Showing 30001 words to 33000 words out of 154870 words

Chapter 11 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1146

biyun suna asibiti wannan rigimar sai da ta kaisu da shan matsiyacin dukan da aka kwontar da su!

Da kansa Elhajin ya bi layin mazan dake tsatsaye, cikin sannin aikinsa da irin kwazonsu ya zakulo maza biyu da BS cikon na ukun domin kuwa har shi ya nemi da a laya duda irin tsadar aikinsa,

A haka ya dawo wajen yan matan, dayar ta fi Hafsat tsayi, da yannayin alamun karfi, Hafsat a yannayin jikinta ba zaka taba tunaninma wai zata saka kafa a wajen nan,
Dan haka ya juyo wajen GN ya maida shi gefe cikin yannayin damuwa ya ce" GN, wannan yarinyar ba zata iya aikinmu ba, ana son yarinya daya da namiji daya su baiwa Ni.ima tsaro, yarinya daya da maza biyu kuwa su baiwa mijinta tsaro ne, dayar da alamun karfi a tatare da ita, aman wannan bana jin zata wani iya wanu abu,

GN cikin yannayin son a yarda da maganarsa ya ce" na yarda da formation din yarinyar, na matukar yarda da ta tsaya saman kaina a lokacin da ba bace cikin jeji, in sha Allah kwakwaluwarta mai ja ce,

Yar gidan waye?

Sai da gaban GN ya fadi, domin Elhaj na daya daga cikin wa.inda suka so bashi wahala sosai kan a fitar da ita a sakata wannan aikin,
Aman ya ya iya, ya fada masa gaskiyar ita ce wace aka fitar daga *KUTKALE*

kana nufin, matar dan ta.adan zaka bamu a matsayin wace zamu je da ita da yarda ta baiwa iyalina tsaro?,

GN ya sada kansa, domin mai gidansa ne, bashi da bakin wani daga murya ko wani abin,
A tausashe ya ce" *a bakin raina*

Sosai abin ya bashi mamaki, a bakin ransa fa ya ce? Idan ta aikata wani abin a kama shi , idan ta kashe a kashe shi? Ya yarda ya daukarwa kansa wannan baban hatsarin a kan dan adam mai iya canzawa saboda kudi? Ko wani ra.ayi nasa mai girma ko marar girma?

Kansa ya jinjina kafin ya kai hannunsa ya daki kafadar GN ya ce" zamu yo signed kan ran ka! Aman kuma ba ita zata baiwa Ni.ima tsaro ba, sai dai ta hadu da baban yaronka su baiwa Oga Abdul Jabar tsaro! Ka ga a wajen namijin mun dauki wanda ya kware mun hada da Abdul, a wajen macen mun dauki wace ta kware mun hada da Ni.ima,

Murmushi GN ya yi a fili mai cike da ma.anoni, kafin su tatara su je a yi du abinda za.a yi, a tarkata su su dauki hanya , suna zuwa cikin gari suka dauki jirgi suka juya inda suka bar Aunty da mijinta,

Suna dira baban gidansa suka zarce,

Kowa na neman hutu banda masu tsaron su, da kuma shi kansa uban tafian,

A lokacin da ya ga Hafsat tsaye a bayansa matsayin wace du inda ya kutsa ta kutsa sai da ya rike kugu ya dafe habarsa ya kare mata kallo tun daga kafarta hat kanta sannan ya yi kwafa a ransa ya ayyana....yanzu wannan ai almubazaranci da sakani a uku ne, toh mana, maimakun na yi ta raina kadai sai na hada da ta jaririyar nan, idan ba son banza irin na iyayenta ba, ya zasu dauketa su kaita irin wannan aikin da sai mazan wajen sun gama kwakule masu yaya sannan a koya masu abubuwa irin na karti, su juye su dawo bawa karti tsaro? Wai yanzu wannan yar jaririyar ce zata kare wani abu ya same ni, ni wannan uban da ni, da na yi imanin da na yi aure da wuri da na zubawa matar cikin yan hudu irinta?

Haka ya juya ya shige inda Hafsat ta sha mamakin ashe wannan bakin mutumen mai sifar samudawan ne za.a baiwa tsaron? Ita walahi du ji take wancen balaraben mai sifar yayan gatan ne za.a baiwa tsaron, domin sam ba.a basu fuskar wata tambaya ko wani cikaken bayani a kan wannan aikin ba, dan kuwa Oga ne da kansa a tsaye a wajen wanda ita saima a ranar ta fara ganninsa da sannin matsayinsa a Niger.

