Showing 90001 words to 93000 words out of 154870 words

Chapter 31 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1167

kashe maka lanwarka, a kashe maka mahaifinka, a kashe maka mahaifiyarka, a zo a kashe maka kuma yar uwarka daya da ta rage maka?

Abdul ya ja ya tsaya , sai da ya dan dafe kansa sannan ya ce" ba yar uwata bace

Muhammad ya tsura masa ido yana kallon sa ya ce kamar yaya?

Abdul ya daga kafadunsa ya ce" ba yar Abdul Basid ba ce,

Aman ya aka yi ka gane haka? Muhammad ya fada cike da mamaki

Abdul ya waiwayo shi sai kuma ya saki murmushi ya ce" tana zaman kanta a saudiya kusan shekara goma sha bakwai, ita din haifafiyar maradi ce, iyayenta du sun mutu, ta fita neman na kanta da kanta ne,

Muhammad ya yi saurin cewa" to me ya kawota nan, me ya hadata da tsohuwar matarka?

Abdul ya shafa sajen fuskarsa sannan ya daga kafadunsa ,

Muhammad ya kasa sammun nutsuwa suka ci gaba da tafia da Abdul har suka shiga baban falonsa,
Muhammad ya ce" Abdul, sai nake gannin hankalinka a kwonce, wannan matar ta zo da niyar cutarka fa, domin ta zo a matsayin wai yayarka, hakan kuma harda tsohuwar katarka, ta zo dan dukiyarka ko dan rayuwarka?

Abdul ya ce" eh, aman ai ka ga Allah ya tsayar da lamarin da kansa

Muhammad ya kura masa ido ya ce" to aman ita matar taka ina take? Ina ta shiga?

Sai da Abdul ya fara tafia dan kuwa jirri yake ji sosai dan hankalinsa ba a karamin tashe yake ba , gaba daya ya sare , tsoro ya lulube masa zuciya na tunanin a wani hali Hafsat take ciki? Ko har an kashe ta ne?

Da kyar ya iya tsayawa ya juyo ya ce" tana boye , ni kaina ban san inda suke bata soin ba!

Haka Muhammad ya yi shiru yana kallon sa har ya shige dakinsa na baci,

Yana shiga nan ya fadi ya rintse idannuwansa yana jin yanda kansa ke sarawa, ya Allah, ya Allah shi ya fi maimaitawa yana mai neman hawaye su zubo masa aman shiru basu zubo ba

Wayarsa ce ta dauki kuka dan haka ya mika hannu ya lalubo ba tare da ya duba mai kiransa ba ya kara a kunnensa yana sauraro

A takaice aka ce" *jarumi ne kai, cikin da ta fita da shi barinsa ta yi bata haife shi ba, zubar da shi ta yi Abdellah, tashi kar a cin maka a lokacin da kake halin kaka naka yi*

Ihu ya yi da haushi ya nausa wayar a kasa


A cikin wannan rayuwar kunci aka ci gaba da tafia da Abdul da Muhammad da mutanen dake tare da shi,

Wa.adin da malan ya dauka na sati daya cir suna wata nafila tsakiyar dare daga shi har Abdul dan neman haske da bayanar Hafsat a wajen Allah ya zo ya cika aman shiru

Hankalin Abdul ya kara tashi, shi dai du ya daburce abinsa aman yana yin bakin kokarinsa yana boyewa dan gudun hargitsa lamarin Muhammad dake tare da shi ba dare ba rana

A rana ta tara , ya tashi da matsananciyar faduwar gaba,
Tazbaharsa ya lalubo ya shiga lazumi zaune saman salayarsa, har lokacin komawarsa baci ya yi na wajen karfe goma aman shiru baya jin bacin ko kadan,

Yana zaunen nan ya ji zafi , ko nace kunci wajen ya yi masa hakan ya saka shi mikewa ya je bakin windows ya ja ya tsaya ya dage labule yana kallon yannayin garin

Idannuwansa ne suka sauka a kan Muhammad dake tafiar sauri sauri ya nufi can wajen bangaren dakinsa na sirri na horo, domin daga dakinsa tsayin ginnin na bashi damar hango du wani abinda ke nesa dake cikin gidan

Har ya juya dan komawa bakin gadonsa ko zai samu baci, sai kuma ya maida dubansa wajen yana kallo,
Gani ya yi wannan sojan daya kwal da ya ragewa Muhamad ya tarbo shi sun tsaya suna yar magana sai kuma suka juya a tare bayan Muhammad din ya amshi wani abu a hannunsa tamkar igiya

Kansa ya girgiza a fili ya ce" Muhammad, me kuma ya kai ka har wancen wajen kai da na maka hani da fita nesa in dai ba zuwa daukan jirgi dan tafia Saudiya zaka yi ba?

