Showing 6001 words to 9000 words out of 154870 words

Chapter 3 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1112

ya ci gaba da fadin" tabas idan ta samu mugun horo, zata kara tsayuwa saman kafafuwanta, zamu dauketa mu bata horo na wata biyar, zata fito a matsayin *BODYGUARD SECRET* zamu bata horo kala daban daban, zamu bata horo na tausasa murya, zamu bata horo na kalolin yaudara, zamu bata horo na jure azaba komai girmanta, sannan zamu horata da yin biyaya,

Shiru ya kuma yi inda ake masa bayanin an gamsu da kyanta? An gamsu da girman gayunta? An gamsu da girman iliminta? An tabata??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r tana jin yare biyar *HAUSA, FRENCH, TURANCI, LARABCI, DA ZABARMANCI?*

murmushi ya yi ya ce sunnanta na gaskiya shi ne *HAFSAT MUHAMAD SA.IT*, yare tara take ji, gaba daya kwaya biyu ne na iyayenta, sayran ta koye su ruwa ruwa je a makaranta zama da masu iya yaren, yarinyar kamar computer take, tana dauke abu nan da nan ba tare da ta sha wahala ba, tun da ta shiga makaranta itace ta fari har zuwa faruwar kadararta, gasa ta school da islamiya sai dai idan ra.ayi ya hanata shiga, in dai ta shiga sai ta lashe,
Tana da kakarfar zuciyar da na yi na.am da ita,
Shekara ashirin kennan ina horon sojoji, polisai, guard, Body guards, ban taba tsayuwa gaban mutun mace ko namiji muka kali juna ido cikin ido ba tare da ya sada kansa ba sai wannan yarinyar, zuwan da nake dan duba yannayin mutanen kason dan zaban wanda zan dauka har na isheta yau ta nuna min bindiga danma bana ajiye bindiga da alburushi da ta dana ta harbe Guard dina,

Haka suka gama magana kafin ya fito ya nufi motarsa inda suka sara masa aka ja shi aka fice da shi .......




Wannan kennan .
..


Ku biyo ni ku sha labari....=?
?
=?
?=?
?=?
?=?
?
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4??


*Free page*



Ana mayar da ita cikin kurkukun dakinsu ta ja ta tsaya sanadiyar ganninsu da ta yi fada suke mata kowace na rantsuwar a barya da ita ta koya mata hankali,

Ganninta ya saka suka fara nufota da yannayin izgilanci suna rantsuwar yau sai dai gawarta, bale masu zaune a wajen da nufin daurin rai da rai,

Da gudu ta warci tabaryar da ake dakan da ita, daidai saratu ta karaso wace ta fi kowa rawar kafa dan samun gidin zama wajen Eliz, sai dai me, batai wata wata ba ta daga tabaryar nan ta sheka mata ita a goshi, sannan ta aniya tarban wa.inda basu rigai sun karaso din ba, ja suka fara yi suna tsayawa, kai danma zaman balaki ne zaman kurkuku? Da me zai saka ka tarban gabanta? Mai zai kaika yin wannan kasadar? Bata ji bata gani, idan ta rufe ido kawai a fado a mutu ne,

Cikin hargagi da iface iface suka shiga dankarawa da gudu, wasu na zagayawa suna nufar wajen sojojin gidan,

Sojojin du mikewa suka yi tsakaninsu suna magana, ba wani abu ba suke cewa sai canko cewa da Aljanar prison ne ake fada, harda masu saka kudi, sannan bakin zuwa sun cika da mamakin wai ita haka take?

Da gudu suka shigo da shirin ko ta kwana, gaba daya suka rufta masu suka shiga dukansu, ba ji ba gani, duka kawai suke sha, sai da suka yi laushi sannan aka barsu, aka tiso keyarsu dan dora garin da suka surfa ba wankewa sai fecewa da suka yo suka kuma daka shi ya zama gari suka dora tuwonsa, inda masu tuka tuwon du suka tafi wanke helunan da zasu tuka tuwon da shi,
Can gefe kuwa Eliz ta hasa wuta da itacen mainan da mazan ke yowa a wajen su hura wutar ta dora tankamemiyar tukunya ta kawo tunjumemen ruwa ta maka ta zuba yan kayan miyan da suka samu, ta afka gishiri, sai dakakiyar miyar da suka dakata da kansu bayan miyar ta tashi sosai ta kawo ta kada da katuwar sanda ba ruwanta da wani burkakewa ta kawo dan mai kadan ta afka abinta ta juya ta zauna tana jira ta yi dan kauri a shiga rabo, yau ta yi niya dan ubanta ba zata samu tuwo ba! Zata nuna mata wanda ke iko a gidan!


