCE YA YI YANDA YA YI YA NUNAWA ALKALI KAI DIN NAN HAKAN TAKE MAI LAIFIN DA YA CANCANCI WANNAN HUKUNCIN NE* dan haka kana iya riskar kanka a ciki),

Sosai ya saka dukan wata hanyar da zai bi, a matsayinsa na lauyan da ya kware a harkar, ya nunata a matsayin budurwar baban yan fashin, inda aka nemi da ko tana da magana?
Cikin ikon Allah ta budi baki ta nuna shi da yatsa ta ce" ni zaka yiwa shari Kadre? Walahi sai na rama, sai na fadawa Malan, sai na ja maka yaseen!,

Tsawatar mata alkali ya yi, kafin a yanke mata hukucin zaman gidan yari, gidan yarinma *KUTKALE* na tsayin shelara goma, aman idan har ta fido da saurayin nata zata samu sasaucin shekarun, a lokacin shekarunta ashirin,

Wannan shi ne mafarin shigarta gidan yari, wannan shi ne dalilin da ta tsinci kanta a gidan yari,
Gidan yarin da mahifanta basu san tana can ba, domin sun yi cigiyar, su ne har asibiti wajen da ake ajiye gawarwakin mutanen da ba.a ga yan uwansu ba, su ne kauyuka, su ne gidan yarin dake xikin gari, su ne jarda kai karar Abdul karim aman ga dukan bincike bashi da masaniya a lamarin, haka mahaifinta ya daura aurenta domin bai fasa ba, aka ci gaba da nemanta, inda yaron na dagawa a ranar da aka daura auren uwarsa ta saka shi sakin auren domin ba zata aminta a yi mata wannan gangancin ba a aura masa yar da bata san darajar iyayenta ba, dan kuwa du ta samu labarun irin abubuwan da take, a ranar ne wajen daurin aurenta du yan unguwar suka ji ainahin sunanta wato ...............


Ci gaba


Fadan nan bai mutu da dadi ba har sai da aka kuma kiran sojojin nan suka shiga tsakani,

Surfe aka zuba masu na abincin ranar da za.a yi, dawa ce, dan haka du wanda bashi da galihu a gidan yarin ya shiga dukan sirfen ba ji ba gani, ciki harda ita cikin yannayin galabaita aman tana yi dan du wanda ya bari za.a zabga masa bulala ne,

Cikin prison din nan, du wanda ya saki kansa, ko nace du wanda bashi da daurin ginda zai zama tamkar gida, du wani kato na iya shigarsa ya fita son ransa, du wanda ya yarda da haka zai samu kariya da kuma shiryawa da kowa a gidan,
Sannan mata ma tsakaninsu suna watsewarsu son ransu,
Watanta takwas kennan da shigowa gidan, a kulun kiyayarta kara daukaka take domin za.a yi du masifar da za.a yi da ita kan jikinta da kuma zagin iyayenta,


Suna tsakar dakan nan aka shigo aka kirayi sunnanta kamar haka *ZAHRA* ta fito,

Shiru gurin ya yi, wata mai sunnan zahra ta mike dan tafia aman sai aka ce ba ita ba,
Dakan da take ta dakatar ta hanyar cire tabaryar ta daga cikin turmin, hade fuskarta ta yi kafin ta dauki hanyar fita waje dan tafia,

Eliz ce ta ce" yau na ga jaraba gannin idona, yau kuma sunnanki ZAHRA? Ke wai wace irin masiface ta fado mana gidan yari rana tsaka? Ni kam na fara tunanin bakya baiwa yan nan sai yan can, shegiya karuwar sojoji,

Juyowa ta yi ta nuno yatsarta, saka yatsar ta yi a bakinta kafin ta fitar ta ce" kin san bilahilazi, kika kuma ce min karuwa sai na kwakwalo idannuwanki kina barci, kin dai san na san lokacin barcin kowa, kuma ina rigayen kowa tashi ko? To mu zuba , ba sarkin matan prison kike ba, koda kuwa uwar me sai na mayar da ke makauniya!

Ido du suka zaro da mamaki, Eliz dai bagwariya ce da ta fito daga kudu, bata da adini, bata da haramun, ta kasance fitinaniya, masifafiya, ya jaraba, shekarunta uku yanzu a gidan yarin sanadiyar kisan kai da ta yi na mutun biyu a cikin tafiarsu ta hijira dan dauke kudinsu na guzuri inda polisan hanya suka kama su suka kamata da laifin aka so mayar da ita garinta su mata hukunci a can sai dai gwamnatinta ta ce idan an kawotama harbeta ne za.a yi, a niger babu Loi din harbe mutun koda ya yi kisa hakan ya saka suka sakata kaso daurin rai da rai,

Tunda ta zo kason sai da ta san yanda ta yi ta zama shugaba, kowa tsoronta yake tamkar rai, basa haye mata, dan ta fada ta kara kashe wani ba damuwarta bane dama ta shigo ne da niyar a fitar da gawarta bata da matsala da hakan!

Haka aka fitar da ita, aka nufi inda ake son gannin nata, nan ta bar su kowa jikinsa mace dan sun san yau ba su ba barci, za.a sha masifa ta bugu da kari!

Turata ya yi dan dakin sannan ya ja ya tsaya yana muzurai,

Daman ta san shi ne, bata san tambayoyin me yake mata ba, bata san me yake nufi da ita ba,

Tana shiga ta kara kallon yannayinsa, a ranta ta ayana ban taba gannin fuska marar annuri irin taka ba,

Shima dake zaune fuska hade ya mike ya dauki abin auna tsayin mutun ya auna tsayinta,
Hannunsa ya daga a lokacin da take tsaye ya zabga mata wani wawan mari wanda ya sa ta daku da jikin bangon wajen,
Da sauri ta taro kanta sannan ta mike tsaye tana dubansa ido cikin ido,

Dakin take bi da kallo, ba komai ciki sai bindiga daya kwal dake ajiye saman table din da ya tashi daga sama,

Da gudu ta nufi wajen bindigar ta dauka ta saita shi ta firfito da idannuwanta ta daga muryarta da kyau ta ce" kai mahaukaci! Me na maka? Me na maka? Uban me kake zuwa nema wajena? Ko jira kake kaima na daga maka jiki? Kan haka zan iya harbeka dan Walahi malan ba zai yi kukan na rasa mutuncina a waje ba! Koda kuwa gawata zama fitar daga wannan bakin gidan!

Da sauri guard din dake waje ya shigo ya nufeta dan karbe bindigar, ai kuwa ta dana ta kara dana kunamar bindigar, sai dai ba alburushi a ciki,
A haka ya karbe yana mai jin zuciyarsa na bugawa dan kuwa shima bai san ba alburushi a ciki ba, ya dauka ya gama mutuwa kennan,

Datijo ne mutumen da ya gannin nata dan haka ya zagaya ya koma wajen zamansa,

Wayarsa ya ciro ya canza harshe zuwa yaren french ya ce" na yarda da taurin zuciyarta, girman mutun, yannayin fuskarsa, ko karfin mulkinsa ba zai sakata yin dar ba idan ta hado su, tsayinta ya kai daidai a dauketa , bata da kakauran jikin da zai hanata daukan formation, zan saka rana a sakata cikin wa.inda aka dauka,

Shiru ya yi yana gannin yanda take waiwayensa bayan an fitar da ita sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login