Biye take da shi a lokacin da ya fito daga dakinsa, inda BS ya bita da kallo, ya so ace shi aka baiwa wannan aikin mai hatsari na ko menene sai ta fara duba zai iya anfani da shi, ko zai ci kai koma menene, ya so ace shi ne da wannan abin ba dan komai ba sai dan a yannayin aikin, wannan mutumen na cikin hadari sosai, wanda sai an yi da gaske, an baza ido, an baza komai kafin idan da rabo a samu galaba....

Kansa ya sada ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya ya ja dayan suka ci gaba da bincikar gidan lungu lungu da kayan aikinsu......

Shi dai bai ce da ita ta koma, ko ta tsaya ba, har suka karaso kofar dakin Ni.ima, wanda suka tarar da Bodyguards dinta tsaye bayin Allah kowanne a kame waje guda,
Sai da ya tsaya ya kara kama tsatso, wanda yake kamar sabonsa ne, ya kare masu kallo,
Murmushi ya yi a fili, shi walahi an kawo masa nishadi, yo nishadi mana, wanna lamari kamar gunkina? Ba um bare umum, du sun kame suna jiran uwar gidansu, shi ko a million goma a wuni ba zai iya irin wannan aikin ba!

Bude masa namijin ya yi ya shiga, sai dai ga mamakinsa, yarinyar dake biye da shi itama ta shigo,

Tsayuwa ya yi ya juyo ya dubeta, sannan ya kai dubansa wajen Ni.ima da ta mike da sauri daga ringeshen da ta yi cikin riga da wandonta na barci ,

Sai da ya ciro harshen sa , ya lashi lebensa na kasa sannan ya kara dubansu a tare,

Wani murmushin yan duniya ya yi, ya rike tsatsonsa ya dubeta da kyau kafin ya ragewa idannuwansa girma su dawo kalar baci ya ce" ni dai a sanina mace daya aka daura min aure da ita a yau, kuma wajenta na zo dan ta kama wannan abin ta rage masa nauyi (=?-?ni dai wannan labari a hargitse yake dan sakin magangannun ciki),
Da hannunsa ya nuna inda yake nufin a ragewa nauyi, wanda hakan ya saka su a tare rintse ido daga Hafsat din har Ni.imar, dan kuwa ba warda ta yi tunanin, ko a tsuman ranta cewa abinda zai aikata kennan,
Ci gaba ya yi da magana bayan ya wani rausayar da kai ya ce" zuwa na yi na kwonta da matata, ko yar biyu za.a yi?

Ya fada yana mai fitarwa da Hafsat gaba daya idannuwansa, sai kuma ya ja wani yaji yaji ya ce" ko a zina ba kyai hada biyu, bale yanzu na bar zina, kin ga ki dan fita na gama sai ki maida ni daki ko?

Hafsat kam, yau ta ga uba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nta a rashin kunya, yau ta ga ikom Allah, da hasken gari ba wai dare ya yi ba, kiri kiri, ra.aine da ra.aine, kunne da kunne, ya dubi tsabar idannuwanta, da na wace a tunaninta a yau aka daura aurensu, ya gangantsaro wadinnan gantsara gantsaran magangannun?

Sai da ta lumshe idannuwanta ta hadiye wani yawu makwat, sannan ta daga kafafuwanta ta shiga kara saka kanta cikin dakin tana mai nufar.......



Comment plz=?O? >د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 4??


Nufar gadon da Ni.ima ke zaune tana zarar ido ta yi,
Irin yanda kirjinta ke dokawa da a lokacin ya yi gigin cewa da ita kekek...ba abinda zai hanata yin dayan biyu, au ta zura da gudu , au ta kwala ihu, domin wannan lamari ba jarumta ya aro mata ba , sai tarin tsoro da fargaba, ko a abubuwan da aka koya mata ba.a koya mata irin wannan ba.

Tsaye ta yi gaban gadon tamkar an dasata , ta tsurawa Ni.ima ido tanai mata kallon da ita kanta bata san na menene ba,
Can kamar an tsikareta ta dan farfado ta karasa da kyau wajen bed din ,
Sai da ta saka hannun mai dauke da abin aikinta na caje abubuwa ta caje gadon nan har kasan sa,
Sannan ta dawo tsaye gaban Ni.ima, wace da ba aikinta ne ya kama da hakan ba, ba zata taba gigin cajeta ba, domin yannayinta bai nuna alamar muguwa ce ba, sai dai a aikinsu babu innocent face da ake ignored, kowama damka ake a bashi kyakyawan kulawan da ya dace....

Hannunta na dan rawa ta shiga bin du wani yaken da ake iya adana abin cutarwa a jikin Ni.ima har ta gama, ita kanta Ni.imar ta cika da mamakinta ta zura mata ido ne tana kallonta,

Haka ta gama ta kuma bi dakin da bincikenta sannan ta juya kanta a kasa ta lalubu hanyar fita tana mai jin zuciyarta na gudun da bata taba yi ba,....namiji?