Sai lokacin rabo ya yi kowa ya zo da robarsa, dominfa wajen nan ba.a kawo masu ziyara bale ka ci abincin gidanki, abincin da kowa ya ci ne zaka ci ko ka mutu,

Nan kowa ya kawo yar robarsa ana zuba masa abincin da daga shi sai kuma gobe, basu da abincin dare ko na kari, aman suma samun isashen da idan sun adana zai masu anfani.

Tana ji tana gani aka hambarar da robarta, aka zubawa ta bayanta,
Hakan ya sa ta mike ta dauke robar ta kai ta adana, dan indai ta harta a nan wani na iya taketa dan kawai ta rasa yar robar cin abincinma,

Waje ta samu ta rakube tana mai jin wata irin juwa, idannuwanta ta rufe ruf kafin wani hawaye mai zafi ya shiga bin gefen fuskarta,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Allahuna ajurni fi masibati, wa khalifuni khairan mine ha, ya Allah na tuba, Allah na tuba Allah,

Allah mamana, Abana Allah, ka sa su yafe min, idan har nan karshena yake Allah ka sa su ga gawata, su yi min adu.a, Allah kar ka basu ikon cin mani, Allah ka wankeni koda kuwa gawata ce, Allah ka yafe min,

Abinda ta yi ta maimaitawa kennan tana istghfari, ita kam ta ga rayuwa, ta ga ilar tsalake maganar iyaye, bata san haka lamarin yake ba, niyarta lokaci ya yi ta tuba wa Allah, niyarta ta tuba idan ta kara girma ta dawo ta shirya da iyayenta, sai gashi, tana raye, suna raye, ta wayi gari, nesa kadan da garin da suke, aman basu san a duniyar take ko ta mutu ba, tana tausayawa mahaifiyarta, tana tuna dumbin kaina da take yi mata koda kuwa tana kokarin boyewa, yau gata a raye tamkar mataciya,
Bata da wani anfani,
Ana yakin kwace mata martabarta, ana yakin raba gangae jikinta da numfashin da take shaka, adininta ya tabu, walwalarta ta gushe, bata da tunanin da ya fi ta budi ido ta ga iyayenta, ta ga farkon wannan ukuba bata san karshenta ba,

Tana nan zaune du suka ci abincinsu, ba wanda ya damu da irin halin da take ciki, kai ba itaba, akoy wa.inda suka fita jigata, suka fita shiga wani halin rayuwa, ba wanda ya damu da su bale ita da ba zaman lafia suke da junna ba,

Sai da tsohuwar nan ta lura da sahun kafa ya dauke, ta lalaba ta ajiye mata abincin nan ta gefen damarta inda zata iya ci ba tare da wani ya kula da ita ba,

Da kallo ta bi matar da kallo,
Tunda ta zo gidan, zata iya cewa wannan matar na bakin kokarinta a kanta, akoy lokacin da ta kwatanta yi mata nasiha kan ta bar kula mutanen nan haka, ta yi hakuri ta daina, aman cikin ikon Allah ta fada mata itafa kan abu biyu ne ba zata iya kawar da kanta ba, darajar mahaifanta, da ita tata darajar dake tare da ita, dan haka indai a kansu ta ga tana fada , karma ta daga dan yatsanta ba zata saurareta ba,

Abincin ta wawura daga gefen nata ta shiga ahawa ba ji ba gani,
Tuwon bashi da wani dandano a harshen bawa, yana gangarawa ne ya je ya dunkule maka a cikin ciki,
Bata damu ba sai da ta cinye shi kakaf sannan ta shiga maida numfashi tana duban yanda ganninta ya fara dawowa,

Godiya ta yiwa Allah da bai barta cikin yinwa ba, ta labe robar tsohuwar sai da ta mike dan gabatar da sallah ta kai mata ta ajiye a boye ba wanda ya kula da an tiso tsohuwar a gaba danme zata hana a yi mata horon yinwa.