Komawa ya yi bakin gadon ya zauna,

Haka kawai ya ji hankalinsa ya kasa kwonciya da nisan da Muhammad ya yi, sannan zuciyarsa sai tambayar me ya je nema nan take masa?

Mikewa ya yi da sauri ya je dakin computernsa,

Yana kunnanwa ya hasko wajen dan gannin me yake a nan, sai dai ya ga duhu ya mamaye screen din, kamar an cire camerar ko an rufeta da wani abu mai duhu dan kar a ga abinda ake a wajen

Gabansa ne ya yanke ya fadi, lokaci guda jikinsa ya dauki rawa, ya salam, kar dai a je yau kuma Muhammad dinsa za.a kashe masa?

Ai zuciyarsa na gama fada masa haka ya wani irin dirkowa daga saman kujerar da ya zauna dan gannin camerar ya fita da wani irin gudun balaki yana mai gyara karamar bindigarsa da ya warto

Yana fitowa su BS suka rufa masa baya suna masu tambayarsa lafia? Aman ina bakinsa ya kasa basu amsa haka kuma ya kasa tsayawa, su kuwa sun kasa cin masa

Da gudu suka karasa wajen, sai dai me, mai tsaron kofar na ganninsu ya ciro bindigar jikinsa da niyar harbin su, sai dai ya makaro dan kuwa kafin ya saki kunamar harbin nasa BS ya dauke shi da bindiga hakan ya saka shi faduwa wajen

Tabas da Muhammad na cikin hayacinsa, da karar faduwar sojansa ta saka shi lekowa dan gannin abinda ya yi kara haka, sai dai ina yana can ya tube zindir hahuwar uwarsa haka kuma ya cirewa Hafsat rigar dake cikinta kokarinsa shi ne ya karasa cire mata wandon jikinta ya idasa nufinsa a kanta aman saman kirjinta ba komai ko bras babu bale a yi tunanin riga, albartun kirjinta gaba daya sun bayana suna kiririta da fitsara abinsu........

Abdul da yannayin tashin hankali ya kali solda din nan sannan ya kalli BS, sarai ya gane niyar soldier din ya harbe shi, aman kuma rudu ya hana shi yarda sai ma komawa da ya yi ya shaki kwalar BS ya buga shi da garu daga baya baya ya rage muryarsa cikin bacin rai ya ce" ya zaka kashe mutun tamkar kiyashi kai mahaukacin ina ne? Ka sani idan na fitar da Muhammad daga dakin nan sai na rufe ka da kai da azalumana dake biye da bayana!

Yana sakin BS ya juya ya wankawa su Hafsat wani wawan harara sannan ya tunkari dakin kai tsaye inda su Hafsat suka bi bayanya

Yana zuwa ya buda dakin gaba daya ya afka bindigarsa a hannunsa a shirye da shirin harbi a kowani lokaci

Wani irin ja ya yi ya tsaya, domin wajen haske ne tar ya haske dakin

A hankali shashekar kukanta ya fara shiga kunnansa da kalma kamar haka" *MUHAMMAD KAR KA KETA MIN HADI, NA ROKE KA KA KASHE NI BA TARE DA KA HADA NI DA KAZANTA BA*


Muhammad da ya bada baya yana hada kwaya cikin jus din maltina dan so yake sai hankalinta ya gushe zai yi bidirinsa a kanta , sam bai ji an buda kofar ba dan kuwa kofar ba mai kara bace sai a bude a rufe bata yi kukan an bude ta ba, sannan kafar Abdul ba ko takalmi bale a jiyo takun tafia, gashi sun yi shigowar da ba za.a jiyo su da sauki ba

Idannuwansa ne suka sauka kanta,
Gefen fuskarta a kumbure kadan dan kuwa ya tasa irin marin da yake wanka mata idan ta bata masa rai,
Lebenta ya yi wani irin jajajir tsabar dantse shi da kukan da take ci na iftila.in rayuwar da ta afka ita ba a duniya ba ita ba a lahira ba,
Gashin kanta gaba daya ya zubo mata ya kare wajen da ya kumburan a fuskarta a hankali ya kai idannuwansa a jikinta, kirjinta gasu nan a bayane kiri kiri jajajir da su sun kumbura sun batse suna rawar nanaye daga ta motsa,
An yi mata wani irin dauri ana shirin rapping dinta!

Kansa ne ya mugun sarawa, ya wani irin sarawa,

Bindigar hannunsa ce ta kubuce ta fadi a daidai lokacin da Muhammad ya juyo daga shi sai dan pant na maza jikinsa ya yi shirin kwasar gara ya sha kwayoyin maza dan niyarsa ya yi mata kaca kacan da ba za.a iya ganeta ba!