Duk abinda take yana tsaye ne a wajen da ta barshi yana kallonta,
Shi gaba daya ta zame masa wani abin nishadi, ikon Allah..wai ita nan caje matar da zai yi mu.amala da ita ta yi kennan? Kar ta kashe shi,

Kafadunsa ya daga, kafin ya juyo da dubansa wajen Ni.ima,
Yannayin da ya ga ta nuna ya jara bashi nishadi,
Gadin ya tunkara kai tsaye, wanda hakan da ta gani ya sakata kara gyara zama tana kara sada kanta kasa tamkar ta zo gaban sarki,
Tsayuwa ya yi yana mai bin ko.ina na jikinta da kallo,
Zama ya yi bakin bed din, wanda ya bashi damar dora gaba daya kafafuwansa saman bed din aman kuma ya tankwashe su yana kallonta ya ce" aman ai kin san zaki yi wani abu dan birge ni ba wai kawai ki zauna min da wadinnan manyan kayan tamkar kin zo gaban liman ba ko?

Gabanta ya yanke ya fadi, abinda zata birge shi? Shi ne abinda ta ayanna a ranta, to aman amarya ai daraja gareta ko bazawara ana shigo mata da fuskar kamala ana ririta ta, duk kuwa da ta san romonta za.a sha ...aman ana mai nuna mata da tafiar ba ta hakan bace,
Sai gata, ita Ni.ima, ya Dadynta da momynta, ya daya kwal a wajensu, mai kananun shekaru domin bata fi ashirin da biyar ba , ta tare gaban namiji ingarma da zuciyarta ta rayu da soyayarsa, darensu na farko, tana hasashen tarairaya ko dan ramin da yake yiwa....sai gata ita zata tarairaye shi?,


Kokarin mikewar da ta fahimci yana yi ya sakata saka hannunta na fama dake rawa ta rike hannunsa na hagu,
Ba zata yi gangancin nan ba, ba zata yarda tana kallo ya fice a wajen nan ba, ba zata manta waye shi ba, dan haka mace ce ita ba zata yi wasa da damarta ba....


Hafsat na fita bata tsaya wajen bodyguards din Ni.ima ba kamar yanda ya dace har ya fito daga dakin..takim takim takim ta nufi tsakar gidan,

Tana fita bata lura da BS dake tsaye yana gadin wajen ba ta yi gagawar dukewa wajen tana mai dafe wajen zuciyarta dan ta tsayar da bugawar da take mata,

Riko damatsunan hannayenta da ya yi ya sakata firgita ta mike da sauri da kuma karfi da nihar kaiwa bugo,

Tarewar da ya yi sannan ya bude bakinsa ya ce " hei Bab, menene haka ? Lafia?

Tsai ta yi da yannayinta ta tsurawa fuskarsa ido,
A *KUTKALE* an sha kokarin haye mata,
Sai dai bata taba gannin ainahin abin, tudunsa ko yannayinsa ba, domin za.a shigo mata tsakiyar dare ne su sha dambe da mai tsautsayin,
Aman yau, dan tudunsa ne ta gani ba wani abu ba, ta tsorata,
Dan me maza fitsararu ne?
Ba sai ya nunawa duniya shi din dan duniya bane za.a yarda, ya bar abinsa a shi kadai mana, ki Allah ya yi hani ga bawa tonon asiri idan ya rufa maka,

Da sauri ta janye kafadunta da ya rike yana son ta dawo hayacinta,
Sai da ta janye ya tuna cewar a duniya ta tsani lamari irinnan a taba mata kafadarta,
Koda wasa bata son hakan,
A hankali ya dan ja baya ya bata spac, hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya ta tsurawa waje daya ido tana mai sauraron yanda BS ke faman kwontar mata da hankali duda bai san abinda ya firgitata ba,
Sun dauki lokacin mai tsayi, domin har duhu ya shigo sosai,
Ita kam tana cikin halin rashin sallah hakan ya saka bata nemi zuwa sallar magariba ba, BS kuwa bai je ya yin bane,
Suna hira tana dan kai dubanta wajen windows din dakin, zuciyarta na cike da tambayoyin da ta san ba zata taba samun amsar su ba..........

Kanta ta kuma dagawa ta kai dubanta wajen windows din, idannuwanta ne suka sauka a kan irin jar fitilar nan da ake daidaitawa jikin garu, wace ke hade da bindigar seti, ana daidaita wajen windows din dakin Ni.ima,

Da idannuwanta ta yi masa nuni, wanda hakan na cikin aikinsa,
Da wani irin matsiyacin gudu ya juya ya fita waje inda ita kuwa ta juya da mugun gudu ta afka cikin dakin ba tare da damuwar wani abin ba kuma,

Tsaye ta tarar da shi wajen windows daga shi sai gajeran wandon dake cikin jalabiyarsa yana tsaye kikam ya lumshe idannuwansa iska, sansanyar iska, mai cike da ni.ima na hura shi, yana jin kansa sakayau,

Wani irin ihu ta yi tana mai cewa" ka kwonta!