Sai da ta zo tsakiyar wajen ta yi tsaye , ta saki murmushin godiya ga Allah, sannan ta bi kowa da kallo, bata da dar, du wace ke jin kanta wata shegiya ce kuwa jiranta take, dan haka a gadarance ta nufi wajen ruwa ta dauka, ruwan da na siyarwa ne ta dawo ta shiga alwallah bayan ta kwonkwada,

Ke ina kudin ruwana?
Muryar mai siyar da ruwan ya daki kunnenta,
Namiji ne , aman kuma dan daudu ne, zamansa cikin prison din ba irin sana.ar da baya yi, shi ke samo ruwansa ta hanyar da masu tsaro suka yarje masa, ba wai babu panpo bane a wajen, da ruwa fa, kawai ana hana su zuwa wajen ruwan ne, sai idan dare ya tsala ake bari, su kuwa da ba abubuwan cika ruwan garesu ba wa zai basu? (Ya Allah ka rufa mana asiri, ka rabamu da kadara muguwar kadara, tabas zaman gidan yari wani nufi ne na Allah wanda idan ya nufi bawansa ba wanda ya isa ya hana, kadarra ce, ya Allah ka kare mu da rayuwar rashin yanci ),

Da sauri ta karasa alwalarta, sosai ta didiki ruwan, sannan tamike tsaye tana dubansa cikin ido yanda yake wani laudi, du fuskarsa ta jeme tsabar shafe shafe da yake dan jaraba a gidan yarinma, sannan fuskar wani tafkekiya da ita da dogayen lebuna da aka kara fitar da su dan dole dan kuwa lankwasa sun da ake ta hanyar sai an yi maganar mata dan dole,

Murmushi ta sakar masa sannan ta ce" kai ko kema sunnan yake, kali sama, rana ta raba, tsuntsaye sun yi shiru, sararin samaniya ya kara haske, wanda ya yika, ya kuma baka ruwan ne zan gaisar, in kuwa baka yafe ba fadi mu ji....

Ta karashe tana harde hannayenta biyu tana dubansa ,

Baki ya tabe kafin ya ce" jarababiya mai bakin uwa (zaginsa kennan sai yace da kai mai bakin uwa, wai nufinsa in ba bakin uwa ba me zai kawo mutun kutkale),

Wartar butarsa ya yi kafin ya zabga mata harara tamkar wata mace, ya ja tsaki ya kuma buga cinya ya juya ya bar mata wajen yana mitar ke kika sani, ah ina dalili ga zafin prison ga na yinwa ga kuma na dambe?, bara in je in yi neman kudina in huta, neman fada ai sai matsiyaci!

Ita dai tunda ya juya itama ta juya dan zuwa ta yi sallah, domin malaman cikin prison din sun yi kiran sallah tun dazu, ( kar ku sha mamaki, kamar yanda na fada, ba abinda babu a gidan yari, )



Gidan Malan Muhammad Sa.it


Sadakar damamiyar madara da kuma abinci dafafe ne ake yau juma.a,

Ko a masalaci da aka gama sallah kamar yanda ya saba, sadaka ya yi sosai, inda shima manyan elhazan nan ke kawonasu gudunmuwar , wasu da sunnan masalaci, wasu kuwa da sunnan malan din da kansa, duda kuwa ya fi karfin hakan, aman ba karamin dadi yake masa ba domin kuwa mutuntawa ne,

Sai da aka watse, ya mike ya gyara salayarsa a ma.ajiyarta yana duba agogo dan karfe hudu yana da wa.azi da gidan tv Tele Sahel,

Abokin shawararsa ne, wato Malan Laminu ya shigo masalacin,

Cikin raha suka gaisa kafin su fito daga wajen sallar suka yada zango a balbalin masalacin wajen shuke shuke na gazon macha Allah,

Dubansa ya yi a tsanake sannan ya ce" yaya karin hakuri? Ya juriya, ya hakurin Matar arziki?

Shiru ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa ya ce" ka san na shaku da yarinyar,
Kai shaida ne komai nata daban ne,
Inada vidioyinmu inda take tatata, tana yi tana fadin Baba..baba tatata,


Malan laminu ya sauke ajiyar zuciya ya ce" ba kai kadai ba malan, ko ni da ta yi karatun alkur.ani hanuna na sha mamakin lamarinta,
Wai ka san tun kafin ta yi sauka ta taba kamo bata a cikin rubutun litafi da malan salisu yake koyon nan da tadawa? A nan na kara dubanta,
Ka duba ka ga a kusan tare ta yi hardar ahlari, kawa.idi, da alkur.ani, tana gamawa ta shiga damkar litatafan adinin nan, kuma ya shiga kwajwaluwar cikin ikon Allah ya zauna,
*UWATA* raye ko mace?