Sai da ya rintse idannuwansa sannan ya kuma budewa, Hafsat dake kallonsa tana lumshe idannuwanta tana mai jin wani irin ciwo , muryarta ciki ciki baya fita da kyau ta ce" *Abdallah*

Abdul ya lumshe idannuwansa dan du kalma daya da ta fito daga bakinta dirrect zuwa ta yi ta samu matsugunni a zuciyarsa, ta mata wata irin duka sannan zufa ta keto masa

A hankali ya daga kafarsa daya ya yi taku daya zuwa ga Muhammad da ya ruruko ido, ya daga hannayensa ya dora saman kansa, gaba daya jikinsa yake bari, haka kuma wandon dake jikinsa sai ga fitsari ya biyo yana gudu nan da nan zarni ya fara tashi

Muryarta ta kara budawa ta ce" *ABDALLAH SHI NE*

Da sauri ya juyo dan kara kallonta a lokaci daya kuma ya ringa gannin duhu na karade wajen baki daya

Lumfashinsa ya ji yana sama, da karfin gaske ya ja numfashin ya sauke, ya kuma ja ya kara saukewa,
Zuciyarsa ce ya ji tamkar ana zuba masa ruwan zafi,
Adu.a ya nema ya rasa ,

Da wani irin karfi ya daki kirjinsa da hannunsa na dama ya kara daga kafarsa ya nufi inda Muhammad din ke tsaye , sai dai ina gaba daya lumfashin nasa ya dauke idannuwansa sukai tsaye tsaye kafin su rufe,

Tun daga tsaye sai ji kake yimmmmmmmmmmm Muhamad ya fadi kasa

Hafsat dake daure Hasana nafamar kunceta bayan ta kare mata kirjinta inda BS da abokin aikinsa suka nufi wajen Muhammad sunna tsaye sunna jiran jin abinda Hafsat ke nufi da bayaninta Hafsat ta kwala kara ta ce" Abdl............


Bata karasa kiran sunnansa ba ta fashe da wani irin kuka jikinta na rawa daidai nan hasana ta kunce ta

Mikewa ta yi ta rukunkume hasana jikinta na rawa ta ce" dama ina gudun wannan ranar, ku duba shi kar ya mutu!

BS dake cikin wani yannayi, na murnar gannin hafsat da kuma katon rudanin da ya hane shi nuna farin cikin nasa na gannin aminin mutumen koma ya ce dan uwansa a tsaye a irin wannan shiga da kuma kalaman da suka fito a bakin hafsat da irin yanda suna kallon abdul din ya sume sun kasa motsawa dan karasawa inda yake dan kuwa sun saka Muhammad din tsakiya BS ya ce" Bodyguard H, wa ya sato ki ya kawo ki nan? Me kike nufi sa maganarki na *Shi ne?* shi ne me?

Hafsat da jikinta zafi rau ta saki Hasana tana kare kirjinta da rigarta ta kai dubanta wajen Abdul sannan ta maida wajen BS ta ce"




Alhamdulilah........comment yan uwa
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 1??


Cikin yannayin rashin tsoro da kyama take duban keayar idannuwan Muhammad dake dan langi sakamakon kwayoyin da ya hadiya ta shiga mayar da zancen duka kaf da ta gano wajen bincikenta, da irin sato tan da suka yi shi da sojansa mai bashi goyon baya, da komai da komai

Sai da ta ja numfashi ta kai dubanta wajen BS da har jikinda bari yake tsabar firgita da ikon Allahn nan, ya ga lamari da yawa, ya ga gaba da yawa, aman bai taba gannin ci amana irin wannan ba

Idannuwanta cike da hawaye ta ce" wannan da kake gani, wanda ba zan iya kiransa da madaukakin sunna irin MUHAMMAD ba, domin ya kasance azalumi, mai izgili da rashin tsoron Allah, wannan aljanin mutumen wanda ban ga sunnan da ya dace da shi a musulunce ba!

Ta kuma rinyse idannuwanta sannan ta ce" *shi ne mai kashe kashen nan baki daya ban cire maka ko daya ba, kuma yana yi ne dan vengeance*

Sai da BS ya dafe gaban kirjinsa dan luguden kidan da yake masa,

Dubansa ya kai wajen algungumin a daidai lokacin da ya daga hannunsa ya nuna Hafsat ya ce" karya ne!