Juyowa ya yi da sauri, da kuma mamakin me ya dawo da yarinyar nan a wannan lokacin da bai nemeta ba? Sai ganninta ya yi a kiftawa da bismillah ta masa wani irin afkowa gaba dayanta a jikinsa wanda hakan ya saka shi zubewa kasa, domin kuwa ba wani shiryawa ya yi ba, ba wani tunanin haka zai faru ya yi ba a ransa,
Suna faduwa kuwa karan harbi mai boyayen kara ya fasa gilas din dakin ya tafi ya huda labulen ya shiga jikin garun domin kuwa bai samu wanda aka daidaita dominsa ba,

Gannin hakan ya saka mai harbin gane cewar an gane zai yi harbin, dan haka da sauri ya tatare ya nemi hanyar tsira.....


BS ba inda bai duba ba, haka abokin aikinsa ya kasa ya tsare a bakin titin yana gannin shige da fitar kowa, ya zubawa ko.ina ido , inda gaba daya sauran masu tsaron gidan aka shiga haya haya ana ta duduba masu shiga da fita, hakama cikin gidan du sun rikice bodyguards din sun fitar da du wani soja daga wajen da ya shafi Abdul da matarsa sai hayaniya ake,

A lokacin da abdul ya gane abinda ya faru,
Ya ganshi yashe kasa, yar yarinyar nan dare dare saman kirjinsa ta saka hannunta ta rufe bakinsa,
Ya rintse idannuwansa yana sauraron yanda zuciyarta ke dokawa,.....
Tabas jaruma ce, sai dai boyayiyar jaruma,

Da sauri ya yinkura ya cireta a jikinsa da niyar mikewa sai dai ta kara damke hannunsa da yannayin tashin hankali ta ce " ka daina yannayin masu kudi ko sangartatu ka gane rayuwarka ke hatsari ka duka, kar ka mike, domin ba.a ga wanda ya yi harbin nan ba!

Yannayin yanda ta yi magana murya a kausashe, da irin yanda ta bashi ordre ya saka shi yin dan tsai yana kallon fuskarta, kafin ya bi hannunta da kallo,

Da sauri ta cika hannun nasa tana mai kara tamke fuskarta , tana kallo ya mika hannu ya dauki jalabiyarsa, ya dan tsurawa Ni.ima ido sannan ya juya ya fice,

Kuka Ni.ima dake dukunkune waje daya ta fashe da shi tana mai bin hanyar da ya fice da kallo,
Shikenan , ta shigo rayuwar hadari, ashe da gaske dai neman ransa da du wani wanda ke tare da shi ake? Yanzu da an same shi, da shikenan har an mayar da ita karamar bazawara?

Da sauri Hafsat ta kawar da kallonta saga kan Ni.imar ta bi bayansa,

Dakinsa ya je, kai tsaye ta ratsa ta shiga inda ya shiga,

Tsayuwa ta ja ta yi dan ta gane wankama shi ya shiga,

Tana nan tsaye ya fito da tawul daure a kugunsa hakan ya saka ta kawar da dubanta daga wajensa,
Ikon Allah ita bata taba gannin bakin namiji mai cikar gashi a fatar jiki irin wannan ba, dama ba sai larabawa, buzaye , fulani, da dai sauransu keda irin wannan izgar gashin?

Hankali kwonce ya cire tawul din, ba tare da damuwar tana dakin ba, ya saka wandonsa na ciki, sannan ya dora wani wandon baki,

Rigarsa ya saka irin mai lafewa a jikin mutun din nan du tana kallon wajen da ba wajensa ba,

Bata tashi juyowa da sauri ba sai da ta ji wani kara yannayi na gyaran bindiga,

Da sauri ta juyo tana mai zaro ido tana kallon irin yanda ya saka kartushi a yar karamar bindiga ya ja ta ya gyarata da kyau sannan ya yi mata kyakyawan ajiya a kugunsa, irin ajiyar da idan ba karantun hakan aka koya maka ba , ba zaka taba iyawa ba,

Bata gama mamaki ba sai da ta ga ya dauko computernsa ya kunna ya ajiye saman table din dake dauke da turaruka shi kuwa ya dora hannunsa na hagu dake jimke saman table din, na daman kuwa ya shiga dadana computern kamar wanda shi ya kirkiri abinsa,

Bakinta da hancinta gaba daya a bude suke tana mai binsa da kallo, har ya gama nuno waje waje a jikin computern dake nuna ciki da wajen gidan, abin mamaki har benen da aka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login