Malan Muhammad ya ce" na so gannin gawarta, na tabata da na hakura na samu nutsuwar zuciya, man laminu, mutuwa bata boyuwa, gani nake koda a ketare da niger ta mutu zamanin android za.a haskota,
Ina ji a jikina *UWATA* na raye, ina ji a jikina tana wani yannayin rayuwa, mahaifiyarta ke bani labarin mafarkinta, takan yi mafarki *HAFSATU* na miko mata hannu, ko ta yi mafarkinta ta dora kanta saman cinyarta tana shasheka tamkar wace ta yi tsere,
Ya Allah ka kare min UWATA du inda take, idan da kafarta ta gudu dan zan mata auren da bata so, Allah ka shiryeta ka dawo da ita gida, idan kuwa fitar da ita aka yi, Allah ka kare min ita,

Shiru ya yi yana duban Malan laminu daje amsawa cike da girmamawa sannan ya ce" idan kuwa Uwata ta rigamu gidan gaskiya, ya Allah ka jikanta, ka sa tana cikin rahamarka, Allah ka hada mu da wanda koda hoton mutuwarta ne ya gani ya fada mana ko hankali uwar daukan cikinta zai tsaya waje guda, ko zata rage yawan fado mani a cikin zuciya ya Arahaman rahimine

Amsa masa adu.arsa yake, inda suka mike suka rankaya gidan Malan Muhammad din, somin yau juma.a ce, gidan malan na cika ne tun da asuba har wata asubar ana raya ranar sosai,,




Bayan sati biyu

Murkashi take na ciwon ciki, ita daya yashe a rana sai juyi take , abin ne ya hadun mata ha yunwa da take ji, ga rashin bacin kirki , ga damuwa, ga kuma al.adarta da ta risketa cikin wannan halin,
Adu.a take so ta yi aman ina, sosai cikinta ke ciwo tamkar ranta zai fita...................



*Domin Samun kutkale, naira dari biyu ne, Niger kuwa 500 franc ta orang money*
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




5??


*Free page*




Wasu kartin sojoji ne hudu suka shigo wajen, nan hankalin kowa ya yi kansu,
Neme neme suka fara yi, kafin dayansu ya je ya birkitata ,
Da yaren french ya ce" c'est elle, la voila chef (ita ce, gatanan sir)

A tare suka nufo wajen, basu yiwa kowa magana ba suka kinkimi Hafsat suka fita da ita ,

Jigum jigum wajen ya yi, Eliz ce ta ce" ko ratayeta dai za.a yi? Wadinnnan mutannan mararsa annuri?

Baba fsohuwa ce ta kaleta da sauri ta ce" kin taba jin an rataye wani a Niger? Ai ba.a hukuncin rataya,

Eliz ta daga kafadarta ta ce" to , an taba yarki ko? To ina fatan su je su yagalhalata sannan su maido mana honkon!

Shiru tsohuwar ta yi, dan ba zata iya ba kam, aman kasan zuciyarya tana adu.ar ba amen ba, haka kuma ta nemi waje ta zauna tana duban hanya


Tafiya ce suka yi ta mamaki, a cikin wata bakar mota wuluk,
Cikin jejin suka kara dafaruwa,
Sai da suka shige wajen da sai dai GPS zai nuna maka nan ne gabas yama kudu ko arewa sannan suka karaso wajen wata bakar kofa,

Basu tsaya wata wata ba suka danna horn,
Nan aka bude masu kofar suka shiga da ita,

Wani irin waje ne mai gine gine, da wajajen gudu, da wajen tatakawa a hau, da 2ajen tsalake igiya, da wajen haura katangu,
Kai gurin dai wani irin tsari ne da shi mai wuyar fasara,

Basu zame da ita ko.ina ba sai wani bangare, nanma get ne, dan haka sai da suka kuma yin wani Horn din aka bude masu suka shiga daga bakibaki suka fitar da ita suka dauketa cimak suka kaita cikin wani daki,

Dan daki ne dan dogo madaidaici, mai dauke da katifa kwonciyar mutun guda, da wani dan table karami, sai sutura wando da riga bakake sakaku sannan na auduga,(kada), sai fankar sama karama ba baba ba, sai fitila daya doguwa, da kuma wasu irin fitilu cike zagaye da fankar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login