Gindin bindigarsa ya saka ya daki keyarsa hakan ya katse masa fitsarar da ya dauko a bakinsa ya silale wajen a sume

Da kallo ya bi shi sannan ya bada umarnin a nufi asibiti da Abdul da Hafsat
Shi kuwa ya dadaure Muhammad dauri irin na huhun goro sannan ya shiga bincike da harhada du abubuwan da zasu isa cikaken shaida haka kuma ya tabo ikon garin wa.inda bai isa ya aiwatarwa da Muhammad wani abu ba sai abinda aka yanke masa a kotu

A lokacin da aka saka masa ankwa bayan sun dankara masa wata gigitaciyar allura mai taba kwakwaluwa aminin Abdul mai sunna Ahmad ya yi tsai yana kallon motar da aka shigar da shi baima san inda kansa yake ba,
Tabas shima ya girgiza, sai dai da wuri ya kwabi kansa a lokacin da ya tuna cewa Muhammad fa mutun ne, dan adam ba, dukan abubuwan da ya ringa yi ke dawo masa a idannuwansa,
Sai da ya kalli BS dake kokarin tayar da mota dan bin bayan su Abdul sannan shima ya buda motar da shiga wace ke dauke da gagan sojoji wa.inda ba alamar sun taba sannin wani abu mai sunna dariya a rayuwarsu sannan ya gyada kai a ransa ya ayyana........shara.ar Muhammad ya dace a barwa Allah, bai ga hukuncin da za.a yiwa wannan bawa a nan cikin duniya ba, bai ga irin abinda za.a iya yiwa wannan bawa ba a huce ko a rama irin abubuwan da ya shuka, tabas zasu tura shi kasarsa a hukuntashi a can, ya tabata kisa ne ta hanya mafi muni ya je can kuma ya fuskanci wanda ya halice shi!



A asibiti kuwa tun a hanya BS ya samu ya kirayi number Malan, domin tun ranar da Abdul ya je BS ya gane akoy fahimta tsakanin datijon da Abdul, a irin yanda Abdul ya zame kasa ya duka ya gaishe shi wanda hakan shi ne gannin farko da ya yi ya mutunta mutun

Bayanin da ya yiwa malan ya saka shi jin zufa ta keto masa, cikin nutsuwa ya nuna masa cewa da zai samu jirgi a lokacin tabas da ya zo da kansa domin kuwa dole Abdul na bukatar mutun a kusa da shi

BS na jin haka ya ce da shi ya kasance cikin shiri koda yaushe ana iya zuwa daukansa in sha Allah za.a kawo shi

BS ma karasawa ya tarar likitoci na kan Abdul , famansu shi ne su dawo da numfashinsa da bugawar zuciyarsa daidai,

Hafsat kuwa na zaune saman kujera an saka mata magana a fuskarta an gyara mata an yi an yi ta kwonta ta huta aman ta kasa tana zaune ta saka wata riga baka mai dogon hannu aman bata canza wandon jikinta ba ta faure kanta da dan kwali baki ta yi zuru da ita tana kallon waje daya, a kasan zuciyarta kuwa sai adu.a take kan Allah ya sa ya yi hakuri ya dauki komai da sauki

Sun dauki kusan awa kafin a fitar da shi a kai shi dakin hutu sai a lokacin ta mike ta koma dakin da ya dace a kwontar da ita ta shiga bayi ta yi wani irin wanka sannan ta fito ta dauki wani wandon da rigar baka da hijab da Hasana ta kawo mata ta saka ta kabarta sallah a nitse

Ta jima tana ramuwar salolin dake kanta, ta dauki lokaci tana sallah kafin ta salamce ta shiga adu.a da godiya ga Allah

Jaka kawai ta tsinci kanta da yi masa adu.a mai nauyin gaske, ta jima tana rokon Allah ya taimaketa ya ji kanta duda baya barin wani dan wani ya ji dadi ita kam bata tunanin zata ci gaba da walwala idan bai mike ya samu kansa ba

Tana ta jero adu.o.in ta ji wata kamilaliyar murya, nitsatsiyar murya, muryar da ta kasance mai yi mata nasiha da lalaba ta, muryar dake tsananin girmamata ta hanyar kiranta *UWATA* muryar da ta kasance daya daga cikin adu.o.inta na Allah ya nuna mata ranar da zata kara jin muryar a duniya

Kasa kunne ta yi tana mai jin zuciyarya na bugawa a lokacin da ta ji BS ya yi magana sai kuma ta ji muryar ta ce" Allahu ya tashi kafadar bawan Allah, ya bashi lada da juriyar wannan jarabawa, domin Abdallah mutumen kirki ne

Wata irin mikewa ta yi ta doshi kofar, sai dai me, Hasana ce ta riko hannunta da karfin gaske ta ce" ki koma ki zauna H, kar ki jazawa kanki kin san kina cikin mission ne

Wani kallo ta yiwa hannunta da ta riketa da shi sannan ta ce" ki cika ni

Hasana ta saketa ta ce" zaki lalata aikin ne

Hafsat bata ce da ita komai ba ta buda dakin da saurin gaske ta fita

Tsayuwa ta yi ta shaki kamshin turaransa, bai canza shi ba shi dai ne har yanzu,

Da sauri ta shiga raraba ido tana neman inda zata gan shi, ina zata ga hasken idanniyarta,

Kyalkyalin tazbaha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login